KINCI DUBU.....

5-6

by @oumhairan1

*KINCI DUBU.....*



*Oum Hairan*


*page 5-6*
Washegari da safe daƙyar Jiddah ya danne Zuciyarta ta fito ta haɗa break shayi kawai ta dafa ta haɗa komai da ta san za'a buƙata a dinning ta ɗumama tuwon da tayi jiya na shinkafa miyar ɗanyan zogale da kusan Baaci ba, sai lokacin ta shiga dakin ta tashi yaran da suke bacci tayi musu wanka tasa sukayi sallah suka saka uniform ta kamo hannunsu suka zauna a dinning ta haɗa musu shayi da bread sannan ta saka musu tuwon data ɗumama sukayi karyawa me kyau suna shirin tashi tace dasu “kuje ku  gaishe da Abbanku" da sauri suka kalleta sukace  “Yaushe ya dawo Mommy?" Murmushi tayi tace “Jiya bayan kun yi bacci" da gudu suka nufi dakinsa lokacin ya fito daga wanka suka maƙalƙaleshi suna dariya shima dariyar yayi yace “Jiya na shigo kunyi bacci ina Mommy?" Haɗa baki sukayi sukace  “Mommy mode nata babu kyau Daddy itane tace Muzo mu gaisheka" shafa kansa yayi yace “Nasan matsalar Kuzo muje mu gaisheta" sake kamo hannunsu yayi suka fito tana zaune a dinning tana danna Wayarta ya sanya hannu ya karɓe tare da zuba mata ido ta kalleshi sau ɗaya ta kau da kai tare da cewa “Barka da tashi" Murmushi yayi yana ƙara saita idanunsa a kanta tayi masa kyau sosai duk da cewa ta ɗan rame koda yake ita dama idan tanada ciki rama take yi tayi haske.
Kamo hannunta yayi cike da soyayya da kulawa yace “Allah ya bawa zuciyar Ibrahim hakuri don Allah a huce haka kar a azabtar Dani" ƙasa tayi da kanta ya kalli yaran yace “Muje na kaiku makaranta Mommy yau ta huta ko?" da murnarsu suka fice da gudu yayi kissing nata yabi bayan yaran ta sauke ajiyar zuciya tare da jan plate ta zuba tuwon ta saka kakile da yajin daddawa ta fara turashi kamar magani ƙasan ranta tana tuhumar kanta dalilin da zaisa ta ɗauki matakin ƙauracewa mijinta a daidai wannan lokacin da wata take shirin kutsowa rayuwarsu, da sauri tayi firgigit a ranta tace “Idan na ƙaurace masa zai gane muhimmaci na, amma sai wata zuciyar tace mata “Mafi girman kuskuren da zaki tafka kenan zaki nisanta kanki da zuciyar Mijinki tun yana damuwa da rashinki har ya saba daga nan kuma kince yaje yayi komai ba komai kenan"  ture tuwon tayi ta tashi ta fara tattare kwanukan ta kai kitchen ta fara wankewa  taji tsayawar motarsa bata fito ba domin Allah ya sani ji take kamar ta shaƙeshi wani haushinsa takeji har cikin ranta saidai tursasawa kanta takeson yi ta nuna masa babu komai but idan tace bata kishin Ibrahim ƙarya ce wadda babu me yadda da ita.
Ji tayi ya Rungumeta ta baya ya ɗora kansa a kafaɗarta Ya sauke ajiyar zuciya cikin Muryarsa me kashe mata jiki yace “Ki manta da komai Don Allah Jiddah ki bari Muci gaba da rayuwarmu kamar yanda muke yinta kar ki ba da kofar da wani zai gani ya shiga Please ki fahimceni Maman Janan ƙarin aure a wajen namiji irina ba yana nufin Na daina sonki bane wlh Tallahi har gobe ke kike haska zuciyata" Idsnunta ne ya kawo ruwa ta sanya hannunta tanason ɓamɓare masa nasa ya ƙara Matseta yace “Wai meke dalilin da Bazaa Barni na gaisa da fetus ɗina ba Naga dai shima yana buƙatar jin motsin Daddynsa ko?".......


_Kar sunan labarin ya firgita ku Amare Kuzo ayi daku zaku ƙaru domin wataran kune iyayen gidan_


*PAID BOOK REGULAR 400, VIP 800 VIA 9031307566 FAUZIYYA TASIU UMAR OPAY SHAIDAR BIYA TA ****


*For more Info....*
*****


*OUM HAIRAN*