FreeArewaPen original
INUWAR KADDARA 🖤
- 1views
- 17chapters
- 0audios
- words
- 0likes
Share:
The story
Synopsis
No synopsis yet.
Sample · MASOMIN LAMARIN
INUWAR KADDARA..🖤**Page 1✍️**Meelah Bazata**Bismillahirrahmanirrahim✅**ƘADDARAR ƊAN DABA*Rayuwa kowa da yadda Ubangiji ya tsara masa rayuwarsa, sai dai kuma akwai waɗanda ƙaddara ita ce take zaɓarsu, mutane suna ganinsa a matsayin ɗan daba mai tsauri, wanda mutane suke tsoronsa kuma ba ya yarda kowa ya taka masa ko kuma ya tsallake iyakarsa.Amma kuma gidansu, akwai wani gefensa da babu wanda yake gani. Duk da zagi da cin mutunci da tsinuwa da ke fuskantar a rayuwar sa ta ɓangaren Al'umma, amma kuma Mahaifiyarsa ce mutum ɗaya da yake tsoron ɓata wa rai, haka kuma Ƙanwarsa ita ce mutum ɗaya da yake karewa fiye da komai a rayuwar sa.Yana rayuwa a ƙarƙashin wata ƙaddara da ta yi masa inuwa tun daga farko — abin da ya faru a rayuwarsa ne ya mayar da shi mutumin da ya zama yanzu, wato DAN DABA, amma duk da irin rayuwar da yake ciki, akwai abubuwan da har yanzu yake ƙoƙarin karewa a rayuwar sa, mahaifiyarsa da ƙanwarsa, da kuma binciko inda mahaifin sa yake.Me ya sa ya zama ɗan daba?Me ya faru da mahaifinsa?Me ya sa yake tsananin kare mahaifiyarsa?Me ya sa ƙanwarsa take da muhimmanci a rayuwarsa?Wane sirri ne ya haɗa rayuwarsa da abin da ya faru a baya?Shin zai iya tserewa daga inuwa ta ƙaddarar da take bibiyar shi?Da ƙarfe 11:47 na dare, unguwar ta yi tsit sosai ba ka jin sautin komai sai kukan tsuntsaye, ga kuma duhun dare, da kuma rashin yawaitar haske saboda rashin wutar lantarki a cikin unguwannin.Hasken fitilun titi, shi ne ya kasance yana haskaka wasu sassan hanyar, yayin da sauran wuraren suka kasance cikin yanayi na duhu.Gudu yake shi kaɗai a cikin wannan dare, wanda karar gudun nasa ita ce abin da ya fi amsa kuwa a cikin wannan dare, gudu yake ba tare da ya waiwaya ba.Haka numfashinsa ya yi nauyi, ƙafafunsa suna bugun kwalta da ƙarfi, amma duk da haka bai tsaya ba.Jami'an ƴan sanda ne suke binsa a wannan lokacin cikin mota, sai dai kuma duk gudunsu sun kasa cimma sa.Yana kai wani ƙaramin lungu mai duhu, ya shige ya tsaya yana jingina da bango, kai ya yana ƙoƙarin daidaita numfashinsa.Se da ya gama daidaita kansa kafin ya fito a wannan maboya tasa, a lokacin waɗannan ƴan sanda suna cikin mota, sun faka duk sun fito suna duban inda za su ga wanda suka biyo, ai kansu ba su san wanda suke bi ba, umarnin da aka ba su shi ne kawai abin da suke yi.Yana fitowa ya zo daidai inda suke kansa har zuwa lokacin lulluɓe yake da hular gashin da yake kansa, ga kuma riga mai hula, wacce gaba ɗaya ta rufe rabin fuskar tasa babu abin da za ka iya gani.Ɗan sandan da yake gabanta yana niyar damƙar hannunsa, amma ganin fuskar waye a tsaye ya sa, ya wani irin zabura har sai da ya kai ƙasa saboda tsorata.Madugu yake gani ko kuwa, abin da kowa ya san shi ne madugu baya guduwa, baya JA DA BAYA, haka kuma babu wani jami'i da isa ya tunƙare sa, to me ya sa ya gudu ayanzu, ta...
Contents
Table of contents
Preview every chapter, see what is free, and continue reading when you join ArewaPen.