MY LADY BOSS

31-32

by @mamanteddy

_Littafin my lady boss na kuɗi ne , Regular payment₦300 vip payment₦500 special₦1000 via 6037312299 Mohammed Aisha keystone bank ko ki tura katin MTN ta wannan number *** ban yarda kika karan ta mun idan baki biyani ba , haka kema don Allah kar ki fitar mun ,duk wanda ya karanta bai biyani ba shida Allah._

Ina kuke masoya makaranta ga wani littafi sabo mai ɗumbim basira tare da faɗakarwa da kuma zallar madarar soyayya mai tafiyar da zuƙata daga hannun Mmn nusaiba kunsan mene sunan littafin kuwa ? A'a nasan shine Amsan ku....ABBBA NE! kar ku sake ayi baku . Complete ₦300 kacal ,zaku iya magana ta wannan number +966599791573 domun ƙarin bayani mun gode!

*AUNTY AISHA MMN TEDDY* ***

Ganin yanda idon Baba Barau ya fito waje ,yana ganin kisa babu daman gudu ko kirar agaji . Wuƙar Bilkisu ta ɗaura akan Maƙogoron kaciyar nasa , Diyana na riƙewa babu imani ... Ganin haka yasa Sumayya saurin kirar sunan Billy tana dakatar dasu da cewa " Billy dakata kuji, nidai gaskiya ina tsoron ganin cire sassan mutum a gaban idona...Yusrah ce da itama tsoro ya kamata tace " Gaskiya nima wallhi tsoro nake ji. Yanxu to abinyi kuyi raga raga da gaban sa , wanda ƙarshen sa sai dai ya naƙasa , maganan Laurat ya katse su. Wanda Diyana cewa tayi " Hakan yayi ma ai . Amma wallahi badon kunce a'a ba ,da yau kunga yanda Tozon nan zai rinƙa tsalle a ƙasa. Dariya Safna tasa ,wanda Yusrah cewa take " lallai Diyana kinyi nisa can. Wani irin duka da Billy tayi mawa baba Barau a tsuliyan sa yasa su duka dakatawa daga maganan da suke yi. Wani ƙara sukaji tauuuuu ,wanda yasa Sumayya rintse ido ganin yanda Billy ke dukan buran sa tana karairaya jijiyoyin. Cikin sauri Yusrah ta fuche tana faɗin nidai ina jirar ku daga waje... Sumayya ne tabi bayan ta tana faɗin nima dai haka , nan itama Safna tayo waje , suna jin gurnanin baba Barau. Wanda Laurat cewa take a ƙara masa suyi masa raga raga wurun ya tashi aiki . Duka Diyana da Billy suke yi wanda kamin wani lokaci Barau ya sume gau ko mutuwa ne Allah ma sani. Buran sa kuwa tayi himmm ta sunduma suntum dagani kasan aƙwai gyara. Laurat ne ta ɗaga wuƙar Bilkisu tana cewa " Nifa Wallahi Allah naso a ƙara masa sabuwar kaciya ne.

Jin haka Bilkisu ba hankali hannu takai tana amsan wuƙar ,keee Billy a'a Fah buga ƙoton wuƙar tayi a gindin Barau , duka sukayi masa a duhu wanda basu san ya sukayi dashi ba , jin kiraye kirayen Sallar subahi na farko yasa su saurin fitowa suna barin gidan cikin hanxari . Hotel suka nufa bayan fitowar su direct , suna cewa " Yau zasu shiga ma Ɗan Asabe shima cikin dare suyi maganin sa.

****

Room 5 up suka kama su duka , wanka sukayi kana kowacce ta gabatar da sallahn shiga Masallaci na subahi. Yusrah ne da Diyana suka ce zasu fita don suyi ma Waiter magana yana kawo masu abincin da zasu ci.

Suna tsaye ne sai ga wata mata tazo wucewa Hjy ce matashiya mai filfilin Naira. Dagani kasan wata ce a gomnati ƴar siyasa ,magana tayi mawa Waiter din tare da sanar masa ɗakin da zai kawo mata nata...tana yi mawa Su Diyana sallama haɗi da wuce su. Juyawa sukayi suna cigaba da mawa waitern magana , sai ga wasu mutane maza su uku sun taho . Tambayar waitern sukayi ɗakin da Hjy Addiya take . Jiki na rawa waitern ya faɗa masu....kai bawan Allah Baka da hankali ne baka ga irin mutanen bane daganin su kasan makasa ne zaka faɗa masu room ɗin da take?". Diyana tayi maganan tana kallon waitern a zafafe.

Hjy baki san komai ba ,kuma ba xaki fahimta ba, wannan matan ƴar siyasa ce babba wanda ta riƙe makamai Yanxu sanate take nema , bakyajin ana Hjy Addiya to itace wannan. Kinsan dama ƴan siyasa wasu rayuwar su na cikin haɗari musamman mata. Duk yanda akayi suna wani ja injan da wani babban ne ,shine yasa azo ayi mata komeye Allah ma sani.

Nisawa Yusrah tayi kana tace " Ba matar Aure bace ba ? Me ya kawota hotel?. Ƴa gaskiya Hjy Addiya yanda nasani bata taɓa Aure ba...bata da iyaye ma ,shi yasa wasu ko nace ƴan hamayyan ta kece mata shegiya marar asali. Asalin ta gidan marayu , data girma ne tabar gidan marayun ta faɗa har kar siyasa. Keee Yusrah yanxu Meye Abun yi?'. Diyana tayi maganan tana kallon Yusrah...hannun ta ta kama cikin sauri suna nufar room ɗin su...

***

Addiya ne ta juyo tana kallon majiya ƙarfin mazan uku da suka shigo mata ɗaki kana tayi murmushi tana cewa ' basai na tambayi wani abu ba nasan wanda ya aiko ku?'. Meyace kuyi mun? Saboda na san shi lusari ne ,wanda yakasa fuskar mace mai kamar maza wato Ni Hjy Addiya ya aiko ku hummm ina sauraren ku. Wani ne daga cikin su ya sauke maƙar mask ɗin da suka sa a fuska yana cewa " Kashe ki aka biya mu kuɗi muyi ...yanxu shi ne kuka zo yi. To Bismillah ai mu munyi tawakalli da annabin Rahma, babu abun da wani ya isa yy mawa bawan shi ba tare da Allah ya hukunta ba.... Tabbas maganan ki haka take domin kuwa indai muna nan ba zamu yarda wani ko waye ya cutar dake ba ,kince kinyi tawasalli mu mahaka.... Muryar Su Sumayya ya katse su da suka shigo su kusan biyaar...Laurat, Summy, Diyana, Billy, Yusrah, Safna. Kallon su Adiyya tayi kana tace " Yara daku Meya kawo ku? Ku gudu ku ƙwaci kanku , rayuwar nan abun gudu ne ,kar wani abu ya taba lafiyar ku a yanda kuke.

Cikin su ba wanda ya bata amsa , sai Bilkisu da ta kalli mazan tana cewa " Basai nace maku bana ji ba ,ina ji! Nice nan Bilkisu tantiriyar ƴar.....Fashi!!! Suka ƙare mata maganan. Kallon su tayi nan taga sun sauke mask din sai taga duk tasan su yaran su ne. Buɗe baki sukayi suna cewa " An gama Billy queen Zamu koma ga honorable Albarkacin ki zamu aika shi ƙiyama. Hakan yayi kyau ,shine abun da Bilkisu tace . Hannu suka haɗe na jinjina ga resu su tantirai. Yayin da Billy ke cewa gyara gyara dai.... Itama tana haɗe hannun irin nasu , nan a lokaci daya ta rigiɗe ta koma su.

Fichewa sukayi suna faɗin Fatan nasara Billy mai tausayi.

Ku mu tafi ko? Bilkisu tayi maganan tana kallon su Sumayya da suka saki baki...Humm muje sukace suna kallon ta.

Hjy Addiya ne tace " Kun taimakeni a lokaci n da nake buƙatan taimako ganin ku a hakq da nayi ,sai naji ina ma Allah ya bani ku ka kasance ƙanni a gareni,duk mahaifiyar da ta haife ɗaya daga cikin ku tabbas Allah ya bata ƴaƴan baiwa , yanda kuka zo kuka riƙe hannu na ,ku ka taimake Ni sai naji ina ma mu riƙe hannayen juna mu cigaba da tafiya ta har ƙarshen rayuwa?". Murmushi sukayi duka yayin da Sumayya tace " me zai hana?". Mu riƙe muje mana kawai ko me kuka ce?. Hakan yayi sosai. Cewan su duka suna kallon Sumayya dake murmushi. Cike dajin daɗi Addiya tace Ku mu zauna yanxu waiter xai kawo mana abinci Kowa sai ya faɗa abinda yake buƙata.

A'a ba munƙi bane , waitern nan ba zai kawo ba , Yusrah tayi maganan tana kwashe masu duk yanda sukayi da mai kawo abincin , dariya suna da , Addiya na haɗa kayan ta a tare suka nufa room ɗin da Su Sumayya suke.

****

Ɓangaren Khamal kuwa tun da Umma tace masa Sumayya tayi tafiya hankalin sa yaƙi kwanciya , a daren ranan ne a baccin sa duk wani abu da Sumayya sukayi kaman an masa vedio a gaban idon sa ya faru. Farkawa yayi da addu'a yana faɗin Sumayya ta koma yawo da ƴan fashi inalallahi wai'ina ilaihir rajiun...dole Nasan Abinyi a satin nan Su Abba su Ɗaura mana Aure , wa'annan ƙawayen nata Duk ban yarda dasu ba daman haɗuwar su ba gaskiya.

****

Ɓangaren baba Barau kuwa gida ya cika harda ƴan jarida asibiti aka nufa dashi kai tsaye...anan mutane suka tsinci takarda n da suka rubuta da manyan baki tare da rubuta Lady boss a ƙasa tare da faɗa mawa mutane dalilin masa wannan duka da rauni. Nan take kowa yafara masa alah tsine. Ƴan jarida kuwa an samu abun rahoto. Baba Barau kuwa a asibiti nan likitoci suka shaida abun nasa ta tashi aiki ,sai dai a yanke ta duka. Wanda ba musu ƴaƴan shi maza suka sa hannu nan aka shiga da shi tiyata ana yanke masa gindin yadawo shafino.... A lokacin ko da ya farka daga shi naɗe da bandage ihu yasa yana ɗauke wuta ya sume nan take. Labarin da yabi unguwa da meaning ɗin LADY BOSS yasa ɗan Asabe tattara yana shi yana shi yana guduwa da shirin barin Lagos a cewan shi baxai ƙara ƙwanan Lagos ba...don duk inda kabi a cikin garin Lagos maganan lady boss akeyi ,Wanda Nan take wasu suke kirar su da ladies ɗaukar fansa . Yanda suka jera sunayen nasu ne aka fara watsawa a magazine da jarida ta ko ina da gidajen tv na Lagos zuwa ko ina na Najeriya ,cewan wasu mata sun fito masu ɗaukar fansar zalincin su da akayi. Tare da rubuta harrufan da suka rubuta kaman haka... L-Laurat A-? D-Diyana Y-Yusrah B-Billy O-? S-Summy S-Safna....wannan abu shi yake yawo lungu da saƙo tare da watsawa gari gari na Najeriya.wannan yasa nan take Ɗan Asabe cewa " Wallahi Sumayya ne da Lauratu da wannan yarinya da akace tabace ashe fyaɗe yayi mata , yanxu gashi nan sun fara ɗaukar fansa . An yanke ma Barau gindi. Shi idan suka zo masa da hannun su zasu yanke ...tuno da muchiyan da Lauratu ta taɓa buga masa yasa shi fitowa da kayan shi aka yana tafe yana cewa " Wallahi zasu aikata ..zasu aikata. Binsaa da kallo Mmn mujahida sukayi suna Ɗan Asabe lafiya? Bai bi takansu ba ya fuche yana faɗin wallahi baxan zauna ba. Mmn fati ne tace anya ba sihiri akayi masa ba , maza kira maza su riƙe sa kar yayi dawa...jin haka da Ɗan Asabe yayi kuma tabbas yasan za'a kama shin yasa shi rugawa da gudu da kaya aka yana wani irin gudu haɗi da barin layin....Tabbas maganan ki ya tabbata cewan Rita tana buga mawa mijin ta kofa akan su fito a taro Ɗan Asabe ya hauka ce ....

***

Shigowa falon hjy Juwairiyya Khamal yayi dai dai kirar Abokin Fahad na shigowa , wanda ya kira shi ya sanar masa labarin da yake ji a BBC na fitowan Ƴammata wai su LADY BOSS....dai dai yana ɗaukar kirar ne shima yaga Hjy Juwairiyya na zaune tana kallon latters din sunan LADY BOSS da ake fidda ko wani harafi ana fassara shi kaman yanda suka aje a rubuce.......... Fahad ne ya katse Khamal da cewa " malami na kiraka ne ka daina kirar Sunan Summy na da LADY BOSS kaga bosses Nan ba ita ba....ɗauke wuta Khamal yayi na tsawon.............

*AUNTY AISHA MMN TEDDY* [9/24, 8:51 PM] ANTY AISHA MMN TEDDY: _🕊️MY LADY BOSS🕊️_