ƘYAURE KARIYAR GIDA

BOOK ONE CHAPTER SIX

by @hindatuauwal

a silale ta kwanta ta baya numfashinta na fita cikeda rauni.




*ALIYA*


Aliya na kwance akan doguwar kujera, har yanzu kalmar Rayyan tana yawo a cikin kunnenta.

“Na gode.”

Sai ta saki murmushi ita kaɗai.
“Wai kalmar na gode ce kawai ta faranta min rai haka?”

Ta girgiza kanta tana murmushi.
“Aliya, ki nutsu mana...”

Asaman kanta taji dariyar wasu mata daga veranda suna sallama.

Aliya ta ɗago kai, kafin ta samu damar sanin ko su waye, sai aka turo ƙofar.

Cousine Sister's ɗinta suka shigo da fara'a akan fuskokinsu.

“Amaryaaa!”

Aliya ta yi saurin miƙewa.

“Sannun Ku da zuwa.”

Suka shigo suna dariya.

Nuwaira ta zauna a gefen ta, ta kalli Aliya daga sama har ƙasa.

“Hmm...”

Aliya ta yi dariya.

“Me kika gani?”

Ta ce“Ina kallon bakin dake mana kukane jiya wai ba zata rabuda gida ba sai gaki kin kwana agidan ki lumui"

Duk suka fashe da dariya.

Aliya ta rufe fuskarta da tafin hannunta.

“Ku daina mana!”

Aunty Aishat tace“Wallahi mun zo ne mu ga ko an yi miki welcome a gidan miji.”

“An yi mana,” Aliya ta amsa cikin murmushi.

“An yi miki? To wa ya yi?”

Aliya ta yi shiru.

Sai Aunty Nusaiba ta yi saurin cewa“Ke! Kada ki ce Ustaz Rayyan ne!”

Aliya ta ƙara sunkuyar da kanta. Dariya ta sake tashi.

“Lallai amarya ta kama dutynta da alama basanya alamarin ki!”

Aliya ta yi dariya tana cewa “Kwaji dashi.”

A wannan lokacin Baba Nafisa ta shigo tana cewa“Me ya sa kuke wannan hayaniyar kamar an tara ku a kasuwa?”

Aunty Aishat tai caraf tace“Baba Nafisa, mun zo ne mu koya wa amarya yadda ake zama matar aure.”

Baba Nafisa ta yi dariya“To ku fara da kanku tukuna.”

“Ni dai na gama makarantar,” fadin Nusaiba.

Baba Nafisa ta kalleta.“Gama makaranta? Ai karatun gidan miji ba'a gama shi ƴar nan, ko Ni tsohuwar babarki kullum sabon karatu nakeyi agidana"

Duk suka fashe da dariya.

Aliya ma ta kasa riƙe dariyarta. Wannan shi ne karon farko tun da ta shigo gidan da ta ji jikinta ya saki sosai.


Kukan da jaririyar dake goye a bayan Aunty Hafsat ta soma yasan yasu shiru.

Saukota tayi tana girgiza ta. Ta buɗe jakarta ta dauko bulun botin yarinyar dake ɗauke da madara ta soma bata.

Cike da tausaya Aliya ta kalli kyakkyawar yarinyar da kallo ɗaya zakai mata kaga kamannin ta da Jamila. Wanda zai tabbatar maka da ɗiyar tace.


Duk wani abu da Jamila tayi arayuwa bai ƙona zuciyar Aliya kamar wofantar da watannan jaririyar da tayi saboda son zuciya ba.



Allah shine masanin dai dai. Amma zataso yarinyar nan ta rayu tazama bangon jinginar Jamila aranar da batada wani bango da zata jingina taji sanyi.



Ɗakin yai shiru na ɗan lokaci. Idanuwansu duk yana kan yarinyar, yayinda zuciyar kuwwa ke nasa kalan saƙan da ban.



Seda Aunty Hafsat ta gama bata madarar ta saɓata a kafaɗa tana jijjigata sannan wata yayarsu mai suna Hajiya Rabi ta taso daga inda take zaune ta dawo kusada Aliya.


Fuskarta ta sauya daga wasa zuwa nutsuwa, Ta kama hannun Aliya.

“Ƙanwa ta... inaso kibani hankalin ki, ki saurareni da kyau "

"Tom Aunty"

Hajiya Rabi ta ce“Zaman aure ba kullum dariya ba ne. Akwai ranakun da za ki yi farin ciki, akwai ranakun da za ki yi kuka. Amma abin da nake so ki sani shi ne... kada ki yanke hukunci akan gidanki alokacin da ranki yaɓaci.”

Aliya ta yi shiru tana saurare.

Ta ci gaba“Idan mijinki ya yi fushi, ba lallai ne ki rama da fushi ba. Idan ya yi shiru, ba lallai ne ki ɗauka cewa baya sonki ba. Wani lokaci namiji yana ɗauke da abin da bai iya furtawa ba ga matar sa musamman yadda akai wannan auren da yadda abubuwa marasa dadi suka wanzu atsakanin sa da Jamila dan Allah kizamar ma iyayen mu sanyin idaniyan su, ki share musu wannan hawayen"

Aliya ta sunkuyar da kai.

Sai Hajiya Rabi ta ƙara“Amma hakan ba yana nufin ki riƙa haƙuri da duk wani abu ba tare da magana ba. Idan akwai abin da ya dame ki, ki zaɓi lokacin da zuciyarku ta yi sanyi ki yi masa magana cikin mutunci.”

Nuwaira tace“Wallahi wannan maganar gaskiya ce Aunty Hajiya kuma inason kizama wayayyiyar mace agidanki kada kiyarda kunya ta lalata miki rayuwa tagina katanga tsakanin ki da Rayyan, idan shi Ustaz ne ki nuna mai ke ƴar duniya ce dan wallahi in Ni ce ko karuwa sai ta saramun"

Duk suka sake dariya sabida kalaman ta na ƙarshe da tace wai ko karuwa sai ta sarama mata.

Aliya ma ta yi dariya.

Sai Nusaiba ta sake kallon Aliya tace"kada ki biyema Nuwaira kice zaki zama fitsararriya ahankali zakibi komai, ki soma samun gurbi azuciyarsa kafin kizama cikakkiyar matarsa duk wata kulawa da soyayya dayema Jamila sai yemiki fiyeda wanda yai mata amma pha sai kin jure kin zama jajirtacciyar mace agidanki, ki manta shekaru da kuruciyar ki, ki zama matar gida wacce zatai yaƙi don karɓo zuciyar mijinta da'aka yasar yake gararan ba cikin ciwon bakin cikin yaudara."



Maganar ta shiga zuciyar Aliya sosai. Ta yi murmushi.

“Insha Allah zan yi ƙoƙari.”

Baba Nafisa ta ɗaga yatsa. “Amma akwai wata karin shawara guda!”

Aliya ta kalleta.

“Ki tabbatar kin iya duk wani girkin abinci da yake so!”

Dariya ta barke a falon. 

Nuwaira tace“Baba Nafisa, ke kenan har yanzu kina ganin girki ne sirrin aure?”

Ta ce“Eh mana ai girki shine mace, idan kikai girki mai daɗi yaci abincin ki ya ce na gode, ai kin riga kin fara samun maki da matsayi a zuciyarsa"

Aliya ta kasa riƙe dariyarta. Sai ta tuna da abincin da ta zuba wa Rayyan da kuma kalmar da ya faɗa mata.

“Na gode.”

Murmushi ya sake bayyana a fuskarta.

Aunty Nusaiba ta lura da murmushin da tayi tace“Me ya sa kika yi murmushi haka?”

Aliya ta girgiza kai.“Babu komai.”

“A'a! Wannan murmushin yana da labari.” fadin Nuwaira.

Aliya ta rufe fuskarta tana fadin“Ku kyale ni mana!”

Duk suka yi dariya.

Yayinda wani abu yafara canjawa azuciyar Aliya, alkawarin data ɗaukar ma kanta na ƙara zama daram acikin kanta saboda magan ganunsu agareta, ta kuma kara samun haske akan shikan shi auren. Aure....ginine ne da ake dora tubali daya bayan daya.

Kuma Aliya ta yanke shawarar cewa nata tubalin zai kasance da haƙuri, kulawa da mutunci.

A can kuwa, a ɗakin Rayyan...tun bayan fitowar sa daga wanka yasanya ƙarananun kaya na shan iska ya kwanta.


Kiraye kirayen sallahn azuhur ya tayar dashi, yamiƙe yaje dauro alwallah yasauya kaya ya fito se asannan yaji dariyar su Aunty Aishat ƙasa ƙasa sabida bacikin hayaniya suke maganaba, anutse suke komai nasu cikin tsantsan ilimi da sanin yakamata.



Hade-haɗen tirarukan sa dayake zama guda daya yabada wani irin musulmin ƙamshi mai ratsa zuciyar mumini yafara isa wurin su kafin ya iso.




Kasancewar sa ƙaninsu kuma babu irin wannan harigidon atsakanin su yasa suka kame kansu alokacin da ya iso yaduka yana gaidasu, nasiha sukai mai tareda fatan alheri yafice abinshi yai na masallaci acan suka haɗuda Zaid suka tafi dakin sa da laasar tayi suka je masallaci sai suka wuce Islamiyya duk da anbama Ustaz Rayyan hutu.



*



Suna fita wasu suka shigo, unin ranar gabaɗaya haka tayishi cikin karɓan baƙi, ƴan makarantar su da kawayen ta sukai ta zuwa suna ganin ɗaki tareda fatan alheri sannan aka kawo mata wasu raguwan kayanta dake gida.


Sai yamma liƙiss kuwwa yawatse, tasake share ɗakinta tai mopping, ta dafa ruwan wanka dama wankan yamma sarartace kuwwa yasani.


Ta dafa wani tasanya ma Ustaz Rayyan a plast yadda in yadawo shima zaiyi saboda tunda yafita da azuhur bai dawo ba.



Zaman kaɗaici babu daɗi duk da ga t.v tafison ta shiga wurin Ummu dan tsoron zama ita kaɗai takeyi aɗakin babu kuwwa hakan yasa tasa hijjab ta shiga sashin Ummu alokacin kuwwa yawatse suka zauna ita dasu Ammar suka baje kolin hira sai da taga dare yayi sosai Ustaz zai iya dawowa a kowani lokaci tai musu sallama ta koma ɗaki ta zauna tana jiransa, bata jimaba sai gashi ya shigo da sallama.


Ta amsa tana miƙewa ta taka zuwa inda yake tsaye ta rungume sa kadan tana cewa


"Sannu da dawowa"


Kamar wani dolo haka yai tsaye yana kallon ta, arayuwar sa gabadaya bai taɓa dawowa an mai tarba irin wannan.....



"Zaɓi ɗaya wanka...ko abinci?"



Ustaz Rayyan ya haɗiye mamakin sa yabata amsa


"wanka zanyi Naci abinci agidan su Zaid"


Ya tsinci kansa dayin mata bayani dalla dalla.


"Zan maka uzuri yanzu by next time karka ƙara, Ni kaɗai ce nake da haƙƙin cika cikin mijina"


Tai maganar da murmushi afuskarta, muryanta ɗaukeda umarni mai sanyi.


For the first time yatsinci kansa dayin murmushi yana wucewa ɗakinsa. 


Yana tsaye yana rage kayan jikinsa tashigo da ruwan wanka takai mai bathroom.


Ta fito. Ta tsaya anesa dashi kadan tace

"zan tafi in kwanta akwai wani abu da kake bukata?!"


"No zaki iya zuwa ki kwanta seda safe"


"Tom Allah ya tashe mu lafiya "


Ta amsa tana ficewa daga dakin. A bakin gadon ta tazauna tana sauke numfashi ta furta"day one"



           ____****____



Zaune take akan sallaya tana addu'an sallahn da ta sallame.


Ƙofar ɗakin aka turo da sallama. Seda tashafa addu'ar sannan tagyara zamanta ta fuskance shi azaunen dayake abakin gado.


"Ina kwana Yaya!"


"Lafiya ƙalau Aliya...ya kike!"


"Lafiya ƙalau" ta amsa da fara'ar ta.


Ya ɗanyi shiru kaɗan sai yasoma magana da muryarsa mai zurfi dake kai saƙo nan take.



"Munyi magana da Ummu a al'adance sai kinyi sati guda kafin ki soma girki, nace a'a abarki Ki girki da kanki sabida fita haƙƙi, so yau zaki fara girka abin karyawa"


"Tom!duk abinda kace haka za'ayi, yanzu mai za'a girka"


Ta tambaye sa duk da tasan favourite foods ɗinsa.


"Kiyi mana duk abinda yasamu kedai ki tabbatar zakiji daɗin sa."


"Jin dadina ba komai bane idan babu naka...zan girka abinda zamu ji daɗin sa muduka"



Be bata amsaba sai miƙewa da yayi, mamakin Aliya na kamasa, inda kafin yanzu wani zai gaya masa Aliya zata iya yin abinda take yi ayanzu kai tsaye zai ƙaryatashi sabida sanin kunya irin na Aliya. amma yanzu da take gwada masa akaran kansa sai yake ganin kamar an sauya ta.


Miƙewa tayi tanaɗe sallayan ta nufi kitchen kai tsaye ta soma tinanin abinda zata girka acikin gwanon abubuwan daya fiso, bayan dogon mahawara atsakanin zuciyar ta da ƙwaƙwalwan ta aka sami dai-dai to akan yam and scrumble egg.



Kayan haɗi ta ɗauko tasoma aiki cikin natsuwa da ƙwarewa, tana gamawa ta kwashe a plast ta ajiye agefe, ta wanke duk wani abu da taɓata, kitchen din tasoma gyarawa sannan taje bedroom ɗinta ta wanke bathroom, tagyara ɗakin harda falo.



Tasanya tiraren wuta, ta kwaso kayan abincin tajera akan ƙaramin carpet ɗin da aka sanya a dining area sabida babu kujerun dining.



Ruwan wanka ta sanya ma kanta, tasake ta ɗora masa nasa, agaggauce tai wankan ta shirya ta fito taje ta sake mai ruwan wanka takai masa bayi sanda tafito sai taga yatashi hakan yasau ƙaƙa mata aiki.


Shi ya shiga wanka ita kuma tasoma gyaran ɗakin kafin ya fito tagama, ta buɗe wadrope taciro masa kayan da zai sanya, dama haka halittar ta yake tanada zafin nama a aiki kamar wacce aljannu ke tayawa.


Ta dawo falo tana zaman jiransa sai gashi ya fito sanyeda kayan da taciro masa wanda batai zaton zai sanya ɗin ba, shishshigi kawai tayi.


Yana isowa gabanta tamiƙe tana murmushi tace"kayi kyau sosai"


Kai yagir giza yawuce ta. Tabi bayansa tana murmushi, tazuba musu abinci suka cii babu mai magana har seda suka gama ta kallesa tace


"Ina binka bashi..."

Sai ya kalleta.

Sanin bazai yi magana ba ta sake cewa"bakai recommending akan girkin ba"


Rigimar Aliya dayawa yake, a taƙaice ya furta


"yai daɗi!"

"Bani maki"

"100%"

Yafada bawai dan kawai tai farin ciki ba, dagaske Aliya ta iya girki tun daa yasani a yauma da tai girkin yai daɗi ɗari bisa ɗari y.....


Rungumar da Aliya tai masa da wasu kalamai da tafaɗa waɗanda basa kaiwa cikin kunnuwansa yakalla.