Miskili da Sha'awa 🔥📖

Chapter 1&2

by @angelbossauthor

chapter 1& 2 

ABUJA NIGERIA 
MAI TAMA 

Hafsa ba ta taɓa yarda cewa mace za ta iya rayuwa cikin farin ciki ba tare da ta kula da kanta ba. Tun tana ƙarama take da son kwalliya, turare da gyaran jiki. Ba wai don tana son nuna wa mutane kanta ba ne, amma tana jin daɗin yadda take ji idan ta kalli kanta a madubi ta ga yarinyar da ta so ta zama.

Da sassafe ta tsaya gaban doguwar madubi a ɗakinta tana gyara dogon gashinta. A kan teburinta akwai turare iri daban-daban, man shafawa da kayan kwalliya da ta tara a hankali. Ta ɗauki ɗaya daga cikin turaren ta fesa a jikinta, sannan ta yi murmushi.

“Yau kam zan yi kyau sosai.”

Ta koma ta zauna a gefen gadonta tana kallon wayarta. Saƙonni ne suka cika screen ɗin, amma babu wanda ya fi ɗaukar hankalinta kamar saƙon da mahaifiyarta ta turo mata tun da safe.

Ki shirya. Za mu tafi yau.

Hafsa ta dafe goshinta.

“Tafiya kuma?”

Ta san wannan tafiyar ba irin sauran tafiye-tafiyen da ta saba yi ba ce. Mahaifiyarta ta daɗe tana magana game da wani gida da za ta je ta zauna na ɗan lokaci, amma Hafsa ba ta taɓa ɗaukar maganar da muhimmanci ba.

Sai dai a yau komai ya bambanta.

Ta mike ta buɗe akwatinta, tana zaɓar kayan da za ta ɗauka. Ta ɗauki riga, ta ajiye. Ta sake ɗaukar wata, ta girgiza kai.

“Wannan ma bai yi ba.”

Ta ci gaba da zaɓe har sai da ta cika kusan rabin akwatin da kaya.

kanwar ta mariya ce tashigo tana kare mata kallo Aunty har yanzu ba ki shiya ba?

Hafsa ta kalleta. “Ina zan je da kayan da ba su yi min kyau ba?”

“Ke dai kin fi son kaya da yawa fiye da komai.
Hafsa ta yi dariya. “Kayan kyau ne fa. Ai mace ta kula da kanta.”

ita fa a jikin ta takeji wannan tafiyar ba alkari bace,

Ba ta san irin rayuwar da ke jiranta ba.
Ba ta san dalilin da ya sa aka tura ta wannan gidan ba.

Bayan tagama shirya wa ta dauki kimono ɗinta pick colour ta daura akan pencil jeans dinda ke jikin ta sai 'yar top karamin veil ta sanya ta yane gashin kanta dashi wanda ya fito da ainihi kyawun ta,

hafsa bata cika son full makeup ba shiya iya lips dinta take gogawa man baki saitayi brush eyelashes da jigara wayar ta tadauka da handbag ɗin ta wacce tayi match da kayan ta

a hankali take jan trolley tana tafiya ta latsa wayarta a parlourn ta zauna tana dannawa mommy kira.

good morning dear tafada tana karyar da wuya okay ina parlourn tayi reaject call 
cike da nutsuwa farar matar da akalla zatayi shekaru 53 take taka step ɗin kyakkyawa ce ajin farko kasance war hafsa Asali kyawun mahaifiyar ta ta ɗauka amma ita ba fara bace kasance War mahaifin ta ma ba fari bane launin fatar sa da ɗauka amma kyau babu abinda ta bari a mahaifiyar ta

tashi tayi tana huge din mommy 
yar albarka kinshir yane yeah dear na shirya kinsan banaso nayi dare a hanya okay kije driver na jiran ki papi yace zai same ki acan okay mommy thanks bey 
tasake huge ɗinta tana fita da trollet ɗin da sauri driver ya fito yana amsar kayan ya sanya a boot yana mai bude mata mota ta shiga.

Please garba dan karɓa min ice cream a waje dear kasance war sun san haka take kiran mahaifiyar tata yasa yace to ranki shi dade da sassarfa ya karasa bakin parlourn yana sallama mikewa mommy dake zaune tayi tana tambayar lafiya 

ehy lafiya Hajiya da Hajiya karama ce tace abata ice cream, tafe kai mommy tayi tana mamaki son zaki irin na hafsa bude freezer tayi ta dauko mata ta mika mashi ya karɓa ya kaima a motar karɓa tayi tana godiya ya ja motar suka bar gidan 
suna cikin tafiya tana shan ice cream tana latsa wayarta tana kuma murmushi saboda tana magana ne da best friend ɗinta wato leema
wani moll sukazo kiftawa da sauri tace garba Please dan tsaya na sauka na shiga moll ɗinnan ina bukar wasu abubuwa to Hajiya 
fita tayi cike da takunta na cikekiyar mace mai aji duk da hafsa baza ta wuce 18 to 19 ba amma idan kaganta sai ka ɗauka babbar macene saboda iya ado da taku

sai da sayi duk abinda take buƙata kamin ta biya kudin aka kawo mata mota suka ƙara ɗaukan hanya.

IBADAN STATE 
JERICHO GRA

bude get din da akayi yabani damar kutsa kaina ciki saboda wata dalleliyar mota dake shirin shiga gidan
Gidan yana cikin wani shiru mai cike da nutsuwa a Jericho GRA, Ibadan. Babbar katangar da ta kewaye gidan ta rufe komai daga idon masu wucewa, yayin da babban gate ɗin ƙarfe yake tsaye a gabansa kamar mai gadin wani abu mai muhimmanci. Da zarar an buɗe gate ɗin, wata doguwar hanya mai shimfiɗaɗɗen fili take kaiwa har zuwa gaban gidan. Gefen hanyar an kawata shi da furanni da bishiyoyi, lawn ɗin gidan kuma yana da kyau sosai, babu wani wuri da ya nuna sakaci.

Gidan bene ne mai hawa biyu, babban falo yana kallon ƙofar shiga kai tsaye. A cikin falon akwai manyan kujeru masu tsada da teburin gilashi a tsakiyarsu, yayin da manyan tagogi suke barin hasken rana ya cika ɗakin. Daga falon akwai hanyar zuwa ɗakin cin abinci da kitchen, sannan wani corridor ya kai ga ɗakunan da ma’aikatan gidan suke amfani da su.

A saman bene kuwa akwai ɗakunan kwana da yawa, amma ɗaya daga cikinsu ya fi sauran girma. Ɗakin yana da babban balcony da yake kallon lambun gidan, kuma shi ne ɗakin da ba kowa yake da izinin shiga ba. Akwai kuma wani ɗaki da yake can ƙarshen corridor, wanda kullum yake kulle. Babu wanda ya taɓa tambayar dalilin da ya sa ake kulle shi, domin a wannan gidan akwai abubuwan da ba a son a yi magana a kansu.

A bayan gidan kuwa akwai wani katafaren lambu mai cike da furanni da bishiyoyi, tare da swimming pool da wurin zama da aka tanada domin hutawa. Komai yana cikin tsari, komai yana da inda aka ajiye shi, kuma babu wani abu da yake fita daga tsarin gidan.

Wannan ba irin gidan da mutum zai iya yin hayaniya ko yawo yadda ya ga dama ba ne.

Domin a wannan gidan, akwai dokoki. Kuma wanda ya kafa dokokin ya fi kowa tsanani wajen ganin an kiyaye su.

TO BE CONTINUED...

MISS NASIR ♥️✍️