33-34
by @mamanteddy
_Littafin my lady boss na kuɗi ne , Regular payment₦300 vip payment₦500 special₦1000 via 6037312299 Mohammed Aisha keystone bank ko ki tura katin MTN ta wannan number *** ban yarda kika karan ta mun idan baki biyani ba , haka kema don Allah kar ki fitar mun ,duk wanda ya karanta bai biyani ba shida Allah._
***
Dariya Fahad yasa masa don bai san dalilin yin shirun nashi ba , koda Fahad ya datse kirar Khamal bai motsa daga inda yake ba kuma bai sauke hannun sa daga kunnen sa ba tare da wayar . Mutuwar tsaye kawai yayi ,ya rasa sanin inda natsuwar shi take. Muryar Mom Juwairiyya ne yaji tana cewa " Kai kuma lafiya? Kana tsaye da waya a hannu ? Naga mood ɗin ka chanja a lokaci guda ne Khamal ? Ta ƙare maganan tana watsa masa idanun ta ,tare da zaman jirar amsan sa gareta.
No mom Ina zuwa! Yayi maganan yana juyawa tare da barin falon cikin zafin nama. Cikin sauri Mom ta miƙe tsaye tare da kirar sa Tamkar wanda bataga fitar sa ba. Tabbas Aƙwai wani abun , window ta nufa tana leƙawa sam ta manta da Oruma dake tsaye tana kallon komai. Au ɓangaren Hjy Ramlah yayi kenan? Tun da itace Uwar shi Kuma uban shi. Bari na kira Hjy naja'atu na shaida mata domin kuwa dole asan yanda za'ayi masu farra'ƙu a rabasu hattanana.
Tayi maganan tana hayewa stairs da sauri tare da barin falon .
****
Labari a layin su Malam Ilu Lagos ya gama waɗewa cewa " An yanke gaban Baba Barau ,kuma Ɗan Asabe ya gudu. Wannan yasa nan danan yanda labarin ke zagayawa ya koma kunnen su Summy. Wanda jin haka yasa Addiya cewa" Su koma gida Zaria kasancewar Ɗan Asabe haifaffar can ,dole can zai koma. A ranan suka nufi tasha da wuraren la'asar ...zama sukayi moton na yin saura mutum ɗaya kasantuwar ƙaramar moto ce . Juyawa sukayi ganin wanda ke gyefe guda sai zare ido yake .... Ɗan Asabe suka gani ya haɗa gumi ,sam baya ganin gaban sa sai kalle kallen wajen taga yake na marasa gaskiya....Au kaine ??? Yaji Muryar Lauratu ya katse sa,wanda yasa su Bilkisu duka kallon wanda take mawa maganan wato Ɗan Asabe ...kallon su yayi yana faɗin inalallahi wai'ina ilaihir rajiun...
Kuyi manage plz zuwa safe. [9/25, 11:02 AM] ANTY AISHA MMN TEDDY: _35-36_
_Littafin my lady boss na kuɗi ne , Regular payment₦300 vip payment₦500 special₦1000 via 6037312299 Mohammed Aisha keystone bank ko ki tura katin MTN ta wannan number *** ban yarda kika karan ta mun idan baki biyani ba , haka kema don Allah kar ki fitar mun ,duk wanda ya karanta bai biyani ba shida Allah._
Ina kuke masoya ga sabon littafi Mai ɗauke da darussa na rayuwa tare da nishaɗantarwa daga Alƙalamin Maman nusaiba...kunsan sunan littafin kuwa? A'a bamu sani ba ,nasan wannan shine amsan ku gare Ni, ABBA NE! littafin complete zaku same shi Inshaallh akan ₦300 masu buƙata zaku na iya tuntuɓar wannan Number +966599791573 domun ƙarin bayani mun gode!
***
Dariya Sumayya ta gimtse tana kallon yanda Ɗan Asabe ke rarraba ido yana watso masu ,wanda ko shakka babu yasan sune LADY BOSS ɗin da'ake magana. Au wai tsoro kake ji? Laurat ta ƙara maganan tana kallon yanda jikin shi ke rawa kar-kar . Yusrah ne tace ma driver me moto jah muje ! Leƙo da kansa drivern yayi yana cewa " Muje ina saura seat ɗin mutum ɗaya. Muje zamu biya ka . Jin haka yasa driver saurin shiga yana barin tasha dasu , Yayin da Ɗan Asabe ke addoui barkatai wasu baima san me yake faɗi ba. A tsakiyar daji Bilkisu tace Ya tsaya ya dakata da tuƙin , parking yayi a gyefen hanya shima kan shi yanxu ya tsorata dasu Sumayya ...sai yanxu yake danasanin ɗaukar su da yayi , sai kuma a sannan ya lura da Kama Ɗan Asabe sukayi .
Driver fita ka bamu wuri xamuyi magana . Jiki a sanyaye driver ya fita , yana cewa " Ƙannina kudau lura ku sani a jeji muke yanxu miyagu mutum da aljan sun yi yawa. Muma shegun kan mu ne...Diyana ta basa amsa tana Matsawa kusa Da Ɗan Asabe dake haɗa gumi ,hannun sa na akan wandon sa , don tunanin sa shima kar yazo suyi masa Raga-raga irin na Bana Barau wanda daga ƙarshe a yanke gindin ,idan akayi masa haka kuma shi ankashe shi ....Kuyi haƙuri don Allah na roƙeku. Na kuma haɗaku da iyayen ku...A lokacin da kake buga mata gotso kayi fata fata da durin ta wani magiya ne batayi maka ba ,saboda zalinci da mugun ta ,sai a yanxu zaka san Allah ɗaya ne?. Lauratu kuwa Allah ki duba iyaye kar ku cire mun !! Ƙyaƙyaƙyaaaaa suka wani sheƙe da dariya ,kamin Lauratu tace " A'a Fah ƙwantar da hankalin ka , marainan kawai zamu cire. Ta ƙare tana dariya har da hawaye . Bilkisu ne ta kalle ta tana cewa " Haka kike so ayi masa?".
Ɗan kallon ta Lauratu tayi kana tace " A'a ku rabu dashi ai a hakan mun firgita ɗan banza ,ku bashi takarda da biro ya rubuta mun takardan saki yanda idan xan koma gidan iyaye na,na koma ba wani nauyi nasa. Yusrah iyayen boko tuni aka fiddo da takarda ɗan Asabe suka baimawa jiki na rawa ya rubuta takardan hannun shi na rawar ɗari . Yana gama rubutawa Laurat ta ɗauka tana cewa " Ka taimaki kanka. Kallon su tayi su duka tana cewa " Mu yarda dashi anan ya ƙara gaba. Sumayya ne ta buɗe masa murfin moton tana cewa " To ɗan Asabe sai wata jiƙon . Suna anxaga shi waje , drivern suka kira ta jah moton suna barin Ɗan Asabe a tsakar dajin Allah babu komai sai ƙarar guguwa....
Hjy Adiyya ce tace masa Driver ya juyar dasu zuwa airport , domin jirgi zasu bi na daga Lagos zuwa Kaduna ,wanda hakan akayi driver ya juya dasu jiki na rawa bakin shi na furta Hajiya sama Hajiya ƙasa.
****
Me nake ji wai shin Alhaji da gaske ne an ɗauka Auren Khamal da Sumayya?. Hjy Juwairiyya tayi maganan tana miƙewa tsaye tare da dafe ƙirji tana fiddo da idanun ta na jirar jin amsa daga bakin Daddyn Khamal. Khamal kuwa kansa na ƙasa tun da Mom ta fara magana bai tanka mata ba. Tabbas haka yake Juwairiyya , tun da yaron nan ya nuna yana son Sumayya , Kuma shi aure ga Yaro ɗanamiji da ya isa....ya isa don Allah Alhaji ya isa??. Wato Ni bare Ni bana da iko a kan gidana kuke keda gida. Ni ba xa'a so haɗa tsitso sani ba shi yasa Har aka ɗaura Aure cikin munafurci ba tare da sani na ba. Inba rashin ƙauna ta ba da rashin son Ni nawa jinin ai tun kamin Khamal yakai haka nake ce masa ina Son na haɗasa da Binafa , yawan jin haka da faɗa da nake yi yarinya ta ɗauki Son duniya ta ɗaura masa ,to Wallh baxai yiwu ba ,sai dai ayi biyu. Wannan ai rashin adalci..... Subhanah Hjy Juwairiyya da girmanki kuke wannan hayaniya? Cewan Hjy babba da take shigowa tare dasu Umma da Abba ... Kaiyaaaa gaskiya banji daɗin jin irin wannan kalami daga bakin ki ba. Baba na shi yace " Yana son Sumayya , kuma a lokacin da aka maida Auren Hjy Ramlah ya roƙa a bashi ,nan kuma take yabada komai , kuma nima na yarda aka daura auren sa amma batare da kowa ya sani ba ciki har da Itama Uwar yarinyar yau yanxu take jin wannan Auren kaman yanda kema kike ji yanxu. Kuma Ni bansaba mawa yarana Auren dole ba baxanyi akan jika na ba.
Eyya Hjy babba kiyi hakuri ba'ayi haka ba dole Hjy Juwairiyya ta ɗaga hankalin ta....Cewan Umma da take gyefen Hjy Juwairiyya da take ta aikin kumburin wuya . Hjy babba kiyi hakuri yanxu komai kibar shi a hannun mu ..Ni a matsayina na mahaifi ga Khamal na yanke hukuncin Za'a ɗaura Auren sa Ga Binafa a satin nanan tarewa kuma duka za'ayi tare dana Sumayya a mako biyu masu zuwa. Sai a fara shiri , Khamal inason magana dakai. Abba ke maganan kai tsaye ba tare da ya duba ko yayi makowa daɗi ba... Murmushi Hjy Juwairiyya tayi tana faɗin to hakan ma yayi ai yanxu naji batu , alhmdllh. Nisawa Umma tayi a hankali tana kama hannun Khamal tana shafa masa alamun rarrashi akan maganan da Abba yayi kar ya jah , wannan yasa shi haɗa ido da Umma idonsu ne suka gauraya cikin juna ,nan taga damuwar da bata taɓa gani ba. A hankali ta motsa bakin ta tana cewa " Allah yabaku zama lafiya. Bai bata amsa ba ya janye hannun shi yana bin bayan Abba, wanda ko ba'a faɗa maka ba kasan ranshi a dagule yake.
Daddy ne ya juya yana kallon su Umma kamin yace " gida ɗaya zasu zauna ,kuma sannnan bama buƙatar komai naku , dukan su mu xamuyi masu komai na ɗaki ku rarrashi Sumayya sosai don bata san maganan ba. Gyaɗa masa Kai Umma tayi kana tace to. Shima barin falon yayi kamin Hjy babba da ta gama ƙufuluwa ta juya fuuuu tana barin falon hjy Juwairiyya. Umma ne ta kalli Mom kamin tace " Muyi masu Addu'ar Allah ya basu zaman lafiya. To Amin Fah sai ki ƙara ƙwantar mawa Ɗan naki Khamal da hankali dole ya rungume dukan su a matsayin matan sa banda banbanci don idan hakan ta faru baxan ɗauka ba. Hjy Juwairiyya ke maganan a siyasance take faɗin mawa Umma maganan wacce bata tnka ba har ta bar falon.
***
Sumayya sai da suka sauka gidan Hjy Adiyya kamin wuraren yammaci suka nufo gidan Umma. A farfajiyar gidan a ƙarƙashin tampol ta hango su Abba da Daddy sai Khamal da fuskar shi babu annuri. Gaishe dasu Abba sukayi , kana su wuce zuwa Part ɗin Umma , wanda a zuciyar Sumayya cewa take " Kullum mutum babu walwala a haka dai , Allah ya kyauta .
Khamal yanxu inaso kaje kuyi magana da Binafa , kaga Sumayya mai sauƙ ne lamarin ta ,gida ɗaya kuke , ina so ka kwantar da hankali n ka. To Abba ,abun da yace kenan yana nufar moton shi ,don shi yasan matsalar sa a yanxu ba Binafa bane Mom ce Da Ammien ta sune kanwa uwan gami . Nisawa yayi a moton sa yana cewa " Har ace na ƙwantr da hankali na , xa'a bani mata biyu a rana ɗaya ? Wanda ko iyayena matan su guda guda ne ...Ni tsiwar wannan yarinyar yafi damuna ,da haukan ta yayi maganan yana tuno da zaman ta a Companyn sa , maganan ta ya tuna tana cewa" Ba zama da taɓa laptop nazo ba , aikin motsa jini nazo ban saba zaman banza ba....ina Sonki Sumayya son da bansan iyakan sa ba. Tun kina yarinya sunanki a bakina masoyiya,sai dai baki taɓa cewa kina sona ba ,sai nuna mun tsana...Tabbas zaman mu da kallo, don baxan ɗau wargin ki ba koda nake Sonki!
*AUNTY AISHA MMN TEDDY* [9/25, 1:31 PM] ANTY AISHA MMN TEDDY: _🕊️MY LADY BOSS🕊️_