AASIYAH

4

by @mamuhgee

Aasiyah

Mamuhgee

4

Wasu gidaje ba sa cike da dariya,

Wasu kuma ba sa cike da kuka,

Akwai gidaje da za'a shiga aga mutane suna zaune tare,

suna cin abinci tare,

suna kwana a ƙarƙashin rufi ɗaya, amma idan aka duba da kyau sai a gane cewa kowanne daga cikinsu yana rayuwa ne shi kaɗai,

Gidan ASHIRU ISMA'IL yana daga cikin irin waɗannan gidajen da rayuwar cikinsa take kamar daban data sauran gidajen sbd asalin son zuciya da son kai dayake cikin jininsa dan kuwa kaf duniya bayan kansa baisan kowa da komaiba sai kuwa yayansa dayake ganin suma komai nasa sak da sak ne dan haka yake alfahari dasu,

Anguwa ce datake cike da mutane sosai tako ina da tarin qananun gidajen da suke a mammatse da juna sbd kusan kowane dan fili ko space komai kankantarsa yanada amfani a irin gidajen dake anguwan shiyasa kusan kowane layi a anguwan gidajen a mammatse suke babu spaces,

Mutane ne sosai a anguwan da yara tako ina dan hakanne yasa kusan kowa yasan kowa hakama kaf anguwan babu gida ko daya da zaka kalla ka gani na masu rufin asiri duka na masu rayuwar  mungode Allah ne da mukeda Rai da lafiya ma.

A layin da karamin masallacin anguwan yake gidan dayake kusa dashi shima qaramin gida ne dayake da dakuna biyu rak sai qaramin soro mara duhu mai budadden sama maana ba rufi a soron  da kitchen sai tsakar gidan da baa matse yake ba amma baida girma,

Gida ne kawai da talauci ya riga ya zama wani ɓangare na bangonsa,

Bangon gidan ya fara yin duhu saboda shekaru,Wasu wuraren simintin sun tsage rufin ɗin kuma yana zubar da ruwa idan damina ta yi ƙarfi bakin ƙofa akwai tsohuwar tabarma da ta yi laushi saboda yawan amfani da ita.

Amma matar gidan ba ta taɓa kallon gidan da ƙiyayya ba ko gajiya da gundura da rayuwar cikinsa,

A gare ta gida ne gidan da ta shigo da mafarkin zama mata ta har abada saidai mutuwa ta raba,

Gidan da ta haifi 'ya'yanta ta zama uwa jajirtacciya data sadaukar da rayuwarta ga yayan da kuma mijin da a yau bai taba kallanta da daraja ba,

Gidan da ta yi shekaru tana ƙoƙarin riƙewa kada ya rushe sbd wanda yake amsa sunan mijinta uban yayanta bai taba kokarin riqewaba bare kallansa da idon daraja,

Ashiru ta auresa ne a lokacinda take da kuruciya sosai kuma aure na soyayya da kauna mai girma a tinanin cewa shine mutumin da zarar sun zauna tare komai zai gyaru a rayuwarta data mahaifinta da basu rayu tareda mahaifiyarta sai iya su biyu kadai ita da Baffanta da Kakarta wadda ta tsufa sodai amma shekaru sun koya mata cewa ba kowanne mutum ne yake canzawa wani rayuwa ba,

Ashiru mutum ne mai taurin rai maana taurin zuciya da taurin kai mai tsanani wanda ba wai saboda talauci ba A'a haka yake kafin kuma talaucin ya qara da nasa,

Haka kawai yake jin tsana da zafinta lokuta da dama sbd tinanin tsananin rashinsa yanada alaqa da nauyin data lafta masa na haihuwan data ringa yi kusan a jejjere ba tazara dan haka sai kawai yaga duk nauyi ya masa yawa ta dorasa akan hanyar da bai shirya ba,

Yana son kuɗi fiye da komai amma kuma baya iya nemansu da wahala da gwagwarma a yanxu sbd ganin ita data hayayyafan gwara ta dauki nauyinsu saita san kuskurenta na hayayyafan batateda tazara ba ko dan ganin basuda komai,

Duk da baya kaunar yawan haihuwan yana son 'ya'yansa sosai sbd ahankali ahankali yake gano halayensa tsaf suke daukowa wanda hakan yana sakasa alfahari dasu dan zasu kasance masu taurin zuciyar kwatar duk abinda sukeso a hannun ko waye matiqar hakan zai samu dan mallakar rayuwar da suke so,

Hakama soyayyarsa ga 'ya'yans tana da wani irin salo,

Ya koya musu su kula da kansu kafin su kula da kowa,

Ya koya musu su so kansu fiyeda kowa a duniya kada su taba san kowa kafin kansu sbd hakanne suka san tsananin karfi da mahimmancin son kai fiyeda komai,

Ya koya musu cewa duniya ba ta taɓa jin ƙai ga wanda baidashi baida karfi baida iko hakan yasa suka girma ba tare da sanin yadda ake jin ƙai ba,

Sanyin safiyar ranar Asabar din ranar ta tashi ahankali daga kwancen datake taja dogon numfashi mai sanyi da rashin kuzari sosai tareda kallan tsohon cikin jikinta dayayi nauyi sosai.

Sake sauke numfashin tayi tareda dan kallan Ashiru dake kwance akan wata yar katifarsu mara girma sosai da shine yake kwanciya akai ita sedai tayi shimfida a qasa ta kwanta dan cewa yake zafi take qara masa tana hanasa shan iska yanda ya kamata dan haka baya son tana rabarsa matiqar ba buqatarsa zai biya akanta ba.

Tashi tayi xaune tareda miqewa tsaye ta nufi kofar dakin ta bude ta saka kafafunta wajen tsakar gida ta fita

Duk da gajiyawar da ke jikinta wanda take kwana da ita koyaushe sbd aikin wahalar datake wuni a cikinsa sai ta ji wani irin nutsuwa ta dan shigeta sbd safiya ita ce lokacin da take samun damar zama ita kaɗai idan Ashiru da yaran sun fita babu me mata ihu,

Buta ta dauka ta isa bandaki ta zagayo tana fitowa ta wanke fuska da kafafunta ta nufi kitchen ta zauna a kujeran katako dake kitchen din qarama ta janyo robar da yan kayan abincinsu yake ciki ta fara dubawa,

Babu wani abincin ci na arziki a cikin rabor bayan gero da da sauran shinkafar da batafi gwanani uku ba.

Idan ta dafa shinkafar yanzu da safe to ba za ta samu abin da za ta dafa da rana ko yamma ba,

Shiru tayi na sekanni tana rasa tinani kamawa kafin daga ƙarshe ta ɗauki geron ta fito kitchen din dan yanke shawaran kunu zatai kafin su tashi su fito,

Cikinta yana nauyi sosai ciwon baya datake fama dashi sbd aikin wahala amma hannuwanta ba su tana daina aiki ba dukda cewa duk wannan aikin nata baya isa wajen mijinta baya isa wajen 'ya'yanta.

Aikin daka kunun tayi da hannuwanta tana yi tana dan taqaitawa sbd kada ta tayar dasu daga baccinsu dan kuwa yaran duka tsayawa zasuyi sune yinwa sukeji abinci suke so yanxu yanxu.

Aikin awa daya saida ya dauketa kusan awa biyu sbd yanayinta da kuma rashin son tadasu daga bacci.

Tana gamawa wuta ta koma ta hura ta dora ruwan kunun wanda shima saida idanuwanta sukai jajir kaman zasu cire kafin ta iya samun wutar ta kama yanda ya kamata kuma a daidai wannan lokacin ne Ashiru ya farkaya fito komai baice mata ba ya fice daga gida.

Waje yaje ya siyo qosan dari hudu ya dawo yana zaunawa a tsakar gidan yaran suka fara fitowa daya bayan daya suna shiga bandaki duk wanda ya fito saiya wanke fuskansa yazo ya zauna gefen uban.

Kunun ta damo ta kawo musu robar gabaki daya ta koma bakin murhu dan kashe wutar sbd manajin gawayin da batason ya qare.

Duk da zafin kunun hakanan suka rabesa tas Ashiru ya bude ledar kosan daya siyo ya rarraba musu kowa uku uku take suka fara shan kunun da zafinsa yaran sbd kada Maman tasu tazo tace zatasha a rage na kowa.

Ashiru na kallansu ya dauki abin fita da kansa ya fara musu firfita dan su samu shanyewa kafin ta dawo dan tana ragesa babu wanda zai koshi a cikin yaran dan haka yahau firfita yana gogewa qaramin uban zufan dayake hadawa kaman barawo.

Koda ta gama kashe wutar a natse ta tattara gawayin ta kai inda rana ta fara fitowa ta shanya ta sake rattara inda tai aikin koda tazo sun shanye kunun tas dukansu sai hada zufa sukeyi baban nasu hadda zare rigarsa yana firfita hankalinsa kwance hakama suma yaran sai a lokacin ne suke gaidata.

Shiru tayi kafin ta amsa a sanyaye tana tattara kayan ta juya batareda tace komaiba sbd babu amfanin maganar ga abinda babu sauransa.

Wani nauyine ya dan danne kirjinta sbd daci da damuwar halinda yayan data haifa suke ciki na rashin jin qai ko tausayinta ko kadan saina magaifinsu wanda bayan soyayyarsa gurbatacciya garesu babu abinda yake musu itace komai nasu.

Bata baqin ciki da tsananin qunci akan komai sai akan yanda tarbiya da tausayinsu tareda jin qai ya gushe tin suna qananunsu yanzu,

Tayi damuwar tayi kukan tayi baqin cikin amma babu sauki bare sauyi dan haka yanzu babu lokacin kuka ta barwa Allah komai sbd kuka ba zai mata maganin komaiba ta koyi yadda ake yin murmushi yayin da zuciya take kuka.

Wanka Ashirun yayi ya fice daga gidan suma yaran haka taiwa kananun wanka suka shirya suka fice islamiya.

Ita kadai aka bari gidan har yamma ba kowa a cikinsu sbd daga makaranta can yake jansu ko su samesa gurin dayake zama ya siya musu abincinsu suci acan daga can su koma makarantar yamma batareda damuwa da ita taci dinba kokuwa.

Shigowa tsakar gidan yayi da sallama can qasan maqoshi wadda ta sanya Maryam dake zaune tsakar gidan tana wanki bata ji ba,

Dakatawa yayi bayan harya ya dan wuceta ya juyo zuciyarsa na tafasowa da takaici da bacin rai mai tsanani ya mata wani kallo tareda bude baki yace

"Tinda ba aikin wahala na kawo miki ba Maryam bazaki kallan da daraja ba ko?

Har lokacin bataji sa ba sbd wasu lokutan da dama bata ji sosai dan baqar azabar data jima da taba lafiyar kunnuwanta.

Juyowa yayi gabaki daya zuciyarsa na sake tafasa da baqin cikinta dana mugun talaucin dayawa rayuwarsa katutu ya daga kafarsa da zafin gaske yayi ball da bokitin datake wankin take ruwan sukai wani fatali har a jikinta da fuskanta ta miqe tsaye ahankali tana dan ja baya kadan tareda dagowa zata kallesa ya katseta da cewa

"Dan girman Allah kadama ki kalleni dan baqin ciki zai iya sakani siqewa anan gurin,

Auren mace dai mara saa a rayuwa baida riba na fada na sake fada,

Banji fadar maaikiba dana kasa aurawa yayana uwa ta gari gashinan daga ni har su muna cikin masifar da batada magani"

Qarasa taka bokitin yayi yana wucewa ciki a zuciye idanuwansa jajir kaman zai kama da wuta yakeji tsabar tafasa da baqin cikin da zuciyarsa ke yi.

Numfashi ta sauke ahankali tareda saka hannu ahankali ta goge ruwan kumfan daya watsu har a fuskanta ta kalli kayan daya watsa din na mutane datake wankin.

Hannuwanta ta saka tana tattarawa ta maida a cikin bokitin ta fara kokarin sauya ruwa batareda tace komaiba taci gaba da aikinta sbd kota ajiye ta tafi gurinsa babu abincin da zata basa din yau dan haka ci gaba tayi gidan tsit babu mai hayaniyar komai harta kusa kammalawa saiga yara sun dawo daga islamiya.

Bulama ne a gaba riqe da allonsa sanye da riga da wando na wani yadin daya gama nannadewa na roba sai nason zufa yakeyi fuskansa sak ta babansa a hade sbd yunwa yake ji sosai daman baiyi niyar zuwa makarantar ba.

Khamis ne bayansa tareda Kaninsu Jamilu wanda yake dauke da allonsa dana Khamis suna isowa tsakar gidan jamilun ya sake allunan a tsakar gidan yana nufar gurinta ta juyo tana kallansa tace

"Jamilu meyasa zaka yarda allon dayake dauke da ayoyin Al'qur'ni a qasa?

Maza dauke"

Juyawa yayi yana wani irin buga kafa ya dauke ya aje kofar dakinsu yana dawowa gabanta ya bata fuska sosai zai fasa kuka yace

"Ni wlh yunwa nake ji mama kiban abinci"

Shiru tayi kafin tace

"Babu abinci amma ka jira na gama wankin nan sai khamis yakai musu acan zasu shanya abinsu idan anbasa kudin sai a siyo gari kusha da siga"

Khamis na jin hakan ya fito dakinsu daya shiga yana cewa

"To kiyi sauri Mama nima yunwa nakeji kuma gurin baba zan koma zan tayasa aikin buga katako da aka kawo masa zai kai dare yau"

Kaman zatai magana sai kawai bata tankasa ba taci gaba da wankin tana cewa

"Jamilu jeka ka zauna zan gama da wuri kaji"

Tura baki yayi yana nufar dakinsu kaman zaiyi kuka.

#MAMUH

***

***