TAKAITACCEN SIRRI

Chapter 3-4

by @momislam11

💋💋💋💋💋💋
*TAƘAITACCEN SIRRI*
💋💋💋💋💋💋
Funny 😂 Love💖 and Romantic 💋

          Mom Islam 

Page 3-4

"Ammu zan fita yanzu zan dawo" Hakeem ya faɗa yana yiwa Ammu murmushi, da sauri ta miƙe tsaye kafin tace "Hakeem tun safe babu abinda kasa a cikinsa bakasan yunwa babbar cuta bace?" 
Kallon garin kwakin da Ammu ta zuzzuba musu tayi kafin tace "kasha ko kaɗan kaji?"
Cikin ladabi ya durƙusa ya karɓi kofin kana yakai bakinsa yasha sau uku sannan ya miƙe,
"Saurin me kake yi haka? Ammu ta tambayesa saboda tanason tasan inda zashi, baiso ya gaya mata ba saboda gudun tashin hankali, kasancewar baya iya ɓoye mata komai yace, ”an koro Ahlam daga makaranta shine zanje in Basu haƙuri" 
”oh ni ƴarnan Allah yasa zamuci jarabawa" Ammu ta faɗa zuciyarta babu daɗi ”Amin ya Allah" Hakeem  yace yana yi mata sallama,
Fatan Ubangiji ya dawo dashi lafiya tayi masa kana ta dage ragowar garin ta kai ɗaki saboda ƙudaje, 
Cikin nutsuwa da izza yake tafiya sai ka rantse wani mai hannu da maiko ne, saboda duk wani abu da akeso d'an adam ya kasance dashi Hakeem ya  mallakesu, kamar su wadatar zuci da kawar da kai ga son abin hannun wani, sannan Hakeem cikkakken namiji ne mai cikar zati kuma lafiyayye, son duk wata lafiyayyar mace mai jini a jika, yanayin zubin halittarsa da kuma izzarsa kaɗai ya isa ka fara zargin ko shiɗin wani ne, sai dai kallo ɗaya zakayiwa shigar da yake yi kasan cewa shiɗin ba kowa bane face talaka sosai wanda bashi da sana'a.
har ya iso bakin get ɗin makarantar, kafin ya kai ga shiga sai da yaɗan tsaya yana nazarin abinda zai gaya musu wanda ya saɓa da na kullum, shigarsa keda wuya ya hango Ahlam a zaune kan wata gajeruwar bishiyar mangoro hannunta riƙe da sanda, ilahirin filin makarantar babu kowa sai ita kaɗai, da mamaki ya ƙarasa gurin dukda idan yace yayi mamaki da aka hanata shiga yayi babban kuskure, saboda koda yaushe kalmar dai ɗaya ce bata sauya zani wato ban haƙuri, 
"Ahlam me kike yi anan gurin...?"
Hake ya kira sunanta tare da tambayarta cikin ɗaga murya,
Bata amsa masa ba har sai da ta sakko daga kan bishiyar, tashi ɗaya idanunta suka ciko da hawaye tace, "Yayah malamin mu ne yace ya koreni a makaranta wai daga yau kar in sake zuwa tunda iyayena basu da zuciya, sannan ya ƙara da cewa babu yaron da ya kaini daƙiƙanci"
Sosai maganar da Ahlam ɗin tayi masa ta sosa masa zuciya amma sai yace "amma nace ki basu haƙuri ko?"
"Eh har da yace in wuce daga baya kuma yace wai in fito"
Ahlam ɗin ta faɗa tana matsar ƙwalla,
Hakeem ya kawar da idanunsa daga kallonta kana  ya riƙe hannunta tare da cewa "babu komai akwai Allah, har sunyi nisa sosai sun kusa zuwa bakin titi daga ƙofar get na school ɗin nasu wani mutumi ya ƙwala wa Hakeem kira, jiki a sanyaye ya juyo da kallonsa ga wanda ya kirashi kafin yace "Ahlam ki jirani anan karkije ko ina" 
"Toh yaya"
Ahlam ɗin tace tana neman wani ƙaton dutse ta zauna a kai.
Bayan ya iso gurin mutumin Hakeem ya miƙa masa hannu suka gaisa mutumin yace "dan Allah idan bazaka damu ba inaso muyi wata muhimmiyar magana dakai"
Hakeem yaɗan jinkirta karɓar uzurinsa na son suyi magana, daga ƙarshe dai yace "toh" ganin mutumin yayi cikin makaranta yasa Hakeem binsa kamar raƙumi da akala har suka iso office wanda babu kowa a cikinsa, kallo ɗaya yayiwa ofishin ya kawar da kai domin bawai kallonne damuwarsa ba,  duk da makarantar ta kuɗi ce kuɗin ba irin sosai ɗinnan ba, 
"Ga guri zauna" mutumin ya faɗa yana yiwa Hakeem alamu da kujerar dake gefe, har yanzu dai jikinsa a sanyaye yake, bayan ya zauna ya mayar da kallonsa ga mutumin.
"Nasan zakayi mamakin kiranka da nayi ba komai bane yasa na kiraka ba sai alkairi, ƙanwarka Ahlam" ambatar sunan Ahlam yasa zuciyar Hakeem tsinkewa saboda baya ƙaunar yaji wani mummunan abu ko abinda ya dangaci rashin kyautawa game da ita, 

Sosai yaba wannan mutumin hankalinsa domin yaji me yakeson gaya masa.
"Kayi haƙuri kaji na ambaci ƙanwarka, gaskiya inada niyar taimakonta, duk da cewar a yanzu shekarunta basufi goma sha uku  ba, i know tana aji biyar. mutumin yai maganar cikin hikima da janyo hankalin Hakeem.
"Ina jinka nabar ƙanwata a hanya Please tunanina gabaki ɗaya ya koma gareta, idan kuma maganar tanada tsayi dan Allah kayi haƙuri ko zuwa gobe insha Allah zan dawo sai muci gaba“.
"A'a malam, a taƙaice dai inason in ɗauki ɗawainiyar karatunta tun daga primary har zuwa Sakandire har gaba da nan, amma..."

Domin neman ƙarin bayani 
***