BA DARAJAFree

ArewaPen original

Non-fictionFreeCompleted

BA DARAJA

  • 1views
  • 8chapters
  • 0audios
  • words
  • 0likes
Start reading

Share:

The story

Synopsis

completed

No synopsis yet.

About the author

Nainarh KD – Nkd's “Every heart has a story — I only give it words.” 📞 Phone Number: *** or ***

More from @nkds

Sample · 1&2

🔥❤️BA DARAJA!!!❤‍🔥        (True Reality Series) ©® Nainarh KD – 𝓝𝓴𝓭'𝓼❦♡ *** > Characters grapple with the tension between destiny and personal choice. ⚠️ Copy is not allowed! ⚠️ Ba kuma zan lamunci a canza min labari ko ta wata siga ba. WRITER'S WORD Assalamu Alaikum Warahmatullahi Wabarakatuh. BA DARAJA ba kawai labarin soyayya ko zaman aure ba ne. Labari ne da ke ɗauke da saƙonni masu zurfi game da rayuwar yau da kullum, musamman irin ƙalubalen da mata da maza ke fuskanta a cikin aure da zamantakewa. A cikin wannan tafiya za ku haɗu da mutane masu halaye daban-daban. Wasu za su sa ku yi farin ciki, wasu za su baku haushi, wasu kuma za su sa ku zubar da hawaye. Amma a ƙarshe za ku fahimci cewa rayuwa cike take da darussa, kuma ba kowane mutum ake gane darajarsa a lokacin da yake kusa da mu ba. Wannan littafi yana koyar da muhimmancin haƙuri, tawakkali, adalci, yafiya da kuma sanin ƙimar mutanen da Allah Ya ɗora mana alhakin rayuwarsu. Ina fatan za ku karanta BA DARAJA da zuciya buɗe, ku ɗauki darasin da ya dace da rayuwarku, ku bar wanda bai dace ba. Nagode da kasancewa tare da ni a wannan tafiya. Nainarh KD ✍️❤️ –– Page 1 _ 2 MABUƊI.. Aure tafiya ce da mutane biyu ke ɗauka tare, tafiya mai cike da furannin farin ciki, inuwa mai sanyaya zuciya, da kuma wasu lokuta na ƙasa mai duhu wadda ke buƙatar haƙuri da juriya ga juna. A lokacin da zuciya ta haɗu da zuciya, soyayya ta fara haskaka kamar sabon hasken alfijir. Akan tashi da murna, akan kwanta cike da annashuwa. Kalmomin kulawa da basu ƙare wa, dariyar da ba ta da iyaka, da hannun da ake riƙewa a lokacin sanyi ko zafi, duk suna zama alamar farin ciki. Amma kamar yadda ruwan sama yake zuwa bayan hasken rana, haka ma ƙalubale ke bayyana cikin aure. Wani lokaci matsala ta samu akan rashin kuɗi. wani lokaci sabanin ra’ayi na kawo rashin jituwa. Wani lokacin kuma kalaman da ba su dace ba na iya raunata zuciyar wanda ake so. Sannan a wasu lokutan a kan sama matsalar ce daga ɓangare guda daga cikin ma’aurata da kafin a ankara wannan matsala ta yi ma zaman aure babban tasgaro. Sai dai asalin ƙarfin aure ba a gwada shi ne a ranaku da lokuta na farin ciki kawai ba; ana gwada shi ne a lokacin da duhu ya lullube hanya. Idan soyayya ta kasance mai tsarki, haƙuri ya yi ƙarfi, da zuciya ta shirya sauraro da fahimta, sai aure ya zama kamar itacen da ya tsayu a gaban iska, ba ya faɗowa saboda tushensa yana ƙasa mai zurfi. A ƙarshe, ma’aurata sukan gane cewa farin ciki a aure ba yana nufin babu ƙalubale ba, yana nufin suna tare wajen shawo kansu. Kuma wannan ne asalin jin daɗin zama tare. Sai dai a ɓangaren Halimatu sam ba haka abin ya kasance ba, domin ita nata auren aure ne da tun farkon fari a ka samar da tushen sa ta hanyar tsaf...

Continue reading free chapter

Contents

Table of contents

Preview every chapter, see what is free, and continue reading when you join ArewaPen.

chapters8
premium0

Continue in the ArewaPen app

Unlock offline reading, audio mode, and sync your bookmarks instantly.

Download on the App StoreGet it on Google Play