BIN ALI

Chapter-06 (The Fisrt Step)💉✨

by @eshamuhd

Afeefa ta ɗan dakata na ƴan daƙiƙu, tana nazarin fuskar mahaifiyarta, tana ƙoƙarin gano ko akwai wata alamar shakku a idanunta. Umma kuwa ta maƙale hannayenta biyu a ƙirji, idanunta cike da tsantsar mamaki da ƙauna.

“Sauran kuɗin aikin duk gidauniyar ce ta biya,” Afeefa ta sake faɗa a hankali, muryarta na ɗan rawa yayin da take ƙoƙarin danne raɗaɗin ƙaryar da take yiwa mahaifiyarta. Dr. Farooq ya ce a ranar Litinin za a tura Rahma ɗakin fiɗa.”

Farin ciki ya bayyana a fuskar Umma, har hawaye suka cika idanunta. Nan take ta durƙusa a kan tabarmar, ta sanya goshinta a ƙasa tana yi wa Allah sujadar godiya. Kalmomin yabo, godiya da addu’a suka riƙa fita daga bakinta.

“Alhamdulillah! Ya Ubangiji, godiya ta tabbata gare Ka! Na gode maka da wannan babbar ni’ima…” Umma ta ɗaga kanta, tana share hawayen farin ciki da ke zuba mata. “Afeefa, ashe har yanzu akwai mutanen kirki a duniya? Allah Ya saka wa wannan mai kuɗi da alheri. Allah Ya ƙara masa buɗi da albarka a harkokinsa, Ya kuma saka masa da mafificin alheri!”

A lokacin da Umma ta ambaci “mai kuɗi” tana yi masa addu’a, zuciyar Afeefa taji wani irin ciwo. Ta san addu’ar mahaifiyarta ta fito ne daga kasan zuciyar Umma, amma hakan bai hana ta jin nauyin abin da ta ɓoye mata ba.

Wanida ita kaɗai ce ta san gaskiyar yadda kuɗin suka fito.

A safiyar ranar Litinin, asibitin City Care ya cika da hayaniya da shirye-shiryen aikin fiɗa.

Umma da Afeefa suna tsaye a wajen ƙofar ɗakin fiɗa (Operation Theatre), yayin da ma’aikatan asibitin suka tura gurney ɗin da Rahma ke kwance a kai. Fuskarta na ɗauke da wani ɗan murmushi mai rauni, saboda tasirin maganin barcin da aka ba ta.

“Yaya Afeefa… na gode,” Rahma ta faɗa cikin raunin murya, cike da barci, kafin ma’aikatan asibitin su tura ta cikin ɗakin fiɗar.

Tura ƙofar ke da wuya, Afeefa ta juyo ta kalli wata ma’aikaciyar asibitin da ta matso kusa da ita. A gefe guda kuma, Umma ta zauna a kan kujerar jiran aiki, tana ta jan tasbihi cikin nutsuwa.

“Afeefa,” Nurse ɗin ta faɗa muryarta a hankali. “Dr. Farooq yana jiranki a Private Laboratory. Ya sanar da ke tun ranar Asabar cewa da zarar an shigar da ƙanwarki ɗakin fiɗa, za ki fara matakin farko na aikin da da za’ayi miki.

Afeefa ta gyada kai a hankali. Wata sabuwar fargaba ta sake mamaye zuciyarta. Ta kalli Umma wadda ta maida hankalinta gaba ɗaya kan addu’a, sannan ta gyara hajabin ta bi bayan ma’aikaciyar asibitin. Bayan ta cewa Umma tana zuwa.

Suka nufi wani sashe na ginin asibitin, inda babu mutane da yawa, sai na’urorin tsaro da suka kewaye wajen. Dr. Farooq yana tsaye sanye da farar rigar likita, yana duba wasu na’urorin da ke cikin In Vitro Fertilization Lab (IVF Lab). Ya juyo ya kalli Afeefa da ta shigo. Babu wani farin ciki a tare da ita; sai damuwa da nauyin abin da ke gabanta.

“Barka da zuwa, Afeefa,” Dr. Farooq ya faɗa da murmushi dauke a fuskar shi. “Muna farin cikin sanar da ke cewa an shigar da Rahma ɗakin fiɗa, kuma komai yana tafiya lafiya.”

“Na gode, Doctor,” Afeefa ta amsa a hankali. “Shin… yanzu ne za a fara komai?”

“A’a, ba a yau za a yi dashen ba,” Dr. Farooq ya bayyana, yana miƙa mata wasu takardun da suka shafi aikin.

“Yau za mu fara ba ki magunguna da alluran shirya mahaifa (Hormonal Injections),” Dr. Farooq ya faɗa, yana nuna mata takardun da ke gabansa. “Za ki riƙa amfani da su na tsawon kwana uku zuwa biyar. Manufar ita ce a shirya mahaifarki yadda za ta kasance cikin yanayin da ya dace da karɓar embryo.”

Afeefa ta ɗaga idanunta ta kalle shi. “Embryo?” ta maimaita a hankali, kamar kalmar ta sauke mata wani sabon nauyi a zuciya. Dr. Farooq ya gyada kai.

“Eh. Wannan shi ne matakin farko. Da zarar an kammala shirye-shiryen da ake buƙata, sai mu duba yadda jikinki ya amsa abin kafin mu ɗauki mataki na gaba.” Afeefa ta mayar da kallonta kan allurar da ke saman teburin.

“Wannan ita ce allurar?” ta tambaya, muryarta na ɗauke da ɗan fargaba. “Eh,” Dr. Farooq ya amsa cikin natsuwa. “Ba za ki ji wani babban ciwo ba, kuma za mu riƙa kula da ke sosai a kowane mataki.”

Afeefa ta yi shiru.

Idanunta suka sake komawa kan allurar, sannan ta ja numfashi a hankali ta sauke.

A wannan allurar da ke gabanta, Afeefa ta ga farkon wata sabuwar tafiya—tafiya da ba ta san inda za ta kai ta ba, ko kuma irin abin da za ta fuskanta a ƙarshenta ba. Ta yi shiru na ɗan lokaci, tana kallon allurar kamar wata ƙaramar ƙofa ce da za ta buɗe mata hanyar shiga wata rayuwar da ba ta taɓa tunanin za ta rayu ba.

“Hakan yana nufin… shi mutumin ba ya buƙatar kasancewa a nan kwata-kwata?” Afeefa ta tambaya, tana kallon Dr. Farooq da ɗan fargaba, kamar tana neman tabbaci daga bakinsa.

Dr. Farooq ya yi murmushi kaɗan, yana kallon Afeefa cikin nutsuwa. “Bin Ali ya riga ya kammala duk abin da ya kamata a ɓangarensa tun kafin ki sanya hannu kan yarjejeniyar. Don haka ki kwantar da hankalinki. Ba sai kin haɗu da shi ba, kuma ba sai kin gan shi ba. Komai zai gudana ne a asirce, ta hanyar tsarin da muka tsara.”

“Komai zai gudana ne ta hanyar tsarin IVF surrogacy, ba tare da kun haɗu da juna ba.”Wata irin nutsuwa ta sauka a zuciyar Afeefa. Aƙalla, ba za ta fuskanci tsoron haɗuwa da mutumin da ba ta sani ba.

Amma duk da wannan sauƙin, akwai wani nauyi da har yanzu yake kan zuciyarta—sirrin da take ɓoye wa Umma da sauran mutanen da ke kusa da ita. Ta san cewa wannan sirrin ba ƙaramin abu ba ne, kuma wata rana gaskiyar na iya bayyana.

“Ina shirye, Doctor,” Afeefa ta amsa a hankali, tana miƙa hannunta domin karɓar allurar farko. “Ku gudanar da komai yadda kuka tsara.”

Dr. Farooq ya gyada kai, sannan ya karɓi allurar daga saman teburin.

Afeefa ta ɗan kawar da fuskarta gefe, tana jan numfashi a hankali. Duk da cewa ta yi ƙoƙarin nuna ƙarfin hali, zuciyarta cike take da fargaba.

A wannan rana, yayin da Rahma ke kwance a ɗakin fiɗa, Afeefa kuma ta fara wata sabuwar tafiya—tafiyar da ta shiga ne saboda ƙaunar da take yi wa ƙanwarta.

Amma abin da ba ta sani ba shi ne, wannan ƙaramin matakin da ta fara a yau zai iya sauya rayuwarta gaba ɗaya. Sirrin da ta ɓoye wa Umma ya fara ne da ƙarya guda ɗaya…

Kuma ba ta san irin farashin da za ta biya ba idan gaskiyar ta fito ba…


Follow My Account For More Update’s🌹