1
NOOR 🤍
Book 1.
By maryam nababa
(Writer of Tawa rayuwar)
Page 1.
The beginning
#A love story
#Brokenheart
#villains
#cultism
#Adventure
Betrayal
Bismillahir rahmanir rahim
Wani irin daki ne daya kasance mai tsananin duhu da ko tafin hannunka ba lallai ka iya gani ba, musamman idan yanxu ka shigo ciki, wani tsoho ne saman kujerar bakin karfe wanda yake lullube da bakin kaya, hatta da fuskarsa bata fito ba gabansa wani teburin bakin karfe ne dogo dayake dauke da wani tsohon littafi, wanda bayan littafin ya kasance anyi shi ne da fatar zaki, daga gefe kuwa mutane ne guda hudu wanda duk kwakwar mutum bazai shaida su ba suma irin kayan da suke jikin tsohon sune a jikinsu, batare dayayi magana ba ya daga hannunsa tare da nuna jikin bango inda wani gunkin zaki yake a rataye sai kuma daga jikin idon zakin wata haske ce take fitowa kadan kadan, dukan su kallon inda hannunsa yake sukayi cikin tsananin firgici suka zaro idanunsu tare da fara wata irin dariya marar dadin ji, sun kusa mintuna 4 kafin sukayi shiru hakan yasa wannan tsohon dake murmushi yace “ TAURARON TA YA FARA AIKI! Lokaci yayi da zaku bazama neman NOOR duk inda take a fadin duniya, wanda duk yayi nasarar samunta ta hanyar aure ko kuma saninta a matsayinta na ‘ya mace tabbas rayuwarsa zata haska, zai zamto namijin fama, idan kuma ya aureta to duniya shi kadai zata dinga kallo, kada ku manta wannan bayanan sun fito daga cikin littafin kaka na na uku sarki LARASH da yayi mulkin wannan kujerar mai albarka, ku tashi ku tafi kuyi nemanta a cikin duniya, dukda hasashe dayawa da mahaifina ya barmin ya tabbatar da cewa tana nan Nigeria, Albarkata ta sauka a kanku “ ya fada yana daga hannunsa sama.
*****
KAUYEN DAKA
Wani kauye ne dake cikin jihar kano, kauyen daka kauyene mai ni’imar ruwa da kuma dabbobi harma da kiwo, gari ne na zaman lafiya wanda duk yaje kuwa zai shaida hakan , saidai kuma ba yadda akejin kauyen ba haka kowa yake, wasu mutanen cikin sa sam basu biyo wannan halin na zaman lafiyar kauyen ba, abinda suka gadama suke yi kuma babu yadda za’ayi dasu domin sun gagari al’umma matuka, daga yadda take dukan yarinyar da iya karfinta zai baka tabbacin cewar ba yar data haifa bace, domin duk mai imani da kuma yasan zafin haihuwa bazaiyi irin wannan dukan ba, koda kuwa mutum bai haihu ba indai yana da imani a zuciya to bazai kamanta haka ba, wani irin kara yarinyar takeyi na tsananin azabar duka wanda ya wuce misali, a wannan halin wata mata ta zagayo cikin gidan a gigice, inda sabo ya cancanta ace SARATU ta saba da jin irin wannan dukar azaban da UWANI take wa NOORHAN saidai sam ta kasa sabawa, hannu biyu ta sanya ta ture yar dattijuwar matar dake kwance saman ruwan yar yarinya matashiya wadda zamu iya kiranta da kwaila, dan shekarunta basu wuce goma sha shida ba, cikin masifa dattijuwar da aka ture ta dago kafin taci kwalar wannan matar data shigo tace “ saratu na rabaki da shigowa gidana amma hakan beyi miki ba, shin wai nan din gidan uban ** ne da zaki dinga shigo min bayan na miki iyaka?”
“Bazan fasa shigowa cikin gidan nan ba domin abinda kikeyi ya wuce gona da iri uwani, kada ki manta yadda kika haifi HUSNA haka itama mahaifiyar yarinyar nan ta haife ta, ki kaddara a ranki kece kika mutu kika bar husna ake gana mata irin wannan azabar dan Allah ya zakiji “
“Banason kina sako sunan ya’ta akan wannan yarinyar….”
“Ohh saboda ita wannan din ba haihuwarta akayi ba?”
“Koma me zaki ce kice amma bazai yiyu iyayenta su mutu su barni da wahala ba kuma ace bazan more ta ba, aiki ma idan na sanya ta sai tayi min shirme yo haka nan zan dinga ciyar da katuwar mace balagaggiya “
Hannu saratu tasa ta kwace gaban rigar ta da uwani ta nannade kafin ta jiyo inda Yarinyar take, fara ce kar irin hasken fulani pure babu surki kuma bata da wata kiba yo ina bala’i zai barta tayi kiba, hancin nan nata dogo masha Allah sai manyan idanu da take dashi tamkar madara saidai abin kuka ya sanya sukayi ja kadan sai dan karamin bakinta mai shape da kuma cikakken gashin gira, sumar kanta kuwa kana iya hangota saboda kan a since yake saidai tarin dauda da yayi saboda babu gyara, dukda wahala da take sha bai hana kyawunta fitowa ba masha Allah, tsayin ta daidai misali ne ba irin doguwa bace sosai kuma ba gajera bace, duk ga sawun su bulala nan wanda wasu sunyi mata tabo wasu kuwa sabbi ne sai kuma jini kadan a gefen bakinta wanda silar wannan dukan ya sanya bakinta ya fashe, sai jan dayake a jikin goshinta alamun duka amma bai kumbura ba.
“Noorhan “
Saratu ta kira sunan ta cikin tsananin tausayi wanda take jin inama tana da iko akan ta da babu abinda zai hana ta dauketa ta adana ta, har tayi mata aure ga mutumin kirki, yarinyar sam bata da matsala amma kuma irin ta ta kaddarar kenan, dago idanu na nayi tare da kallon mama saratu, mace guda daya da take matukar taimakona da kuma bani kariya daga cutar da uwani take min, murmushi nayi mata saidai hawaye ne suka zubo daga cikin idanu na na tsantsar shan wahalan danake yi yau da gobe, a hankali ta taka ta kama hannuna idanunta suna cika da kwalla tace “ kici gaba da hakuri noorhan wata rana zai zamto labari tamkar ba’ayi ba “ tana gama fadin haka ta sakeni tare da juyawa ta fice saboda kukan dayake kokarin kubce mata, saidai bata da yadda zatayi har kara ta kaiwa mai gari amma dayake uwani tana lasa masa wani abu daga kudinta sai ya koreta yaki sauraron kukanta akan wannan marainiya.
“Munafuka tashi kije ki dauko ruwan ki dawo kuma kizo ki min wanki ga kuma talla tana jiranki “
Tashi nayi kamar yadda ta umarta na nufi inda wani tsohon farin bokiti yake wanda tsabar dadewa da yau da gobe ya koma brown, doguwar riga ce a jikina ta tsohuwar atamfa sai hijabina da take tamkar an saka ta a cikin bakin kura tsabar dadewa da tsufa da tayi sai takalmina da ake kira dan madina wanda shima ya lale matuka, bokitin na dauka ina dingisa kafata saboda ciwo da kuma yadda dukkan gabbai na suke amsawa, kofa na nufa zan fice saidai yadda aka kira sunana cikin wulakanci yasa na juyo cikin sanyin jiki, budurwace kamata ta fito daga daki tana mika wanda shekarun mu ma dayane saidai ita tana da gata, ni kuma bani dashi saidai a wajen Allah, wata yar bingilar riga ce a jikin ta bakin cinya sai wani bata rai take a dole tayi bacci ta tashi, husna kenan wadda ta bani wata daya kacal a duniya kuma ya’ ga uwani, bayan ta gama harare hararen ta tace “ idan kin dawo nima zaki yi min wankin “
Da to na amsa mata kafin na daga kaina ina kallon hadarin daya fara harhaduwa na farkon damina, gashi wajen dibar ruwan ma nisa gareshi rafin, ga wankin uwani ga nata ga kuma talla ta dare dazan fita, sauke nannauyan ajiyar zuciya nayi kafin na juya na fice, zuciyata tana min nauyi, a haka na fito daga cikin kauyen mu dayake rafin a bayan gari yake, na ci gaba da tafiya cikin zullumin rayuwa da rashin kwanciyar hankali na, danake kwana dashi ina tashi dashi, saida na wuce duwatsu da wasu suke har cikim kauyen namu kafin na fara hango rafin daukar ruwanmu inda bishiyoyi sukayi masa kawanya suka kawata shi wajen ya kara zama mai ni’imar gaske, a hankali weather yake kara canjawa iska tana wani kadawa ga ruwa yana gudana, saidai yadda zuciyata ta hango min shi yasa na fara kalle kalle da fatan ingan shi, domin zan iya cewa bayan mama saratu duk duniya bani da kamar shi tunda iyayena sun rasu, shidin wani jigone a gareni kuma wani kariya ne a gareni, shidin ya kasance mutum na farko a duniya danayi wa son da bantabayi wa wani ba bayan Allah da manzonsa saw da iyayena da suka rasu, jikina yana bani cewar yana kusa dan haka na shagali da dube duben hanya, tare da fatan ganin abin begena, kamar daga sama naji an duro hakan yasa na juya da sansanyan murmushi anan nayi tozali da fuskarsa dake dauke da farincikin ganina, takowa yayi har inda nake yana sanye da kaya irin na fulani harda hular ma, saurayi ne ko kuma muce matashin samartaka wanda a shekaru bazai wuce 24 ba
Dogone marar jiki sosai gashi fari tas sak fulani na kauye wanda babu wani surkin hausawa a tattare dashi saidai zama da hausawa a gari daya ya sanya duk kowa yana jin fulatanci da kuma hausa amma still zakiji maganar su ya nuna zallar fulani ne, murmushi yakeyi saida yazo daidai ni kafin ya tsaya, “masoyi “ na fada ina rufe fuskata da tafin hannu farinciki na yana wanzuwa bakinciki na yana yayewa “masoyiya meyasa yau baki kirani nazo na tayaki daukar ruwa ba?”
Ya fada cikin taushin murya, girgiza masa kai nayi nace “ banason kasha wahala “
“Nima banason kina shan wahala, minene wannan a goshin ki da gefen bakin ki? Kamar fa jini nake gani “
Saurin kai hannu nayi na goge jinin daya riga ya bushe nace “ faduwa nayi dazu a gida “
Nayi maganar batare dana kalle cikin idanunsa ba, hakan yasa ya sauke nannauyan ajiyar zuciya yace “ dukan ki yau ma tayi “
Girgiza kai nayi nace “a’a masoyi ba dukana tayi ba “
“Kada kiyi min karya nasan komai fa ni ba mutumin da zaki boyewa damuwarki bane “
“Masoyi da gaske nake fa, kaga yau inada aikin yin a gida bari in tafi idan anjima in shaa Allah sai mu hadu a dandali kaji “
“Shikenan bari in taimaka miki “ yayi maganar da daukar bokintin ya tsunduma sa a cikin rafin ya cikosa tas kafin ya dauka yace min muje, haka muka jera muna yar hira dake nuna shakuwar mu sosai da kuma kaunar juna har ma da tausayi.
Saida muka gab da shiga gari nace to ya bani in dauka gudun kada a samu matsala wani ya ganmu aje a fadawa uwani, saboda ta min iyaka dashi saidai ni kuma bazan iya rabuwa dashi ba, na gaskiya sunansa shine SAMIR kuma shima kauyen mu daya dashi saidai shima gidansu talakawa ne gara ma namu, tunda uwani tana daga cikin masu kudin kauyen mu wanda da kasuwar danake mata ta samu kudin, shida mahaifiyarsa marar lafiya suke zaune a gida daya mahaifinsa kuwa ya rasu kuma shi kadai iyayensa suka haifa, mahaifiyarsa komai sai yayi mata kuma shi zai nemo abinda zasu ci , kuma yar gona ce garesa dayake cire amfani duk shekara wanda suke samu suna ci, samir mutumin kirki ne kuma a kalla munfi shekara 3 tare muna soyayya mai dadi har akwai lokacin danake fakar idon uwani inje in taimaka inyiwa mahaifiyarsa NANNE wanna da kuma wanki wata rana har girki nake musu kafin in na gama in dawo gida inda zan amshi hukuncin dadewar danayi, saidai a hankali a hankali na saba matuka wanda na mayar da aikin gidansu wani jigo a gareni, na sanya shi cikin ayyukan rayuwata, samir mutum ne daya dade da nuna yana sona nima kuma na amince masa domin yana bani kulawa mai tsafta da kuma farincikin dana rasa, kuma shi yayi secondary school a cen cikin local government din da muke karkashin ta, ni kuwa bakina primary shima da kyar yau in naje gobe ba lallai uwani ta barni inje ba, kuma har yanxu yarta husna tana zuwa dan yanxu tana ss2 inda suke haduwa da ya’yan mai gari kawayen ta suyi tafiyarsu, ni kuma karatunma ta hanani tace idan na tafi makaranta waye zai mata aikin gida da talla, husna ta dade tanason samir saidai sam be taba bata kofa ba balle ta kawo masa wargi, kuma dukda haka tana nan tana masa naci, shiyasa uwani ta yanke alaka ta dashi kwata kwata, hakan yasa muke zuwa nan mu hadu ko kuma a gidansu idan naje yi musu hidima, wanda har mahaifiyarsa munyi sabo matuka haka zatayi ta sakamin albarka da maganar ta da bata fita sosai.
Bani yayi cikin jin tausayi na yace “ komai zai wuce Noorhan dita zamuyi farinciki a rayuwar mu in shaa Allah kawai dai inaso ki kulamin da kanki “
Jinjina kai nayi fuskana tana dauke da shagwaba dan banaso mu rabu ji nake tamkar an ciremin wani bangare na jikina nace “Allah ya yarda masoyi, kayi kokari kazo da wuri kaga sai muyi hira sosai “
“Tohm zanzo, amma kiyi maza kije gida ga hadari nan yana gab da bamu ruwa “
Kallon saman nayi, naga yadda gari ya fara duhu dukda kuwa a lokacin baifi karfe 5 na yamma ba amma tamkar magriba saboda duhun da hadarin ya haifar nace “ shikenan bari inje, amma fa anya hadarin nan zai bari azo dandali kuwa?”
“Me zai hana koda anyi ruwa an dauke ne sai munzo in shaa Allah “
“Tohm shikenan ka gaishe min da mamana , ka kuma kulamin da ita kafin inzo gobe in shaa Allah “
“Kema ki kulamin da kanki mai sunan yan gayu “
Dariya maganarsa ta karshe ta bani wani mai sunan yan gayu, sallama muka sakeyi ya juya ya koma ni kuma na taho gida cike da begensa.
***
Chat only