INUWAR KADDARA 🖤

THE BOSS🔥

by @meelahbazata978

INUWAR ƘADDARA 🖤

Book 1

Page 3✍️

Meelah Bazata

Shi kuwa yana fita daga makarantar bai yi hanyar gida ba, domin akwai inda zai je. Yana dawowa kafin lokacin Ammah ta fita, alkawari ya ɗauka yau sai ya yi rashin mutunci a gidan.

Kasantuwar yanzu garin ya waye, mutane suna ta fita kowa da uzurinsa, ’yan makaranta nata tafiya haka masu fita nema, akwai hada-hada na jama'a sosai, da yake unguwar babbar unguwa ce, kuma akwai masu shi da mara sa shi.

Wata hanya ce da ta kai shi wani tsohon fili da ke bayan unguwar, inda babu gidaje da yawa, sai wasu tsofaffin gine-gine ne haka da wuraren zama irin na matasa, saidai kuma akwai dakuna-dakuna wanda akayi su kamar baca, babbar baca ɗin sa ma a wurin take. Nan ne inda yaransa suke zama, domin duk wani mara ji da yake unguwar to nan ne gurin zamanta, kuma ba su isa su yi komai ba tare da umarnin sa ba, gurin gaba ɗaya mallakinsa ne, wanda guri ne mai girma da kuma ɗimbin tarihi, wanda shine abinda yake lalube a rayuwar sa.

Babban abinda yafi tara matasa a gurin shine shagon uban harkalla, wato mai saida sigari da wiwi na gurin, shine babban shagon da yake saida duk wasu kayan maye a da, kwayoyi da duk wani nau'in kayan maye, shiyasa babu wanda bai san shagon Uban Harkalla ba, saidai kuma a yanzu in ka cire sigari da wiwi babu abinda yake saidawa da danganci maye, domin kuwa Madugu ya hana, babu wani shago wanda ya isa ya saida duk wasu miyagun kwayoyi a kaf unguwar tasu.

Haka kuma duk sanda ya kama mutum da waɗannan makamancin kwayoyin, to a ranar hukuncinka na daban ne, kuma ’yan sanda ma ba su isa su kama yaran sa ba.

Kaf unguwar Tudun Wada Kwaru babu wanda bai san waye Madugu ba, saboda shine yake shugabantar fadan daba na yankin da ke waye baki ɗaya, babu wani ɗan daba da yake da izinin shigowa unguwar da niyar fada ko kuma saurara wani daga cikin yaran Madugu ɗin, haka kuma yaransa ba su isa su kai farmaki ba, amma kuma idan har aka fara kai musu farmaki, to lallai martanin Madugu babu daɗi.

Tun daga nesa yake jin hayaniya da ƙarar dariyarsu da iFace-ifecen su.

Haka shima kafin karasowar sa, sun san da zuwan sa, domin taken Rocky ne, suna shiga unguwar wani ihu da yayi shine abinda ya sanar da zuwan Madugu ɗin.

Yana ƙara matsowa kusa, ɗaya daga cikin samarin da suke tsaye a bakin wajen ya fara ganinsa.

Nan take ya daka ihu ya ɗaga hannu sama yana kirarin kamar yadda suke gaisuwar su ga sarkin nasu.

“MADUGU UBAN TAFIYA! JA ZUGA UBAN TAWAGA, WALLAHI ALLAH!” ya fada yana zubewa ƙasa alamar jinjina.

Kamar an zuba musu ruwa haka wajen ya yi shiru na ɗan daƙiƙu, kafin kowa ya fara bashi hanya.

Kujerar sa da yake zama ɗaya daga cikin yaran nasa wani ya maza ya dakko wani ɗan towel ya goge ta, sabida kura, babu mai zama a wannan kujerar tasa ce, wanda dama da ya zo unguwar akan ta yake zama domin hukunci duk waɗanda suka yi wani laifin anan suke karbar hukunci, dama kuma saidai su yi ’yan kananan laifukan nan a ɓoye, amma sace-sace da kwacen waya karya ne, a cikin unguwar da kewayen ta gaba ɗaya, ba kamar sauran unguwannin wanda hakan ya zama ruwan dare ba, amma kuma duk wanda ya tashi fadar magana shine Madugu, shine shugaban duk wani ɗan daba da ke yankin tare da sace-sace da kwace.

“Takawarka lafiya Madugu, gida naka dawa taka.”

“Ubanmu maganin kukanmu!”

“Jagoranmu hakimin sarkin mu!”

Irin kirarin da suke tayi masa kenan, shikuwa wannan fuskar tasa har zuwa lokacin kamar tayi aman wuta da waɗannan idanun nasa da a ganin farko zaka gansu kamar idanuwan mashaya.

Jagwa babban yaronsa ne ya fito daga cikin wani daki, sharbebiyar kuka ce a hannunsa tana ta kyalli wacce da alama yanzu ya gama wasa ta duba da yadda take ta kyalli.

A ƙasa yasa ya karta ta tayi wani irin ƙara tare da tartsatsin wuta, sannan ya ɗaga ta sama yana kallon Madugu tare da yi masa kirari.

“Se ka sha Oga kadade kayi lasting kayi shekaru kamar na dabino, cau-cau-cau, me kudi uban matsiya ta, kariyar Allah ta tabbata gareka, kainuwa dashen Allah,

Su soka ko su kika, babu yadda suka iya wallahi Allah.

Umarni na ka cika aiki na mu wallahi Allah,

Ya Shugaba namu, naku, nasu, nakwari baki ɗaya........

Ba tuba baki ba duna ma ya mike yana wani irin fito da da yasa karnukan da suke gurin duk suka fito gaba ɗaya, gurin ya ɗau sowa kowa da abinda yake fada, Duna na fadin.

“Jamuje shuga, ba kai din allurar cikin ruwa ce, kainuwar makiya ba zatar masana wallahi Allah, ina gwanin wani ga nawa, babban goro se magogin karfe. Eh mana! Anahaka! Eh mana, hakan ma yanayi!”

Wasun kuma suka ɗaga hannu sama suma suna masa kirari, kowa dai da abinda yake fada.

Sauran dama da suke zaune duk sun mike gaba ɗaya, babu wanda zai zauna har sai Madugu ya zauna.

Duk kiraranin da suke masa da gaisuwar da suke masa fuskarsa a daure take tamau, anya kuwa yana dariya ma? Shine ni dai tambayar da nayiwa.

Babu murmushi, babu alamar wasa.

Hannu ya daga musu yace,

“A lafa haka kwari.” Yana fadin hakan cikin husky voice dinsa, gurin yayi shiru kuwa kamar an yi ruwa an dauke.

Yana zaune ya hakimce kamar wani sarki yayin da ya umarci kowa yake ya cigaba da aikin sa.

Wasu duk sun tafi ya rage sauran manyan yaransa ne su uku, Jagwa, Duna, sai Baushe, sune manyan yaran nasa, duk inda Madugu yasa kafa to suna biye dashi, duk wata harkalla tasa tana hannunsu, abinda yake rabasu shine in zai tafi gida, saboda duk inda yaje Ammah tafiso ya dawo gida ya kwana, shiyasa mawuyaci ne ya kwana a nan, amma dakinsa na musamman yana gurin.

“Madugu.” Shine abinda Jagwa ya fada.

“Hm?”

“Mun gama abin da ka umarta.”

Madugu ya kalle shi, kamar bazai yi magana ba, kafin yace,

“Abinda nace kenan?”

“Aa, komai yana tafiya yadda aka tsara.”

“Waye ya yi kuskure a cikinku?” Tambayar da ya jefo musu kenan.

Shiru sukayi tsit, yayin da shi kuwa yana gefe yana zare ido saboda yasan yayi kuskure, gashi azabar tsoron Madugu bazai barsa yayi masa magana ba.

Madugu kuwa ya sake maimaitawa, yana wurga musu wani kallo mai kama da harara, da alama masifaffene.

“Na tambaya, wa ya yi kuskure, kun yi min shiru, ko sai na tashi ne?”

Wannan saurayin da yake ta rawar jiki ya ɗaga hannu zuba sai zubo masa takeyi, bakinsa na rawa yace,

“Ni ne.”

Madugu ya kalle shi tare da jefa masa idanuwansa masu matukar razanarwa.

“Zo.”

Saurayin ya matsa kusa, yiki na rawa.

“Me ya sa?”

“Na yi kuskure, bazan kara ba, Me gida.”

“Gayamin kuskuren ka da kanka.”

“Shegiyar nasha, Madugu, kuma daga yau ba kari, dan Allah kayi min afuwa.”

Madugu ya ɗan yi shiru kamar bazai ce komai ba, sannan yace,

“Na taɓa gaya maka abin da zai faru idan ka yi abin da ban umarce ka ba?”

Saurayin ya sunkuyar da kai ƙasa yace,

“Eh.”

“Me?”

“Za ka min hukunci.”

Madugu ya ɗaga kai ya jinjina yace,

“Ka sani kenan kuma ka aikata.”

Ya yi shiru bai iya cewa komai ba.

Shi kuwa Madugu yace,

“Karfe nawa yanzu?”

Da kanshi saurayin wanda akalla bazai wuce shekara 19 zuwa 20 ba yace,

“9:30 AM.”

“Je ka lafa a can, daga yanzu zuwa karfe biyu na rana.” Abinda ya fada yana nunawa saurayin wani guri wanda ina kallon gurin naga wata irin ƙwallaliya rana ga kuma kayoyin da suke gurin, gurin mai tsananin zafi.

Ko musu saurayin bai yi ba, ya mike domin yasan ahakan ma ya masa da sauki ne, kuma ko da awa dari Madugu yace yayi to babu fashi, kuma bai isa ya mike ba bare kuma ya ki aikatawa, hakan yasa ya mike ya tafi domin cika aiki.

Kallon Jagwa da Duna yayi yace,

“Wasu kwari ne jiya suka zagi ta area ta?”

Amsa suka basa da,

“Wurin arewa yana lafiya.”

“Wurin kudu babu matsala.”

“Amma akwai wasu mutane da aka gani suna yawan zagaye kusa da ekar mu.”

Madugu ya ajiye ruwan da yake sha ya dago.

“Su waye?”

“Ba mu san su ba Madugu, amma dai nafi zaton mutanen Kibiya ne.”

“Me kuka yi ku?”

“Mun bibiyi ɗaya daga cikinsu, munso kamo sa, saidai ya ankare da wuri ya tsere.”

“Ku ci gaba da sa ido.”

“Madugu, akwai wata magana kuma.” Inji Duna yana miko nasa bottle din hannunsa.

Madugu ya kalle shi, bai yi magana ba yasan amsa yake jira, shiyasa yace,

“An ce akwai wani mutum da yake ta tambayar sunanka, da wasu bayanai akanka, saidai da alama sabo ne anan kuma nafi zaton jami'i ne.”

Mikewa yayi harya fara tafiya kafin ya ɗan tsaya kadan ya kallesu yace,

“Na gama da wannan matsalar tun jiya, yanzu haka yana can yana jinyar jikinsa, gobe ya kara bibiyar sawun Madugu.”

Yana kai nan ya cigaba da tafiya, Rocky yana take masa baya.

Gida ya nufa ganin karfe goma tayi, yasan yanzu Ammah ta fita, wanda kuma yake bukatar hukuntawa iyanzu yasan yana gidan, yana tafe cikin izza wacce kai kana gani kasan wannan ya ma wuce ɗan daba, saidai uban daba.

Koda ya shigo cikin unguwar tasu akwai ɗan saukin jama'a, haka ya nufi gidan nasu wanda da yawa wasu in sun gansa zasu jiya wai kuma su zube ƙasa suna kwasar gaisuwa.