ƊAURIN ZUCI

Chapter 13

by @maryamstar248

𝘿𝘼𝙐𝙍𝙄𝙉 𝙕𝙐𝘾𝙄🔐
         𝘽𝙔
𝙈𝘼𝙍𝙔𝘼𝙈 𝙐𝙈𝘼𝙍 
(💪𝙅.𝙒.𝘼💪)

Chapter 13
    "Kar kiyi tunani akan kan ki, kiyi tunani akan ɗumbin al'umar da za,a cutar ta sanadiyar ki, ba ke kika yi ba amma akwai gudumuwar da za ki basu su aikata zalunci karki kasance cikin mutane masu son kan su zanji zafin hakan matuƙa ki kasance tamkar ni ɗin nan, ki haɗa hannu da ni mu gwabza yaƙi a tare mu ceci bayan Allah waɗanda basu jiba basu gani ba, ki kasance a bayana kuma me ƙarfafamin gwuiwa ni kuma namiki alƙawarin tsayawa kai da fata wajen ganin na ceci waɗanda basu san komi ba sannan inbaki kariya koda hakan na nufi zan rasa rayuwata."
    Ya faɗa yana nutsar da idanuwansa cikin nata, yana buƙatar koyaya ne ta fahimci kalamansa ta kuma ƙarafafa ma shi gwuiwa, baya son ganin tsoro ko rauni a tare da ita.
     Sosai ta ƙarfafa kanta ta hanyar tsayuwa akan hayyacinta, taƙi bawa ruhinta da aka tsaface damar futar daga gangar jikinta du kuwa da yanda ta ke jin kamar zata mutu a lokacin.
    Ta yi nasarar buɗe baki tare da buɗe ɗaurariyar zuciyarta wacce kamar bata aiki a ƙirjinta tsabar yanda aka tsafaceta.
    "Zan kasance tare da kai."
Ta faɗa tana jin yanda harshenta ya yi mata nauyi sosai, a cikin kunenta ta ji muryarya kamar ta sauya daga ainayin yanda ta ke, yayinda kanta ya nemi bugawa ganin kallon da Muhammad ke yi mata a firgice.
    "Innalillahi mi kuma ya samu muryar ki, please sake yin magana inji."
Ya faɗa gumi na karyo ma shi tako ina.
Kafin ta samu damar furta koda kalma wani lamari da basu taɓa tunanin aukuwar shi ba ya auku a lokacin.
     Wani haske ne fari tasss irin me shiga har cikin kai ya baibaye ilahirin ɗakin, ta yanda ko allura ce ta ta faɗi komi ƙarantarta za,a ganta a wajen.
    Du yanda hasken ke shiga idanuwansu hakan bai saka sun ɗauke ganinsu daga gare shi ba, gaba ɗaya ha kalinsu ya tattaru ne akan abin da zai faru da bayyanar wannan hasken, da ace suna da iko da zukayansu a lokacin, tsabar shock ɗin da suka shiga za su tsaf zasu daina dokawa.
    Wani abu siriri kuma dogo me tsayin gaske wanda ya bayyana da suffa irinta mutane sai dai kallo guda zaka yi mishi ka tabbatar da ba mutum bane.
    Ko ina na jikin shi haske ke fitar kamar walƙiya yayinda shigen muryar da Zunaina ta yi magana sa ita ta karaɗe duka girman ɗaki cikin amsa kuwa ake gaɗi da wani sauti me razanarwa amma kuma babu hayaniya a cikinsa.
    "Assalamu alaikum ya masu karamci."
    Aka yi sallama da muryar, Muhammad ne ya samu ƙarfin halin amsawa muryar shi na rawa.
    "Wa'ailaka salam, daga jin wannan muryar da kuma sallamar da aka yi mana na tabbatar da koma waye to ɗan uwanmu musulmi ne, kuji tsoron Ubangijinku  karku cutar da rayukan da basu ji ba basi gani ba, kada ku ɗora akan zaluncin da ake kan yi mana haƙiƙa mu mutane ne kuma masu rauni ababen tausayi."
    Ya faɗa yana saisaita yanayin tsoron shi.
    Sake matsawa Zunaina ta yi kusa da shi sosai tare da rirriƙe shi da hannayenta tanata faman zare idanu.
    Sassanyar dariya aka yi sannan sauti ya biyo baya da faɗin.
   "Muhammad bawan Allah, kayi sani cewa banzo nan da cutar da ku ba, hasalima na zo giftawa ne na tsinkayi firarka, ban kuma bayyana ba sai da nayi zuzzurfan bincike akanku na tabbatar sa gaskiyarka sannan tausayinku ya sakw kama ni shiyasa na bayyana gare ku.
Ni ba ɗaya daga cikin jinsinku na mutane bane, ina daga jinsin fararen Alhannu sunana Kanzul Mujulu ina son ku kwantar da hankalinku sannan ku nutsu zan yi muku cikaken bayani akaina."
    Jin yanda  Zunaina ke sake rirriƙe shi ya saka shi cewa.
    "Ma sha Allah amma zamu so kaɗan rage hasken da ke tattare da kai yana cutar da mu."
     Babu musu Aljani Kanzul mujulu ya soma noƙe hasken shi har sai da ya zamana marar cutarwa sosai ya kuma rage girman hakittarsa sannan ya ce.
    "Ya ku bayin Allah ina mai baku haƙuri akan cutarwarda na yi muku da halitta ta zan so ku gafarce ni  akan hakan."

Sai da Muhammad ya kalli Zunaina jin ya sassauta riƙon da ta yi mishi sannan ya maida kallon shi sashen Aljanin tare da faɗin.
   "Muma masu kuskure ne babu komi akan hakan."
Sai kuma ya ɗora da faɗin.
"Zan so sanin ta yanda aka yi ka iya zuwa nan har ka kawar da halittun da ke zagaye da mu ka bayyana a gare mu bayan nasan ba kowa ke da ikon yi  hakan ba musamman da aka haɗa da tsafi me ƙarfi."
    Basa iya ganin fuskar shi da kyau amma suna iya jin sautin murmushin da ya yi, cikin sautin shi me shigar musu kai ya ce.
     "Tsafi baya cin zuri'armu hasalima muke girgiza matsafa mu wargaje shirinsu, tsafi bai isa ya hanamu shiga waje ba idan mun so, muna amfani da ƙarfin da Allah ya hore mana wajen yin du abin da muka so, ba iya nan ba zan iya shigo kowane irin waje du girmansa kuma du ƙarantarsa du hatsarinsa zan shiga idan na so."
    Jinjina kai Muhammad ya yi sannan ya ce.
     "Kamar yanda ka faɗa da farko ka ce taimakon mu zaka yi  na gamsu da hakan, ba kuma dan na yarda da kai ba saboda nasan halin jinsin ku sam basu da alƙawari, zata iya yuyuwa kaima ka rikiɗe koka cutar da mu a nan gaba."
(Kai wannan Muhammad ɗin ɗan nema ne kai da za'a taimaka miya kawo na gindaya sharaɗi kuma, wataƙila baka gaji da zaman wajenba🙄🤔).

******
Chak ya tsaya da takon da ya ke, idanuwansa na sauka akan mutumin da ke kwance akan lafiyayyen gadon alfarma, yawata idanuwansa ya ke daga kan fuska har zuwa yatsun ƙafar shi, a kallo guda ya gama gano asalin ramar da  mutumin ya yi.
    A hankali ya soma takawa wani abu me nauyi na fashewa cikin ƙirjin shi.
     Bai san yanda aka yi ba kawai de ya ganshi a durƙushe hannayensa na damƙar na mutumin.
     Sake buɗe idanuwan shi waɗanda ciwo ya gama ramar da su yayi kamar meson tabbatar da abin da yake gani ya ƙure shi da kallo.
      Badan yana kallon fuskar shi ba da ba lallai ya gane yayi managa ba.
    "Son."
Ita ce kalmar data fito daga laɓɓan shi ba tare da sauti ba.
    Wasu irin zafafan hawaye ne suka shiga tsere akan kumatukan shi yana jin ƙwarin gwuiwar shi na sirewa.
    "Aaaaahhhhh Ab,,,,,Abiy."
    Ya faɗa sassanyan kuka na ƙwace ma shi.
    Kalmar Abeey ce ta daki dodon kunnen Saminaka da ƙarfi, nan take ya rumtse idanuwansa yana jin wani sanyin daɗi na zagaye shi lokaci ɗaya, sai da ya tattake ya tattaro duka ƙarfin halin daya rage ma shi sannan ya ce.
    "Junaid."
 Gƴaɗa kai Junaid ya soma yi kamar ƙadangare yana sake tabbatarwa Saminaka a zahiri ne ba a mafarki ba.
    "Ya Abiy."
Ya faɗi kamar me son yin magana amma kuma ya kasa.
    "Taimaka min in tashi zaune."
Babu musu Junaid ya haura kan gadon tare da kama shi, du yanda ya so ya zaunar da shi abin ya gagara yanayin rashin ƙarfi da kuma rawar da jikin shi ke yi hakan ya sake tabbatar ma shi da ba ƙaramin jin jiki yake ba.
  "Ba zan iya zama ba Son jinginar da ni a jikinka ina son jin gumin jikin ɗana."
   Baby musu ya riƙe shi da kyau tare da gyara zaman shi akan bed ɗin sannan ya jingina shi da ƙirjin shi yana shafa kan shi har lokacin bai daina hawaye ba ya ce.
  "Ashe abin har ya kai haka, innalillahi wa'inna ilaihi raju'un garin ya hakan ta faru Abeey?."
    Yayi maganar a matuƙar raunane.
   "Hannu na ƙyarma Saminaka ya shafa sajen Junaid sannan ya ce.
    "Hakan ta faru ne da izinin Ubangijin da yakr bawa azzalumai ikon zartar da zalunci, karka damu da tawa rayuwar ka fuskanci taka rayuwar ta hanyar gyara wasu kusakurai dana shafe lokaci ina maka sha'awar gyarawa tun kafin lokaci ya ƙure maka."

****
Da wani irin sauri ta dinga taka matattakalar tana saukowa ƙasa, yayinda wani yanayi ya baibaye fuskar ta  sauri kawai ta ke ta tabbatar da abin da ta samu labari a yanzu.
    A parlorn ƙasa ta iske su Uncle sun baje suna fira, iya fara'ar fuskarsu ta isa ta shaida mata da gaskiyar abin da ya faru, wata ƙara cikinta yayi mararta na ɗaurewa tamau ta durfafi ƙofar sashen ba tare da ta kula da gaisuwar da su Uncle ke yi mata ba.

      Sai da numfashinta ya tsaya na wasu daƙiƙu sanda ta tura ƙofar room ɗin ta hangi Junaid riƙe da mahaifinsa.
     "Junaid kaine da gaske bansan da zuwanka ba babu wanda ya sanar da ni."
Ta faɗa tana ƙarasa shigiwa room ɗin  bayan mamaki harda wani yanayi akan fuskarta wanda shi kaɗai ya fahimci dalilin wanzuwar yanayi.
    Sai da ya gama shafawa Abiy ruwan zamzam ɗin da ya tofe da addu'o'i sannan ya kalleta da lumsasun idanuwansa tare da faɗin.
"FIRST LADY nine a ƙasarku yau fatan na same ku lafiya."
    Wani makirin murmushi ta saki sannan cike da  kwarewa da kissa ta ce.
   "Lafiya kam ai babu ita, bakaga halin da Daddynku ya ke ciki ba."
    Da ace tasan amsar da zata fito daga bakin Junaid da bata yi wannan maganarba. 
   Kan shi tsaye ba tare da shakka ba ya ce.
   "A,a ai ina tunanin shi kaɗai ne babu lafiya, domin kuwa shi kaɗai na taras a room babu kowa a tare da shi ko zan iya  sanin dalilin hakan?."
    Kasa kunne President ya yi yana jiran jin amsarta, duda baya cikin ƙoshin lafiya amma yana jin ciwo yanda du tarin zuriyar shi babu me kasance tare da shi, har gara su Uncle sune ke zama su jima kuma su ke yi mashi du wani abu da zai buƙata amma ita da take matsayin matar shi bai wuce sai ɗaya jal yake ganinta ba a wuni, kullum cikin bashi uzurin tana office ta ke, ba iya Doctor da Security yakr buƙata ba yana tsananin buƙatar kulawar iyalan shi a tare da shi.....✍🏻

MARYAM STAR