KINCI DUBU.....

1-2

by @oumhairan1

*KINCI DUBU......*
_(Uwargida me capacity)_


*Oum Hairan*


*Page 1-2*

Hauwa'u kiyi hakuri bawai ina nufin kin  kasa bane kawai dai naga ɗawainiyar gida da yara tayi Miki yawa har ta fara ɗauke Miki hankali daga kulawa dani Shiyasa nake kallon aure a matsayin hanyar da kowa zai samu salama Ni da ke  Kinga idan na samu wacce bata da nauyin komai zata bani lokacinta ta kula Dani kema zaki huta da ƙorafi na" cewar Ibrahim dake zaune bisa gadon yana fuskantar matarsa Jiddah da ke zaune ta haɗe kai da gwiwa tana wani irin kuka me ban tausayi, tunda ya fara maganar sai yanzu ta ɗago tace “Kace ba wai don na gaza bane zaka kara aure kuma a cikin kalamanka kace na rasa lokacin kulawa dakai IB yaran nawa guda biyu sune suka sa kake ganin na gaza Meyasa idan wani abu kake buƙata wanda ban fahimta ba bazaka zaunar Dani ka sanar dani don na gane na gyara ba sai ka yanke shawarar shigo da wata cikin rayuwar da muka shafe shekaru muna ginata ba tare da ita ba, Meyasa memakon ƙarin aure ba zamu nemi wata maslahar ba? IB har yanzu samunka bai kai wanda zaka ƙarawa kanka nauyi ba Dani da ya'yan da muka haifa har yanzu ba yanda ranka takeso kake riƙe damu ba ko kana mantawa rayuwa kukeyi 60/40 a gidan nan yanzu kana tunanin yin aure shine mafitarka? IB kana da kuɗin aure aka koro Jannah daga School amma ka kasa biya mata....." 
Ɗaga mata hannu yayi cikin faɗa yace dakata Jiddah ba fa na faɗa Miki zan ƙara aure ne don ki zauna kina zayyanomin matsaloli ba gaskiyar magana ita ne Ni inason Aure ne ba wai don bana sonki ba a'a kina kokari amma Jarabar neman kuɗinki ta hana ki bani lokaci yanzu Yaushe rabon da na zauna a gidan nan da rana ki samu lokacin da zakizo ki kula Dani?  yaushe rabon da da daren ma ki bani damar na kusanceki so uku haka? Haba don Allah ku mata Meyasa kuke da son kanku ne to Gsky kiyi hakuri kuɗin auren Atika an riga an kaisu tun wata biyar baya yanzu haka bikin saura wata biyu" Zuciyarta ce ta buga da ƙarfi tace “Wata biyu IB amma sai yanzu zaka faɗamin?" cikin isa ya juya ya kwanta yana jan bargo yace yanzu naga damar faɗa" Wani Murmushi tayi me ciwo Ta yunƙura ta mike cikin sanyin murya me rawa tace “Allah yasa maka albarka a aurenka Ibrahim yasa Abokiyar Arziƙinka ce" tana faɗin haka ta juya da nufin ficewa daga ɗakin domin idan taci gaba da kallon fuskar Ibrahim zata iya shiga sahun matan da labaran su ke trending a media cewa ta kashe mijinta, Amma maimakon ya barta ta tafi sai ya mike ya kira sunanta da wata murya me rauni ta tsaya Cak tana sauke ajiyar zuciya wani kuka yana ƙoƙarin ƙwace mata ya tako ya shige bayanta ya ɗora hannunsa a kunkuminta yace “Kiyi hakuri Jiddah Har abada baki da tamka a cikin matan duniya wlh Aure na da Atika ƙaddara ce kawai ba soyayya ba amma duk wata soyayya na gama mallakawa Hauwa Kuluwa ta ke kaɗai ke mulkin zuciyar IB ɗinki don Allah kar maganar nan tasa ki juya min baya kinji"...........



*for more Info....*
*****

*OUM HAIRAN*