BIN ALI

Chapter-05 (A Secret She Can’t Reveal)🤐🥀

by @eshamuhd

A cikin ƙasaitaccen ofishinsa na gida, wanda aka kewaye shi da kyamarori da na’urorin tsaro na zamani, Bin Ali yana tsaye a gaban wani katon gilashi da ke kallon lambun cikin gidan. Sanye yake da farar riga mai V-neck, hannayensa biyu a cikin aljihun wandonsa, yayin da ya juya wa kofar shogowa baya.

A bayansa kuwa, Taufeeq yana tsaye, yana miƙa masa takardun yarjejeniyar da Afeefa ta sanya wa hannu.

“Duk gwaje-gwajen asibitin sun kammala. Afeefa tana cikin ƙoshin lafiya,” Taufeeq ya faɗa, yana ajiye file ɗin a kan teburin dake gaban shi. “Abin da ya rage yanzu shi ne ka sanya hannu a naka ɓangaren, sannan zaku hadu kai da ita yau da dare, kamar yadda muka tsara.”

“A’a.”

Kalmar guda ɗaya ce kawai Bin Ali ya furta, amma ta fito da ƙarfi, har sai da Taufeeq ya ya dago kai ya kalle shi. Muryar Bin Ali ta katse maganar Taufeeq dake shirin bude baki yayi magana. Muryarsa ta fito cikin sanyi, amma tana ɗauke da wani irin nauyi.

Har yanzu bai juyo ba, don haka Taufeeq bai iya ganin irin yanayin fuskar da yake ɗauke a kan fuskar ta shi ba.

Taufeeq ya ɗan gyara glasses din sa, yana kallon Bin Ali cikin mamaki. “Bin Ali, yarjejeniyar fa ta tanadi cewa dole ku sanya hannu a gaban juna domin tabbatar da amincewar kowane ɓangare da kansa…”

"Ba na buƙatar ganinta, Taufeeq,” Bin Ali ya katse shi. Muryarsa ta ƙara yin ƙasa, amma mai cike da amsa amo.

“Aikin likitoci ne su kula da batun dashen ciki. Ni kuma aikina ne kawai in biya kuɗin da aka buƙata. Ba na buƙatar ganin fuskarta, kuma ita ma ba ta buƙatar ganin tawa. A tura wa Dr. Farooq takardun, ya sanya sa hannuna ta hanyar digital signature. A gama komai a asibiti.”

Taufeeq ya yi shiru, yana duban bayan abokinsa. Ya san halin Bin Ali sosai—da zarar ya yanke shawara a kan wani abu, ba ya saukowa daga matsayinsa. Tsananin ra’ayinsa da kuma yadda yake kare sirrin rayuwarsa ba su ba kowa damar tilasta masa yin abin da bai so.

“Shi ke nan,” ya ce a hankali. “Zamu tsara komai da Dr. Farooq.”


A gefe guda kuma…

Afeefa tana tafiya a hankali a kan titin da zai sada ta da layinsu, kafafun ta suna mata nauyi tamkar an ɗaure su da sarka. Magariba ta riga ta yi, hasken fitilun titi yana jefa inuwarta a ƙasa. Kanta na sarawa saboda ɗumbin tunanin da ya addabi zuciyarta.

Kuɗin aikin Rahma, har ₦750,000, sun shiga asusun asibitin City Care. Likitoci sun tabbatar mata cewa za a shigar da ƙanwarta ɗakin fiɗa ranar Litinin. A ƙarshe, an samu mafitar rayuwar Rahma…

Amma ta wace hanya?

Ita da kanta ta sanya hannu kan takardar da za ta sauya ƙaddararta har abada. Za ta ɗauki cikin wani mutumin da ba ta taɓa gani ba, wanda ba ta ma sanshi ba sai sunan shi da take ji a gari. Amma akwai wata matsala da ta fi komai ɗaga mata hankali a yanzu:

Umma.

Ta yaya za ta gaya wa mahaifiyarta, wadda ta raine ta cikin mutunci da amana, inda ta samo wannan makudan kuɗin har ₦750,000 cikin ƴan sa’o’i kaɗan?

Shin za ta ce mata aiki ta samu na gaggawa?

Amma wane irin aiki ne zai iya kawo mata irin wannan ɗumbin kuɗin a ranar farko irin haka?

“Idan na ce mata aiki na samu… Umma ba za ta taɓa yarda ba. Zato da zargi za su shiga zuciyarta,” Afeefa ta furta ƙasa-ƙasa, tana haɗe hannayenta biyu saboda tsananin fargaba. “Idan kuma na faɗa mata gaskiya… zuciyarta ba za ta iya daukar abin ba. Za ta gwammace mu rasa Rahma da ta gan ni a cikin irin wannan hali.”

Kowace mota da ta wuce gefenta, ko mutumin da ya gitta ta, ba su dame ta ba. Hankalinta yana can nesa, yana yawo tsakanin farin cikin samun kuɗin da zai ceci rayuwar ƙanwarta da kuma tsoron abin da zai biyo bayan hakan.

A ƙarshe, ta iso ƙofar gidansu ta shiga gida bayan sauke wasu tagwayen akiyar zuciya da tayi na wasu yan seconds.

Hannunta yana rawa ta ɗaga labulen ƙofar dakin su, idanunta suka sauka kan Umma da ke zaune a kan tabarma a tsakar dakin. Carbi ne a hannunta, tana jan zaren carbin tana tasbihin a hankali, damuwa ta bayyana a fuskarta saboda jiran labarin Rahma daga asibiti. Afeefa ta lumshe idanunta.

Ta haɗiye yawu mai ɗaci, zuciyarta na bugawa da ƙarfi. ta san dole ta shiga, amma ba ta san me za ta faɗawa umma ba.

A wannan daren, Afeefa ta gano cewa ceton rayuwar Rahma ba shi ne ƙarshen jarabawarta ba… Shi ne farkon ta.

“Afeefa? Ke ce a tsaye a nan?”

Muryar Umma ta sake ratsawa ta mata tunanin da take yi. Afeefa ta haɗiye wani yawu mai nauyi, sannan ta matsa a hankali ta shigo cikin dakin. Ta sunkuyar da kanta ƙasa, tana ƙoƙarin danne rawar da hannayenta ke yi.

Umma ta miƙe tsaye a hankali, ta gyara hijabin ta, sannan ta ɗaga idanunta zuwa gare ta. Hasken kwan nepar da ke haskaka cikin dakin ya sauka kan fuskar Afeefa, yana ƙara bayyana irin tashin hankalin da ke tattare da ita.

“Tun ɗazun nake jiran dawowarki,” Umma ta faɗa, muryarta cike da damuwa. “Na ga har kusan ƙarfe takwas ba kya nan. Wane labari kika taho da shi daga asibitin? Ko dai an samu wata matsala ne?” Afeefa ta tsaya cak.

Tambayar ta sauka a kan zuciyarta kamar dutse. ta ɗan buɗe baki, amma kalma ta gagare ta fitowa daga bakin nata.

Saboda ta san cewa daga wannan lokacin ne za ta fara faɗin ƙaryar da za ta iya sauya mata rayuwa gaba ɗaya.

Afeefa ta durƙushe a gefen tabarmar dakin Umma take, tana maida numfashi a hankali. Idanunta suka cika da ruwan hawaye amma ta yi sauri ta goge su daga idanun ta kafin mahaifiyarta ta fahimci halin da take ciki.

"Umma... an samu mafita," ta faɗa da rawar murya.

Umma ta riƙe numfashinta na ɗan lokaci, sannan ta matsa kusa da Afeefa cikin sauri.

“Afeefa! Da gaske? Ta yaya? Wane ne ya taimaka mana?”

A wannan lokacin ne ƙirjin Afeefa ya fara bugawa da ƙarfi. Ta ɗan lumshe idanunta, tana ƙoƙarin tattara nutsuwarta. Ta san Umma sosai. Idan ta faɗi ƙaryar da ba ta da tushe, idanunta da muryarta za su iya fallasa ta kafin ta ƙarasa magana.

Afeefa ta ja numfashi a hankali, sannan ta ɗago idanunta zuwa ga mahaifiyarta.

“Umma…” ta fara a hankali, muryarta tana ɗan rawa. “Dr. Farooq ne da kansa.” Ta ɗan yi shiru, tana kallon fuskar Umma domin tabbatar da cewa har yanzu tana sauraron ta.

“Ya shaida min cewa akwai wata gidauniyar agaji da wani mai kuɗi ke ɗaukar nauyinta, wadda take taimaka wa marasa lafiya da ba su da halin biyan kuɗin jinya.” Afeefa ta sake yin shiru na ƴan daƙiƙu.

“Bayan na yi masa bayanin halin da muke ciki da kuma irin matsalar da Rahma ke ciki, sai ya ɗauki bayananmu ya gabatar da su gaban kwamitin gidauniyar…”

Ta haɗiye yawu, tana jin nauyin kalaman da ke fitowa daga bakinta. “Daga nan ne suka amince za su ɗauki nauyin aikin Rahma.”