SANTSI

9

by @bilynabdulll



.........Maimakon Umma taji tashin hankali kota ƙwaɓesu sai cikin faɗa cewa tai, “Ni fa kun isheni da surutu. Kuyi-kuyi mu ƙarasa ku tashi ku shirya ku fita min da abinci kar dare yayi yaƙi ƙarewa bana son iskanci”.
         Shiru babu wanda ya ƙara magana. Dan sun san halinta, yanzu zai ta fara musu tijara gaban ƙannensu da masu shigowa sayen abinci. Haka suka kammala kowacce ta tashi. Mai son yin wanka ta nema ruwa, wadda bata buƙata ta nema na kwaskwarima. 
      Ummul-khair kuwa data zuba tuwo tana gefe tana waska lauma, da gani kasan yunwa take ji sosai. Ƙannenta dake kusa da Auta ne yazo ya zauna kusa da ita. Yayi dagaje-dagaje da datti da majina da hawaye alamar kuka yayi.
       “Ummul-khairi zanci”.
Kallonsa tayi, sai kuma ta yamutse fuska. "Kai Anunu jibeka kamar ba'a maka wanka ba. Ni gaskiya bazanci da kai a haka ba. Ɗakko roba na saka maka ko kaje wajen Yaya Gimbiya gata can a wajen miya ta saka maka”.
       Fuska ya ɓata zai mata kuka. Cikin haushi ta tura masa kwanon ta tashi. Shima baki ya tura yaja kwanon gabansa ya fara cin.....

             ★_________________★
                   ««KADUNA»»

         Kamar yanda Farouk yay ma yaransa alƙawari jiya da safiyar yau ya dawo Kaduna. Sai dai an samu akasi sanda ya shigo su an tafi kaisu makaranta. Daga masu aiki sai Deenah a gida. Sannu Mari keta jera masa bayan gaisuwar da tai masa. Shi ko yana amsawa cikin sauƙi dan tsakaninsa da duka ma'aikatan gidan akwai adalci. Duk da dai iyakar gaisuwar ke haɗa su kawai kasancewar mutum ne shi bamai zama ba. Ba ma shi kawai ba, ko ita Deenah tana ƙyautata musu, yanda take mu'amala da Mari a gidan ma sai ka ɗauka bamai aiki bace ƴar uwarta ce ta jini.
         Yanda ya ɗan gajin nan kwanciya yake buƙata. Kasancewar shi da kansa ya tuƙo kansa tun daga Abuja. Tun kuma bakwai na safe. Amma sai maimakon ya nufi sashensa ya huta ɗin sashen Deenah ya nufa kai tsaye. Ba sanin dawowar tasa tai ba, hakan yasa shigowar tasa tazo mata a bazata. Tana a dining ne tana ƙaryawa. Kayan barci ne a jikinta alamar ko wanka bata yi ba. Kallon sa tai na fisha ta kawar tamkar bata ganshi ba. Sai yanda tayi ɗin ya saka shi sakin ƙaramin murmushi.
          Inda taken ya iso, batare da yayi magana ba yaja kujerar kusa da ita ya zauna kawai ya zuba mata idanunsa. Har a yanzun ma bata sake kallonsa ba, alamar ma tasan da zuwansa wajen bata nuna ba. Ƙaramin gyaran murya yayi da ɗan taɓa ƙafarta da tashi, sai ta sake ɗaure fuska. Bai fasa ba ya cigaba da zungurinta. Nan ma taƙi kulashi, sai ma miƙewa da tai fuuu alamar barin wajen. Cikin zafin nama ya riƙota, a saman cinyarsa ya zaunar da ita, tare da rungumeta sosai a jikinsa.
       Cikin son janye jikinta ta ce, “Malam bana son irin wannan. Please, leave me alone”.
         “I miss you”.
     Ya faɗa yana sumbatar cikin kunnen maimakon kula zancenta.
Cikin takaici ta ce, “Matsalarka ce wannan, ni dai sake ni”.
      Ya murmusa. Ita kuma ta ƙwace jikinta ta tashi. Bai sake yinƙurin riƙeta ba yanzu. Sai ma harɗe hannayensa da yay a ƙirjinsa ya bita da kallo kawai harta shige bedroom ɗinta tana bugo masa ƙofar. Ya ɗan runtse idanu kaɗan yana girgiza kai. Abincin data tashi ta bari ya ja kofin tea ɗin da plate ɗin chips and eggs ɗin gabansa kawai ya cigaba da ci. 
          Abincin yake ci kamar baya so. Kai daga gani kasan akwai tunanin da yake yi. Motsin da wayarsa tayi ya sashi motsawa shima, cirota yay a aljihu yana dubawa. Message ne, ganin sunan daya turo saƙon ya sashi sakin murmurshi. Buɗewa yay kai tsaye. Yana karantawa murmurshin sa na sake faɗaɗa. Sai dai bai ce komai ba ya kife wayar a table ɗin kawai yana sauke ajiyar zuciya.      
          Abincin ya cigaba da ci, tas ya cinye alamar dama yana buƙata. Bai tashi a wajen ba ya cigaba da zama kusan mintina talatin idonsa akan television dage aiki a dining area ɗin. Sai da ya tabbatar lokacin da yake buƙatar ya tashin yayi sannan ya miƙe. Kai tsaye ƙofar da Deenah ta shi ya nufa...
        Baiyi zaton zata barta a buɗe ba. Amma a mamakinsa yana murɗa handle ɗin sai ta buɗe. Ya ɗan sauke ƙaramar ajiyar zuciya tare da tura ƙofar ya shiga. Ɗaki ne babba sosai da yaji kayan more rayuwa. Ga wani ƙamshi mai daɗi. Can gaban ƙaton mirror ɗin dake cike da kayan shafe-shafe ya hango gimbiyar tasa. Tayi wanka har taci ado cikin wani material daya haska kyakkyawar fatarta dake lashe maƙudan kudaɗe wajen gyarawa. Ɗan kwali take ɗaurawa yanzu..
         Hannayensa ya harɗe a kirji ya cigaba da takawa inda take idanunsa a kanta. Daga bayanta ya tsaya yana ƙare mata kallo ta cikin mirror ɗin. Shi shaida ne matarsa ƙyaƙyƙyawa ce data isa a kirata babbar mace. Ta haɗa abubuwa da yawa da tai zarra a cikin mata. Indai sirrin gyaran jiki ne da gayu da ƙwalisa a bar mata kayanta. Domin ta ɗauki babban kambu..
         “Kinyi ƙyau sosai Habibty”.
    Ya faɗa a hankali yana duƙowa kanta sosai. Baki ta taɓe, kamar bata jisa ba ta yinƙura zata tashi. 
      “Ina kuma zaki?”.
    “Inda ake buƙata ta”.
  “Nan ke nan?.” ya nuna kansa. 
Baki ta ƙyaɓe da faɗin, “Humm”.
       Ya murmusa kawai. Cikin sake kwantar da murya ya ce, “Kiyi haƙuri kiɗan bani lokacinki muyi magana. Bana son yaran nan su dawo su samemu a wannan yanayin da basu saba gani ba.”
     “Wace magana ce kuma ta rage tsakanin ni da kai Farouk? Kace zaka ƙara aure. Nace ban yarda ba. Kaga zaɓi na hannunka. Kana akan bakanka na sai ka ƙara ɗin, ni zanyi gaba. Ka janye zancen ka, mu cigaba da zaman mu yanda muke.”
        “Humm Deenah kenan. To naji, muje muyi maganar dai tukunna.”
     “Nifa gaskiya fita zan yi, zaka ɓata min lokaci”.
    “Wace fita kuma mijinki ya dawo gida. Kwana biyu fa bamuga juna ba. I want you by my side too”.
        “Kai dai faɗi wani abun ba wannan ba. Fita ta kuma tana da muhimmanci. Dan haka na baka minti ashirin”.
     Idanunsa ya ɗan zuba mata cikin tsoro da mamaki, dan ba haka matarsa take ba, kamar an canja masa ita a kwan biyu. Deenah ko makaranta zata ɗaukar yara idan driver nada uziri sai ta masa message ko kiransa. Kai ko baƙuwa tayi ya kama zata mata rakkiya sai ta kira shi a waya ko masa saƙo akan ta ɗan fita. Amma yanzu gashi randa ya dawo daga tafiya da in yayi a baya takan tarbesa kamar sarki ne take shirin fita ba tare da neman izinin sa ba ma....
       “Wai ko ka fasa ne?”.
  Ta katse masa tunani. Ajiyar zuciya kawai ya sauke da faɗin, “Bismilla mu zauna”.
       Kai a sama ta nufi sofa ɗin ɗakin ta zauna. Shima sai yabi bayanta ya zauna a gefenta............✍️