Chapter 7-8
by @momislam11
💋💋💋💋💋💋
*TAƘAITACCEN SIRRI*
💋💋💋💋💋💋
Funny😂 Love💖 and Romantic 💋
Mom Islam
_Nace ba, wannan littafin yana ɗauke da darussa da yawa, ban dariya soyayya mai sanyi da tsayawa arai, gwagwarmaya tare da sadaukarwa💫_
Page 7-8
Bakinsa na rawa ya durƙushe a gurin cikin tausayin Ammu yace "kiyi haƙuri Yaya Amina wlhi tallahi ko sauyin fuskar da kikaga nayi Inna ce ta sa ni dan Allah ki koma gidanki anan gidan ba zaki samu ba"
Ammu ta share zafafan hawayen dake ta faman sintiri a saman kumatunta, cikin zafin rai da nadamar zuwanta gidan ta tona asirin cikinta, cikin Muryar kuka tace "wlhi tallahi Inna ki sauya hali kafin mutuwa ta riskeki.." daga faɗar haka ta juya ta fice da sauri, dan bata san taci gaba da kasancewa a cikin gidan tana ƙunsar baƙinciki.
Da sauri Inna ta janyo mayafi zata fice, yaya Usman yai saurin shan gabanta, cikin faɗa da nuna tsantsar tsanar Ammu tace "Usman wlhi tallahi idan baka bani hanya na wuce ba zan saɓa maka, "haba Inna kiyi haƙuri mana dan Allah, wannan ƙiyayyar da kike nunawa Ammu sam bata da amfani, baki da tabbacin mu a wane hali zamu kasance, shin zaki rayu damu ko kuma mu zamu rayu dake Allah shine masani, Yaya Usman ya faɗa ransa a ɓace.
Inna ta bangajeshi gami da cewa "Allahu Akbar ashe ka fara wa'azi ban sani ba?, ai sai kacemin bakinku ɗaya da ita, nidai ina ƙara gaya muku ko bayan raina duk wanda ya taimakawa yarinyar nan wlhi Allah ya isa ban yafe muku ba"
Dukkansu suka buɗe baki sbda ada sun ɗauki abin kamar ba har ƙarƙashin zuciyarta take faɗa ba, yanzu kam sun tabbatar da gaskiyar zance.
Ammu na komawa gida ta samu Hakeem na zaune a tsakar gida Ahlam na kwance a saman cinyarsa tayi barci, lokacin ƙarfe 12:pm na rana, Ammu tayi sallama ta ƙara so, Hakeem na ganinta ya fara yunƙurin miƙewa tare da ɗaga Ahlam yana cewa "Ammu an dace kuwa?"
"Hakeem ina aka dace kai duniyar nan da kake gani idan baka dashi ka zamo banza, nidai abinda nakeso dakai ka guji ɗaukar kayan da ba naka ba, sannan ka tausaya min Hakeem, Ammu ta faɗa tana fashewa da kuka, shima kukan yakeyi, ta karɓi Ahlam ta shigar da ita ɗaki, a ranar sam ta kasa taɓuka komai jikinta yayi sanyi sosai, ga tunani iri iri da suka addabi zuciyarta, kiran sallahar Azhar da akayi yayi daidai da farkawar Ahlam daga barci. "Yunwa nakeji Ammu.." Ahlam tai maganar cikin shagwaɓe murya,
Cikin yanayi na damuwa Ammu ta buÉ—e baki zatayi magana kenan...
Gabaki ɗayansu hankali a tashe suka miƙe cak Ammu ta dafe ƙirji, sakamakon kwaɗa sallama da ake ta yi babu ƙwauƙwautawa, "munshiga uku Ammu" Hakeem ya faɗa yana wulli wulli da idanu, kafin Ammu ta yi yunƙurin furta kalma ɗaya sukaji wasu mutane sun faɗo cikin gidan suna cewa "ku shiga kuga gidan" wani mutumi na gefen mai maganar shikuma yana cewa "nifa banason ɓata lokaci idan da ace kunbi zaɓina da gobe gobennan zansa azo a fara gyare-gyaren gidan" a kiɗime Ammu tace "Haba dan Allah ya zaku faɗo mana gida babu neman izini bare ma kuyi sallama?" Mutumin da ya fara magana daga farko yace "kinga baiwar Allah kiyi haƙuri mijinki ya riga da ya mutu, sannan kuma yabar basusuka, munan da kike gani taimakonsa muke yi saboda ya samu ya kwanta a kabari cikin salama, "hakane amma tozarci bashi da daɗi idan muka bar wannan gidan ina zamu?" Ammu tai maganar zuciyarta na ƙuna.
"Idan muka gama ciniki zan ware miki kuÉ—in da zaki kama haya, amman adalci nayi miki da"
Wanda aka kira ya siyi gidan ya faÉ—a yana wani É—age wa Ammu gira.
Sai da suka leƙa ko ina kafin sukayi mata sallama tare da ce mata sun bata nan da kwanaki goma ta tattara kayanta,
Sosai Ammu ta zubar da hawaye, tashi É—aya mutuwar Baba ta dawo mata sabuwa fil,
"Ammu dan Allah ina dangin Baba suke naga baki taɓa zuwa ba, kuma shima lokacin da yake raye ban taɓa ji yace zai je ba"
Hakeem ya watso mata tambayoyin da kunnuwanta suka tsaya da saurarar komai har na tsawon lokaci,
Sai da ta sauke gwauron numfashi kafin tace "Hakeem kenan, ka manta da abinda marigayi babanku ke gaya muku kullum?"
Hakeem yace "Ammu nasan dai yana ce mana mu guji abin hannun mutane sannan mu tsayar da gaskiya"
"Huhmm" Ammu tayi murmishin yaƙe wanda yafi na kuka ciwo kafin tace "mahaifinku Maraya ne, shikaɗai iyayensa suka haifa, baban mahaifinku ruwa ne ya tafi dashi, bayan an samo gawarsa ciwon zuciya ya kama mahaifiyarsa wanda ya zamo ajalinta har lahira, bayan rasuwarta mahaifinku ya shiga tashin hankali tare da fuskantar tsana daga dangin mamansa da babansa, akan wani dalili".
Sai kuma Ammu ta fashe da kuka,
"Ammu kinyi shiru dalili kuma?"
Hakeem ya tambaye ta sbda ya shiga ruÉ—u sosai.
"Kaf ilahirin mutanen ƙauyen sun tsani mahaifiyarsa wai tana da kambun baka, gaskiya wannan ƙarya ne dan kuwa banga wanda ya taɓa kamawa ba, dalilin yasa bayan mahaifinku ya girma yakai munzalin aure yayi aureni"
Hakeem zai yi magana Ammu ta dakatar dashi,
Kana tace "nasan zakace mai yasa aka bashi aurena ko?"....!