Chapter 7
by @rukyelmuaz
RIKON KAKA
Written by
Rukayyat
(Rukyelmuaz)
Book 1
YOTA
Chapter 7
***
Zanyi anfani da wannan damar inyi godiya zuwa ga bangon sikari me jingina da ke baya lami. Hauwa'u Jibrin Sulaiman (Hauwajay _Writes) Nagode sosai Allah ya saka da alkairi da tsayamin a duk lokacin da nike buƙartar ki nagode sosai da taimakon ki nike rubuta wannan labarin tabbas kin bada muhimmiyar gudun mawa Allah ya ƙaro dubun nasara da ɗaukaka kwanciyar hankali yalwar arziki.
Abuja Nigeria
**************
Mommy ta gyara kwanciyarta ta juya baya tabar Jannat tsaye tana kallon ta.
Wardrobe ta buɗe ta ɗauki key ɗin motar ta fita ta koma parking space ɗin.
Buɗe motar dake gurin tayi ta shiga kamar anyi mata dole Ganin ta shiga motar ne yasa Malam Audi saurin buɗe mata Gate yana ce wa " Adawo lafiya Hajiya.
Yau dai ko arzikin gaisuwa bai samu ba ficewa tayi Fuuuuuuuuuuuuuuuu kamar wacce ke Shirin zuwa gasar tseran mota. Ta fito da motar daga kyakkyawan get ɗin Jabi Lakeside Estate, ta ɗauki babban titin Yar'adua Way domin zuwa ga address ɗin da mommy ta aike ta. Ko da yake tafiyar ba ta wuce ta minti goma ba kacal.
Tana Driving Ruwan sama ya fara sauka da ɗan karfi hakan yasa ta rage gudun motar take driving a hankali a kan kwalta. Gilashin motar, ta ke kallon yaddda ruwan ke rarrafe a jikin gilashin har zuwa lokacin da ta iso daidai ƙofar 4U Supermarket da ke kan titin Adetokunbo Ademola...
Har lokacin ruwan bai ɗauke ba hakan ya sa ta kashe motar ta ɗauki wayarta dake gefen kujera ta ɗan yi adjust na kujerar motar ta gyara zamanta kamar tana kwance wayanta ta kunna ta shiga Snapchat tana ɗaukar videos ɗin kanta.
Ba'a jima ba ruwan ya tsaya ta fito ta shiga supermarket ɗin ta ɗauki basket tana zagayawa a hankali tana riƙe da takardar da mommy ta bata a hankali take ɗaukar duk abinda ke jikin takardar tana sakawa a cikin kwandon har ta gama duk siyayyar da zatayi ta zo tayi payment bata wani jimaba ta fito rike shopping bags a hannunta.
Bayan mota ta buɗe ta zuba kayan siyayyar da tayi sannan tazo ta shiga motar ta bar gurin da sauri.
Direct gida ta wuce ko minti goma ba'ayiba ta Isa bakin gate.
Malam Audi yaji ƙarar tsayawar mota hakan yasa da sauri ya leƙo domin ganin waye da hanzari ya buɗe mata gate ta shiga parking motar tayi a parking space sannan ta dawo bakin gate ɗin ta ce.
"Baba Audi ni munɓata da kai shine kanaji kana gani Yaya na ya ɗauki motar Daddy baka hana shi ba".
Da sauri Malam Audi ya zaro ido ya ce. "Hajiya ni na Isa in hana Alhaji ƙarami fita da mota a gidan nan Jannat ta ce.
"To ai saika zo ka kira ni da gudu in fito.
Wata dariya mai karfi Malam Audi ya saki ya ce.
"Ayimin afuwa zan gyara Hajiya.
Itama dariya ta yi ta ce. "Good morning na fita bamu gaisa ba".
Da sauri ya sake washe haƙora ya ce. "Ahhhhhh ai ba komi Hajiya barka da dawowa"
Da fara'a ta ce. "Lafiya lau Baba Audi bari in shiga ciki ko please akwai kaya a motar ka miƙa su ciki don Allah please bazan hau sama gurin mommy ba don Allah please kaji Baba Audi"
Tayi maganar alamar neman alfarma ta bashi key ɗin motar ta shiga ciki direct bedroom ɗinta ta shiga tasa key ta kwanta.
Malam Audi ya buɗe motar ya ciro shopping bags ɗin ya rufe motar ya shiga cikin gidan.
Shigar shi tayi dai_dai da saukowar mommy daga sama zata shiga kitchen kayan ya aje a falo sannan ya durkusa ya ce.
"Barka da safiya Hajiya"
Mommy ita ma durlusawa tayi ta ce. "Lafiya lau don Allah Baba Audi ka daina durkusawa in zaka gaidani kaji please".
"Ahhhhh ai babu damuwa Hajiya. Ya faɗa Yana miƙewa ya bata key ɗin motar zai fita mommy ta ce. " Ina Jannat ɗin take???? Ahhhhh Hajiya ta ce. Zata shiga ciki ne. Yana faɗin haka ya fita.
Mommy ta ɗauki siyayyar tana dubawa ɗaya bayan ɗaya ko akwai abinda ba'a sayo mata ba ganin komi a muhallin shi yasa ta fara maida kayan a cikin bags ɗin tashi tayi ta shiga kitchen ta ajiye kayan. Sannan ta fito kamar zata ɗakin Jannat sai kuma ta tsaya kamar mai tunani saita fasa ta koma sama da sauri kamar wacce tayi mantuwa.
Tana komawa sama bedroom ɗinta ta shiga ta buɗe wani ƙaramin akwati ta ɗauki key ta fito.
takawa take da sauri ta isa wani ɗaki tasa key ɗin ta buɗe ta kunna hasken ɗakin zama tayi a kan gadon dake cikin room ɗin tana binshi da ido tana ƙare mishi kallo.
Ɗaki ne da akayi ma ado da komi light pink furnitures ɗin dakin ne kawai akayi su white and pink ga taddy an saka a saman bed ɗin da decorations masu ɗaukar hankali.
Hannun ta kai saman wani photo dake ajiye a saman wani dressing mirror kusada bed ɗin ta ɗauka tana murmushi.
Wata mata ce kwance a gadon asibiti ansaka jariri a saman ƙirjinta an kifa shi kamar irin anason yaro ya yi bacci hancinta ansa oxygen idon ta rufe ta ɗaura hannunta duka biyun a bayan baby ɗin dake cijinta.
Hawaye mommy ta fara suna biyowa kumantunta tana kuka mara sauti tana murmushi tana hawaye duk a lokaci ɗaya.
fuskarta ta canja lokaci ɗaya hawaye sunƙi daina zubowa cije lips ɗinta tayi ta girgiza kai alamar takaici ta kalli photon dake hannunta ta ce.
" Kinsan yanzu banida abokiyar shawara, Kinsan yanzu in damuwa ta dameni sai dai in zubar da hawayen takaici ni kaɗai saboda na rasa wanda zan faɗawa damuwa ta ya rarrashe ni.
, "Babu wanda zan kaima matsala ta ya shiga damuwa fiye da yanda zan shiga damuwa.
"Nayi kewarki kin cika sheƙara 14 da rasuwa.
" Yau kuma ɗiyata take cika shekara 15 da haihuwa." Kinga yanda kikeson tsarin ɗakin ta haka na tsara ma ta shi har yanzu ban manta irin tsarin da kike so ba da favorite color ɗinki.
Saita ja numfashi saboda kukan da take yi sai kuma ta ci gaba da magana ta ce.
"Kinga ta zama ƴar budurwa na kusa amsar siriki"
"Amma ta ce ita Daddy take so shine mai saya mata sweet da chocolate.
Sai tayi dariya ta sauke a jiyar zuciya ta ce.
"Kullum kamar ku ƙara bayyana takeyi da ita saidai kinsan meye banbancin ku?????
"Kinaji dani sosai kamar ki goya ni amma ita kishi ta ke dani wanda hakan kesa nike son ta kasance dani saboda baki taɓa nuna kishi a kaina ba tun da kike a rayuwar har ƙarshen numfashin ki kina son in fara samun komi kafin ki samu".
Ta kai ƙarshen maganar tana murmushi tasa haɓar gyalenta ta share wayen fuskar ta tana murmushi.
Kin san me ta ce last time da tazo hutu saboda ita sarkin rigima ce.
"Ta ce ... "Daddy ka dawo gidan kaka mu zauna tare ba saina dinga zuwa gurinka ba kaga kai na wa ne ni kaɗai ko.
Saita shafi photon tana sake kallon fuskar wacce ke jikin photon ta ce.
"Allah ya jikan ki ya kai haske ƙabarinki ya haɗa fuskokin mu a gidan Aljanna ya shirya abinda kika bari. "Nayi kewar ƴar uwa dangi na guɗa ɗaya tilo.
"Binta ke kaɗai ce dangin Maryama a duniya wanda ya rage take kallo take jin daɗi gashi yanzu kin bar Maryama ita kaɗai a duniya. Allah ya jikanki nasan banida iko akan rayuwar ki addu'ar ita kaɗai zanyi miki.
Saita maida photon ta ajiye shi in da ta ɗauke shi.
Miƙewa ta yi taje zata fita saita tsaya ta kashe light ɗin dakin sannan ta fito ta rufe ta koma bedroom ɗinta ta aje key ɗin inda ta ɗauke shi sannan ta fito ɗakin ta kulle.
Kwance jannat take a bed ɗin ta ko kayan jikin ta bata sauyaba wayarta ce tayi ƙara hakan yasa ta yi saurin kai hannu ta ɗauka ganin me kiran nata yasa ta ɗan turo baki gaba kamar tana gaban me kiran na ta har wayar ta yanke aka sake kira, kamar bazata ɗauka ba sai kuma ta ɗauka. Kamar zatayi kuka muryan can ƙasan maƙoshi ta ce. "Hello my...." Sai tayi shiru ta ƙare maganar cikin murya mai rauni.
Daga ɗayan ɓarayin aka ce. "Jannaty nayi miki laifi ne yau kike azaftar dani kike hukunta ni??????
Kamar batason maganar ta ce. "Honey ni babu abinda kayi min.
"To amma mai yasa nayi miki over 10 messed calls baki amsa ba. ya yi tambayar cikin salon son jin amsar ta.
Kamar jira take ta fara kukan shagwaba ta ce. "Honey Yaya Julaibeeb ne ya tafi Batsari ya barni kuma munyi da shi zai tafi dani sannan kuma......".
Sai tayi shiru bata ƙarasa maganar ba.
"Ohhhhhhh fushin da ake da big bro ne ya shafeni to ayi haƙuri da kaina zan kaiki kafin in bar ƙasar insha Allah.
Cikin farin ciki ta ce. " Da gaske yaya Khamal???
"A'a da wasa". Ya bata amsa.
Sai kuma ta rufe ido kamar tana kallon shi alamar kunya.
"Yau ko fira mai daɗi ban samuba daga gurin Jannaty ɗina sai ƙorafi. Ya faɗa da sigar zolaya.
"Kayi haƙuri to ka biyo ni bashi anjima zan biya ka. Jannat ta juyawa saman bed ɗin tayi kwanciyar rufda ciki ta ɗaga ƙafafunta sama tana ƙarkaɗa su.
Basu wani da ɗe suna fira ba sukayi sallama ta koma ta kwanta.
Mommy ta sauko ƙasa ta shiga kitchen domin ta ɗaura girkin da takeson ɗaura saboda dawowar Daddy daga England. Ga kuma girkin sadaka saboda ƴar uwar ta da takeson ayima addu'a. Ita kaɗa ce a kitchen ɗin saboda bata son masu aiki a gidan ta domin ita a cewar ta meye amfanin su tafison komi tayi da kanta. Don ma girma yasa yanzu ta kan bari duk sati. Mai wanki da guga ɗinsu tana zuwa tayi musu wanni tayi guga domin rage aiki. Shima saboda gani take tafison wankin hannu akan na washing machine.
Duk da kasancewar kayan Jannat ne ake wanke wa ita ba wai tara wanki take ba. Kuma ba kowa takeson ya taɓa ma ta kaya ba. Don Julaibeeb ne kawai ke ɗaukar kayan ta ya wanke saboda yasan bata son wani ya wanke ma ta sai da kanta. Shi kuma baya iya jurar ganinta tana aikin wahala yafi son kullum tana zaune a kusa da shi domin shiba mutum bane mai abokai ko yawan shiga cikin jama'a.Iya kar shi zuwa Company ne saboda ragema Daddy aiki.
Kullum ita ce abokiyar firan shi ko yaushe yafison suna fira suna nishaɗi in dai bai je aiki ba.
A hankali take aikin ta cikin kwanciyar hankali ƙamshin girkin ya buɗe ko ina a cikin gidan.
Ba wasu aguguwan masu wahala sosai tayi ba saidai duk wani abu da zai gyara mata girki yasa ƙamshi da daɗin girki tayi amfani dashi a cikin girkinta. Domin indai irin wannan ranar tazo tana ƙokarin ganin ta faranta ran mabuƙata domin farin ciki ya yi yalwa a zukatan su tana ganin hakan a matsayin hanyar da zasuyi addu'a sosai ga wadda tayi dominta.
Ƙarfe 12:30pm ta gama koma da ta tsara zatayi a ranar abinci ne kala biyu tayi.
Jollop Fried Rice And Chicken.
Steak And Onion Dibi
Sai Coconut milk drink da tahaɗa.
Tana gamawa ta shirya komi ta ajiye sannan ta fito kitchen ɗin ta fita zuwa bakin gate gurin Malam Audi domin yazo ya ɗauki kayan abincin da ta haɗa ya tafi ya kai gurin da aka saba kaiwa. Tana zuwa ta iske ya fito daga ɗan ƙaramin daƙin shi dake bakin gate da murmushi ya ƙarasa gurin da take ya ce.
"Hajiya barka da fitowa akwai abinda kike so ne????
Dariya dayi mishi cikin sanyin murya ta ce.
"A'a Malam Audi dama yau za'a fita da abincin sadaka ne a kai shi inda aka saba kaiwa" Ta ƙare maganar kamar tana shirin sake sabon kuka.
"Hajiya kin manta jiya jumu'atu babbar rana ai jiya ne kika manta bakiyi ba".
Malam Audi ya yi maganar don tunatar da Hajiya cewa ba ranar juma'a suke ciki ba.
Murmushi ta sake yi sannan ta ce. Nasani Malam Audi wannan na sadakar da aka saba ne duk shekara.
Malam Audi ya yi rau_rau da ido alamar maganar ta shige shi ya fara magana kamar zaiyi kuka.
"Allah sarki rayuwa kenan Allah yasa a mizani ya jiƙan wanda suka rigamu gidan gaskiya". Ya kai ƙarshen maganar yana matse idanu alamar yana son ya yi kuka.
"Ameen Malam Audi kazo ka ɗauka zan shiga ciki yanzu"
Tana kaiwa karshen maganarta ta juya ta shiga ciki.
Malam Audi ya bita a baya domin amsar saƙon da mommy ta ce.
Kitchen ta wuce ta bashi abincin da zai kai inda ake kaiwa sannan shima ta bashi na shi abinci.
"Malam Audi ka jira in kawo ma key ɗin mota kaje ka kai, "Kaga mun fara kewar Ahmad da yanzu shine zai kai don kar abar gate ɗin babu kowa"
Malam Audi ya yi dariya ya ce. "Ai flowers ɗin gidannan kan su sun fara kewar shi tunda ya na nan ai bazai barsu ba tare da rage musu matattacen ganye ba"
Shikenan bari in kawo ma Key ɗin.
Juyawa tayi ta fita kitchen ɗin Malam Audi ya fara fita da abincin da zai kai gurin mabuƙata.
Dawowar shi tayi dai_dai shigowar Mommy kitchen ɗin ta miƙa mishi key ɗin ya ɗauki sauran kayan ya fita.