5
by @mamuhgee
Aasiyah
Mamuhgee
5
Ana kokarin kiran magrib ta kammala wankin ta bawa khamis ya dauka yaje yakai yana kaiwa kuwa aka basa kudin sai kawai bai dawo gida ba ya wuce gurin Baba Ashiru wanda basu dawo gida ba sai bayan ishai da wata soyayyar awara mai dan yawa da gurasa ya tada bulama da Jamilu da sukai bacci ya ajiyesu gaba suka zagaye suka ci suka koshi bayan ya dibi awara uku da yankan gurasa biyu ya bata suka sha ruwa suka gyatse sukai kwanciyarsu suka barta zaune da zallan mamakin khamis da damuwa mai tsanani sbd lamarin ya fara tashi daga hankali.
Da safe bata kyale khamis dinba bayan fitar baban ta masa fada sosai fadan da nuna masa baci ranta ya bata hakuri amma tana gamawa suka fice shi da bulama aka bar jamilu daga ita sai shi dan haka dole ta fara dubarar abincin da zaici da rana kafin ya fara mata kukan yunwar rana sbd sam basada hakuri ko kadan su dai kawai abasu shi suka sani.
Babu aikin wankin da aka kawo mata yau dan haka sauran shinkafar data rage gwangwani biyu ta dafa ta ajiye musu itada jamilun su ci tinda ba kowa a wata kula mara murfi ta rufe da plate ta wuce tayi wanka ta nufi daki ta dan kwanta dan hutawa kafin lokacin sallah yayi.
Bacci ne ya dauketa mai dan dadi da karfi sai guraren karfe daya da rabi ta farka a natse tareda tashi zaune tana jin jikinta yayi nauyi musamman cikinta.
Fitowa waje tayi tsakar gidan shiru bata ga jamilu ba bataji motsinsaba,
Buta ta dauka ta nufi bandaki ta kamo ruwa ta fito tayi alwala ta koma daki tayi sallah a natse cikin sanyi.
Fitowa tayi bayan ta idar ta nufi dakin yaran ta leqa taga jamilun baya nan
Bude baki tayi ta dan kwala kiransa tana kallan hanyar kofar fita.
Shiru bai amsaba alaman baya nan dan haka ta nufi kitchen tana isa taga shinkafa a qasa kadan kadan alaman anci abinci ta kalli inda tabar kular abincin taganta a bude plate din data rufeta ma a gefe yashe.
Isa tayi ta leqa kular taga babu komai ancinye abincin tas.
Mamaki mai girma ta shiga sbd sanin jamilu kadai kila bazai iya cinye abincin shi kadai ba dan haka ta fito damuwa na shigarta ta sake kwala masa kira sbd yunwa take ji mai karfi duk da daman bazata taba tina yaushe ta taba ci ta koshi a gidan ba kullum yunwa ce abokiyar rayuwarta fiyeda komai.
Jiri taji yana neman dabanta sbd numfashi ma daqyar take jansa sosai sbd rashin karfi da kuzari na yunwa,
Zaunawa tayi a tsakar gidan tana dafa tsohon cikinta daya dunqule guri daya shi kansa,
Numfashi ta sauke ahankali tana jin idanuwanta na dan cikowa da hawaye amma bazasu taba saukowaba sbd batasan wa zataiwa kuka ko hawaye ba tinda yayanta ake magana batason zubar musu da hawaye ko kadan duk qunci da rashin jin qai da suke nuna mata sbd batason Allah ya kamasu da hakan ko ya sakasu a jarabawa mai girma dan shine ciwo da quncinta fiyeda komai na sanin Allah saiya jarabcesu da wannan abubuwan da suke mata amma tanata rokon Allah kada ya kamasu da wannan laifin tana yafe musu komai akoda yaushe gasu yara wani abubuwan duka quruciya ce.
Tana nan zaune shiru batasan me zataiba bayan shan ruwa kusan kofi biyu ta cika cikinta dasu harma wani amai taji yana taso mata amma hakanan ta daure ta zauna tana karatun Al'Quran dinta wanda tinda taxo gidan dashi tazo dan haka ya dan tsufa kuma shine abokin rayuwarta a gidan fiyeda mijin da yayan data haifa wainda kaf duniya tana ganin nata yayan ne daban haka.
Sai bayan laasar jamilu ne da bulama suka fara shigowa gidan kowannensu riqe da rake mai kauri da dan girma.
Kallansu tayi tana amsa gaisuwan da bulama yayi mata tana maida kallanta akan jamilu wanda yayo gurinta yana nuna mata rakensa tace
"Jamilu ina ka tafi?
"Gurinsu Baba naje nima"
Kallansa ta kuma yi tace
"To kaine kaci abinci kafin ka fita ne kokuwa haka da yunwar ka tafi?
Bai kalleta ba ya nufi ruwa ya diba a ranta yasha kafin yace
"Na dauka ne nakai can mukaci tareda su baba dasu khamis saina dawo da kulan na sake komawa"
Zuba masa ido tayi tana jin wani irin nauyi mai tsananin daci yana danne kirjinta sbd yanda ya tsallaketa batareda tinaninta ba ya dauki abincin gabaki daya yakaiwa babansa da yan uwansa suka cinye abincinda baida yawa yaron da bai wuce shekara tara ba.
Dauke idanuwanta tayi daga kansa ta maida akan bulama wanda ya zauna yana shan rakensa hankalinsa kwance..
Babu mai niyyar san mata duk da ba sha zataiba.
Bata sake cewa komaiba har baban ya dawo tareda khamis dauke da ledar katon bread da sugar da madaran sachet da suka siyo.
Sannu da zuwa tai masa ya amsa yana cewa ta dora musu ruwan zafi idan anyi magrib zasu sha shayi.
Bude baki tayi tace
"Babu gawayi a gidan ya qare"
Kallanta yayi yana matse fuska amma dai bazai bata ransa a banza ba yana cikin dan farin cikinsa na wannan dan aikin daya samu zaiyi kwana biyu sosai yana samun yan kudadensa da yayansa.
Dari biyu ya ciro ya bawa khamis yace
"Miqa mata a siyo gawayin"
Shima khamis din cikin yar walwalansa yake dan haka gaidata yayi ya bata yana juyawa zai wuce tace
"Kaje ka karbo gawayin"
Buta ya dauka yana cewa
"Mama dan Allah bulama yaje bandaki zan shiga ni"
Bulama na jin hakan yace
"To ni bakaga rake nake sha ba shine zaka ce ni,ni gaskia sedai jamilu yaje ai kulluma na nine nake siyo mata yau sedai wani yaje"
Jamilu na jin hakan shima ya kwala kiran sunan babansu yana cewa
"Baba,baba kaga zasu saka a aikeni ga magriba tayi kace na dena fita da dare"
Fitowa Ashiru yayi duk yana jinsu ya kalleta yace
"Maryam ki daure kije mana da kanki kina ganin magriba tayi zaki aika yara gidan mutane kuma baki ganin dik abinci suke ci,daure kije ke kinji"
Yana gama fadar hakan ya juya dakinsa ya koma dan tubewa yakeyi wanka zaiyi.
Khamis na jin hakan yaqi fitowa da wuri har sai dayaji fitar wani alamar wani ya tafi siyan gawayin.
Yana fitowa dakinsu ya fada ya saka wasu kayan ya fito yana kallansu bulama yace
"Kai bakaje ba Mama ka bari taje dan ka rainawa mutane wayo ko"
Ko kallansa bulama baiyiba yaci gaba da shan rakensa.
Babansu ne ya fito ya dakatar da rigimar tinda maryam din ta tafi da kanta.
Tana dawowa batacewa komaiba ta nufi kitchen ta ajiye ta fito ta kalli yanda sukaiwa tsakar gidan kaca kaca ta kalli bulama tace maza yayi shara yanzun nan.
Miqewa yayi ya dauko tsintsiya zai fara kenan bababsu ya fito daga bandaki ya kalleta yace
"Yanzu maryam sbd rashin lissafi ana kokarin kiran magriba zaki saka danki shara salon ya share kan wani aljanin ki janyomun masifar da batada magani"
Kallan tsakar gidan tayi tace
"Idan aka kwana da wannan sharar da suka tara tsinnaku zasu mana yawa ne kuma sune suka bata gurin lafiya kalau suka tarar dashi"
"To dan sun bata sai akace saisun share majalisar aljanu?
Bakisan da magrib tayiba suke baje nasu majalisunba kana musu ganganci zaka ga ganganci,
Kinga dan Allah banason fitina da neman damuwa ana zaune kalau abar sharar nan harda safe kawai"
Bulama na jin hakan ya ajiye tsintsiyar da sauri yana cewa
"Mama to bari na hura miki wutar"
Kitchen ya nufa ya hada wutar yafara kokarin hura mata sbd duk sun iya dan tana sakasu aiki sosai idan ubansu baya nan kuma kafin su sake girman hakan.
Ana gama sallar magrib ruwan shayin ya hadu ta juye ta kawo musu a tabarmar dayake zaune da yaran sun zagayesa sunata firarsu da farin ciki sosai dan shine babban farin cikinsu a rayuwa.
Tana ajiyewa ta tafi itama dan yin sallah tabarsu a gurin.
Khamis ne ya hada musu shayin ya zubawa kowa tareda cikawa kowa kofi ya barwa Mamansu nata suka fara sha cikeda farin ciki da murnar yau shayi sukesha hadda madara abinda sai dace dace.
Maryam sai data gama sallah ta jima kafin ta fito.
Batai tsammanin zasu rage mata ba sai gashi aka miqo mata harya huce baida wani zafi ta karba ta koma gefe ta zauna a kujeran tsuguno ta fara sha a natse tana sauraran firarsu da jamilu ke kokarin sakota yana fada mata kalan abubuwan da babansu ke siya musu suna ci a waje tana jinsa tana murmushin karfin hali da gyada masa kai shi kuwa baba Ashirun sai murmushin jin dadi da kaunar yaran yakeyi yana sake jin matiqar yana samu komai zai iya siya musu dan su sosa su kaunacesa fiyeda komai da kowa duniya dan yanada babban buri akansu mai girma.
Tana gamawa miqewa tayi ta tattara kayan takai kitchen ta wuce daki tayi sallan ishai daga can ta fito taje ta gyara musu shimfidar kwanciya sbd jamilu dayake qarami tana gamawa ta shige ta kwanta sbd ko fira basa wani yi da ita itama batason firarsu sbd duk wtaa irin rayuwa ce Baba Ashiru yake dorasa akai yana kwadaita musu ta abinda ba lallai su samu ba shiyasa bata iya zama cikinsu.
Aurenta da Ashiru shekaru kusan goma sha biyar da yara uku,Khamis shine babba 'dan shekara goma sha hudu,sai bulama wanda yake shekara sha uku da watanni sbd babu wata tazara sosai tsakani,
Jamilu shine qaraminsu dan shekara tara da dori shima sai tsohon ciki na yanxu.
Rayuwar datake tsakaninta da mijinta da yaranta zuwa yanxu da zuciyarta take kasa dauka tafara tinanin yanda zaayi su koma hannun mahaifinta da zama duk da ya tsufa sosai amma amma acan zasu fi samun tarbiya da dawowansu a hanya mai kyau dan anan ko tayi aikin banza ne mahaifinsu ne wanda sukafi so dan haka sukafi daukan tasa tarbiyar.
#MAMUH
#LOVE
#SECRETS
#REVENGE
#FAMILY
#SELFISHNESS
#THE BINNAH'S
#SAM BINNAH
#AASIYAH
***
***