SANTSI

7

by @bilynabdulll





.........««ABUJA»»

         Sosai yake kallon wayar cikin damuwa. Kira na kusan biyar kenan yana mata amma anƙi a ɗaga. Hakan na nufin har yanzu tana fushi da shi. Shi kam ya zai yi da Deenah a rayuwar nan. Mi yasa a wannan gaɓar bazata fahimcesa ba kamar yanda ta saba fahimtarsa a baya?. Mi yasa zata canja daga ƙyaƙyƙyawan zaton da yake mata?. Ko da gaske ne da ake cewa baka sanin ainahin halayyar matarka sai zaka ƙara aure?..”
        Huci ya ɗan furzar yana mai ture tunanin daga zuciyarsa, bai haƙura ba ya sake dialing number ɗin nata dai. Yanzu ɗin ma har ta katse ba'a ɗaga ba. Kansa ya girgiza kawai, tare da zamewa cikin kujerar da yake zaune yana mai kwantar da kansa da lumshe idanunsa. Ya ɗauki tsawon lokaci a haka, sai kuma ya sake buɗe idanun nasa yana tashi zaune da ƙyau. Agogon dake ɗaure a tsintsiyar hannunsa ya kalla. Ƙarfe uku da wani abu, ya tabbatar yara sun dawo daga school yanzu, ba kuma su isa fita islamiyya ba. 
        AMNAH babbar ƴarsu mai shekaru goma cif a duniya nada waya, sai kawai yayi tunanin bari ya kirata ko yaji su yaya suke tunda Mamansu taƙi ta ɗaga masa. Cikin sa'a kuwa bugu biyu aka ɗaga. Cikin ƙaramar zazzaƙar muryarta ta ce, “Assalamu alaikum Daddy”.
         A hankali ya sauke ajiyar zuciya tare da murmurshi a lokaci guda. Sai kuma ya miƙe yana faɗin, “Babyna ya kuke?”.
        “Lafiya lau Daddy, ina yini?”.
   Murmurshi ya sake saki mai sauti tare da amsawa. Ya tambayeta school da ƙannenta. 
    “Lafiya Lau muke Daddy. Ga shi muna shirin islamiyya. Amma bamuga Mummy ba. Mari tace tana sama ko mun dawo kada mu dameta. Daddy, we miss Mummy”.
       Murmurshi daya kasance ɗabi'arsa ya saki. Batare da yace komai akan batun Mummy ɗin ba ya ce, “Turn on the Wi-Fi, na kira vedio call”.
        Cike da ɗoki ta ce, “Okay Daddy, I love you”.
     Ta yanke kiran. Ji yayi zuciyarsa ta masa sanyi. Ya koma ya miƙe zuwa balcony ɗin ɗakin hotel ɗin da yaken. Sai da ya bada kamar minti biyu kafin ya danna video call... 
     Ƙyawawan yara ne guda uku suka bayyana. Su duka suka kama da shi, musamman ma mazan da kallo ɗaya zaka fahimci twins ne. Sosai fuskarsa ta kasa ɓoye farin cikin ganinsu. Kamar yanda suma kana kallon su kasan haka ne daga gare su. Cike da murna suke gaishe shi. Shi ko yana amsa wa da kulawa. Twins suka fara bashi labarin school a yau, yayinda Amnah ke tambayarsa yaushe zai dawo?.
        Amsar daya bata ta cewa, ”Gobe in sha ALLAHU da safe”. 
     Ya saka su a farin ciki su duka. Sai kuma suka fara jera masa tsarabar da suke son ya yo musu. Kowa da nashi ra'ayi, bai kuma damu ba yace in sha ALLAHU zuwa anjima duk zai fita shopping ya sayo musu. Ganin lokaci zai ƙure na islamiyyar su yace suje su ƙarasa shiri idan suka dawo zai kira...

        Yana gama waya da yaransa ya sake gwada kiran Deenah. Yanzu ɗin ma bata ɗaga ba. Sai ya girgiza kai kawai. Yana ƙoƙarin ajiye wayar kira ya shigo masa. Har yayi zaton itace ma. Sai dai yana ɗauka sai yaga saɓanin hakan. Sunan da ya bayyana ɗin ya saka idanunsa ɗan lumshewa, ya kuma buɗe a lokaci guda yana sauke ajiyar zuciya. Bai ɗaga ba harta tsinke. Sannan shi ya kira back yana miƙewa ya koma cikin ɗakin...

           ★_________________★
                 ««KADUNA»»

        Duk kiran da Farouk yake akan idon Deenah ne. Ɗagawa ne kawai bata da buƙatar yi, tama kanta alƙawarin babu zama lafiya tsakanin ta da shi har sai ya janye maganar auren nan. Idan kuma yaƙi sai dai ai ɗayan biyu. Gaba ɗaya ji take ta tsanesa. Kai duk ma abinda ya shafesa, hatta da yaransu bata son gani yau. Gidan kansa ji take ya mata muni da matsatsi. 
          Hawaye masu zafi suka shiga sakko mata. Tabbas Farouk yaci amanarta kuma ya cuceta, ko'a haka aka tsaya baiyi auren nan ba ya barta da tabon da bazata manta ba. Shiyyasa manya ke cewa namiji ba ɗan goyo bane. Kalla fa yanda take matsawa kanta da dagewa akan gyara jikinta duk dan ya mora, ya kalleta yaji alfaharin samun macen fita kunya. Ga soyayya da bata iya ɓoyewa a kansa ga kowa. Kullum ƴan uwanta suna faɗa mata ta rage nuna masa wannan mahaukacin son a fili, amma duk tai kunnen uwar shegu da hakan. Shi ne Farouk ya rasa da mi zai saka mata sai kishiya! Kishiya fa jama'a. Lallai namiji rigar ƙaya ne. Namiji SANTSI. Ka taka ka zame, ya taka ka ya zauna dai-dai. To ita wlhy bazai taka ta ya tsira ba, sai ta tabbatar masa ta banbanta da sauran mata. Kuma su zuba su gani, ita ba zata taɓa zama shashasha ba...
           Da wannan tunanin ta share hawayenta tare da ɗaukar wayar zata kashe gaba ɗaya. Dan har yanzu bai daina kira ba. Kamar jira saƙo ya shigo, ta sake jan wani wawan tsaki ganin Farouk ne dai. Ta saman notification taga abinda ya turo kasancewar guntu ne. 
       (Please, Habibty. Pick my call. I miss you). 
     “Munafuki, ƙaniyar miss you ɗin taka. Na kuma bi Habibty da gudu ba wando”. 
       Ta sake jan tsaki tana kashe wayar gaba ɗaya. Saman makeken gadon nata tayi jifa da wayar ta miƙe abinta...

        😥Deenah ayi haƙuri dai🤭.

     
            ★_______________★
                   ««GUSAU»»

        “Aunty wannan Itace event planner ɗin da muka kawo daga Lagos. Ms. Adaora da nake baki labari. Zan ma iya cewa kin san aikinta a zahiri. Dan itace ta shirya bikin ƴar Vice President shekarar data gabata.”
          Fuskar hamshaƙiyar matar ƙawace da murmushi take jinjina kai, idanunta akan wadda akace Event planner ɗin. Sai kuma ta motsa lips a hankali tana amsa gaisuwar da take mata. Kafin ta sake maida kanta ga wadda ta kawota ɗin.
      “Kinyi abinda ya dace Rufaidah, kuma nafi gamsuwa da zaɓin nan naki fiye da duk wanda aka kawo min. Dan tabbas bikin ɗiyar VP kam yayi min ƙyau da nutsuwa. Ms. Adaora ina fata muma anan zaki yi abinda ya dace?.”
           “Yes, Ma'am. zaki sameni yanda kike so. Na miki alƙawari wannan bikin ma sai yafi wanda ya birgeki na ɗiyar Vice President. Saboda a yanzu mun ƙara inganta ayyukanmu da kayan zamani fiye da na baya. Yanzu dai zan so ku sanar min abubuwan da kuke buƙatar a shirya ne kawai. Kamar tsarin events ɗin da yanda al'adanku anan yake. Daga nan sai naga Amarya dan zamu fara kawo mata tailor ɗin mu ya ganta, domin shirya kayan da za tai amfani da su.”
       “Wannan duk ba damuwa bace. Ga Rufaidah nan ku tattauna komai daya dace. Ni dai kawai abinda nake buƙata ku kawo min iya adadin kuɗin da details ɗin da za'a saka. Sai dai akwai ɗan ƙaramin taro da muke buƙata zuwa jibi saboda masu kawo lefe, anan gidan za'ayi komai kuma.”
          “Okay. Ma'am. Duk wannan ba damuwa bane”.
      “Shike nan. Rufaidah sai kuje can sashen IBTISAM ɗin kuyi komai daya dace. Kar dai ku taushe hannu dan anjima kaɗan inada baƙi, ba lallai kuma ku sake ganina ba sai gobe.”
       “Okay Aunty. Bara muje to”.
    “Okay”.
Ta faɗa a taƙaice tana ɗauke kai...........✍️