ƘYAURE KARIYAR GIDA

BOOK ONE CHAPTER FIVE

by @hindatuauwal

Jikinta har yanzu yana amace saboda wani wutan sha'awa dake cii aduk wani sassa na jikinta.

Ba da jimawa ba aka sanar da ita cewa wasu manyan baƙi sun zo.

Ta gyara zamanta da kyau alokacin da kofar falon ke budewa.

Wasu manyan mata suka shigo, ƴan gayu kai daga ganin su kasan kudi ba matsalar su bace arayuwa, ga sarƙar zinare da zobuna na haskawa ajikin su da kamshin turare mai ƙarfi.

Tare da su akwai wani matashin saurayi.

Jamila ta ɗaga ido. Sai idanunta suka sauka kansa.

Matashin saurayin ya kasance kyakkyawa.

Dogo ne sosai irin tsayin nan mai tsari dake kama zuciyar ƴan mata, kyakkyawar fuskarsa tai matukar dacewa da zubinsa, English wears ne ajikinsa da ya nuna cewa shi ma ɗan ƙwalisa ne.

Jamila ta kalle sa ta tuna lokacin da Samir ya taɓa nuna matashi ahoton da sukayi atare sanda yaje London tare dashi.

“Sunansa Raihan. Ɗan wurin Sister nace sunanta Suhaila, tazo haihuwar sa ta rasu, shine sai Mimi ta rai nesa but Raihan ɗanane...ina sonsa sosai da sosai duk wani soyayya da nake ma mahaifiyarsa ayanzu shi nake masa, ko ƴaƴana na kaina na haifa bana jin zan sosu kamar yadda nake son Raihan"

Raihan!.

Sai zuciyar Jamila ta yi wani irin bugu. Ta yi saurin kawar da idanunta.

Me ya sa?

Ita kanta ba ta sani ba. Ba saboda kyawunsa kaɗai ba.

Domin Jamila ma kyakkyawa ce, kuma ta saba da ganin maza masu kyau da kuma masu iya kwalliya.

Ba kuma don salon shigarsa ba. Dan tasaba da ƴan ƙwalisa jinin ƴan gayu sosai.

Amma wannan karon… Akwai wani abu da ta kasa ganewa.

Wani abu ne kawai da zuciyarta ta fara yi ba tare da izininta ba.


Ta kalli Raihan na wani ɗan lokaci. Shi ma ya kalle ta, idanunsu suka haɗu.

Jamila ta kawar da nata.

Bayan gaisawa da ɗan tattaunawa, matan suka ce jirginsu zai tashi kuma lokaci ya yi da za su tafi.

Jamila ta mike domin yi musu rakiya. Suka wuce zuwa veranda.

Iskar waje ta ɗan bugi fuskarta. Ta yi murmushi tana musu sallama.

“Allah ya kai ku lafiya.”

“Yawwa Jamila. Ki kula da kanki.”

“Insha Allah.”

Matan suka juya suka nufi hanyar mota.
Jamila ta tsaya a wurin.

Sai Raihan ya tsaya.

Ta kalle shi.

Shi ma ya kalle ta.

A fuskar sa akwai murmushi mara nauyi.

“Bye, Aunty.”

Kafin Jamila ta fahimci abin da zai faru… Raihan ya matso.

Ya rungume ta.

Nan take duniyar Jamila ta yi shiru. Idanunta suka buɗe suka ƙara girma.

Numfashinta ya tsaya na ɗan lokaci. Jikinta na mutuwa muruss!

Ba don rungumar ta kasance mai tsawo ba.

A’a.

Amma saboda ba ta shirya ta ji irin wannan kusanci daga gare shi ba.

Ta ji bugun zuciyarta yana ƙaruwa. Kamshin turaren Raihan ya dabai bayeta har ya gusar da nata.

Ta lumshe ido na ɗan lokaci.

Wani yanayi mara suna ya ratsa jikinta. Sai ta buɗe idanunta da sauri.

Me ke faruwa da ni? Ta tambayi kanta.

Raihan ya janye daga gare ta yana murmushi, kamar babu abin da ya faru.

“See you later, Aunty.”

Jamila ta tsaya cak.

Ta kasa amsa masa nan take. Kawai ta kalle shi.

Ya juya ya tafi.

Ta bi shi da kallo har ya isa wajen motar, motar ta tashi ta ci gaba da kallonta, har sai da ta ɓace daga ganin ta.

A hankali ta ɗaga hannunta zuwa kirjinta.

Zuciyarta kuwa….Har yanzu tana bugawa da sauri.

Tuk…!tuk…!!tuk…!!!

Ta lumshe idanunta.

“Me ya sa?”

Ta furta a hankali.

Sai ta girgiza kai.

“A’a…”

Ta juya da sauri ta koma cikin gida.

Amma abin da ba ta sani ba shi ne—Wani ƙaramin abu da ya faru cikin ƴan daƙiƙu kaɗan, zai iya zama farkon wata babbar jarrabawa a rayuwarta.

Domin ba kowace ƙara ce ta zuciya take nufin soyayya ba.

Wasu lokutan…jarabawa ce kawai da ta zo cikin mummunar fuska.




  *ZAINAB*

Zaune take akan kujera mai cin mutum ɗaya. Suduka yaran na kan carpet suna hidimomin su.

Wanda idan za'a samata wuka a wuya bazata iya cewa ga abinda sukeyiba.

Ita dai tasan zuciyarta na manne da tinanin rayukan da basu san muhimmancin taba arayuwa.

Ga wani irin tsoro da takejin yana shigarta ta kowani kapha na jikinta.



Abubuwan da suke faruwa a yanzu suna matuƙar bata tsoro matuƙa gayan.


Ko imagine bata taɓayi akan mijinta zai iya betraying dinta arayuwa ba.



Asamada komai na rayuwa tanada tabbacin mijinta na ƙaunanta, yana sonta yana nuna mata tatacciyar soyayya da babu gauraye.


Amma ayanzu yabarta, yakama hannun wata daban yasaki nata hannun, bata san.....


"Matsa ku bani wuri....."

Tsawarda muryar Ahmed tayi cikin wannan maganar ta daki dodon kunnin Zainab yasanya zuciyarta dakatawa daga tinanin da takeyi ayanzu.

Miƙewa tayi a hankali ta taka zuwa jikin tagar da takejin sautin muryar Zaliha

Idanuwanta ne suka sauka akan fuskar mijinta.


Ta matso tagar a hankali.  

Ta gani da kyau. 

Zaliha tana tsaye a ƙofar motar, run gumeda mijinta a kirjinta, kan ta akan kafadarsa.  

Kuma murmushin da ke fuskarta ba na kunya ba ne. Na nasara ne.  

Ta ɗaga kai.  

Idanunta suka hadu da nata ta cikin tagar.  

Ta yi zaton za ta sunkuya.  

Ta yi zaton za ta juya fuskarta.  

Tayi zaton zata cewa Ahmed: “Bari inje inga Zainab.”  

Amma se ta yi murmushi.  

Murmushin da ya ce: “Ga shi na samu. Kuma ba zan sake shi ba.”  

Sai ta juya.  

Ta kama hannun Ahmed. Suka shiga sashinsu tare.  

Ƙofar ta rufe da ƙara mai nauyi. Kamar ƙarar da ke rufe ƙofar wani rai har abada.  

Ta koma ta zauna.  

Zuciyarta ta fara dokawa.  

Dokawa mai ƙarfi, mai zafi, kamar zai fasa allon ƙirjinta ya fito waje ya nuna wa duniya abin dake cin ta.  

Ƙarar buɗo kofar da taji yasanyata ɗago kanta tasauke ƙwayannin idanunta akan fuskar yaranta da suka shigo.

Ramlat ma kuka takeyi haiƙan Khadija na riƙe da ita tana bubbuga bayanta ahankali.

Akan fuskokinsu taga damuwar da suke ciki, kuma idan har ta canka dai dai to ƙarar motar mahaifinsu sukaji, suka fita domin yin mishi oyo-oyo, shine yadaka musu tsawa da tambayar data sanyata dawowa hayyacinta alokacinda tafaɗa kogin tinani.


Khalid bece komai ba yakama hannun Anis suka fice daga falon.

Arayuwarshi gabaɗaya karanta kalmar 'Betrayal' kawai yakeyi batareda yasan ma'anar taba, beta ɓama fahimtar me ake nufida kalmar ba se ayau dayaji zuciyarshi ta tarwatse asanda Zaliha ta bayyana amatsayin matar Abbansu.

Duniya batace dashi ta juya musu bayaba seda Ramlat ta rungume Abbansu yada kamata tsawa da kalmar

'Matsa kiba Ni wuri?".....

Suduka suka matse space ɗin dake tsakaninsu da soyayyanshi phal zukatansu yaja baya yana jefa musu kalmar data sanya kanshi dauke wuta ruwan da ke cikinta na kafewa, wani irin tashin hankali na lulluɓe duniyarshi kamar katon bargo.

"Matsa ku bani wuri....."

Kalmar tadawo mai da wani irin ciwo mai zafi, idan harsu da suka ga wannan side dinnashi ayanzu sun shiga wannan halin to me Mami takeji anata zuciyar....

Jin gina bayan shi yai da garun ɗakinsu da suka shigo.

Kanshi dake sarawa yadafe acikin tafukan hannayen shi jikinshi na ɗaukan kyarma.


Katifa Anis yahau ya laphe yana sauke ajiyar zuciya mai sauti, don haryanzu razanin tsawan da Abbansu ye musu be sake suba.

              ___________

Sakin hannun Ramlat tayi ta ƙaraso inda Mami ke zaune.

Hannunta ta saƙala acikin nata, muryanta narawa tasoma magana

"Nasha jin labarai akan mahaifin da yajuya ma iyalansa baya saboda yaƙara aure....

Amma ban taɓa jin inda akace mahaifiya ta juyama ƴaƴanta bayaba....

Ƙaunar dake tsakanin mahaifiya da ƴaƴanta mai girma ne......

Inada tabbacin zamu iya rayuwa idan babu Abba amma idan babu ke....."

Kalaman dake cikin kanta ne suka watse zuciyarta na karyewa hakan yabama hawayen da take dannewa damar saukowa saman fuskarta.

Kai Zainab tagirgiza, takamo haɓar Khadijah tana ƙoƙarin yin murmushin da yakasa rufe ko bakinta.

"Kamar yanda kika fadane ko wani mutum yana gina gida yai tafiyarsa hankali kwance ba don komai ba se don yasan akwai ƙyaure mai kyau awannan gidannasa.

Ayanzu Abbanku yatafi yabar gidannan amma ba abinda ze sameku saboda akwai ƙyaure mai kyau acikin gidannan.

Ko wani ƙyaure kariya ne ga gida, Nice watannan ƙyauren da zata kare ku akan komai kafin Abbanku yadawo gareku.

Kunada makaranta gobe kitashi kije ku kwanta seda safe."

Kai Khadijah tagyaɗa tana kallon murmushin dake kan fuskar Mami, magan ganun da tagaya mata na zama mata abayan wutar dake babbaka zuciyarta.


Hannun ta Khadijah taka ma da zimman su tafi Ramlat ta doge, 

Zainab na kallonta ta tako zuwa gareta tarungumeta da faɗin

"Good night Mami"

"Ubangiji Allah yatashemu Lafiya"

Ta fadi tana sumbatar goshinta.

Janye wa Ramlat tai tana murmushi, idanuwan Zainab na kafe akansu har suka shige ɗakinsu.


Ta lumshe idanunta zuciyarta na cigabada numfasawa da wani irin ciwo mara misaltuwa.



Ahaka daren ya shuɗe yabada kwana ɗaya daya wuce.

Kwana na biyu yazo yawuce.
  
Kwana uku har zuwa kan bakwai.

Kowace safiya mota ta fita.  

Kowace yamma ta dawo.  

Amma ma mallakin gidan bai taɓa tsayawa ya ko kalli part din Zainab ba balle ye tinanin shiga.
 
A kuma kowace fita ko dawowa da zeyi kunnuwanta na jin maganganun su da darurrukan su, wasu lokutan harda musayen kalamai masu daɗi.

 
Abin da ta ji shekaru goma sha biyar, yanzu wata na jin sa.  

Kuma kowace rana da ta wuce, tazarar da ke tsakanin sa da iyalinsa kara girma take.

Nisan da bata girma da faɗa ko hayaniyaba seda shiru mai nauyin datafi komai ƙuna arayuwa.
 
 
Shirun da ke cewa: “Ka zama bako a gidan da ka gina.”  

Sun riga da sun fahimci komai ayanzu babu mai cewa

 “Abba ya fita?”  

"Yaushe Abba ze dawo?...."

"Inaso idan Abba yadawo ya taimaka yasiya min kaza....!!"

Sun gane.  

Mahaifinsu ya canja.  

Ba saboda wani abu na rayuwa ba..  

Saboda ya zaɓi wata a kan su.  

A dare na bakwai, Zainab ta zauna a gefen gadonta bayan sunyi sallama da yara.  

Kallon ɗakin tai kewar mijinta da ciwon rashinsa na mamaye ta kamar kowani dare acikin kwanaki 7 ɗinnan.

Tinanin ta yaɗibeta yawatsata shekaru goma sha takwas da suka wuce.

Ranarda aka daura auren su, Ahmed na zaune a gefen ta kamar yadda tazauna yanzu.

Zata iya rantsuwa akan tanajin sautin muryanshi acikin kunnuwanta, idanunta na hasko mata alkawarin da nashi ƙwayannin idanun sukai mata asanda labɓansa ke motsawa.

 “Zainab, ke ce duniyata. Idan duniya ta bar ki, ni ba zan bar ki ba.”  
 
Akaro na farko hawaye suka sauko saman fuskarta.

Yau duniya ta bar ta.  

Kuma shi ne ya bude mata kofa.  

Ta ɗaga hannu ta riƙe ƙirjinta.  

Zuciyarta har yanzu na dokawa.  
  
a silale ta kwanta ta baya numfashinta na fita cikeda rauni.