Chapter-08 (The Secret That May Be Expose)😳🔥
by @eshamuhd
A cikin ƙasaitaccen gidan da ke kewaye da kyakkyawan lambu, Hajiya Amina mahaifiyar Bin Ali wadda kowa ke kira Ammie tana zaune a kan kujera. Fuskarta cike take da damuwa. Abu ɗaya ne kawai ya fi damunta a wannan lokaci: tana matuƙar son ganin jika kafin kwanakinta su ƙare.
Bayan rasuwar mijinta, Bin Ali ne kaɗai ya rage mata a matsayin ginshiƙin farin cikinta. Shi ne ɗanta tilo, shi ne abin da zuciyarta ta ke matukar so.
Amma yadda yake nisantar mata, yana mai da hankalinsa gaba ɗaya kan kasuwancinsa, ya zama wani abu da ke yawan raunana zuciyarta. Duk da irin ƙaunar da yake yi mata, akwai wani abu da take matuƙar so daga gare shi—ta ga jikanta kafin lokaci ya kure mata.
Sautin takunsa ya sa Ammie ta ɗaga kai ta kalli ƙofar. Bin Ali ya shigo cikin falon cikin nutsuwa da kwarjini, sanye da baƙin kaya masu sauƙi. Fuskarsa a sanyaye take, kamar yadda ya saba.
“Barka da yamma, Umma,” ya faɗa cikin girmamawa, yana dukawa har ƙasa domin gaishe ta.
Ammie ta ɗaga idanunta, ta kalle shi daga sama har ƙasa. Amma maimakon ta amsa gaisuwar tashi da murmushi, sai ta ƙara haɗe fuska, ta kawar da kai gefe. “Hmm…” kawai tace ba tareda tace komai ba, saida ta nisa kafin ta kira sunan shi.
“Aliyu…” ta kira sunansa a hankali, muryarta cike da gajiya da halin shi. “Gaisuwarka ba za ta sa zuciyata ta yi farin ciki ba, idan har kana ci gaba da barin na cikin wannan baƙin cikin na jiran abu guda da na fi so a rayuwata daga gare ka.”
Bin Ali ya haɗiye yawu a hankali, sannan ya zauna a kan kujerar da ke kusa da ita. Ya san abin da Ammie ke magana a kai. Wannan ba sabon zance ba ne a gare shi.
“Ammie, mun yi wannan maganar a makon da ya gabata,” ya faɗa cikin very calm voice, ba tare da wata damuwa a fuskarsa ba. “Ina gudanar da dukkan harkokin kasuwanci ne domin kare ku da kuma kiyaye mutuncin sunan mahaifina…”
“Ban tambaye ka kuɗi ko mulkin Bin Ali Holdings ba, Aliyu!” Ammie ta katse shi, tana ɗaga hannunta yayin da hawaye suka fara taruwa a idanunta. “Dukiya da mulki ba sa mayar da mutum uba. Kusan shekaru arba’in kenan da kake a duniya, amma ba ka da mata, ba ka da yaro. Abokan mahaifinka, kowa yana yawo da jikokinsa a gabansa, amma ni? Ranar da na mutu, ba zan bar wa duniya wani abu da ya fito daga jininka ba!”
Bin Ali ya sunkuyar da kansa ƙasa, hannayensa biyu a dunƙule. Shi kaɗai ya san nauyin secret ɗin da yake ɗauke da shi a zuciyarsa.
Ya kuma san cewa duk tsarin da yake gudanarwa a private clinic ɗin nan, duk saboda abu guda ne ya samu wannan jikan da Ammie ke nema, ba tare da ya kawo wata mace cikin rayuwarsa ba, ko kuma ya jefa kansa da ita cikin haɗarin maƙiyin da ke kewaye da su.
“Ni ba ruwana da kuɗinka!” Ta sake katse shi, tana kallon cikin idanunsa. “I need a grandchild, Aliyu! Idan har kana son farin cikina da samun albarkata, kayi aure na samu jika! Muddin ba haka ba…” Ta yi shiru na ɗan lokaci, sannan ta ƙara da kakkausar murya, “Ka daina takowa inda nake da batun kasuwancinka.”
Bin Ali ya yi shiru na few seconds, fuskarsa ba ta nuna wani sauyi ba. Bai ce komai ba, sai ya miƙe tsaye a hankali, ya sunkuyar da kansa cikin girmamawa.
“Zan yi miki biyayya, Ammie.” Ya ɗan yi shiru, sannan ya ƙara da very calm voice, “You will get what your heart desires… sooner than you think…”
A gefe guda kuwa, bayan tsawon kwana sha huɗu cif (two weeks)...
Afeefa tana tsaye a cikin ƙasaitaccen private consultation room na asibitin City Care, fuskarta jawur saboda matsananciyar anxiety da fargaba. Sanye take da hijabinta mai kalar soft grey, tana matse yatsun hannunta guda biyu.
Dr. Farooq yana tsaye a gabanta, yana riƙe da takardar sakamakon pregnancy blood test na ƙarshe da aka gudanar.
Taufeeq shi ma yana tsaye a gefe, fuskarsa cike da serious concern da idanunsa, Ya san cewa abin da ke cikin wannan takarda na da matuƙar muhimmanci ga makomar Bin Ali da kuma Bin Ali Holdings gaba ɗaya.
Dr. Farooq ya duba takardar, sannan ya ɗaga kansa tare da sakin wani ƙasaitaccen murmushin dake nuna samun nasara.
“Alhamdulillah…” Dr. Farooq ya faɗa cikw da murna. “Afeefa, our IVF procedure was a 100% success! Gwajin ya tabbatar da cewa… kina ɗauke da ciki na exactly two weeks!”
Afeefa ta taka baya kaɗan, tana jin kamar she couldn’t breathe. Hannunta ya sauka a hankali saman cikinta wanda har yanzu babu wani alamun a kwai ciki a tareda ita.
Wani irin tsoro da firgici suka mamaye zuciyarta, hawaye na taruwa a idanunta ba tare da ta iya hana su ba.
A ƙarshe… yarjejeniyar da ta sa hannu a kai ta zama gaskiya. Tana ɗauke da cikin mutumin da ba ta taɓa gani ba.
Taufeeq ya sauke numfashin da ya daɗe yana riƙewa, sannan ya ciro wayar sa da sauri. Ya danna lambar Bin Ali, ya kai wayar kunnensa, yana jiran ya ɗaga.
“Boss…” Taufeeq ya faɗa lokacin da Bin Ali ya ɗaga wayar, cikin muryarsa ta natsuwa. “The test results are out. Everything went according to plan. Afeefa is officially pregnant with your child.”
A ɗayan ɓangaren kuma, a cikin penthouse office ɗinsa, Bin Ali ya yi shiru na wasu daƙiƙu yana sauraron muryar Taufeeq daga ɗayan ɓangaren wayar. Fuskarsa ba ta nuna murna sosai ba, amma idanunsa sun lumshe a hankali, cike da deep satisfaction.
Ya ɗaga idanunsa zuwa hoton mahaifiyarsa da ke jikin bangon ofishin. Ya ɗan tsaya yana kallon hoton na wasu daƙiƙu. At last, his legacy was safe. Kuma shirin da ya daɗe yana ginawa ya fara zama gaskiya…
AFEEFA..
Sanyin safiyar ƙarfe bakwai bai iya sanyaya fargaba da firgicin da ke ci gaba da ƙaruwa a tsakar gidan su Afeefa ba.
Afeefa tana tsaye a gaban ƙaramin madubin da aka manna a bangon ɗakinsu, tana ƙoƙarin ɗaura ɗankwalin atfarta. Hannayenta na rawa sosai sakamakon matsananciyar morning sickness da gajiyar jiki data tashi dashi.
Duk lokacin da ta rufe idanunta, sai ta ji wani irin jiri mai nauyi yana neman kayar da ita a ƙasa.
"Afeefa... lafiya kuwa kike?"
Muryar Umma da ta shigo ɗakin sanye da hijabi ta katse mata tunani. Umma ta kafe ta da ido, fuskarta cike da concern da tsantsar nazari.
“Wannan wane irin zazzabi ne da bai son ƙarewa? Tsawon kwana uku kenan, kullum da safe sai kin fito fuskarki a jawur, ba kya iya cin abincin kirki. Ko dai muje wani Sadi mai chemist ne ya duba ki?”
Afeefa ta yi saurin goge fuskarta da dan kwalin da take kokarin daurawa, sannan ta saki murmushin ƙarfin hali domin kawar da zargin da Umma ke yi…
Follow My Account For More Update’s🌹
ESHA MUHD
***