Miskili da Sha'awa 🔥📖

Chapter 3&4

by @angelbossauthor

miskili da Sha'awa 🔥 đź“– 

fitowa yayi daga cikin motar fuskar sa dauke da fara a kowa y gani sai ya gaisar dashi saide wa'in da ya girma ya su gaishe shi ya amsa cike da mutumtawa kofar parlourn ya nufa yana kutsa kai ciki wata dattijo wace tana goge goge ta dago tana kallonsa

barka da safiya innaye Barka de 
imamu Please innaye kidena ɓatamin suna yafada a shgwabe, ni sunana imam to naji zan kuya sai ina fadama okay innaji ina big bro yana sama kasan shiba sauko wa yake da wuri ba okay bari na haura kinsan yau zakiyi bakuwa kimata girki na musamman aa kace yau na baje basirata a wajen girki baka da matsala amma wacece zatazo kede innaji zaki ganta bari naje gon bro
sai ka sauko to innaji na yada yana manna mata peck a kumatu.

A hankali yake taka step din yana zuwa bakin wani bedroom ya yayi knowking can cikin wata hoskey voice ta ratso kofar come shiga yayi a hankali yana karema daki kallo 

Da zarar an shiga dakin sa zaka ga komai nasa dabanne komai yana cikin tsari mai tsauri. Babban gado yana tsakiyar ɗakin, an shimfiɗa shi da farin zanin gado mai kyau. Gefensa akwai ƙananan tebura guda biyu, ɗaya ɗauke da fitilar dare, ɗayan kuma agogo da wasu littattafai.

A gefen dama akwai babban wardrobe mai ɗauke da kayan sawa da aka tsara cikin tsari. Babu kaya da aka jefar ko'ina, babu takalma a ƙasa, babu wani abu da bai kamata ya kasance a wurinsa ba.
Babban taga yana kallon lambun gidan, a gabansa kuma akwai doguwar kujera da ƙaramin tebur. Wurin ya kasance mai natsuwa sosai, musamman da dare, saboda daga can ba a jin hayaniyar gidan sosai.

A gefe guda kuma akwai teburin aiki mai faɗi, a kansa akwai laptop, wasu takardu da littattafai. Bayan teburin akwai wani ƙaramin shelf cike da littattafai.
Bathroom É—in yana haÉ—e da É—akin, mai faÉ—i kuma mai tsabta. Komai yana da wurinsa, daga tawul zuwa turare da sauran kayan amfani.
Duk da cewa É—akin yana da kyau kuma yana da tsada, babu wani abu mai yawa da zai sa ya zama cike da hayaniya. Tsarinsa ya yi kama da mai É—akin kansa, shiru, tsafta da tsauri.

saida ya gama kare ma É—akin kallon kafin ya karasa kusa da shi tsaye yake a bakin taga yana kallon farfajiyar gidan 

Kasancewar yabashi baya yasa ya hangi kwantacciyar sunarsa dake sheki

Azeen mutum ne mai tsayi daidai gwargwado, jikinsa kuma ya nuna irin kulawar da yake yi da kansa. Faɗin kafadunsa da kyakkyawan tsarin jikinsa suna ƙara masa wani irin kwarjini da ke sa mutum ya lura da shi tun kafin ya yi magana. Ba shi da jiki mai nauyi sosai, amma yana da ƙarfi da tsari, musamman yadda bayansa yake miƙe kuma yake tafiya cikin nutsuwa.

Fuskarsa tana da kyau irin wadda ba sai ya yi murmushi ba kafin ta ɗauki hankali. Dogayen gashin girarsa suna zaune a saman manyan idanunsa masu zurfi, waɗanda suke da wani irin kallo mai tsauri amma a lokaci guda akwai nutsuwa a cikinsu. Hancinsa madaidaici ne, leɓunansa kuma suna da kyau, sai ƙananan gemunsa da ya ke gyarawa cikin tsari suka ƙara masa girma da kamala.

Abin da ya fi jan hankali a tare da shi shi ne yadda yake motsi. Ba ya saurin tafiya, ba ya yawan motsa jikinsa ba tare da dalili ba. Ko lokacin da yake sanye da farar riga mai sauƙi da wando, tsayuwarsa kaɗai tana ba shi wani irin kwarjini. Idanunsa ne kawai ke iya nuna abin da yake tunani, domin bakinsa ba ya yawan faɗin abin da ke zuciyarsa.

Kuma idan ya yi murmushi, ko da kuwa na ɗan lokaci ne, tsananin fuskarsa kan sauya gaba ɗaya. Wannan murmushin nasa ba kasafai ake ganinsa ba, amma duk wanda ya taɓa ganin sa zai fahimci cewa a ƙarƙashin wannan halin na Miskili akwai wani mutum daban da yake ɓoye sosai.

good morning bro 
cike da nutsuwar da tazame masa jiki ya juya yana zuba mashi lumsasun idanuwan sa a hankali yayi kasa da kansa saboda baya iya jure kallon yayan nasa a hankali ya fara motsa labban sa Imam mike faruwa?
dama nazo nafada ma yar gidan uncle Taufiq na hanya ware idanuwan sa yayi yace Imam miyasa nace bansan hayaniya miyasa 
sorry bro nima ba laifina bane umma tace tazo ta zauna na wani lokaci.

dafe goshin sa yayi Saboda dogowar maganar da yayi har kansa yafara ciwo
karasawa kan kujerar dake gaban table É—in karatun sa yayi ya zauna yana mai daura kafa daya kan daya saida yaga san iskar sa kamin yace okay Imam kafada mata dokina bansan hayani You know?

okay bro insha'Allah 
zaka iya tafiyar, dama manager yace infada maka wannan kwangilar da muke nema suma sunyi accepted 
okay gobe zamuyi magana akai kace innaji ta kawomin coffee okay 
yafada Yana barin dakin a hankali ya lumshe idanuwan sa yana jin yadda kanshi ke sarawa saboda maganar da yayi.

Imam na fita ya samu innaye na Kitchen ya Ć™arasa ya fada mata sakon Azeem 
fita yayi duk yadda ya kifta sai masu aiki sun gai dashi hakan yasa yake ta haba haba dasu kasance warsa ba halinsu daya da yayan nashi ba mai mugun tsauri da dokoki mota yashiga ya nufi gidan mahaifiyar su

tun tana jin daɗin tafiyar har abin ya isheta sai gashi ta bungire da bacci ba su suka isaba sai bayan magrib tun abin 10 na safe ga wata uwar yunwa dake ƙwaƙwalar yan hanjinta bama tasan lokacin da suka isaba sai jin muryar garba tayi yana tashin ta a hankali ta bude sexy eyes ɗista masu ɗauke da bacchi fitowa tayi tana ƙarema gidan kallon a zuchiyar ta tace wow domin gidan yayi mata yadda ya kamata innaji dake tsaye bakin kofar Parlourn ne ta karaso aa lale da mutanen Abuja da sauri hafsa ta juya jin muryar innaye babu shiri ta rungume ta tana sankin ihun farin ciki ohh my god innaji dama kinan tafaɗa a gwabe kiji yar nema ina zanje da nayi fishi ta faɗa tana juya mata baya.

afuwa shalelen mommy ta a kuwa ta juyo tana sakin murmushi muje ciki kinji naga kin kwaso gajiya
garba ka shigo da kayan kaji to yace ya dauko trolley da kayan makulashe da abubuwan da tasiya ya shiga da su ya ijeye a parlourn ya fita suna gaisawa da mai gadi.
innaye nifa kinsan nayi fushi dake Saboda ba kya zuwa garin mu kinzauna a wajen dan baĆ™in halinnan 
lalala Azeemunne dan baƙin hali shine mana tada ta tura baki....

miss Nasir ♥️✍️