Chapter-07 (The First Clue)👀🔥
by @eshamuhd
Kwanaki uku da suka kasance tsakanin nasarar aikin Rahma da matakin ƙarshe na dashen cikin sun kasance daga cikin kwanakin da suka fi tsayi da wahala a rayuwar Afeefa.
A duk lokacin da ta kalli fuskar ƙanwarta tana samun sauƙi a hankali a kan gadon asibiti, zuciyarta kan cika da godiya ga Allah. Aƙalla, aikin ya yi nasara, kuma Rahma tana fara farfaɗowa. Amma duk lokacin da Nurses suka zo yi mata alluran shirya mahaifa (hormonal treatment), wani nauyi kan sake sauka a zuciyarta.
Sai ta tuna da yarjejeniyar da ta sanya hannu a kanta. Ta tuna da kuɗin da aka biya domin ceton Rahma. Ta tuna da ƙaryar da ta yi wa Umma.
A wannan lokacin, farin cikin ganin Rahma tana samun sauƙi kan haɗu da tsoron abin da ke gabanta. Ta san cewa saura kaɗan ne ta shiga matakin da zai iya sauya rayuwarta gaba ɗaya.
Ranar Alhamis ce ranar da Dr. Farooq ya tsara domin gudanar da ainihin Embryo Transfer. Sanyin ɗakin gwaje-gwajen sirri na City Care ya cika wajen, yayin da sautin na’urorin likitanci ke tashi a hankali.
Afeefa tana kwance a kan gadon gwaji, sanye da doguwar rigar asibiti mai sauƙi. Idanunta na akan rufin ɗakin, yayin da ta dunƙule tafukan hannayenta biyu a kan ƙirjinta. Zuciyarta na bugawa da sauri.
Ta san abin da ke gabanta ba ƙaramin abu ba ne. Wannan shi ne matakin da yarjejeniyar da ta sanya hannu a kai za ta fara zama gaskiya a jikinta.
Ta lumshe idanunta na ɗan lokaci, ta ja dogon numfashi, tana ƙoƙarin kwantar da hankalinta.
A cikin zuciyarta, ta tuna da Rahma. Ta tuna da Umma. Sannan ta tuna da sa hannun da ta sanya a kan yarjejeniyar.
Afeefa ta buɗe idanunta a hankali.
“Ya Allah…” ta furta a ƙarƙashin numfashinta. “Ka sa abin da nake yi ya zama alheri.”
Dr. Farooq da wata babbar ma’aikaciyar asibiti da aka amince da ita ne kaɗai suke tsaye kusa da Afeefa. Dukansu suna sanye da rigunan kariya na likitoci, yayin da suke shirye-shiryen fara aikin.
“Afeefa, ki kwantar da hankalinki,” muryar Dr. Farooq ta fito cikin sanyin murya da girmamawa. “Wannan mataki ne mai sauƙi, kuma ba ya buƙatar a yi wani fiɗa ko kuma ki ji wani babban ciwo. Za mu yi amfani da wata siririyar na’ura wajen shigar da embryo ɗin zuwa mahaifarki. Komai zai gudana ne a hankali, kuma za mu kula da ke sosai.”
Afeefa ta rufe idanunta a hankali, tana karanta addu’o’in neman kariya a cikin zuciyarta. Tana jin motsin na’urorin da likitocin ke sarrafawa, amma abin da ya fi komai nauyi a gare ta shi ne tunanin abin da ke shirin faruwa.
Wani ɓangare na halittar mutumin da ba ta taɓa gani ba, wanda ba ta san fuskarsa a zahiri ba ko ma sautin muryarsa ba, yana shirin samun muhalli a cikin jikinta.
Ta haɗiye yawu, zuciyarta tana bugawa da sauri. Wannan shi ne karo na farko da ta fahimci cewa abin da ta sanya hannu a kai ya kusa zama gaskiya a jikinta.
Bayan mintuna goma sha biyar na natsuwa da amfani da fasahar zamani, aikin ya kusa kammala. Afeefa har yanzu tana kwance a kan gadon gwaji, idanunta a rufe, tana jiran Dr. Farooq ya sanar da ita cewa komai ya kammala lafiya.
“Alhamdulillah. An kammala,” Dr. Farooq ya faɗa, yana cire safar hannunsa ta roba. Ya juyo ya kalli Afeefa wadda har yanzu take kwance a kan gadon gwaji.
“Duk abin da ake buƙata an kammala shi lafiya a yau. Yanzu za ki kwanta a nan na tsawon sa’o’i biyu domin ki huta. Bayan haka kuma, daga yau za ki ci gaba da amfani da magungunan da za su taimaka wajen tallafa wa mahaifarki da kuma ci gaba da aikin da muka fara.”
Afeefa ta yi shiru, tana sauraron sa. A zuciyarta kuwa, ta san cewa rayuwarta ta fara shiga wani sabon mataki.
Afeefa ta buɗe idanunta a hankali, waɗanda suka cika da ruwan hawaye. Ta kalli Dr. Farooq, sannan muryarta ta fito a kausashe, amma a hankali. “Shi ke nan, Doctor?”
“Shi ke nan, Afeefa,” Dr. Farooq ya amsa cikin sanyin murya mai ɗauke da tausayi. “Daga nan kuma, sauran aikin halitta ne da ikon Allah. Nan da kwana goma zuwa sha huɗu, za mu yi gwajin jininki na farko domin tabbatar da ko an samu ciki.”
Afeefa ta yi shiru, hawaye na taruwa a idanunta. Ta juya kanta gefe, tana ƙoƙarin sarrafa abin da ke yawo a zuciyarta…
A gefe guda kuma, a can saman ginin Bin Ali Holdings, yanayin ya kasance daban.
A babbar sakatariyar kamfanin, komai yana tafiya cikin tsari, amma akwai wani abu da ke shirin sauya yanayin ranar gaba ɗaya.
Aliyu Bin Ali yana zaune a kan ƙasaitacciyar kujerarsa, cikin nutsuwa. Kansa a sunkuye yake, idanunsa na kan screen din laptop ɗinsa, yana karanta wasu bayanai cikin tsanaki. A cikin ofishin kuwa, shiru ya mamaye wajen, sai sautin sanyin air conditioner da kuma ɗan motsin yatsunsa a kan madannin kwamfutar.
Sautin buɗe ƙofa ya san ya shi ɗaga idanunsa kaɗan. Taufeeq ne ya shigo cikin ɗakin, yana ɗauke da wani file a hannunsa. Ya tsaya na ɗan lokaci kafin ya rufe ƙofar, sannan ya nufi inda Aliyu yake zaune.
Taufeeq ya ajiye file din dake hannun shi a kan teburin Bin Ali, sannan ya tsaya yana kallonsa cikin nutsuwa.
“Dr. Farooq ya aiko da sakon tabbatarwa,” Taufeeq ya faɗa yayin da ya zauna a kujerar da ke fuskantar Bin Ali. “An kammala Embryo Transfer ɗin yau. Komai ya tafi daidai, kuma babu wata matsala a ɓangaren lafiyarta.”
Bin Ali bai nuna wani farin ciki ko canjin yanayi a fuskarsa ba. Har yanzu yana cikin nutsuwarsa, fuskarsa a sanyaye, kuma yanayinsa cike da izza. “Yaya batun tsaron ta?” Bin Ali ya tambaya cikin sanyin murya.
“Muka shirya komai,” Taufeeq ya amsa da sauri. “A yanzu ba sai mun tura ta ko iyalinta wani wuri ba, sai dai mu jira sakamakon gwajin bayan makonni biyu. Amma na tura mutane biyu da na yarda da su su riƙa kula da su daga nesa, domin tabbatar da tsaronsu daga duk wata matsala ko maƙiyi.”
Bin Ali ya gyaɗa kai kawai yana cigaba da abinda yake yi.
“Good. Ba na son wani kuskure ko sakaci ya faru daga ɓangaren ma’aikata ko asibiti. Kuma ka tabbatar duk kuɗin abincinta da magungunanta ana biyan su ne ta asibitin, ba tare da an bayyana sunana ba.”
“Za a yi yadda ka umarta, Yallabai,” Taufeeq ya amsa…
A gefe guda kuma, can cikin wani tsohon filin ajiye motoci, wani abu daban ne ke shirin faruwa.
Bello wanda Hajiya Halima ta ɗauka aiki—yana tsaye kusa da motarsa. Yana kallon wasu hotuna da aka turo masa a wayarsa, yana nazarin kowanne daga cikinsu a hankali.
Hotunan sun nuna Lauya Taufeeq yana shiga da fita daga asibitin City Care a ranaku daban-daban. Wasu hotunan kuma sun nuna Afeefa tana fitowa daga ɓangaren sirri na asibitin tare da wasu ma’aikatan asibitin.
Bello ya ƙara matso da wayarsa, yana kallon hotunan ɗaya bayan ɗaya. Wani ɗan murmushi ya bayyana a fuskarshi.
“Na sani akwai wani abu,” ya furta a hankali.
Ya sake kallon hoton Afeefa, sannan ya kalli hoton Taufeeq. “Amma menene suke ɓoyewa?”
Bello ya danna lambar Hajiya Halima, ya kai wayar kunnensa. “Hajiya… akwai sabon labari,” Bello ya faɗa bayan hajiya Halima ta ɗaga wayar. “Lauyansa, Taufeeq, ya kwashe kwanaki yana shiga da fita daga ɓangaren sirri na asibitin City Care. Kuma ba shi kaɗai ba ne. Akwai wata yarinya daga wata unguwar talakawa, wadda muke yawan ganin tana fita daga wannan ɓangaren na asibitin itama.”
Ya ɗan yi shiru, sannan ya ƙara da cewa:
“Har yanzu ba mu san ko wacece ita ba, amma ina ganin akwai wani abu da suke ɓoyewa.”
A ɗayan ɓangaren, Hajiya Halima ta gyara zamanta a kan kujerarta. Idanunta suka ƙanƙance, cike da zargi da mugun shiri “Hmm…” ta furta a hankali.
“Yarinya daga unguwar talakawa?” Hajiya Halima ta tambaya cikin mamaki. “Bin Ali ba ya mu’amala da mata. To me zai haɗa lauyansa da zirgar-zirgar asibiti, tare da wata yarinya daga unguwar talakawa?”
Ta yi shiru na ɗan lokaci, sannan ta ce:
“Bello, ina son ka gano min wace ce wannan yarinyar, da kuma abin da suke ɓoyewa a wannan asibitin. Ina jin akwai wani abu da suke boyewa a nan asibitin… kuma ina ganin wannan ne zai iya zama farkon matsalar Bin Ali.”
Follow My Account For More Update’s🌹
Esha muhd
***