Chapter 12
***
𝘿𝘼𝙐𝙍𝙄𝙉 𝙕𝙐𝘾𝙄🔐
𝘽𝙔
𝙈𝘼𝙍𝙔𝘼𝙈 𝙐𝙈𝘼𝙍
(𝙅.𝙒.𝘼)
Chapyer 12
Aikata son ransu.
Cikin ƙanƙanin lokaci komi ya sauya, aka samu yawaitar zubar jini, satar mutane ga kuma tsadar rayuwa, gaba ɗaya mutane sun gigice sun fita a hayyacinsu tashin hankali ya disashe murmushin su kowa zakigani a rame a ƙanjame ga yunwa ga tsoro ga dashin hankali abin yayiwa talakawa yawa.
Ana cikin haka ne lokacin zaɓe ya ƙarato, yayinda talakawa suka maida lamuransu ga Allah tare da laluben mutumin kirki me karamci a matsayin wanda zasu tsaida ya amshi kokensu.
Alhaji Abubakar Saminaka shi ne wanda aka tsayar a takara, duda lokacin na soma fita a hayyacina saboda tsaface ni da Makafa ke yi amma sai da na shiga tsananin tashin hankali jin wanda suka tsayar takara bama wannan ba yanda suka soma shirye-shirye gadan-gadan da kuma irin tsarin da suke bi wanda na tabbatar da ya banbanta dana saura waɗanda suka ɗora mulki abin ya ƙazanta.
Daidai da rana ɗaya ban taɓa samun nutsuwa ba har sai da aka yi zaɓe aka gama lafiya, babban abin burgewa game da mulkin Bawan Allah yanda ya zage wajen kawo cigaba da sigogi da dama ya zage yayi aiki tare da yaƙi da matsalolin tsaro, har sai da ya kawo kwanciyar hankali gami da salama a zukatan bayin Allah kowa ya gamsu da mulkin shi domin kuwa alamun karamci da adakci ƙarara sun bayyana tattare da shi.
Muna haka aka shanye shekara ɗaya, ta biyu ta shigo itama ta raba zuwa tsakiya babu wani abun kaico a cikin mulkin shi saima ƙara ƙaimi da ya ke yi wajen tabbatar da adalci ga bayin Allah.
Ba zance miki nasan abin da ya faru ba bayan shigar shi shekara ta biyu akan karagar mulki ba, saboda ni kaina shekarar ta riske ni cikin sauyin yanayi, Makafa ya tsaface zuciyata ya ɗaure ta cikin sarƙa ina ji ina gani yake aiwatar da ƙudurin da ya saka shi barina na kawo wannan matakin da rayuwata.
Babban tashin hankalina bai wuce sanar min da yayi ba a wata rana da daddare, bayan ya gama shayar da ni jini wanda nike kyautata zaton jinin na mutane ne.
"Muhammad lokaci ya yi da zan sake ka ka yawata duniya domin samo min ɗayar tauraruwar wacce ta ɓoye min kanta tsayin shekaru, tsafina ya sanar da ni kaine kaɗai zaka lalubo ta, saboda haka dole ne ka fita ka nemo min ita."
Tsanar shi fal a idona na ɗaga tare da kallon shi babu alamar tsoro na ce.
"Babu inda zanje Makafa kai baka isa ka tursasani yin abin da kake so ba, kamar yanda ka fara lalata rayuwata to abin ya tsaya iya kaina amma babu wanda zan gayyato cukin rayuwata bare kuma mace, macenda sanda nike da buƙatar ta a rayuwata ka yi min shamaki saboda baƙin zaluncinka."
Ina iya jin yanda halittun da ke tare da shi suka soma huci saboda ɓacin rai da ke ƙoƙarin bayyana akan fuskar sa, ina jin zafin hucinsu na barazanar ƙona ni da raina kamar yanda nike mamaki akan yanda ya mayar da rayuwarshi tare da su, yake kuma sarrafa tunaninsu bayan su ɗin sun kasance mugaye kuma ababen tsoro.
A taƙaice ya ce da ni.
"Babu wanda ya isa ya dakatar da ni akan abin da nike shirin yi, kuma a yau ba sai gobe ba zan turaka duniya domin ka nema min abin da nike da buƙata."
Kafin in samu nasarar cewa wani abu ya huro min wani abu me kama da hayaƙi daga bakinsa, nan da nan na fita ahayyacina na manta komi na kuma manta wanene ni.
Bayan wani lokaci na tsinci kaina ina yawo a sassa daban-daban kamar me lalube, yayinda nike jin sauyi me girma a tare da ni musamman sarrafa kwanya da zuciyata da ake yi, sannan ina jin huci zafi irin wanda nike ji idan Mafaka na waje, bansan adadi yaushe kwana nawa, sayi nawa, shekara nawa na ɗauka ina yawo ba kawai de tsinci kaina a wata unguwa wacce ta kasance shiru, ina jin sautin shirun na sama min da wata nutsuwa gami da salama, a ranar da ƙaddara ta nemi ta haɗa ni da ke bazan manta ranar ba, antashi da wani irin ruwa da sanyin safiya, yayinda wannan nayi tozali da ke tun fitowarki daga wani gida, a ranar zuciyata ta fincike daga riƙon da aka yi mata, ta soma dokawa da wani irin ƙarfi kamar me shirin ɓallewa daga ƙirjina ta fito wace.
Ban janye idona daga kallon ki ba har sai da kuka ɓacewa ganina, a can cikin kaina na soma jiyo maganganun Makafa na maimaita kansu, a ɗimauce na soma ƙoƙarin juyawa domin barin wajen, nan take aka sake ɗaure ni, na koma asalin yanda nike kafin fitowarki, a nan wajen ruwan sama me ƙarfi yayi min dukan tsiya.
Na sake samun ƙwarin gwuiwa ne a sanda kika dawo kuma kai tsaye idona ya faɗa a cikin naki, banso hakan ba musamman dana son akwai tsafi a cikin nawa idon, kuma banso sake ganinki ba duda can ƙarƙashin zuciyata nada muradin hakan, yayinda tsoron abin da zai faru lokacin da kika tunkaro ni ya tada hankalina, neman ƙarfin halin guduwa nike yi amma amma na kasa saboda bani kaɗai bane.
Daga sanda kika kusanta kanki da ni, idona ya shiga cikin naki idon, na tabbatar da aikin gama ya rigada ya gama.
Dalilina kuma na nace maki bai wuce wani zafi da nike ji na ƙona sassan jiki da jinina ba, amma idan na kusanci koda ƙofar gidan ku ne ina samun sassauci, bana iya sarrafa kaina wajen hana ni kusantar inda kike ko a ranar da naje gidanku na ɓalle ƙofar ki ba zan iya cewa ga ta yanda aka yi na shiga ba, kawai de na tsinci kaina a can kuma na samu nutsuwar dana rasa, har ƙasan zuciyata ina jin na aikata ƙaton laifi dana kasa tsayarda kaina daga kusantar ki, nasan ni na buɗewa Mafaka ƙofar da zai shiga rayuwarki ya lalata ta.
Zuciyata ta yi rugu-rugu a sanda kika zaɓe ni kika amince da aurena, hankalina ya tashi matuƙa jin hukuncin da kika zartarwa wayuwarki bayan baki san koni waye ba, hasalima tsorona ya kamata ace kina ji kamar yanda sauran mutane ke tsoro da guduna musamman saboda launin idona da aka narka da tsafi, ni kaina nasan Makafa na bincike ta hanyar idona daga can inda yake.
Bayan wanda yake riƙe da ikon dake ya aura maki ni wata sabuwar ƙaddarar ta auku, tashin farko na lura da wannan mutumin daya ɗauke mu yana ɗaya daga cikin mutanen Makafa, bansan su duka ba domin ba ganinsu nike ba, amma nasan tambarinsu ban kuma san dalilina na kasa tsayar da ke daga binshi ba, saima binki da nayi muka shiga rayuwarsu.
A gaban idona ya kawo maki jini a kofi kuma da hannun ki kika amsa kika aje a matsayin ruwa, sai de tun lokacin na lura ba ruwa bane jini ne kawai de an tsaface shi, a lokacin ma an hanani ƙardin ikon sarrafa kaina ankuma saƙe ɗaure zuciyata sannan aka sakar mi wani yanayi me wahalarwa.
Runtse idona na yi a lokacin da kika sha wannan jinin domin kuwa nasan me afkuwa ta afku, kin rigada kin shiga hannu rayuwarki ta soma fuskantar ƙalubale, kin shiga duniyar dana jiye maki tsoron shigarta tun gabanin insan wacece ke, hakan kuma na sake tabbatar min da faruwar wani abu wani abu wanda nike fircigi gami da tsoron faruwar shi, ƊAURIN ZUCI shine abin da zai biyo baya kema zai ɗaure taki zuciyar domin ya samu abin da yake so rayuwata da taki sun rigada sunyi cuɗanya mun zama taurari masu hasken da zasu haskawa azzalumai hanyar da zata kaisu da cikar burukansu.
Sai de kuma bansare ba duda haka, ina tunanin wannan ta zama hanyar da Ubangiji zai sauya komi, baya zalunci kuma baya goyon bayan masu aikata shi, haka zalika masu iya magana sunce rana dubu ta ɓarawo rana ɗaya tak tame kaya, yanzu za'a soma yanzu ƙulluka zasu soma kuncewa ganzu rayuka zasu samh salama yanzu zalunci zai zo ƙarshe gaskiya zata bayyana da izinin Ubangijin kowa da komi."
Ya faɗa yana kallonta da idanuwansa da ke cike tab da ruwan hawaye, yayinda ya sake danƙe hannayenta a cikin nasa yana son fahimtar da ita ainahin kalar ɗacin da ke danƙare a ƙasan ransa.
Idan ta ce bata girgiza da abin da ya sanar da ita ba tabbas ta yi ƙarya, duda tana fita daga ainahim hankalinta amma maganganunsa na zaune daram a ramin kunnuwanta da kuma cikin kwanyar kanta harma da can cikin ɗaurarrar zuciyarta, ta fahimce shi kuma ta gane abin da yafu sannan kuma ta samu amsar da ke ƙoƙarin tarwatsa kanta saboda tunani.
Ɗaga idanuwanta da suka sauya launi ta yi kamar me ƙidaya haka ta soma bin innuwoyi da ke zagaye da ɗakin tana kallonsu ɗaya bayan ɗaya kamar tana son tantance adadinsu.
A hankali ta buɗe busassun laɓɓanta da wani sauti can ƙasa sosai wanda bata yi tunani Muhammad zai ji ba ta furta.
"ƊAURIN ZUCI."
Tana jin yanda zuciyarta ke billayi kamar me son ƙwacewa daga ɗaurin da aka yi mata.
Ɗan jijjiga hannunta Muhammad ya yi da alamun son ya sawo da ita hayyacinta sannan ya ce.......✍🏻
KU BIYO NI DAN JIN YANDA ZATA KAYA A CIKIN WANNAN ZAZZAFAN LABARI, NICE TAKU HAR KULLUM.
MARYAM STAR⭐.....✍🏻