AASIYAH

6

by @mamuhgee

Aasiyah

Mamuhgee

6

Washe gari haka ya tattara yaran ya fice dasu gurin aikin nasa suka barta ita kadai ta wuni a gida baci bare sha haka ta wuni da yunwa sai ruwa data ringa sha tana cika cikinta dashi yakai ruwan dawo mata yakeyi,

Yamma lis aka kawo mata wani wanki mai yawa haka ta tashi da karfin hali ta lallaba ta fara wankin sbd tana tsananin buqatan kudin dan samun na cin wani abu ko babu yawa.

Sai daf da ishai ta gama wankin ta dauka da kanta takai musu daman bata shanya anan duk wankin da zatai sbd kaya bacewa sukeyi ita kanta saita rasa garin yay hakan yake faruw dan haka sedai tayi wanki duk yawansa ta kai maka gidanka ta shanya maka ko ka shanya da kanka.

Kudin data karbo na wankin daqyar ta iso gida sbd tsananin zazzabi da sanyin wankin datai takeji sosai da gaske yunwarta ma harta gama cinyeta dan haka kunun dare da akeyi me zafi ta siyo da fanken dare tana dawowa dakinta ta kasa sha sbd amai data ringa yi haka ta kwanta zazzabi mai karfi ya rifeta ta lullabe.

Bata farka ba sai tsakar dare bayan zazzabin yadan saketa ta tashi zaune taga Ashiru na baccinsa hankali kwance dan batasan yaushe suka dawoba,

Fita daki tayi taje bandaki tai fitsari ta fito tayi alwala sai a lokacin tayi sallan ishai tana gamawa ta janyo abincin data ajiye sai kawai taga babu fanken kunun ma ba yawa kadanne ya rage dan haka ruwa ta qara masa kadan ta kai bakinta ta shanye tas a hankali takoma ta kwanta,

Da safe sunata shirin ficewa yaran nata murna da farin cikin bin babansu da sukeyi yanzu tana kallo suka karya kumallo da waina mai miya daya aika aka siyo musu aka ci hadda ita kula biyu aka bata suka cinye sauran tas tana kallo yace sbd su zasu fita aiki suna buqatan abinci suna gamawa suka ficewansu aka barta ita kadai.

Maryam ta fara gajiya,ba gajiyar da bacci zai iya warwarewa ba,

Ba gajiyar da zama na awa ɗaya zai iya ragewa ba,

Gajiya ce da ta zauna a cikin ƙasusuwanta da gangar jikinta,

Gajiya ce da ta shiga zuciyarta da ruhinta,

Gajiya ce da ta fara sakata tambayar kanta ko da gaske akwai wani abu da ake kira godiyar da ake samu daga wanda ka sadaukar da rayuwarka saboda su dan kuwa tsawon shekarun nan ta bayar ta bayar da lokacin ta,

Ta bayar da ƙarfin ta,

Ta bayar da lafiyarta,

Ta bayar da duk wani abu da ta mallaka

Amma duk lokacin da ta kalli mutanen da ta yi wa wannan sadaukarwar sai bata ganin komai a idanuwansu,babu godiya,babu yabo babu girmamawa.

A safiyar ranar Maryam ta farka tana jin jikinta ya yi mata nauyi fiye da kullum ta buɗe idanunta a hankali tana tasowa ta fito daga daki har wani irin zafi takeji duk da akwai hadari ne sosai yayi baqi qirin shiyasa zafin yayi yawa dan haka sai zufa takeyi ta dauki bokiti tana nufar khamis dayake zaune yana wanke rigar babansa tace

"Khamis debomun ruwa a jijiyar kofar gida na watsa ruwa"

Dagowa yayi ya kalleta yana gaidata tareda karban bokitin ya ajiye gefe yana cewa

"To mama bari na gama wanke rigar baba sai naje"

Kallan rigar dayake wankewan tayi ta bude baki tace

"Ka aje ka debomun idan ka dawo saika qarasa mana"

"Mama na kusa gamawa daurewa kawai zanyi fa"

Daukan bokitin tayi ta juya ta kalli bulama daya fito daga bandaki tana bude baki ya fara turo baki yana cewa

"Mama wlh cikina ke ciwo zawo ma nakeyi yanxu haka shi nayi ga yaya khamis nan fa ya gama wankin ko ya kawo na qarasa daurayan sai ya debo ruwan"

Mamaki ne ya sake kamata jikinta na qara sanyi mararta ta kulle ahankali wani ciwo mai kaifi yana ratsa mararta ta ajiye bokitin ta zauna akan kujera ahankali tana dan lumshe idanuwanta sbd abinda takejin ya toshe kirjinta.

Jamilu ne ya fito daga daki yana hamma ya kalleta yace

"Mama ina kwana,yunwa nakeji ki siyamun kunu"

Kasa hakura tayi ta kallesa cikin kulawa da sauran dan hope tace

"Jamilu dauki bokitin nan ka debo mun ruwa a kofar gida ka dawo tukuna kaji"

da sauri ya dauki bokitin yana cewa

"Zaki siyamun kunun hadda kosai ko fanke ko mama??

Gyada kai tayi ahankali daqyar sbd yanayin datake ji da dacin abinda su khamis suka sakata ya saka komai na jikinta tado ciwon mararta gadan gadan.

Daukan bokitin yayi da sauri ya fice yana murna sbd shi indai zaa basa yaci ya koshi tabbas a tsakanin iyayensa to baida matsala.

Ruwan ya debo baifi rabin bokitin ba sbd bazai iya daukosa ba idan ya ciko ya ajiye mata har kofar bankaki yayi kitchen ya dauko qaton kofi da zaa basa ya siyo kunun ya zauna jiranta ta fito.

Ta jima a ciki tana fama da kanta kafin ta fito lokacin iska yafara dan kadawa hadarin yana kokarin tasowa da alaman iska sosai.

Binta jamilu yayi har daki yana neman fara mata rigima dan haka sai ta dauki hamsin din datake da ita ta basa ya fice da saurinsa siyan kunun duk da tasan babansu zai basu abinci idan sun fita gidan.

Kasa komai tayi ta koma ta sake kwanciya sbd da alama naquda taso mata takeson yi gashi kuma bata kai wata tara ba a takwas take.

Tana daga kwance Ashiru ya tashi yayo wanka yana mata magana tana amsawa ahankali sama sama harya gama shiryawa ya fice tareda yaran kaf suka tafiyarsu gurin aiki.

Iska ne ya taso mai karfin gaske hade da ban tsoro dan kuwa rufin gidan kaman zai cire haka iskan ya riga tafiya da abubuwa da dama da wata irin qasa koina yayi jajir da duhu ita dai tana daki kwance jikin takeji matiqa.

Ruwa na fara sauka da wani irin karfin gaske ta miqe zaune ahankali tareda tashi tsaye ta nufi kofa ta fito tsakar gidan ta dauko bokitan gidan da dan drum din ruwanta tana tarawa sbd tara ruwan saman tinda su take sha hakama tinda batada masu debo mata a waje gwara ta tara na saman.

Karfin gaske ne da ruwan wanda tana shiga cikinsu taji suna mata wani irin duka ko gabanta bata gani take jikinta ya dauki rawa amma bata komaba tai karfin hali ta isa ta dauko bokitan duka ta tara.

Rigar Ashiru da khamis ya wanke ta gani a qasa iska ya yar sai ruwa take sha ta sauya kala gabaki daya ta isa ta dauke masa dan tasan akanta zata iya mata baqin cikin da zuciyarta zata iya qarasa bugawa.

Bokiti daya ta dauka wanda ya riga ya cika da ruwa ta dagasa sama zata rage ruwan ciki ta saka rigar tana dagawa ya subuce mata sbd wani mugun santsin daya jata mai karfi tayi sama ta fado a kife ta gefe take wani irin jini ya kufce mata taji kaman mahaifarta ta fashe sbd wata gigitacciyar azabar data ratsata tana saka ganinta da jinta daukewa.

Tafi mintina biyar a gurin yashe bata motsaba ruwa na sauka akanta kafin ta motsa kadan ahankali tana daddafa hannuwanta tafara motsawa tana jan jikinta zuwa daki duk da bata gani sosai.

Jini sosai yake fita daga jikinta ta isa daki da jan jiki tana kokarin dafe cikinta datake jin ya dunqule mata guri daya bakin mararta amma hannuwanta basa iyawa rawa sukeyi sosai.

Tsakiyar dakin ta dakata tana dunqulewa guri daya jikinta na rawa gabaki daya,

Ruwan aka cigaba da zubawa da karfi wanda suka cika tsakar gidan har suka suka fara shigowa dakin datake kadan kadan tana gani sama sama amma bata iya komai.

#MAMUH

***

***