BAYA TA HAIHU

14

by @rabiattu0444

*BAYA TA HAIHU*
14

Ummu Maher (Mrs green)🍀

*AREWA WRITTER'S ASSOCIATION*


*🗣️Kar ki wuce ba tare da kin karanta ba Please👏🏻 domin na tabbatar da kuma watarana za ki zama kamar Ummufadeel da ga shirye sai ki fara siyarwa👏🏻🗣️💃🏼*

*_UMMUFADEEL!_*
_*UMMUFADEEL!!*_
 FOODMART🍊🍋🍎🍏🥦🥬🥑🥝🥥🍇🍓🍒🍌🥔
*UMMUFADEEL*
*Ƴar Jos💃🏼*
*UMMUFADEEL*
_Gidan sauƙi_
*Ummu fadeel me gidan gonar kayan marmari kowanne iri, da nau'ikan kayan tsirrai ko wanne iri, tana bayarwa akan sari*

*_SHIGA GROUP DOMIN GANIN KOMI DA IDONKA_*
***

*1_Citta ɗanya🫚 buhu ko bucket*
*2_Kaninfari kwano ko buhu*
*3_Cinnamon*
*4_Kimba*
*5_Masoro*
*6_Rosemerry*
*7_Tafarnuwa*
*8_Amla*
*9_Habbatussauda*
*10_Man kwakwa*
*11_Zaituun*
 Da dukkan nau'ikan kayan ƙamshi na gida da na waje, dukkaninsu za ku same su cikin sauƙi da kuma rahusa gami da aminci, trust and thrusted.
_______________
*_Kar ku ga Ummu Maher ta fiye faɗin sunan, ku tambaye ni menene? Tabbas Ummufadeel ta shahara a fannin kawo muku kayan tsirrai, da kayan lambu, nau'in su Fruits, vegetables, ko wani nau'in kayan fruit da na lambu tana kawowa, kamar su;_*
*Strawberry🍓*
*Roseberry🍒*
*Inibi🍇*
*Ayaba🍌*
*Fiya🥑*
*Kwasha kwasha🥝🥝*
*Apple 🍎🍏*
*Mango🥭*
*Plum*🍑
*Cocumber🥒*
*Latas🥬*
*Cornflower*
*Doya🥔*
*Dankalin turawa*
*Dukkaninsu tana siyarwa a raha da kuma rahusa, ku dai ku hanzarta ku neme ta akan lambarta kamar haka ****
*_Idan na ce zan jero muku za mu daɗe ba tare da na gama ba, sannan tana siyar da na'uikan tsirrai kusan rabi da kwatansu tana siyarwa cikin aminci da kuma rahusa, tana siyar da danƙwala-danƙwalan doya, dankalin turawa, dankalin Hausa, makani._*




   Yau kasuwa ta yi wa Habibu daɗi, saboda har masu sauran kaya sun fara zuwa shagonsa domin sari cikin ƙanƙanin lokaci ya samu abin da bai taba tunanin zai samu ba ashe dama can jari ne ba shi da shi shi ne yasa yake ta neman kuɗin amma bai samu ba, yana ta murnarsa yau kasuwa ta yi riba ya shigo gidan.

Tsayawa ya yi cak, ganin Billy a lokacin sakar gidansu jikinsa ya yi wani irin bala'i mutuwa ya ji tamkar kasa ta tsage ya shige saboda ya tabbatar wannan ƴar barikin ta gama tona masa asirin da yake ta ɓoyewa.
Billy ta murmusa sannan ta ce"Allah sarki sannu da zuwa, dama tun ɗazu nake jiranka na ga yau ba ka zo wajen aiki ba".
Ganin Mero tana ta kallonsa tana son sanin gaskiyar lamarin, sai ya sunkuyar da kansa ya kuma wayance sannan ya ce"eh wallahi Bilkisu kwana biyu kasuwa ce ta ɗauke min hankali, da niyyata ma na haƙura da kamfani ba ki ɗaya tun da na samu abin da ya fi wancan aikin". Ta faɗi hakan yana murmushi, sai kuma a lokacin ya ga murmushin Meronsa ta ce"gaskiya dai kasuwanci ya fi wannan aikin kamfanin shi yasa ma nima nake ganin gwara ya haƙura kawai".


Billy ta gallawa Mero harara amma ba ta ganta ba, cikin wayancewa ta ce" uhum ni zan tafi dama oga ne ya aiko ni in isar da saƙo kuma na isar ina fatan Allah yasa albarka a cikin kasuwancin na ka".
Tana fadar hakan ta miƙe tana yiwa gidan wani banza kallo duk da an gyara sa sai ta ji kamar ta yi amai duk da tsaftar da suke da shi. Dama Ammi ba ta nan sun je gidan biki ita da ƴammatanta saboda haka yasa Billy ta ji kamar ta rufe Mero da duka da ta yi musu tsuru-tsuru ta sanya musu ido sannan sai a yanzu ne ta ji anya kuwa ita ma ba za ta ƙulla alaƙa da Habibu ba ganyen fa ya haɗu ta ko'ina Amma dai za ta zauna ta yi tunani domin ba za ta bar Hafsah ta kwashi garaɓasa ita kaɗai ba, yadda take ƴar barikin nan sai ta san yadda ta yi ta ci kuɗin Hafsah sosai har ma tafi Hafsah ɗin cin kuɗin.


Habibu ya yi saurin bin Billy, tana ganinsa ta sa dariya sannan ta ce"wai da a tunaninka ka ɗauka bakin rijiya wajen wasan makaho ne? Shi yasa na biyo ka har gida domin na tuna maka abin da ka manta, tun da yanzu karvi moriyar ganga sai ka yadda ƙotarta ko? To saƙo daga Hafsah ta ce kaje tana son ganinka a yau ɗinnan komi dare".


Haushi da nadamar aikata zina suka sanya shi a ɗimuwa, har Billy ta tafi bai iya furta komi ba gani yake tamkar ba shi bane shi ɗin mutum me tsoron Allah amma mace ta ja ra'ayinsa akan kuɗi to ga shi yanzu ya zo yana nadama sai dai abin da ita ma Hafsah ɗin ba ta sani ba daga yanzu zai shiga yaƙi da ita gadan-gadan.




Yana shigowa gida Mero ta fara yi masa tambayoyi,   ta ce"Hammah ni fa wannan matar me kalar karuwai ban ga gane bin ka gida da ta yi ba, in ba mace ƴar bariki ba ina ita ina biyo ka gida?.
Habibu ya rasa abin faɗi, amma da yake matarsa ce kuma yasan yadda yake lallaɓata sai ya ce"ki yi haƙuri ita ma ba laifinta bane, ita ma fa kina ji dai tana cewa ita oga ne ya aiko ta kin ga kuwa ita ma ba aiken ta bane in ban da haka me zan yi da ita kina ganinta ba kalar mace me mutunci ba".


Na gamsu sosai Da abin da ya faɗa, saboda na yarda da shi sosai kasan ba zai taɓa cin amana ta ba nadan waye shi tun ba yanzu ba.



***

Washe gari


_HABIBU_

Da wuri ya isa zuwa gidan Hafsah, ai kuwa kamar kullum ita da Billy ya same su suna ta hira suna ganinsa kowacce ta shiga taitayinta musamman ma da suka kalli fuskarsa, sam babu imani ko kaɗan a fuskarsa. Ya zauna ya fuskance su sosai sannan ya ce"na samu saƙon ki Hafsah amma ina son ki sani taura biyu ba ta taunuwa sannan rana da sanyi basa haɗuwa saboda haka na yi tuba ba zan koma kuskurena na baya ba, ko da kuwa za ki nunawa duniya wannan bidiyon".

Ran Hafsah ya kai maƙura a tashi, soyayyar Habibu ta gaza ɓoyuwa a fili ta ce"tabbas idan ka guje ni komi zai iya faruwa da ni, don girman da manzonsa ka soni kamar yadda nake sonka".
Habibu ya murmusa sannan ya ce" ko da kika ga na biye miki a baya igiyar talauci ce ta ja ni, amma wallahi ba don ina son ki ba saboda ke kin san babu wata mace a raina idan ba Mero ba da ita kaɗai na saba, a halin yanzu bana ganin wata mace a gabana idan ba ita ba, bana jin marmarin ganin kowacce mace idan ba ita ba, bana son kusantar kowacce mace idan ba ita ba, ki fuskanta ita zina ba ado bace face ƙazanta da kuma najasa saboda haka wallahi tallahi kin ji na yi rantsuwar musulmi babu ni babu ke, sannan idan kina tutiya da bidiyona nima ina da shi a wayata na ki, idan kuma kina son gani yanzu sai na buɗe miki". Ya fara shirin buɗe code ɗin wayarsa ƙirar Tecno, ta dakatar da shi da wani irin yana yi na damuwa ya hango tsagwaron tsoro da kuma nadamar abin da ta aikata wajen kuskuren nuna ita me wayo ce.


Ta ce cikin kuka da tsoro tana mai dafe da ƙirjinta, don girman Allah da manzonsa ka da ka nuna min ka ƙyale ni na ji da halin da nake ciki na rashin ka sannan wallahi zan goge bidiyon ka nima don Allah ka goge na wa".

Habibu ya fara murmushin mugunta sannan ya ce"uhum daga baya kenan ki cigaba da ajiye na wa nima zan cigaba da ajiye na ki sannan wayoyi uku na siya na sanya record ɗin a cikin kowacce waya biyun suna gida, sannan ina son yadda na goge lambar wayarki nima ki goge ta wa".
Da sauri hannunta yana matuƙar girgiɗi ta fara goge lambarsa, sannan ta tsugunna har ƙasa tana ba shi haƙuri".

Ai kuwa Habibu bai saurare ta ba ya ta shi tsaye, tare da sanya hannayensa duka a cikin aljihun jins ɗinsa yana mai matuƙar murmushi.
Haka ya sanya kansa ya fice ba tare da ya ƙara waiwayo su ba.



Habibu yana tafiya Billy ta kalli Hafsah cike da takaici ta ce"kai gaskiya dai wanda ba dan bariki bane sai a hankali, su ke yanzu har kin saduda? Yaushe ma aka yi daren balle gari ya waye? Kin san dai ba inda za ki samu kamar Habibu ko? Saboda haka wallahi ki yi ƙoƙari ku zauna musan ta inda za ku ɓillo masa".

Hafsah ta share hawayenta ta zauna akan danƙareriyar one seater wacce take a cikin dankareren falon na ta, ta jingina bayanta sosai kamar me tsohon ciki sannan ta kalli sama ta fara magana kamar haka"wallahi Billy jikina ya yi sanyi sosai fiye da kima, ada ina kallon Habibu a matsayin marar wayo, ashe ni ina masa kallon wawa shi yana min kallon sauna ban taɓa tunanin zai yi min bidiyo bane shi ya sa, kuma na fara ji a jikina dangantaka ta da shi ba za ta taɓa cigababa saboda haka na tabbatar da cewa dole mu rabu matuƙar ina son asirina ya rufu".
Billy ta galla mata harara sannan ta ce"uhum a tunaninki cewa Habibu zai iya watsa bidiyon ki, to idan ma mafarki kike to ki farka na hango tausayi da imani a idonsa Habibu ba zai taɓa aikata haka ba, ki kwantar da hankalinki kamar tsumma a ruwa ya tabbatar in har ya tona miki asiri yasan kamar ya tonawa matarsa ne, tun da uwa ɗaya uba ɗaya kuke kin ga kuwa ba zai so ya tozarta ki ba ya yi haka ne domin kema ki  goge na wayarki kin ga daga haka ba ki da wata hujja akan ki, saboda haka kar ki yarda ya ci galaba akan ki kawai kice koma meye zai yi dai-dai kike kema da shi".



Sosai zugar Billy ta samu wajen zama a kwakwalwar ta saboda ta tabbata Billy ba za ta cutar da ita ba, kuma gaskiya ta faɗa mata ta tabbatar ba zai taɓa yaɗa tsiraicinta ba sannan tasan kyawawan halayen Habibu ba zai taba yin abin da zai lalata sunan gidan surukansa ba. Da wannan shawara ranar ta kwanta cikin farin ciki sannan idan ta tashi da safe tasan da abin da za ta zo masa.





Allah shi ke da safiya ba mutum ba, domin kwana Hafsah ta yi tana zazzaɓi ga kuma amai da yake Billy a gidan ta kwana ita ta dinga taimaka mata tana gyara jikinta ko kafin safiya ai ta gama galabaita taimakon likita kawai take buƙata, ya yin da Billy take wani tunani a ciki zuciyarta ta ce"tab lallai akwai ƙura".





***
Mrsgreen ce.