5
..........“Siyama ki daina danganta rayuwata da matsalar dana kawo miki yanzu. Sannan ni banga aibu a yanda nake ba. Nifa mace ce, kina so ne na rayu tamkar wata ballagaza ne? Mace fa da gyara aka santa, shi kansa Farouk ɗin da bana gyara kan nawa kamar haka zai dinga min wannan mahaukacin son ne? Har ya dinga jin baya ƙaunar na rabu da shi. Ke dai kawai ki bani shawara akan wannan mayyar yarinyar da yake shirin kwaso min, inaga ma asiri ta masa. Dan wlhy ni shaida ce Farouk ko kallon mata baya yi”.
Siyama dake kallonta tai murmurshi kawai tana girgiza kanta. Sai kuma cikin sauke numfashi da kamo hannayenta ta riƙe cikin nata ta ce, “Shike nan na bari. Kuma ni bance kar ki gyara kanki ba, ki dai dinga sara kina duban bakin gatari nake nufi, kiyi komai dai-dai da yanda addini ya tsayar damu, sannan kodan lafiyarki ma Deenah, kina da ilimi fa na addini dana zamani. Deenah idan mukace komai sai munyi domin birge maza zamu tsinta kammu ne kawai a cikin wuta batare da mun shirya ba. Tabbas mace ƴar ƙyale-ƙyale ce, mazan wannan zamanin kuma na son hakan. Mu kuma matan a son mu faranta musu muke jefa kanmu a masifa tun daga nan duniya ma, gashi shi kuma namiji dan kinyi abinda yake so bashi zai hana ya hango wata ba, abinda ma zai baki mamaki idan kina a wata siffa kika canja zuwa abinda yake so shi kuma gobe zaki iya ganinsa a matsayin wancan suffar da kika bari ce ke birgesa, to zaki sake komawa ne saboda shi?....”
Deenah ta girgiza kai.
Siyama ta cigaba da faɗin, “Alhamdullahi, mu mata ya kamata mu san muhimmancin kammu a matsayin ƳAN ADAM. Mu fara kallon mi muke so?, mi ya dace damu?, ina muke son zuwa?. Ba laifi bane muyi gyara domin mazan aurenmu koma samari, ita mace ƴar kwalisa ce, amma ki sani akwai abinda idan kikayi kece a ciki. Kuma zaki amshi sakamakon sa, wannan kuma bazai hana mijinki yaga wata ba, ko saurayi ya yaudareki. Mata nawa ne ƙyawawa aka saki a gidan aure? Mata nawa ne ƙyawawa ke rayuwar wahala a gidan aure? Mata nawa ne ƙyawawa mazansu ke neman matan waje, mata nawa ne ƙyawawa ke son aure babu mijin?. Sannan mata nawa ne masu ƙarancin ƙyau ke a gidan aure mazansu na kishi, na killacewa, na ƙauna?. Mata nawa ne masu ƙarancin ƙyau a waje ke ɗauke hankulan mazan dake da ƙyawawan mata a cikin gida?. Idan duk wannan basu hana maza komai ba mu miyasa matan zamu shagaltu a saɓama UBANGIJI domin kawai birgesu su same mu yanda suke so?.”
“Deenah. Ita mutuwar nan fa da muke ji anata faɗa gaskiya ce, tako ina kuma zata iya zuwa mana. Irin wannan gyaran koyi da yahudawa ne, gashi dai ALLAH ya bamu dai-dai wanda ya dace da halittarmu ta baƙaƙen fata da zamu yi kwalliya, ba sai mun ɗauki wani da baida tsarki mun dasa ba bayan mun san akan ibadarmu ma akwai ayar tambaya. Haka farce namu ma ance mu dinga yankewa bayan kwanaki arba'in. Dan ALLAH kije ki cire su na roƙe ki ƴar uwata, idan mutuwa ta riskemu ba sai mun wahalar da masu mana wankan gawa ba. Gyara yana farawa ne daga tsafta, ƙamshi, kwalliya, cin abincin mai ƙyau, kula da lafiya da kuma ado cikin iyaka duk mun sani. Duka kuma ALLAH ya baki damar yi da samu. ALLAH yayi ki ƙyaƙyƙyawar mace da ko maƙiyinki ya kalleki yasan kina da ƙyau, ki godema ALLAH da wannan ni'imar da yayi miki ta hanyar kiyaye dokinkinsa. Mu iyaye ne yanzu, bama buƙatar duk wannan, saboda ita tarbiyya basai kace ma ɗanka yayi kaza yabar kaza ba, daga ɗabi'unmu suke fara koyon tarbiyyar mu, kuma sune suke yi musu naso a cikin jini. Uwa ta gari ko bata rayu da abinda ta haifaba zai iya tashi nagartacce daga nason jininta ne. Shiyyasa a taɓarɓarewar tarbiyya ta wannan zamanin ba daga ƴaƴan bane ko ƙarshen duniya kawai, har daga mu iyayen ne matsalar take farawa. Yanda MAHAIFIYA-UWA take haka ƴaƴanta suke kasancewa, idan kin fara ganin matsala daga tarbiyyar yaranki ki nutsu ki nazarci kanki da mahaifinsa, dole akwai inda tawayar ta fara. Iyayenmu sun taka rawar gani sosai a rayuwarmu, wajen kiyaye abubuwa koda suna so domin mu mu samu nagarta.”
Sosai Deenah da jikinta yayi sanyi ta sauke ajiyar zuciya. Cikin jinjina kai da lumshe idanu ta ce, “Na fahimceki Siyama. Kuma na gode sosai da kika fahimtar dani ta sigar data dace. In sha ALLAHU zan cire, zan kuma kula bazan sake sakawa ba. Dama ruɗi ne na zuciya da zamani. Kin san idan kana kallon wane ya saka ya masa ƙyau kai ma sai kaga ai kwalliya ce bari ka saka ɗin. Kuma gaskiya ne wannan ba dabi'ar musulunci bace ba, koyi muke da yahudu da nasara.”
“Na gode ma ALLAH da kika fahimceni cikin sauƙi. ALLAH ya yafe mana kuraluranmu gaba ɗaya”.
“Amin ya rabbi. Sai maganar auren nan, Siyama wlhy hankalina a tashe yake. Siyama yarinyar nan asiri taima mijina, ina jin haka a raina. Na rantse miki jiya banyi barci ba, kin san yanda nake da kishi, Siyama na rantse ba zan iya jurewa ba....”
“Zaki iya Deenah. In dai kika riƙe UBANGIJI da haƙuri. Batun asiri kuma zargi bashi da amfani, tunda ke kanki bama kisan wacece ita ba har yanzu”.
“To mi sanin nata zai amfana min Siyama? Bana son ma na santa har abada. Ni sai naga kamar baki damu ba, ko dan bake za'aima kishiyar nan ba ne?”.
“Kiyi haƙuri ba haka bane, wlhy ina jin zafi kuma ina tayaki jin kishi kamar yanda nasan kema idan nice a wannan matsayar zamu raba damuwar tare ne. Gaskiyar data dace na faɗa miki nake gaya miki dan ina ƙaunarki. Sannan batun saninta zai kuwa amfanemu, dan zaki yi dubi da ita wacece ɗin ki ƙara gyara gidanki kafin ta shigo ciki. Zan kuma ƙara gaya miki gaskiya. Ki ajiye duk wannan damuwa da tashin hankalin a gefe ki maida hankalinki akan yaranki, ki kauda idonki daga aurensa. Ki ƙara kusanta kanki ga UBANGIJI wajen ibada zai saka miki salama a zuciya. ALLAH na tuba indai namiji ne ma kwana nawa ne, ɗoki ne dai na amarci dole ayi, wata shida tayi yawa zaku zama dai-dai, musamman idan kika daure ma ranki sai ki barshi da kunyarsa”.
“Ai wata shidan ne bazan iya haƙurin gani ba sam balle ma wanda zasu biyo bayansa. Wlhy Siyama bari na sake tabbatar miki, bafa zan iya raba Farouk da kowace mace ba. Sai dai ko mu rabu, ko ya haƙura”.
“Rabuwa kuma Deenah?”.
“Kwarai da gaske”.
“Ya subahanallah. Dan ALLAH ki daina ma wannan maganar bata da ma'ana, kina cikin fushi ne kawai yanzu ma. Idan kin rabu da shi kinji tsoro kenan kin bar mata mijin? Sannan makomar yaranki fa? Kin san dai Abban Amnah bazai taɓa bar miki ƴaƴansa ba ko?”.
“Idan na yarda kenan nima. Tunda tare muka haifa nima ina da iko da su bashi kaɗai ba ai”.
“Humm Deenah kenan? Ki dai sake dubawa dan ALLAH, kada ki taka SANTSI tun a matakin farko”.
“Babu wani SANTSI da zan taka, idan ma na taka shine ya zubar a hanyar tafiyarmu, kinga kuwa ni da shi duk mun riga mun ɗora ƙafafu. Mai rabon nasara sai ya tsallake batare da ya zame ba, mai tsautsayi kuma ya faɗi. Na gama ma yanke hukunci. Zan koma gida na jira shi ya dawo daga Abujan muyi duk wacce zamuyi. Ya BARI ko na BARSHI ni. Na barki lafiya kema. Zaki ji duk yanda mukayi”.
Bata ko jira cewar Siyama ba ta ɗauki haɗaɗɗiyar bag ɗinta da key ɗin motar ta ta fice abinta...........✍️