1&2
by @nkds
🔥❤️BA DARAJA!!!❤🔥
(True Reality Series)
©® Nainarh KD – 𝓝𝓴𝓭'𝓼❦♡
> Characters grapple with the tension between destiny and personal choice.
⚠️ Copy is not allowed! ⚠️
Ba kuma zan lamunci a canza min labari ko ta wata siga ba.
WRITER'S WORD
Assalamu Alaikum Warahmatullahi Wabarakatuh.
BA DARAJA ba kawai labarin soyayya ko zaman aure ba ne. Labari ne da ke ɗauke da saƙonni masu zurfi game da rayuwar yau da kullum, musamman irin ƙalubalen da mata da maza ke fuskanta a cikin aure da zamantakewa.
A cikin wannan tafiya za ku haɗu da mutane masu halaye daban-daban. Wasu za su sa ku yi farin ciki, wasu za su baku haushi, wasu kuma za su sa ku zubar da hawaye. Amma a ƙarshe za ku fahimci cewa rayuwa cike take da darussa, kuma ba kowane mutum ake gane darajarsa a lokacin da yake kusa da mu ba.
Wannan littafi yana koyar da muhimmancin haƙuri, tawakkali, adalci, yafiya da kuma sanin ƙimar mutanen da Allah Ya ɗora mana alhakin rayuwarsu.
Ina fatan za ku karanta BA DARAJA da zuciya buɗe, ku ɗauki darasin da ya dace da rayuwarku, ku bar wanda bai dace ba.
Nagode da kasancewa tare da ni a wannan tafiya.
Nainarh KD ✍️❤️
––
Page 1 _ 2
MABUƊI..
Aure tafiya ce da mutane biyu ke ɗauka tare, tafiya mai cike da furannin farin ciki, inuwa mai sanyaya zuciya, da kuma wasu lokuta na ƙasa mai duhu wadda ke buƙatar haƙuri da juriya ga juna.
A lokacin da zuciya ta haɗu da zuciya, soyayya ta fara haskaka kamar sabon hasken alfijir. Akan tashi da murna, akan kwanta cike da annashuwa. Kalmomin kulawa da basu ƙare wa, dariyar da ba ta da iyaka, da hannun da ake riƙewa a lokacin sanyi ko zafi, duk suna zama alamar farin ciki.
Amma kamar yadda ruwan sama yake zuwa bayan hasken rana, haka ma ƙalubale ke bayyana cikin aure. Wani lokaci matsala ta samu akan rashin kuɗi. wani lokaci sabanin ra’ayi na kawo rashin jituwa. Wani lokacin kuma kalaman da ba su dace ba na iya raunata zuciyar wanda ake so. Sannan a wasu lokutan a kan sama matsalar ce daga ɓangare guda daga cikin ma’aurata da kafin a ankara wannan matsala ta yi ma zaman aure babban tasgaro.
Sai dai asalin ƙarfin aure ba a gwada shi ne a ranaku da lokuta na farin ciki kawai ba; ana gwada shi ne a lokacin da duhu ya lullube hanya. Idan soyayya ta kasance mai tsarki, haƙuri ya yi ƙarfi, da zuciya ta shirya sauraro da fahimta, sai aure ya zama kamar itacen da ya tsayu a gaban iska, ba ya faɗowa saboda tushensa yana ƙasa mai zurfi.
A ƙarshe, ma’aurata sukan gane cewa farin ciki a aure ba yana nufin babu ƙalubale ba, yana nufin suna tare wajen shawo kansu. Kuma wannan ne asalin jin daɗin zama tare.
Sai dai a ɓangaren Halimatu sam ba haka abin ya kasance ba, domin ita nata auren aure ne da tun farkon fari a ka samar da tushen sa ta hanyar tsaftatacciyar soyayyar da ta yi nasarar kai su ga aure ita da mijinta Abbas.
Shekaru da dama sun shuɗe da auren da ya ginu ta hanyar gaskiya da soyayya mai tsafta, a farkon auren Halimatu ba zata ce akwai wata rana da ta taɓa ganin gazawar mijinta Abbas ta ko’ina ba, zama suke na farin ciki da fahimtar juna har zuwa lokacin da suka sama rabo Allah ya azurtata da samun ciki, ƙwarai taga kulawa da tarairaya daga wurin mijinta dama danginsa musamman ma Mahaifiyarsa da yake a lokacin basu yi gidan kansu ba suna zaune a gidan Mahaifin Abbas da yake Mutum ne mai iyali kuma Abbas ya kasance ɗan matar sa ta biyu ne kuma shi ne na biyu a Ɗakin su, shi ya sa ɓangaren surukai inda su Halimatu ke zaune daban haka ma ɓangaren surukan nasu wato iyayen mazajen.
Tun a lokacin da Halimatu ta yi haihuwar fari ta fara fahimtar wani abu daga wurin surukarta wato mahaifiyar Abbas; ƙwarai da gaske Matar tana nuna ma ta ƙauna da kulawa daidai gwargwado sai dai fa a inda gizo ke saƙan shi ne, ita mahaifiyar Abbas wato Mama Tsahare da surukanta ke yi laƙabi da Inna wasu kuma ke kiranta da Innar Samir, (Wato autan ta) ƙalubalen da Halimatu ta fara fuskanta shi ne a lokacin da ta yi haihuwarta na fari ba laifi sosai Abbas ya zage ya yi ma ta kaya cikin ɗoki ita da jariranta biyu da ta haifa mace da namiji, kuma a ranar da ta yi haihuwar ya kawo da yake tarawa yake yi cikin zumuɗi irin na wanda za'ayi ma haihuwa na fari shi ya sa bai sanar da kowa ba sai ranar haihuwa kawai aka ga kaya, sosai jama'an gidan suke yabawa dan kuwa kaya sun yi sai dai fa ban da Mama Tsahare Mahafiyarsa dan koda taga kayan a maimakon ta yaba a'a sai ɓata fuska da ta yi ta kuma hau suratai marasa kai, wai a kan me Abbas zai wahalar da kansa ya jibgo wannan uban kaya haka? Ai yanzu aka fara masa haihuwar ya bari mana a hankali a hankali sai yake yi da yawa ba wai ya takura kansa ba.
A lokacin da take wannan magana su biyar ne cikin Ɗakin, Halimatu dake kan gadonta sai Abbas daga gefe sannan sai Yayar Abbas ɗin mace da suka haɗa uba ɗaya (Domin Mama Tsahare yaranta duka maza ne) sai kuma Matar Yayan Halimatu da ta fara zuwa ganin lafiyar mai jego da jariranta.
Duk sai suka ɗauke wuta jin abin da Mama Tsahare take faɗa. Cikin ɗan mamaki Matar yayan Halimatu ta kada baki ta ce:
“Ni kuwa ai sai naga abin ki yaba masa ya yi, domin hakan yana nuni da nan gaba zai ƙara jajircewa ne ya yi abin da ya fi haka...”
“Baiwar Allah dakata ai da’ace so yake na yaba da ni zai bawa kuɗin na siyo komai tun da ni ce uwarsa amma bai yi hakan ba, ya tashi ya kwashe kuɗi ya jibgo wannan kaya kamar mai shirin buɗe shago!”
Mama Tsahare ta katse Zainab Matar Yayan Halimatu da wannan kalamai cikin nuna hali na ko'in kula.
Shiru Zainab ta yi tana bin Halimatu da ta yi tsuru da kallon tausayi dan kuwa tasan da matsala a gaba muddin aka ci gaba da tafiya a haka, domin kuwa ta fahimci Mama Tsahare gaba ɗaya irin Matan nan ne da ko kusa basu Ƙaunar ganin ƴaƴansu maza suna kashe ma matansu kuɗi ko kuma suna basu wata kulawa ta musamman da hakan kuma ba ƙaramin kuskure suke aikatawa ba da ba za su fahimta ba sai tafiya ta miƙa.
A ganin Zainab mene ne na jin babu daɗi dan kawai kina da ɗan da yakeyi ma Matarsa hidima? Abu na farko dai hakan yana nuna ɗan ki ya sama tarbiyya daga uwa ta gari, sannan kuma ai abin ke kiyi alfahari ne bawai baƙin ciki da hassada ba.
Wasu surukan fakewa suke da basu san ƴaƴansu su wahala. To amma ke kin manta kina da mijin kuma ai zakiso ya hidimta miki da ƴaƴanki fiye da kowa ko?.
Zainab bata sani ba shin rashin tunani ke saka wasu uwayen mijin kishi da matan ƴaƴansu ko kuwa hassada kawai ko kuma da suke fakewa da basu san ƴaƴansu su wahala basa tunani ne a kan meka je ya dawo zuwa nan gaba?.
Tun daga wannan lokaci Halimatu ta fahimci wani abu guda shi ne surukarta Mama Tsahare irin waɗan nan iyayen mijin ne da basu Ƙaunar ganin ƴaƴansu na wahala akan matansu sai su fake a kan basu san ƴaƴan su wahala ne shi ya sa da ta fahimci haka sai taci maganin zama da ita domin ta fahimci duk sauran surukan Mama Tsahare suma sun fuskanci wannan matsala daga gare ta ko a ce ma suna kan fuskanta sai dai tana addu'a Allah ya ganar da ita gaskiya ta gane wannan ba ƙauna take nuna wa ƴaƴan ba fa ce wata gurɓatacciyar hanya da zai yi babban illa ga iyalansu nan gaba.
Ba laifi koda ranar suna ta zago Mama Tsahare ta saki jiki an yi hidima sai sam Barka, kuma washe gari aka wuce da Halimatu zuwa wankan gida da hakan ya yi ma ta daɗi.
Sai dai cikin ikon Allah lokacin da Halimatu ta kai kusan rabi da wankan sai mahaifiyarta ta haihu ita ma, sai dai haihuwar tazo ma ta da tasgaro domin tun da ta haihun ba lafiya hakan ya sa a asibiti suke zaune ana cikin haka kuma ita ma Zainab Matar Ɗan Juma wato ƴaƴan Halimatu ita ma ta haihu lokacin kuma Halimatu ta kammala wankan kuma a ranar da ta gama washegari aka mayar da ita gidan mijinta sakamakon har zuwa lokacin mahaifiyar nata tana asibiti ba lafiya. Kuma ita kaɗai ce wurin mahaifinsu Halima shi ya sa aka ga dacewar Halima ta koma gidanta domin hakan zai fi.
Kwanaki sun ci gaba da ja har aka wayi gari Zainab ta kammala wanka ya zamana sai komawa ya rage, domin ita ma wankan gida aka ɗauke ta. Sai dai fa ƴan uwa da danginta sun kasa sun tsare akan ba inda zata koma har sai dangin mijin sun kawo kayan da ake kawowa bayan gama wanka kafin a mayar da ita.
Inda aka sama matsalar ke nan! Domin shi Ɗan Juma hankalinsa ba'a kwance yake ba domin har lokacin jikin mahaifiyarsu yaƙi sauƙi. Shi ya sa ya nema alfarmar su bari a dawo da Zainab ɗin in yaso zuwa wani lokacin sai ya yi kayan ya ɗauki alƙawari.
Yayin da dangin Zainab suka ce ina! Sam su basu yarda ba, domin an sha ɗaukar irin wannan alƙawarin amma daga baya a kasa cikawa, haka dai aka yi ta tataburza tsakani, to da yake Allah ya nufa ƙarshen zaman ke nan sanadin wannan kayan gama wanka da ba'ayi ba Aure ya mutu, zama tsakanin Zainab da Ɗan Juma ya ƙare.
Halima bataji daɗin faruwar haka ba sam domin Zainab ta wuce matsayin matar wa a gare ta, ban da amintar dake tsakaninsu kallon yar uwa take yi ma ta. Sai ta tuna ita nata lokacin da ta gama wankan ko maganar kawo wani kayan gama wanka ba'ayi ba haka a ka mayar da ita kuma ta haƙura ta zauna, ita da danginta basu biye ma son zuciya ba kamar yadda dangin Zainab suka yi, dama kuma hakan ya saba faruwa babu adadi Aure ya mutu akan rashin kai kayan arba'in bayan kuma ba'a addini hakan ya zo ba kawai dai al'adar malam bahaushe ne.
Suna tsaka da jimamin mutuwar auren kuma Allah ya ɗauki ran mahaifiyarsu wannan al'amari ba ƙaramin jijjiga ƴan uwa da dangi ya yi ba domin mahaifiyar su Halima irin matan nan ne da ba ruwansu basu ɗauki duniyar da wani zafi ba ga ta da son zumunci Halima bata mantawa lokacin da dangin mahaifiyar nata suka zo gaisuwa kowa da irin nagartattun halayenta da yake faɗa. Wata ƙanwarta ta yi kuka sosai tana faɗin bango ya faɗi hakika sun yi babban rashi.
Haka dai al'amuran suka ci gaba da wakana mahaifiyar su Halima bata yi kwana arba'in da rasuwa ba ita ma jaririyar da ta haifa ta bita. A wannan lokaci haƙuri da kuma tawwakali ne kawai ya yi tasiri akan Halima domin ta shiga wani hali mara misaltawa bata manta wa ba yadda batayi da Abbas ba a kan ya bari ta riƙe jaririyar da mahaifiyar nata ta bari tun kan mahaifiyar nata ta rasu amma fafir yaƙi ba kuma wai don yana gudun mata wahalan haɗa ya'ya har uku ba, kawai dai nashi ra'ayin ne domin tana da masu rauno baja-baja facalolinta sun nuna ma ta kara ta wannan ɓangaren, yaran basa cikakkun minti goma a hannunta in ba shan mama ba, shi ya sa take ganin haɗa ukun ba zai zama matsala ba sai dai Abbas ya buɗa ma idanunsa toka, ya hana, haka nan ta haƙura, to ashe ma yarinyar ba zama tazo yi ba.
Haka ta hakura ta ci gaba da rainon ya'yan ta gefe guda har yanzu suna zumunci da Zainab sai dai sama-sama domin ƴan uwanta da suka gano sai suka nuna ma ta ɓacin ransu a ganinsu bai kamata ta ci gaba da hulɗa da Zainab ba duba da abin da danginta sukayi ma ɗan uwansu, sai dai Halima ta toshe kunnenta domin a nata ganin Zainab bata da laifi danginta ne suka matsa har sai da auren ya mutu ba ita ba.
*
Wata rana da aiki ya yi ma Halimatu yawa ga rainon ƴan biyu tana tsaka da haka Abbas ya dawo gidan ya sameta sai ya zauna yana tayata wasu ayyukan suna ɗan taɓa fira can sai ga Mama Tsahare kamar wacce aka turo da yake takan shigo ɓangaren nasu lokaci zuwa lokaci taga halin da Haliman ke ciki sannan ta tayata goyon yaran, a lokacin da ta shigo ta sama Abbas ya cire riga ne daga shi sai dogon wando da vest tasu ta maza ya zage yana yi ma Halimatu wankin kayan yaran yayin da ita kuma take bakin murhu tana tuƙa tuwo. Basu san da shigowarta ba kwatsam sai jin salallami da ta ɗauka suka yi, sai duk suka ɗago suna kallonta da mamaki kuma a ɗan tsorace dan sun yi zaton wani abin ne yake faruwa.
“La'ilahaillahu Muhammadu ɗan Abdallah! Abbas me idanuna suke gani haka? Wanki?! Yanzu Fisabilillah ka rasa abin da za kayi sai wanki wa mace, ni kam Tsahare naga ta kaina yanzu idan wankin kakejin yi kazo mana ai ga nawa can kayi min yadda zan saka maka albarka da zaka ga amfaninta nan gaba cikin Rayuwarka...”
Duk sun yi tsitt suna saurarenta an rasa mai bakin magana, Halimatu dai sai girgiza kai kurum ta yi tana ci gaba da tuƙin tuwonta dan ta gama fahimtar inda Surukarta ta dosa.
A ganinta in banda son zuciya irin na Mama Tsahare menene laifi dan aiki ya yi ma ta yawa Abbas ya tayata?
“Haba mana Mama kiyi shiru mana yanzu mene na duk wannan ai naga ba wani abu ba ne dan nayi ma ta wanki shigowa nayi naga abubuwan sun yi ma ta yawa ga rainon ƴan biyu shi ya sa na taimaka ma ta da wasu yanzu da naga wankin kayan yaran ya ɗan taru sai na ce bara nayi ma ta su a wuce wurin....”
“Shikenan ni kuma naga rayuwa, yanzu Abbas ashe abin naga yakai har haka wanki taya aiki duk kake ma mace saboda ita ta haifar min kai?.”
Tsam Halimatu ta miƙe tsaye tana gyara goyon da ta yi ba tare da tanka ma Mama Tsahare ba ta nufa Ɗakin ta tare ta zama a kan kujera tana zabga tagumi, daga haka dai sama sama take jiyo muryar Maman har batasan lokacin da ta bar ɓangaren ba bayan ta gama sababi.
Da haka suka ci gaba da gurgura Rayuwa ƙana ƙanan abubuwa irin wannan na ci gaba da faruwa kuma Mama Tsahare bata iya kauda kai a kansu.
A zaman Halimatu da Abbas bazata ce tana samun komai daga garesa ɗari bisa ɗari ba sai dai ba laifi yana iyaka baƙin ƙoƙarinsa wurin ganin ya yi ma ta komai da zata buƙata dan ma a wasu al'amurran Mama Tsahare tana yi musu katsalandan badan hakan ba abin da zai ke ma ta sai ya fi haka amma duk da hakan ma tana godiya ga Allah sannan bata taɓa yi masa ƙorafi akan halin mahaifiyarsa ba sam ta dai dage a kan addu'a tana miƙa lamurranta ga Allah.
An ci gaba da gurgura Rayuwa zuwa lokacin yan biyu sun yi wayo sosai har an ya yesu kuma Halimatu ta sama wani cikin a lokacin ne kuma kwatsam Abbas ya tado da zancen ƙarin aure.
Ita Halima bata masan da maganar ba domin Mama Tsahare da Abbas su suke kiɗa da rawansu a ganin Mama gwara ta bari ya ƙara auren domin gani take in ba hakan ba nan gaba sai abin da Halima ta umarta zai yi gudun hakan ya sa ta amince masa kuma ta sa a dole mahaifinsa Malam mai allo shima ya amince duk da ba haka taso ba lokacin da ta sama labarin wacce zai aura bazawara ce da ƴaƴanta ba ɗaya ba, ba kuma biyu ba kuma da alama idan basu yi sa'anni da Abbas ba to tabbas zata girme masa, sai dai haka ya gani ya kuma ce yana so harda rawar jiki ita kuma ta shige masa gaba.
Halima bata tashi sanin wainar da ake toyawa ba sai da biki ya rage saura satikai lokacin taje Anguwa take jin zancen cikin gari bata yarda ba har sai da ta dawo gida ta tarda facalolinta suna zancen har da ɗaɗɗaga zanen anko, da yake yayan Abbas wanda yake bi matansa biyu ne to ɗayar ta biyun ba wani shiri suke da Halima ba dalili kuwa lokacin da Halima take amarya sai ake yawan yima amaryar surukinsu satar ba dama ta shanya surfaffen wake na ƙosan da take yi sai an ɗauka dan tsiya kuma har da matankaɗi da ta shanya akai ana haka an rasa wake yin wannan aika-aika kwatsam aka tsinci matankaɗi a barandar ɗakin Halima.
A lokacin haka Amaryar surukin nasu da suke kira Ladi tayi ta tsiya sai dai kasancewar babu hujja akan Halima ce mai yi ma ta sata koba ita ba sai maganar bata yi nisa ba Malam mai allo ya kashe zancen sai dai fa masu zargin Halima ce mai satan basu dena ba.
Abin da yake ɗaure wa kowa kai shi ne ita Suwaiba wato Amaryar Amadu yayan Abbas shi ne yadda ba'a ganin tana wanke wake sai dai kwatsam aga tana alale, shiru kawai aka ma ta sai dai masu mamaki nayi dan Akwai lokacin da aka ma ta magana sai ta ce ai daga gidansu ake aiko ma ta da waken surfaffe.
Badan an yarda ba aka kyale ta cikin ikon Allah kuma wata rana da dubu ta cika sai aka gano ita ce mai sace surfaffen wanken Amarya Ladi. Amma kuma ta so mannawa Halima laifin sanadin hakan har kusan sakinta sai da Amadu ya yi dan sai da ta yi kwanaki a gidansu sannan akan dole Mahaifinsu Malam mai allo ya sa ya dawo da ita duk da ba sakinta ya yi ba.
Tun daga lokacin da ta dawo kuma sai Halima ta yi baya da ita sosai gaisuwa kaɗai ke haɗa su.
To wannan dawowa da Halima ta yi ta tarar da bidirin da ake yi shi ne sanadiyyar da ta san da maganar ƙarin auren mijin nata, tabbas abin ya yi ma ta ciwo a ganinta me ya sa ya ɓoye ma ta tun da ya riga ya yi niyya ai ba hana shi auren zata yi ba.
Shiru kawai ta yi tana kuma biye mishi har zuwa lokacin da da kansa ya sanar da ita zancen bayan ya gama kwana-kwanar batayi ƙorafi akan ɓoye ma ta da ya yi ba sai binsa da ta yi da fatan Alkhairi shi kuwa ba kunya ya tashi domin shirin tafiya ɗaurin aure dan a ranar ya sanar da ita.
Halima ta yi haƙuri ta kuma jure an sha biki an gama amarya kuma ta tare a ɗakin da yake kusa da na Halima.
Ba laifi zaman nasu da amarya ba faɗa bare gaba sai dai kowa harkar gabansa yake yi ana haka har amarya Binta ta sama ciki lokacin kuma cikin Halima ya isa haihuwa lokaci kawai ake jira kuma cikin ikon Allah ranar wata laraba ta haifi ɗiyarta mace da ta ci suna Khadija bayan tataburza da aka sha da Abbas a kan ya sanya sunan mahaifiyarsa amma fir yaƙi a ra'ayinsa sunan bai masa ba dama kuma tun lokacin da Halima ta haifa ƴan biyu akaso macen taci sunan Mama amma yaƙi sai ya sakama ɗiyarsa Hauwa'u namijin kuma Habib.
To wannan karon ma da aka sake haka Halima ta ɗauka Mama Tsahare zata yi fushi sai kuma taga bata nuna komai ba illa iyaka girgiza kai da ta yi bayan ta ce "gwara da bai saka ma ta ba, ai sunan nawa na tsoffi ne”
Ta faɗa tana murmushi na yaƙe, domin tabbas taji ciwon abin da Abbas ɗin ya yi Allah ya gani kaff cikin ƴaƴanta ba wanda take so kamarsa amma ya nuna ma ta hali irin na ƴaƴan yau ka haife su baka haifi halinsu ba.
Ita dai Halima bata ce komai ba domin lamarin bai shafe ta ba a ganinta sun fi kusa..
–––
Alhamdulillah Nainarh KD ta dawo muku cikin wannan sabuwar tafiya mai cike da abin al'ajabi sarƙaƙiyar rayuwa da kuma gwagwarmaya.
Tun daga farkon labarin kun san ba labari ne na zubar wa ba domin akwai daru.
Ku kasance da alƙalamin Nainarh KD domin jin yadda zata kaya!