3-4
by @oumhairan1
*KINCI DUBU.....*
*_(Uwargida me capacity)_*
*Oum Hairan*
*page 3-4*
Shigewa tayi jikinsa wani Marayan kuka ya ƙwace mata da tun ɗazu take gudun fitowarsa amma q wannan lokacin bazata iya hana kukan kwacewa ba, Matseta yayi sosai zuciyarsa na bugawa da ƙarfi ya Dagata Cak ya ɗorata a gadon ya kwantar da ita yasa harshensa yana lashe Hawayen ta a sanyaye yace “Bantaɓa zama silar kukanki ba Jiddah don....don Allah ki daina wlh zuciyata zata iya bugawa da ganin hawayenki Please Jiddah don girman Allah kiyi hakuri ki fahimceni Kinsan Ni ba me burin cutar dake bane kuma wlh babu yanda Zanyi ne Bazan iya cewa da mahaifina Bazan auri Atik......" Rufe masa baki tayi Jikinta yana tsuma ta Tureshi tace “Don Allah Ibrahim don girman Allah kayimin shiru da maganar wannan yarinyar kaje Kayi aurenka ai na riga na gane kuma na fahimci duk abinda kake so na gane kuma na gode saidai ka sani Indai Ni Hauwa'u haihuwar Isma'il da Mariyatu ce Bazan ƙara maka magana akan aurenka ba kuma Banson jin komai daya shafe shi kazalika haƙƙoƙina dana ƴaƴana daka sakarmin ka dauki abinka ko kuma na Barka da wanda yasan gaibu Ibrahim kanada kuɗi mugunta ce tasa kake sakarmin ragama ashe kuɗin aure da lefe kake haɗawa babu komi kanka kayiwa ba Hauwa ba"......
Fuuuuu ta fice daga ɗakin ya mike ya bita da sauri amma ko kafin ya kai bakin ƙofar ta datse ta zube a jikin ƙofar ta rushe da kuka tana furta “Innanillahi wa inna Ilaihirraji'un" Addu'o'i kala kala takeyi daƙyar ta samu sauƙin bugawar da zuciyarta takeyi taja ɗuwawunta ta koma gefen gadon ta kifa kanta ji take kamar tayita kurma ihu a gidan tunda take a duniya bata taɓa tunanin wannan ranar zata zo gareta ba a yanda suke rayuwa da IB iyakar saninta ko waya bata taɓa ji yayi da wata mace ba yar uwarsa ba amma yau shine yake kallon tsabar Idsnunta yake ce mata ta gaza zai kawo wata ne saboda bata kulawa dashi?......
A wannan daren Jiddah kasa runtsawa tayi shi kansa IB ranar kwanan zaune yayi yana jin a ransa kamar ya fasa auren saidai idan ya tuna lokacin da ya kwararo yana shirye shiryensa cikin sirri da kuma yanda Atika ta mutu a kansa sai yaji bai kamata ya Rusa burinsu na mallakar juna ba musamman yanda Atika ke bashi kulawa da alƙawarin ninkin ta yanzu idan sunyi aure gani yake zai samu wacce tafi wadda Jiddah take bashi amma kuma Itama Jiddah tanada wani muhimmaci na musamman a cikin rayuwarsa wanda Allah ya jarabceshi da ko kaɗan baya son ɓacin ranta musamman da yasan itan mace ce me hakuri da kawaici Da yawan abun da kake tunanin ya isa kallo a wajen Jiddah baikai ba takan kalli abubuwa da fuskar nazari da tunani tare da yanke musu hukunci bisa adalci amma meyasa yanzu taƙi fahimtarsa? Meyasa ta yanke hukuncin Barshi shi kaɗai a wannan daren da yaci burin samun kulawarta da tarairayarta bayan shafe kwanaki kusan biyar basa tare? Iska ya furzar shi kam Allah yayisa wani irin namiji ne da Indai ya buƙaci kwanciya da Jiddah duk inda yake to sai ya waiwayo gida bare kuma yana gidan tare da ita to amma ta ina zai fara rarrashin gimbiyar tasa bayan ya riga yasan halinta sarai tunda ta bore masa saidai ya barta ta sauko dan kanta, da wannan ya shiga bathroom ya zare doguwar rigar jikinsa ya kama Ak tasa da ta miƙe sosai yana shafawa a hankali wani kwaɗayi da sha'awar matarsa na sake bijiro masa saidai a wannan lokacin dole ya daure ya haɗiye maitarsa kar ya cika takurawa Hauwa tayi masa tawaye yasan baƙin kishinta sarai akansa gashi yazo mata da abu mafi munin da take yawan faɗa masa tana tsoron ranar da zaizo, baya mantawa ko ranar da zai tafi Kwatono data rakashi suka rungume juna tayi kissing nashi tare da shafa fuskarsa tace “Kullum idan na tuna wataran zaka iya zuwa kace zaka ƙara aure mu zama mu biyu muka mallakeka Sweet sai Naji dama na mutu kafin ranar".........
_Kar sunan labarin ya firgita ku Amare Kuzo ayi daku zaku ƙaru domin wataran kune iyayen gidan_
*PAID BOOK REGULAR 400, VIP 800 VIA 9031307566 FAUZIYYA TASIU UMAR OPAY SHAIDAR BIYA TA ****
*For more Info....*
*****
*OUM HAIRAN*