SARƘAƘIYA

04

by @umaimahadogaya905

Chapter 4 page 7

Mrs. Khaujud ta gyada kai a hankali, yayin da wani ɗan murmushi mai cike da ƙunci ya bayyana a saman fuskarta.

"Ina fatan Ubangiji Ya bani damar ganin Fakiha ko da sau ɗaya ne kacal a rayuwata kafin Ya ɗauki numfashina daga gangar jikina. Allah Ya haɗa ni da ita cikin aminci. Allah Ya sa tana cikin hannu da kafadar mutanen kirki masu tausayi da jin ƙai."

Muryarta ta ɗan karkace a ƙarshen maganar, alamar irin raɗaɗin da ta daɗe tana ɗauke da shi a zuciyarta.

"Amin ya Allah." Mr. President ya amsa cikin sanyin murya. Sannan ya matsa kusa da ita kaɗan yana kallon fuskarta.

"In sha Allah, Allah zai amsa addu'arki. Ban san dalili ba, amma zuciyata tana bani tabbacin cewa ranar haɗuwarku tana tafe."

Ya ɗan yi shiru kafin ya sake cewa cikin salon zolaya: "Yanzu kuma ki share waɗannan hawayen naki ki sakar mini murmushin nan mai kyau.Ni sai nake ganin  a yanzu ma ya fi kyau fiye da lokacin da kike yarinya."

Dariya ta subuce wa Mrs. Khaujud duk da yanayin da take ciki.Ta girgiza kai tana kallonsa.
  "Kai ko? Allah Ya yafe maka. Ko da yake, na san kana tsokanata ne kawai. Amma gaskiyar magana ka yi amarya ne ka daina ganin kyawun tsohuwar matarka."

Mr. President ya zaro idanu kamar wani saurayi ɗan shekara ashirin. "Innalillahi wa inna ilaihir raji'un! Masoyiya Khaujud, ki gaggauta tofar da yawu. Wacece tsohuwa?"

Ya ɗora hannunsa a ƙirji tamkar wanda aka yi wa babban laifi.

"Wa ya ce miki kin tsufa? Kuma wa ya gaya miki akwai wata mace da ta kai ki kyau a idona?"

Ya ɗan yi murmushi. "Har yau bana ganin tsufa a tattare da ke. Abin da nake gani kawai shi ne ƙarin kamala, nutsuwa da wani irin kyau da shekaru suke ƙara wa mace ta gari."

Idanunsa suka sauya zuwa na tunani.

"Musamman idan na tuna irin gwagwarmayar rayuwa da muka sha tare. Wallahi Khaujud, ba zan taɓa mantawa da komai ba. Amma yanzu komai ya wuce kamar komai bai faru ba.Rayuwa kenan, tabbas duk nisan jifa kasa zai dawo. Yanzu dai ki ga waye zai ce mu ne wadannan mutanen na baya?"

Mrs. Khaujud ta jinjina kai cikin taɓuwa.

"Hakika duk tsanani sauki yana tafe a bayansa.. Yanzu ne nake ƙara fahimtar karin maganar hausawa da suke cewa duk nisan dare gari zai waye. Tabbas  Allah Ya nuna mana kwanaki masu wuya, amma yanzu gashi nan komai ya shude,halin da muka shiga a baya ya koma tamkar bai faru ba,tamkar dai a mafarki komai ya faru.

Ta ɗaga idanunta sama.

"Muna roƙon Allah Ya sake dubanmu da rahama, Ya ceci ƙasarmu daga halin da take ciki."

Shiru ya ɗan ratsa tsakaninsu na wasu daƙiƙu.

Sai Mr. President ya sauke numfashi sanna. ya fara  fadin  "Duk da cewa lokacin cin abinci ne, akwai abin da nake son sanar da ke."

   Mrs. Khaujud ta maida hankalinta gaba ɗaya kansa.

Ya ɗan gyara zamansa kafin ya ci gaba.

"Khaujud, gaskiyar magana ita ce, mafi yawan matsalolin da ƙasarmu ke ciki ba daga talakawa suke fitowa ba."

Ya girgiza kai cikin takaici.

"Mu manya ne muke haddasa yawancinsu."

Fuskarsa ta ƙara nuna damuwa.

"Yawancin ayyukan ta'addanci, cin hanci, da sauran abubuwan da suka addabi Najeriya suna da alaƙa da wasu daga cikin masu dafe da madafan iko."

Mrs. Khaujud ta zuba masa ido tana sauraron shi.

"Shi ya sa na yanke shawarar cewa ba zan zauna ina kallo ba. Zan yi iya bakin ƙoƙarina wajen ganin na taimaka wajen ceto ƙasata."

Ya ɗan yi shiru.

"Mutane suna ganin har yanzu ban fara manyan ayyuka ba. Amma ba su san cewa ina tattara bayanai ne ba. Ina nazarin waɗanda suka jefa ƙasar nan cikin wannan hali."

Wani ɗan murmushi mai ma'ana ya bayyana a fuskarsa.

"Akwai wani babban shiri da nake gudanarwa a ɓoye. Amma lokaci bai yi da zan bayyana komai ba."

Mrs. Khaujud ta dafa hannunsa cikin ƙauna. "Zan yi alfahari da kai ko da yaushe."

Ta yi magana cikin kwarin gwiwa.

"Allah Ya ba ka ikon kawo canjin da kake fata. Allah Ya yi riƙo da hannunka, Ya kare ka daga makiyan da ba ka sani ba da waɗanda ka sani."

"Amin ya Allah." Ya amsa yana murmushi.

"Sai dai kafin na ceci ƙasa, akwai wani abu mafi muhimmanci da zan fara yi yanzu."

Mrs. Khaujud ta ɗaga gira. "Mene ne?"

Ya miƙe tsaye yana dariya. "Na ceci cikina daga yunwa!"

Dariya suka yi tare.Ya miƙa mata hannu.
"Mu je mu ci abinci kafin su Haijat su fara tunanin mun manta da su.". asMrs. Khaujud ta sanya hannunta cikin nasa, sannan suka fice daga falon cikin annashuwa.

Chapter 4 page 8

***KANO***
     Tun daga ranar da Fujeerat ta gano ainihin wace ce ita, abubuwa da dama suka sauya a rayuwarta.

A karon farko cikin shekarar nan, ta samu wani irin natsuwa da kwanciyar hankali da ta daɗe tana nema amma ba ta samu ba tun bayan rasuwar Abbanta.

  Duk da cewa har yanzu tana ɗauke da tarin tambayoyi marasa amsa a zuciyarta, amma ta daina jin irin ɗacin da take ji a baya.

 Mafi girman canjin da ya faru kuwa shi ne yadda soyayyarta ga Ummi ta sake girma a zuciyarta.

A da tana sonta ne saboda ta haife ta kuma raineta.

Yanzu kuwa tana sonta ne saboda ta fahimci girman sadaukarwar da matar ta yi saboda ita.
Shin Wace irin mace ce za ta ɗauki jaririn da ba nata ba, ta raine shi cikin ƙauna, ta hana shi jin ƙarancin gata har tsawon shekaru?Duk lokacin da Fujeerat ta tuna da hakan, sai ta ji idanunta sun cika da hawaye.

A hankali kuma ta fara kawar da duk wani tunanin soyayya ko aure daga ranta.Ta yi imanin cewa rayuwarta ta riga ta ɗauki wata hanya ta daban.

A ganinta, tabon da rayuwa ta bar mata zai yi wuya ta samu mutumin da zai karɓe ta gaba ɗaya.Saboda haka ta tattara duk wani lissafin soyayya ta ajiye shi gefe.

A yanzu burinta guda ɗaya ne,ta yi rayuwa cikin mutunci.Ta kula da waɗanda suke sonta.Ta kuma yi aiki domin ta tsaya da ƙafafunta.Saboda haka ta maida hankalinta gaba ɗaya kan aikinta.

   Kasancewar bayan kammala makarantar sakandare ta yi karatun catering na tsawon watanni shida inda ta samu Diploma, aikin kitchen ya zama abin da ta fi iya yi hakan ya sanya ta nemi aiki a wani kamfani,in da take aiki a bangaren kitchen a matsayin chief.

   Yanzu haka tana tafiya cikin harabar kamfanin zuwa sashensu na masu shirya abinci.

Ta isa wurin lockers ɗin ma'aikata, ta ajiye jakarta da sauran kayanta kafin ta yi signing kamar yadda dokar aikin ta tanada.Daga nan ta nufi kitchen.

Tun kafin ta shiga sosai, wata murya mai cike da annashuwa ta doki kunnuwanta.
"Fujeerat!" Muryar Maryam ce.  

Da sauri ta ƙaraso gare ta fuskarta cike da fara'a.
"Wallahi har na fara damuwa. Na yi tunanin yau ba za ki zo ba." Fujeerat ta ɗan yi murmushi kawai tana daukar rigar aiki.

Maryam ta tura baki. "Haba mana! Ina magana kina kallona kamar ba ki gane  ni ba?"

Ta ɗan matso kusa da ita. "Lafiya dai ko? Kwana biyu ina lura da ke kina ƙara shiga duniyar tunani da wannan dan banzan miskilancin naki"

Fujeerat ta girgiza kai. "Ba komai."

Sai dai Maryam ta san wannan amsar sosai.Duk lokacin da Fujeerat ta ce "ba komai", to akwai wani abu da take ɓoyewa.

"Kina da zurfin ciki da yawa wallahi." Maryam ta faɗa tana dariya.

Fujeerat kuwa ta ɗauki apron ɗinta tana cewa,
"Ki bani hanya. Ina da aikin yi."

Maryam ta zaro idanu."Wato ni ba ni da aikin yi kenan?" Kitchen din gabadaya ya kaure da dariya. A kullum haka tsakanin Fujeerat da Maryam yake. Ita Maryam magana,yayin da Fujeerat ba ta son magana. Sannan a dole Maryam tace sai tayi magana. 

Fujeerat ta gaida Mama Sa'a wadda take shugabar sashen Kitchen da sauran ma'aikantan da suke cikin kitchen din a lokaci guda kuma tana sanya apron din hannunta. 

"Maryam!" Mama Sa'a ta kira ta. Ta juya tana kallonta tare da amsa wa. 

Mama Sa'a ta dora da fadin "Ke kam kin ji dadin Rayuwarki. Mai yasa ne ke ba kya gajiya da neman magana ne? Wai ni kam bakinki ba ya ciwo saboda surutu kuwa?" Kitchen ɗin gaba ɗaya ya ɗan kaure da dariya.

Maryam kuwa ta sosa kai tana turo baki gaba. "Allah Mama wata rana sai kun yi kewar surutun nan nawa. Ku yi ta cewa dama Maryam za ta zo ta dame mu da surutun nan nata. 

A gefe kuwa, Saliha ta ɗaga gira. "Ni kam ma bana ganin surutun ki Maryam. Kawai dai ta gaban goshin maman ce take ji da kanta kamar wata diyar sarki." Ta yi maganar tana kallon Fujeerat.

Sarai Fujeerat ta ji maganar amma kamar yadda ta saba, ba ta bi ta kanta ba.

   Ta buɗe fridge ta fara fiddo naman da za su yi amfani da shi. Yayin da Maryam ta yi saurin kare kawarta.
   "Aunty Saliha, ai haka halinta yake tun ranar farko da ta zo."

"To Allah Ya shirye ta."Saliha ta amsa.

"Ni dai kam a ganina idan mutum yana da kirki, ba zai yi ta kallon mutane sama-sama ba."

Maryam ta fashe da dariya. "Harare garki ce ashe.Yo in ba harara garki ba wane yake kallon sama-sama Auntie Saliha? 

Saliha ta nuna ta da yatsa. "Ke ma dai ba ki da kirki Maryam. Yanzu na shiga face-face cikin fadanki amma ki dibi kasa ki tula mini a ido?"

Nan take kitchen ɗin ya sake cika da dariya.

Sai Mama Sa'a ta dakatar da su. "Ku bar hayaniyar nan don Allah. Kowa ya mayar da hankalinsa kan aikin da yake yi zi yi wannan maganganun."

Kowa ya koma kan aikinsa.

Bayan wasu mintuna, Mama Sa'a ta sake cewa,
"Kuma ku yi sauri. Yau muna da babban baƙo."

Saliha ta ɗaga kai. "Waye kuma?"

"Yallabai mai kamfanin nan."

Da jin haka, fuskar Saliha ta sauya.Kai tsaye ta ajiye cokalin da ke hannunta.

"Subhanallah!" Ta dafe ƙirji. Ta dora da fadin "Wai Yallabai  Mubarak ne zai zo?"

Maryam ta tintsire da dariya.

"Aunty Saliha, kamar dai kina da wata matsala da mutumin nan."

"Matsala kuma? Ba dai matsala ba Maryam,amma ba zaki gane komai ba,ki bari ya zo za ki fuskanci abin da nake nufi."


  Fujeerat kuwa Ko kallonsu ba ta yi ba.Ta ci gaba da aikinta cikin nutsuwa.Amma ba tare da ta sani ba.Sunan da ta ji an ambata ya bar wani irin motsi marar suna a cikin zuciyarta.Kamar wani abu ne da yake shirin faruwa.Kuma zuciyarta ta fara jin sa tun kafin idanunta su ganshi.

Bayan sun kammala shirya abincin ranar, aka miƙa wa masu rabawa domin kaiwa sassa daban-daban na kamfanin.

Su kuwa ma'aikatan kitchen suka samu damar hutawa kaɗan tare da cin nasu abincin.

Bayan ta gama cin abinci, Fujeerat ta miƙe tana goge hannayenta da ƙaramin towel.

Ta dubi Maryam.

"Maryam, don Allah zo ki raka ni locker. Zan ɗauko wayata, ina son kiran Nadiya."

Maryam da ke kurɓar ruwa ta ɗaga gira.
"Ni kuma me ya sa sai na raka ki?"

Fujeerat ta ɗan yi murmushi.
"Saboda kina da ƙafafu biyu kamar ni."

Maryam ta turo baki gaba.
" Bari na fito miki a mutum. Wallahi kishi nake yi da wannan Nadiyar."

Fujeerat ta yi dariya.
"Kishi kuma?"

"Eh mana! Duk magana Nadiya. Duk labari Nadiya. Duk damuwa Nadiya."

Ta nuna kanta.
"Ni da nake binki kamar jela fa? Sam ba kya ta ni."

Fujeerat ta girgiza kai cikin raha.Sai ta ɗan matso kusa da ita.
"Haba Maryam."Kema kin san kina da matsayi na musamman."

"To me ya sa ba kya nuna mini hakan?"
Maryam ta faɗa tana sake turo baki.

Fujeerat ta yi murmushi.
"Saboda idan na fara, za ki raina ni."

Kitchen ɗin ya sake cika da dariya.

Maryam ta nuna ta da yatsa.
"Wallahi wata rana zan rama."

Fujeerat ta ɗaga gira. "Ke din?Ni kam ban ga ranar ba."

Daga ƙarshe da ta ga Maryam ba za ta raka ta ba, sai ta juya ita kaɗai ta fita.

Tafiya take a hankali cikin corridor mai faɗi.A karo na ba adadi ba, ta sake jin kanta baƙuwa a wannan katafaren kamfani.Har yanzu ba ta saba da girman wurin ba.Har yanzu tana jin kamar idanun kowa suna kanta duk lokacin da take wucewa.Ko saboda tana cikin shakku ne?Ko kuma saboda rayuwar da ta taso cikinta ce ta koya mata zama cikin taka-tsantsan?Ba ta sani ba.

Sai dai a yau tunaninta yana wani wuri daban.Tun lokacin da ta gano gaskiyar rayuwarta, zuciyarta ta kasa samun cikakkiyar amsa.

Wace ce mahaifiyarta?

Me ya sa ta rabu da ita?

Me ya sa ta bar ta tun tana jaririya?

Shin da son ranta ne?

Ko kuwa akwai wani abu da ya fi ƙarfinta?

Numfashinta ya ɗan yi nauyi.

Wani sashe na zuciyarta ya rada mata mummunar tambaya.

Tambayar da take tsoron yi wa kanta.

"Ko kuwa an same ni ne ta hanyar da ba ta dace ba?"

Nan take idanunta suka cika da hawaye.

Ta yi saurin girgiza kai.

"A'a..."

Ta furta a hankali.

"Ba zan yi wa kaina wannan hukuncin ba."

Amma duk da haka tambayar ta ci gaba da yawo cikin ranta.

Saboda tsabar shiga tunani, ba ta lura da wanda ke tahowa gabanta ba.

Sai kawai Bam! Ta yi karo da wani.A gigice ta ja baya.
"Subhanallah! Ka...." Ta faɗa cikin sauri Sai dai kafin ta ƙarasa maganar Idanunta suka haɗu da nasa.Lokaci guda komai ya tsaya mata.Kamar sararin duniya ya yi shiru.

Mutumin da ke gabanta ya kasance irin mutanen da Allah ke halitta da wata baiwa ta musamman.
Dogon saurayi ne mai cikar kamala.Fatar jikinsa fara ce mai haske.Idanunsa masu zurfi suna da wani irin nauyi da ke sa mutum ya kasa kau da kai daga kallonsu.Hancinsa dogo ne kuma a tsare.
Fuskarsa kuwa cike take da kwarjini da annuri.
Suit mai launin navy blue ne a jikinsa.Farar riga da baƙar necktie sun ƙara fito da kamalarsa.Agogon da ke hannunsa kaɗai ya isa ya nuna cewa mutumin ba ƙaramin matsayi yake da shi ba.

Amma duk wannan bai kai abin da ya fi ɗaukar hankalin Fujeerat ba.Kallonta yake yi.Kallo mai cike da mamaki.Kallo kamar wanda ya ga abin da bai taɓa tsammanin gani ba.Kamar wanda ya ga wata fuska daga wani tsohon tarihin rayuwarsa.

Fujeerat ta ji gabanta ya faɗi.Da sauri ta sauke idanunta ƙasa.

"Am sorry... ban gan ka ba ne."

Shiru na wasu dakiku bai ce komai ba.Sai kuma ta ji muryarsa.Muryar da ta kasance mai nauyi amma cike da nutsuwa.

"Mene ne sunanki?"

Ta ɗan ɗaga kai cikin mamaki.Ba tayi zaton abin da zai fara fita daga bakinsa kenan ba.

Sai dai ta amsa. "Hafsat Muhammad."

Ta ɗan yi shiru kafin ta kara da fadin 
"Sai dai ana kirana Fujeerat."

Ya maimaita sunan cikin sanyin murya.
"Fujeerat..."

Kamar wanda yake gwada yadda sunan yake a harshensa.Sannan ya ɗan jinjina kai.

"Kina aiki a nan ne?" Ya sake jefo mata wata tambayar.

"Eh." Ta amsa a gajarce

"A wane sashe?" Ba tare da jinkiri ba yayi saurin sake jefo mata wata tambayar.

"Kitchen." Ta sake amsa masa a takaice.

Ya sake kallonta na wasu daƙiƙu.Da alama akwai abubuwa da yawa da yake son tambaya,Amma ya haɗiye su.A ƙarshe ya ɗan yi murmushi.Murmushin da ya ƙara rikita Fujeerat fiye da yadda take a da.

"Nice to meet you, Fujeerat."Ya faɗa a hankali.

Daga nan ya wuce.cikin takunsa na zaratan maza c
Mai cike da ƙarfi, nutsuwa da kwarjini.Fujeerat ta tsaya tana kallon bayansa har sai da ya ɓace daga ganinta.Sai kuma lokacin ta tuna da numfashin da take riƙe da shi.Ta sauke ajiyar zuciya tare da dafa ƙirjinta.

"Wai me ke damuna ne?" Ta tambayi kanta.Amma ba ta samu amsa ba.Abin da kawai ta sani shi ne.,Tun bayan tafiyarsa, zuciyarta ba ta koma yadda take ba.


   A hankali Mubarak ya ci gaba da tafiya cikin corridor ɗin kamfanin.Sai dai duk da tafiyar da yake yi, zuciyarsa ta kasa ci gaba da tafiya tare da shi.
Wani ɓangare na tunaninsa ya tsaya a wurin da ya bar yarinyar kitchen ɗin.

"Fujeerat." Ya maimaita sunan a zuciyarsa.Wani suna ne mai sauƙin furtawa, amma da wani irin nauyi da ya kasa fahimta.

Da ya isa bakin lifta ɗin da zai kai shi saman bene, mai taimaka masa na musamman ya matsa ya buɗe masa ƙofar.

"Sir."

Mubarak ya jinjina kai kawai ya shiga.

Ko da liftar ta fara motsi, har yanzu fuskarta ce ke yawo a gabansa.Ba wai saboda kyawunta ba.A'a.
A matsayinsa na mutum mai hulɗa da jama'a da yawa, ya saba ganin kyawawan mata.

Amma akwai wani abu daban a tattare da ita.Wani abu da ya kasa sanya wa suna.Ya lumshe idanunsa na ɗan lokaci.Ina ne ya taɓa ganin irin waɗannan idanun?Ina ne ya taɓa ganin irin wannan fuskar?Tambayar ta sake dawowa masa.Sai dai duk yadda ya matsa tunaninsa, ya kasa tuna komai.Kawai yana jin kamar akwai wata tsohuwar ƙwaƙwalwa da ke ƙoƙarin buɗewa amma ta kasa.

   Da ya isa ofishinsa, ya cire suit jacket ɗinsa ya rataya.Sannan ya nufi kujerarsa ya zauna.Amma maimakon ya fara duba takardun da aka ajiye masa, sai ya zura ido ta tagar ofishin.

"Fujeerat...". Ya sake furta sunan a hankali.

Sai kuma ya yi murmushi shi kaɗai.
"Wataƙila a gurin wani aikin na taba ganin mai irin fuskar." Ya fada a hankali kamar mai yin maganar da wani.  Ya girgiza kai. "Amma sai nake ganin kamar fuskar was so familiar, ba kamar wanda aka taba haduwa da shi a wani lokaci guda daya ba."

Ya ƙarashe maganar yana buɗe laptop ɗinsa.A daidai lokacin  ne kuma  wayarsa ta yi ƙara.Hankalinsa ya kau daga tunanin Fujeerat.Aikin ranar ya fara jan hankalinsa.Sai dai ko kaɗan bai san cewa wannan yarinyar da ya haɗu da ita a corridor ba...Za ta zama ɗaya daga cikin mutanen da za su sauya alkiblar rayuwarsa a nan gaba.Za ta zama silar budewar wani dadaddan boyayyen sirrin da ba wanda ya taba hasaso shi.......

  Za ku jini shiru kwana biyu,Wayata ce ta ci screen. Amma zan yi kokarin cigaba da kawo muku ta wata wayar daban kafin na sayi sabuwar waya ko Laptop. Masu groups don Allah ku taimaka da sharing ta yadda Update zai je ga wadanda suke jira. Kuma a dage da ruwan likes da comment hakan ne zai sanya na samu kwarin gwiwar yi muku updates a kai-kai. Za ku ga ba editing wayar ce babu Hausa Keyboard amma zan yi kokari na sauke shi. Na gode. 


Umaimah Ado Gaya Ummu Ahmad 🥰.