7
by @mamuhgee
Aasiyah
Mamuhgee
7
Ruwan basu tsagaita ba sai yamma dan wuni akai na yinsu sai a lokacin Ashiru ya dawo da yaran sunata murnarsu.
Jamilu ne ya ringa kiran sunanta yana son nuna mata takarman da aka siya masa amma shiru shima bulama kiranta da nemanta ya hau yi sai a lokacin suka shigo dakin suka ganta a zube qasa kaman babu rai a jikinta.
Da sauri suka iso gurinta bulama na ambatar sunanta Jamilu kuwa sunan baban ya kwala yana cewa
"Baba Mama ta fadi da jini sosai"
Dakin Ashiru ya nufo yana cewa
"shine zata shige daki kuma da jinin"
Yana shigowa yaga halinda take ciki saiya kalli khamis wanda ya shigo dakin da dan sauri yana kallanta yace
"Jeka ka kira Iya baraka tazo ta duba inaga haihuwa ce"
Da sauri khamis din ya fita shi kuwa baban ya tura su Bulama waje yana durqusawa qasa yana ambatar sunanta amma bata iya ko amsawa.
Iya Baraka tsohuwar mace ce mai shekaru masu yawa datake dan karban haihuwa sosai tin bata tsufa ba dan haka ma ta dena karban haihuwa sai can can baa rasaba,
Ana kiranta bata wani jimaba tazo sbd tana kaunar Maryam sosai kaman yarta sbd tausayinta da kusan kowa anguwan yake,
Tana shigowa dakin ta nufa kai tsaye ta kalleta cikin duhun daya fara ta haskata taga halinda take ciki take taji hankalinta ya tashi ta fito ta kalle Ashiru tace
"Ashiru wannan ba naquda ce kawaiba gaskia matsala ce babba inaga ayi gaggawan kaita asibiti kaman zaifi dan naga jinin data zubar yayi yawa kuma ko motsi bata iyayi"
Kallanta yayi ya dan yi shiru kafin ya bude baki yace
"Wace asibiti kuma ana zaune kalau iya Baraka?
Haihuwa daman bata rasa yan matsaloli shiyasa nace a kiraki,
Kawai ki dudduba ki taimaka mata ta qarasa haihuwan tinda dai akwai naqudar a ciwon nata tana haihuwa komaima warkewa zaiyi amma nikam sam ban wani kama maganar zuwa asibiti ba tinda duka sauran yayan babu wanda aka haifa a asibitin"
Kallansa Iya Baraka ta kuma yi tana bayyanar masa da shakka da fargabanta tareda tausayin maryam din tace
"Gaskia Ashiru ka daure a kaita asibiti zaifi....
Katseta yayi da cewa
"Ina maganar daurewa tinda ba tauri nakeyi ba Iya Baraka,
Bazan iya daurewan bane dan haka na nemo mata ke"
Komawa tayi dakin tafara taimakawa Maryam din da ganin ko zata iya karban haihuwan amma sai taga babu ta inda ma haihuwan zata fara buqatan masana lafiyar gaggawa maryam din ke buqata dan haka ta fito ta sanar masa nakuda haihuwan ba zata karbu yanzu dole saida masunan lafiya.
Shima cewa yayi ta tafi idan nakudar ta taso gadan gadan zaa sake kiranta amma bazaa tafi asibitin ba.
Tafiya tayi zuciyarta cikeda tsoro da fargaban halinda maryam din take ciki dana haka ko bayan komawanta gida addua ta ringa bin maryam din dashi akai akai.
Shima Ashirun dakin ya shiga yayi mata sannu ya fito ya saka yaran a gaba suka ci abinci har dare ya dan yi sosai tukuna suka shige suka kwanta ya shigo dakin shima ya kwanta yanawa maryam din sannu akai akai hardai yaji bazai iya kwana a dakinba sbd karnin jinin dayake hawa kansa ya tashi ya koma dakin yara ya kwanta acan ya kwana basu fito ba sai asuba yaje sallah da Khamis da bulama suna dawowa bulama ne yaje ya dubata kafin khamis shima sukaje suka sake kiran Iya baraka wadda daman kiran take jira ta sake dawowa.
Maryam dai tayi mugun nisan da ba lallai ta take ba dan haka iya ta sake qasqantar da kanta ta rokesa akan ita zata kaita asibitin da kudinta amma sam yace aa sbd idan ta kaita shi zaa bari da sauran dawainiyar wadda baida abin yinta dan haka a qara jira haihuwan dai tazo da kanta.
Kasa tafiya iya baraka tayi ta tsaya akan Maryam din wadda batada tabbaci tanada rai har lokacin,
Karfe tara ya saka yaran gaba suka fita iya baraka na ganin hakan hankalinta ya sake tashi sbd yau take sake tabbatarda rashin tausayi da imanin Ashiru da yayansa da ake fada akan maryam.
Bayan fitarsu ruwan zafi tasaka ta gyara maryam din ta sauya mata zani har zata tafi taga bazata iya ba ta dawo idanuwanta cikeda wasu hawaye masu tsananin zafi ta fidda wayarta qarama data gama tsufa daga zaninta ta nemo alaman da danta kabiru ya saka mata na sunansa ta saka kiransa.
Yana dauka komai bata bari ya furta ba tace masa gidansu maryam ya dauko mahaifinta da mashin dinsa ya kawo sbd shi kadaine zai iya daukanta yakaita asibiti da gaggawa dan ita batada wannan hurumin.
Tana kashe wayarta ta sake tattara maryam din tafara kokarin dan bata taimakon gaggawa ta hanyar shafa mata ruwa a fuska da ambatar sunanta tana son ko dan farfadowa ne tayi.
Tana cikin hakan kuwa sai ga Baffa kabirun ya daukosa manyanci ya kamasa amma hakanan ya taho sbd jin maryam dinsa ba lafiya.
Kallo daya yayi mata ya sauke ajiyan zuciya da wani numfashi mara karfi baice komaiba yace a fito masa da ita.
Kabiru ne ya samo musu adaidaita aka saka maryam din shima ya shiga aka jasu sai asibiti batareda Iya baraka ba sbd fita rigimar Ashiru.
Kabiru ne ya bisu asibitin sbd Baffan ba komai zai iyaba na yawon asibiti suna isa kuwa aka amsheta da gaggawa anata musu fada sosai na ganin halinda take ciki.
Kabiru na gama masu komai shima tafiyarsa yayi ya barsu asibitin.
Tinda aka shiga da ita baa sake fitowa da ita baa ce masa komaiba sbd kusan kabiru ya biya musu komai kafi ya tafi dan haka ana can ana neman ceton rayuwarta abinda yake cikinta kuma a
Tin suna zuwa ba jimawa aka sanar dasu ya mutu dan haka rayuwarta ta rage a gani idan zaa iya ceta bayan idan ansamu cire abinda yake cikin nata.
Baa fito da ita ba sai kusan yamma lis a lokacin baffa ya taso da gudu bagareda damuwa da tsufansa ba sbd lokacin da ya ga 'yarsa jikinsa rawa yafara da jin duniyarsa na rushewa da radadi ya manta da shekarunsa sbd ita daya ce hasken idaniyarsa da farin cikin dayake dashi a duniyar sai uwarsa data tsufa batama gani sosai.
dogon dakin masu jinya aka nufa da ita aka kwantar da ita gadon da aka basu aka gama mata komai na rubuce rubuce da daura ruwa da allurai aka tafi aka barsa tsaye akanta ya sake sauke numfashi yana kallanta da idanuwansa da sukai jajir har lokacin hannuwansa dan rawa sukeyi amma tinda allah yasa ya samu maryam din yana masa godia mara adadi.
Zaunawa yayi ahankali akan kujeran robar da wani mai jinyar gadon kusa dasu ta miqo masa sbd tausayin yanda yake tsaye jikinsa na dan rawa.
Godia yayi mata yana dan kama jikinsa sosai sbd dakin na mata duka dukda ga maza nan masu zuwa dubiya da wanda matansu suke jinya.
Har dare sosai maryam bata farka ba haka ya kwana zaune shiru sedai yaje sallah ya dawo hankalinsa a rarrabe sbd acan gida itama inna bata tareda kowa.
Bayan sallan asuba maryam ta farfado sedai sam babu sauki a tattare da ita sedai godiyar Allah.
Bayan farkawanta ya tafi gida ya duba inna wadda tace yayi jinyar maryam din kawai ita zatai manaji ta lallaba insha Allah.
Hakan ya saka ya maida hankali sosai gurin jinyar maryam wadda hatta tafiya bata iyawa,
Yaje da kansa ya roki Ashiru ya bada khamis yazo ya tayasa jinyar kokuma yaje gida can ya kula da inna amma bai turo masa khamis dinba ko bulama,
Ya sake komawa harso biyu akan hakan amma babu alaman zaizo dubata shi kansa bare barin yayanta suzo suyi jinyarta duk da yaran sunzo zuwa sosai sbd yanxu da batanan kuma kewanta sukeyi duk da hankalinsu na daukuwa sosai da hidimar gabansu.
Hakura baffan yayi yaci gaba da jinyarta da taimakon wadda ke kusa da gadonsu masu jinyarta mata dake taimaka masa sbd tausayinsa da suke da ita kanta maryam din wadda ko magana bata yi ta zama wata iri sanyinta ya qaru sosai ta zama kaman kurma bayan ido da sukai zurfi babu abinda take dashi.
Jinyar sati hudu sukai tukuna suka samu sallama bayan sun bushe qayau dan kuwa komai nasu ya qare baffa yakai baida komai dan haka daqyar suka ga dai an sallamesu suka tattara suka koma gida.
Suna isa gida suka tararda takardar sakinta Ashiru ya kawo akan laifin ankaita asibiti bada izininsa ba har tsawon wata guda.
Baffa baice komaiba kaman yanda itama inna koda ya aiko yayansa suka kawo batace komaiba karba tayi ta ajiye.
Fata sukaiwa maryam na allah yasa hakan shine mafi alkhairi ga rayuwarta.
Jinyarta taci gaba dayi a gida hankalinta ya dan kwanta duk da zuciyarta na cikeda wani irin radadi da kuncinda harta mutu bazai taba gogewaba sbd ko yaranta ace basu taba zuwa dubata kamarma ya gogeta daga rayuwarsu suma sun manta da ita shi kadai suka sani.
A bangare daya kuma shine Maryam din data shiga asibiti ba ita ce Maryam din data fito daga ciki ba sbd a lokacinda 'dan dayake cikinta ya mutu ya fito ya fito ne tareda kowace sauran alaqa data hada sunan Ashiru dashi gabaki dayansa daga kirjinta da jininta da rayuwarta dan haka koda ta tadda takardar sakinta qarasa cire kammaninsa ma da sunansa tayi a cikin labarinta na baya,
A yanzu ita 'ya ce kuma tana fatar koba akan yayan data haifa ba ta xama uwar da zaa kira uwa mai daraja.
#MAMUH
***
***