KADDARAR MASOYA

Chapter 3

by @maryammuhammad230

ƘADDARAR MASOYA*

Written by Maryam Muhammad (shalele)

Join my Facebook group 👇

***

Join my WhatsApp group👇
 ***

Join my WhatsApp channel👇 

***

****
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
*(J.W.A)*
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️



I DEDICATE THIS BOOK 
“To every woman who has fought battles in silence, survived what she never thought she could, and still found the courage to keep going—this story is for you. ❤️”

DISCLAIMER 
Wannan littafi kirkirarre ne, ba wai an rubuta shi ne bisa rayuwar wani mutum kai tsaye ba. Sunaye, wurare, da abubuwan da suka faru an tsara su ne domin labarin.

Idan har wani mai karatu ya ga wani ɓangare na labarin ya yi kama da irin rayuwarsa ko abubuwan da ya taɓa fuskanta, hakan ba wai yana nufin an rubuta labarin ne a kansa ba. Don haka, idan ka ga makamancin rayuwarka a cikin wannan littafi, ka yafe min kuma ka karɓe shi a matsayin labarin kirkira. ❤️📖

Bismillahir Rahmanir Raheem 


PAGE 3

Ummi ta koma dakinta, ta rufe kofar a hankali.

Dakin ba shi da girma. Wata tsohuwar katifa ce shimfide a gefe guda, yayin da wasu littattafan makaranta suka jere a kan karamin teburi da ya yi shekaru yana amfani da shi

Ta dauki jakar makaranta, ta fara saka littattafanta daya bayan daya.

Mathematics

English

Biology

Sai ta tsaya tana kallon littafin Islamiyya da ke gefen teburin.

Ta dauke shi ma ta saka a cikin jaka.

A yau tana da makaranta da safe, sannan daga baya ta je Islamiyya.

Ta kalli agogon bango.

Ya Allah! Zan makara.

Da sauri ta ɗauki takalminta ta zauna a bakin katifa.

A lokacin da take ƙoƙarin saka takalmin, sai aka ji karar kofa

Aunty Ummi!

Nana Khadija ce

Ummi ta daga kai tana murmushi.

Me ya faru, Nana?

Ƙaramar yarinyar ta shigo da gudu.

Aunty, Mama ta ce ki zo ki ci abinci.

Kin ci naki?

Nana ta girgiza kai.

Har yanzu.

Ummi ta yi murmushi.

Ke dai kina jiran nawa ne ki ci tare da ni.

Nana ta yi dariya.

Eh.

Ummi ta mike, ta kama hannunta.

Zo mu je.

Suna fita daga dakin, sai suka haɗu da Abdullahi a tsakar gida. Yana zaune a kan wata tsohuwar kujera yana gyara takalminsa.

Ya dago kai.

Ummi, kin shirya?

Eh.

Ki yi sauri. Yau ma za ki makara.

Ummi ta kalle shi.

Abdullahi, kai ma ka san ba ni ce nake son makara ba.

Abdullahi ya yi murmushi.

Toh ki daina yawan gyara hijabinki a gaban madubi.

Nana ta fashe da dariya.

Abdullahi ya kama Aunty!

Ummi ta kalle su duka.

Ku biyu kun haɗa kai kenan?

Daga gefe kuma sai Sadiq ya fito yana dauke da karamin littafinsa.

Me ya faru?

Abdullahi ya ce:

Babu komai. Aunty Ummi ce kawai ta makara.

Sadiq ya kalli Ummi, sannan ya yi murmushi.

Allah ya taimake ki.

Ummi ta girgiza kai tana dariya.

Ku bar ni kawai.

A cikin gidan, irin wannan kananan hirarraki ne suke sa ranakun su kasance da dan dadi duk da irin karancin abin da suke da shi.

Mama ta fito daga ɗakin.

Ummi, ga abincinki.

Na gode, Mama.

Ta zauna ta ci kadan, sannan ta dauki jakarta.

Mama ta kalle ta.

Allah ya kiyaye hanya.

Amin

Ki kula da kanki.

Insha Allah.

Ummi ta fita daga gidan tare da sauran yaran.

Da ta taka karamar hanyar da ke gaban gidansu, sai ta ɗan tsaya.

Ta kalli gidan na yan dakiku.

Ba shi da girma.

Ba shi da kyau kamar gidajen da take gani a wasu unguwanni.

Amma a gare ta, wannan gidan yana dauke da duk abubuwan da suka fi muhimmanci a rayuwarta.

Mama.

Ƙannenta.

Tarihin rayuwarta.

Da kuma mafarkan da take son cika su.

Ta gyara jakarta a kafada, sannan ta ci gaba da tafiya.

A zuciyarta tana maimaita wata magana da ta saba faɗa wa kanta:

“Rashin abin duniya ba zai hana ni cimma burina ba.”