MATAR GIDA

MATAR GIDA PAGE 69

by @maimunabala209

MATAR GIDA BOOK 2



SHUUKRAN/022



YOTA ASSOCIATION 




P69




Unaisa na nan kwance har magrib tana bacci ba ita ta farka ba sai da aka idar da sallar magrib,da wani irin ciwon ciki ta farka da kyar ta rarrafa ta shiga bathroom ta yi tsarki kafin ta dauro alwalah bayan ta idar da alwalah tana tafiya tana dafa bango a haka ta shiga ɗaki da kyar ta yi sallar magrib bayan ta idar da sallah bata samu damar addu'a ba saboda yadda cikinta ke juya mata,kwanciya ta yi kan darduma tana riƙe da ciki,ta dauki lokaci haka kafin daga bisani amai ya taso mata da wani irin sauri ta yunƙura da gudu ta yi hanyar bathroom,kusan gaba ɗaya abinda ta ci unin ranar sai da ta yi aman sa kaf cike da juriya ta wanke fuska kafin ta fita daga bathroom,a daddafe ta shiga ɗaki ta kwanta kan gado tana ji ana kiran sallar isha'i sai dai baza ta iya tashi a wannan lokacin ba,a haka bacci ya dauketa tana cikin bacci Amirah ta shigo ɗakin ganin tana kwance tana bacci yasa Amirah fita  tare da ja mata kofa,karfe tara dai dai Ɗalha ya shigo ɓangaren Unaisa kasancewar ita ce da girki har ya shiga ɗakinsa sai kuma ya fita ya buɗe kofar ɗakinta ganinta ya yi kwance ta kuɗunɗune cikin bargo taɓe baki ya yi ya fita daga ɗakin,a cikin bacci ta ji amai na taso mata babu shiri ta tashi ta shiga bathroom ta yi ta ƙaƙaren amai amma babu abinda ya fita kasancewar babu komai cikinta,har sannan cikinta bai daina mata ciwo ba,bayan ta kuskura baki tana shirin barin bathroom taji cikinta ya ƙulle mata da wani irin sauri ta zauna kan sitter bayan ta gama biya bukata ta yi tsarki sai a sannan ta tuna bata yi sallar isha'i ba,hakan yasa ta daure ta dauro alwalah cike da jureya tana tafe tana dafa bango da ƙyar ta samu ta yi sallar isha'i lokacin sha biyu na dare,bayan ta idar da sallar ne amai ya kuma taso mata da gudu ta shiga bathroom sai dai kamar ɗazu ta yi ƙaƙarenta ta gama babu abinda ya fita bata bar bathroom ba cikinta ya juya hakan yasa ta zauna sitter da sauri,tun Unaisa na kirga adadin shigarta bayi har lissafi ya kwafce mata har karfe uku na dare tana abu ɗaya amai da judawa zuwa wannan lokaci jikinta ya yi sanyi sosai bata da wani sauran karfi ko tafiya bata iya yi,hakan yasa ta yi zamanta kofar bathroom da ta ji amai zata rarrafa ta shiga haka zalika bayan gidan agogo dake manne bango ɗakinta ta ƙalla ta ga karfe uku da mintina goma na dare a hankali ta ce ''bazan iya ba l can't take it anymore'' daga haka ta rarrafa har ta fita daga ɗakin sanin kanta ne in zata shekara tana buga masa kofa bazai buɗe ba hakan yasa cike da juriya tana jin yadda cikin ta ke juya mata ta kai hannu ta buɗe kofar,ɗakin ya yi duhu babu haske,sai hasken farin wata dake shigowa ta tagar ɗakin daga inda take tana iya ganinsa,ganinsa ta yi zaune kan darduma da alama bai dade da idar da sallah ba tana jin ƙara carɓi da yake ja a hankali Unaisa ta shiga kiran sunansa,waigowa ya yi yana kallonta cikin duhu can kuma ya tashi ya kunna wutar ɗakin ganin haka yasa Unaisa miƙo masa hannu so take ya riƙe ko da hannuta ne ko zata samu sassaucin ciwon ciki da ke damunta,a wahale ta ce ''Abbam ciwo zai kashe ni cikina ciwo yake min''sai kuma ta yi shiru har sannan tana miƙo masa hannunta,waje Ɗalha ya samu ya zauna yana ƙare mata kallo da gaske ciwo take amma bai jin zai iya taimakonta ba ya tunanin zai iya fita cikin daren nan a kasalance Unaisa ta kalle sa ta ce ''taimake ni Abbam kar na mutu ka kai ni asibiti'' ganin baida niyyar riƙe hannunta kawai ta sauke hannun a hankali tana mayar da numfashi tana kallonsa harda halin ciwo da take ciki tana ƙara jinjina rashi tausayi irin na Ɗalha a hankali ya buɗe baki ya ce ''Allah ya ba ki lafiya amma ba zan iya fita yanzu ba ki daure zuwa safe sai na kai ki asibitin'' hawaye ya shiga jangaro daga idanun Unaisa da ƙyar ta buɗe baki ta ce ''tun sha biyu nake ciwo ban ko rintsa ba ka taimaka ka kaini asibiti ba dan halina ba dan girman Allah'' ta ƙare magana tana kuka sosai  Ɗalha bai ji komai cikin zuciyarsa ba kawai ya tashi daga inda yake zaune ya koma kan darduma daga haka ya mayar da dubansa gareta ya ce ''da Hausa na yi magana ba da wani yare ba,ki jira gari ya waye sai na kai ki'' daga haka ya tayar da sallah da ido kawai ta kallesa zuciyarta na mata zafi sosai ga zafin ciwo ga wulaƙancin da rashin tausayi da Ɗalha ya gwada mata nan take ta ji kirginta ya fara mata nauyi kamar yadda ya nata ɗazu da safe da sauri ta shiga jan numfashi tana saukewa ta dauki a ƙallah mintina biyar a haka kafin ta rarrafa ta fita daga ɗakin Ɗalha,ta nufi ɓangaren Amirah dai dai sanda ta shiga babban parlour ta fara ƙaƙaren amai banda yawo babu abinda ta fitar,a hankali ta ja jikinta ta jingina bayanta da kujerar parlour tana sauke numfashi ta dauki a ƙallah mintina biyar zaune a wajen kafin daga bisani ta cigaba da rarrafawa zuwa ɓanagren Amirah bayan shigarta ɓangaren ta rasa cikin ɗakuna wanne ne na Amirah,can wata dabara ta faɗa mata ta shiga ɓude ɗakuna ɗaya bayan ɗaya,ɗakin farko Sudais da Suhail sai Rayyan da Afef ne kwance suna bacci hankali kwance kallonsu Unaisa ta yi cikin hasken fitilar marar haske sosai a hankali ta ja masu kofa ta rufe daga haka ta ɓude daki dake gefe,wutar ɗakin a kunne cike da jureya Unaisa ta ɗago gajiyayyun idanuwanta tana bin ɗakin da ido,Fauziyya ta gani kwance kan gado tana bacci hankali kwance daga haka idanunta sun sauka kan Amirah dake zaune bisa darduma tana karatun Alkur'ani murya ƙasa ƙasa jin motsin buɗe kofa yasa Amirah saurin mayar da dubanta ga kofa ganin Unaisa kwance cikin halin ciwo yasa ta rufa Kur'ani da sauri ta yunƙura ta nufi inda Unaisa ke durkushe kofar ɗakin ganin haka Unaisa ta sake kuka wani irin sanyi ta ji zuciyarta tana kuka tare da murmushi lokaci guda sosai ta samu nitsuwa cikin zuciyarta ganin Amirah sanin kanta ne Amirah baza ta cire mata ciwo ba amma ta sani insha Allah zata samu mafita wani irin ajiyar zuciya ta sauke kamar yaro da ya uni bai ga mahaifiyarsa ba yayin da ta ganta

















Da sauri Amirah ta karaso inda Unaisa ke durkushe ta kai hannu kafaɗunta tare da ɗago fuskarta tana tambayarta me ke damunta Unaisa da ta gama galabaita da ciwo da kyar ta ɗago idanunta ta zuba wa Amirah cikin muryar ciwo ta ce ''mutuwa zan yi cikina ke ciwo taimake ni ki kaini asibiti'' sakinta Amirah ta yi ta fita daga site ɗin bayan fitarta bata tsaya ko ina ba sai ɓangaren Unaisa bayan shigarta ta buɗe kofa da take da tabbacin nan ne ɗakin Ɗalha kamar yadda ta yi tunanin kowa ganinsa ta yi zaune kan darduma yana tilawar Alkur'ani,wani irin sauri ta ƙarasa shiga ɗakin zama ta yi gefen sa gaba ɗaya bata cikin nitsuwarta kallo ɗaya Ɗalha ya mata ya kai karshen aya da yake karantawa yana shirin magana ta ce ''Unaisa ce ba lafiya dan Allah ka tashi ka kaimu asibiti jikin nata sosai ne'' ba tare da motsa daga inda yake zaune ko nuna  alamar damuwa ba Ɗalha ya ce ''na sani na ce mata ta jira in Allah ya kaimu gobe da kaina zan kaita asibiti'' wani irin kallo Amirah ta masa kafin ta ce ''me ka ke nufi da gobe ka ganta kuwa?" hankali kwance yana buɗe shafin Kur'ani ya ce ''ɗazu ta bar ɗakin nan'' fuskar Amirah cike da mamaki ta ce ''a'a wasa ka ke kana nufin kana sane yarinyar nan bata da lafiya kuma ta faɗa maka amma ka bar ƴar mutane da ciwo ga ciki jikinta ka ce sai gobe zaka kaita asibiti?" Amirah ta ƙare magana cikin ɗan ɓacin rai ganin ran Amirah ya fara ɓaci Ɗalha ya rufe Kur'ani dake gabansa ya ce ''me ki ke so na mata?" hannu Amirah ta kai ta dafe goshi ta ce ''this is unbelivable i can't take this ,me ka ke nufi da me nake so ka mata?'' Amirah ta ƙare magana fuskarta dauke da mamaki can ta ce ''oky mu je asibiti ka kaita asibiti is what l want'' ɗage kafaɗu Ɗalha ya yi daga haka ya ce ''fine'' wani harara Amirah ta banƙo masa yayin da ya juya baya yana rufe darduma fita ta yi daga ɗakin,ɗakin Unaisa ta shiga saif dake ɗakin ta nufa inda ta ɗaukarwa Unaisa sweatsuit da hijab tana shirin barin ɗakin idonta ya sauka kan wayar Unaisa dake kan bed daukar wayar ta yi daga haka ta fita daga ɗakin,da taimakon Amirah Unaisa ta yi wanka  a daren dalilin ta ɓata jikinta da amai da yawu,Amirah ta shiryata cikin sweatsuit ta sa mata hijab daga haka sun fita daga gidan Amirah na riƙe da Unaisa,kofar baya Amirah ta buɗe inda ta taimakawa Unaisa ta shiga kafin itama ta shiga,bayan Amirah ta shiga ne Unaisa ta daura kanta cinyar Amirah tana sauke ajiyar zuciya har sannan bata daina kuka ba hawaye kawai ke zuba daga idanunta har yanzu ta ƙasa daina mamakin Ɗalha,asibitin kuɗi wanda yake mafi kusa da su Ɗalha ya kai su,bayan ya yi parking ne Amirah ta fita ta sami wata nurse a reception ta faɗa mata tare take da patient sannan patient ɗin baza ta iya tafiya hakan yasa nurse ɗin daukar keke da ake tura marasa lafiya ta fitar har inda motan Dalha yake,Ɗalha na zaune cikin mota Amirah da nurse suka taimakawa Unaisa sun daura ta kan keke daga haka sun shiga da ita emergency word Allah ya taimaka akwai likitoci biyu dake aikin dare nan suka dukufa kan Unaisa,har sannan Ɗalha na zaune cikin mota, duk abinda yake ba gangan yake ba har cikin zuciyarsa baya jin komai game da Unaisa baya jin sonta ko kaɗan haka zalikah baya jin wani abu mai kama da tausayinta cikin zuciyarsa,ita ko Amirah ta ƙasa tsaye ta ƙasa zaune sai kaiwa da komowa take a reception,bayan mintina arba'ain ɗaya daga cikin likitoci ya fita daga emergency word nan ya kira Amirah sai a sannan Amirah ta dawo hankalinta nan ta ga ita kaɗai ce a reception babu Ɗalha kenan hakan yana nufin bai fita daga mota ba, gaba ɗaya Amirah ta ƙasa gane kan Ɗalha kwana biyun nan bata san dalilinsa na canzawa Unaisa ba taɓe baki ta yi ta bi bayan likitan bayan shigarta ofishin likita ne ya nuna mata kujera ya ce bismillah zama Amirah ta yi kafin ta mayar da dubanta garesa  gyarar murya likita ya yi kafin ya ce ''duk wata bincike da muka yi ba mu ga wata matsala ba,is Possible pregnancy hormone ke bata wahala,yes bamu ga abinda ya jawo mata amai da gudawa ba,kawai shawarar da zan baku shine ku mayar da hankali kanta sosai eh a tabbatar da tsaftar duk wani abinda zata ci shine kawai yanzu mun sa mata ruwa isnsha Allah zata samu karfin jiki sannan zata samu sauƙin gudawa'' godiya Amirah ta yiwa likita daga haka ta fita daga ofishin inda Ɗalha ya yi parking mota ta nufa,kofar gaba ta buɗe daga haka ta shiga motar ta zauna bayan ta shigarta ne Ɗalha ya mayar da dubansa gareta ya ce ''ya ake ciki me suka ce yake damunta'' shiru Amirah ta yi kamar baza ta ce komai ba can ta taɓe baki tana ƙara mamakin Ɗalha daga haka ta yi masa bayani kamar yadda likita ya faɗa mata 









SHUUKRAN