Sirrin baya
chapter 30️⃣
Sheikh Muhammad Kabir ya sauke numfashi.
Abin da ya faru da ni bai fara ranar da aka ce na mutu ba.”
Sabreen ta saurara.
Ya fara shekaru da suka wuce.”
Zayyad ya ce:
“Project Sabreen?”
Sheikh ya kalle shi.
Eh.”
Sabreen ta tambaya:
Menene Project Sabreen?”
Sheikh ya ce:
Ba aikin da na fara bane.”
“Su suka fara shi?”
Eh.”
“Me suke yi?”
Sheikh ya yi shiru na ɗan lokaci.
Sun kasance suna gudanar da wani ɓoyayyen bincike.”
“Bincike kan me?”
Kan yara.”
Sabreen ta ji sanyi ya ratsa jikinta.
Yara?”
Sheikh ya gyada kai.
Yaran da ba su da ikon kare kansu.”
Zayyad ya matse hannunsa.
Me suke yi musu?”
Gwaje-gwaje da abubuwan da bai kamata a yi wa ɗan adam ba.”
Sabreen ta rufe bakinta.
Abba…”
Shi ya sa na fara bincikensu.”
RANAR DA YA GANO GASKIYA
Da farko ban san girman lamarin ba.”
Sheikh ya ci gaba.
“Na yi tunanin wasu mutane ne kawai ke aikata laifi.”
Amma daga baya na gano cewa akwai manyan mutane a bayansu.”
“Mutane masu kuɗi.”
“Mutane masu iko.”
“Mutane waɗanda za su iya sa mutum ya ɓace ba tare da kowa ya tambaya ba.”
Zayyad ya tambaya:
Rabi tana cikin su?”
Sheikh ya kalli Zayyad.
Rabi ta taɓa kasancewa kusa da su.”
Ta yi aiki da su?”
“Eh.”
Amma daga baya ta juya musu baya.”
Sabreen ta tambaya:
Me ya sa?”
“Saboda ta gano gaskiyar abin da suke yi.”
RANAR DA AKA HAIFI SABREEN
Sheikh ya kalli Sabreen.
Ranar da aka haife ki…”
Ya yi shiru.
Abin da ya faru a ranar ne ya canza rayuwata gaba ɗaya.”
Sabreen ta saurara.
An haifi yara biyu.”
Sabreen ta sunkuyar da kai zuchiyar ta na bugawa jin ya ambaci yara biyu
Ni dawa abba .”
ke da yar uwarki abokiyar tagwaicinki
sosai zara tashiga mamaki haka Zayyad ma domin shi bashi da wannan labarin
Me ya sa aka raba mu?”
Sheikh ya yi shiru.
Saboda sun gano cewa ina da yara biyu.”
Zayyad ya tambaya:
Sun zo neman su?”
Eh.”
Me suke so da su?”
Sun so su ɗauke ɗaya daga cikinsu.”
Sabreen ta tambaya:Me ya sa?”
Sheikh ya ce:
Domin su saka ta cikin bincikensu.”
Sabreen ta ji hawaye sun cika idanunta.
Shi ya sa aka ɗauki Sumayya?”
Sheikh ya sunkuyar da kansa.
Eh.
Ka san inda aka kai ta?”
Na san inda aka kai ta a lokacin.”
Amma yanzu?”
Sheikh ya girgiza kai.
Ban san inda take yanzu ba.”
Sabreen ta share hawaye.
Amma tana raye?”
Sheikh ya yi shiru.
Abba!
Ban da tabbacin komai a yanzu.
DALILIN DA YA SA YA ɓACE
Zayyad ya tambaya:
“Me ya faru da kai bayan an ɗauki Sumayya?”
Sheikh ya ce:
“Na fara tara hujjoji.”
Na san ba zan iya yakarsu da ƙarfi ba.”
Saboda haka na tattara takardu, bidiyo, sunaye da bayanai.”
Na shirya fallasa su.”
Sabreen ta tambaya:
Shi ya sa suka nemi su kashe ka?”
Eh.”
Ranar da aka ce ka mutu…”
Sheikh ya gyada kai.
“Sun shirya kashe ni.”
Amma ka tsira?”
Rabi ta taimaka min.”
Zayyad ya ɗaga kai.
Shi ya sa na gan ku tare?”
Eh.”
Me ya sa ba ka kira ni ba?”
Sheikh ya kalle shi.
Saboda kana kusa da Sabreen.”
Zayyad ya yi shiru.
Idan suka gano cewa kana taimaka min, za su yi amfani da kai wajen kai mata hari.”
RANAR DA ZAYYAD YA GAN SHI
Sheikh ya kalli Zayyad.
Na san ka bi motar.”
Zayyad ya yi mamaki.
Ka sani?”
Na sani.”
Me ya sa ba ka tsaya ba?”
Saboda ina son ka gano inda takardar take.”
Takardar?”
Eh.”
Wadda na samu?”
Sheikh ya gyada kai.
Wannan takardar ita ce ɗaya daga cikin manyan hujjojin Project Sabreen.”
to be counted..
MISS NASIR ♥️✍️