Chapter 14
***
𝘿𝘼𝙐𝙍𝙄𝙉 𝙕𝙐𝘾𝙄🔐
𝘽𝙔
𝙈𝘼𝙍𝙔𝘼𝙈 𝙐𝙈𝘼𝙍
(𝙅.𝙒.𝘼)
Chapter 14
A ɗan daburce ta ce.
"To Junaid in banda abinka mutum irin mahaifinka ai basa buƙatar mutane kusa da su alokacin da suke jinya, basa son takura da hayaniya a tare da su bare ma wannan ciwon na shi da aka gaza gane kan shi, amma dai tunda gaka ka zo saika kula da shi zaka iya yi mashi abin da mu muka kasa yi ma shi ai ko?."
Wani irin sarawa tsakiyar kan Junaid yayi, yana jin yanda memories ɗinshi na baya sanda yayi rayuwa a gidan na dawo ma shi.
Wannan mugun halin nata yana nan, kamar yanda ya lura wannan kissar da take fakewa da ita ta aikata zalunci ko son rai tana nan, babban abin da ke ƙara cin zuciyar shi bai wuce yanda akomi na gidan zaka same shi da saka hannunta ba ya zama jaraba cikin ahalin Samunaka da zame musu ƙarfen ƙafa baƙar innuwa da ke zagaye da su tana musu gashin ƙuma.
A ɗan fusace ta juya tare da dicewa daga room ɗin, dama ba wani abu ya kawota ba illa tabbatarwa kuma ta tabbatar da shi ɗin ne, shine kaɗai ke kutse cikin lamuranta, amma a yanzu tana jin anzo gaɓar da zata shata layi a tsakaninta da shi dama tana tsumayin zuwan shi shiyasa ba kaɗan ta yi farinciki da zuwan shi ba.
"Fahad ka lura da yanayin Maamah kuwa ina tsoron faruwar wani abu sarai kasan halin Jay halin da Daddy ke ciki bai isa ya hana shi yi mata wani abun ba."
Tiredly Fahad ya ce.
"Oh my god wallahi Uncle na soma gajiya da wannan issue ɗin why not Broth ya sauka a house ɗin shi hankalin kowa zai fi kwanciya rashin lafiyar Daddy ba zai hana shi tankawa a wasu lamurran ba."
Sai da ya nisa sannan ya ce.
"Zo muje mu duba shi bana so ran shi ya ɓaci daga saukar shi yau ko hutawa bai yi ba.".....
Ture duka tunanukan da ke addabar zuciyar shi ya yi, tare da sake mayar da hankalin shi sosai wajen nazartar zanen da ya sha matuƙar wahala wajen zana shi a cikin loptop ɗin shi, yana yi yana sipping hot milk cooffie da yayi making a tea cup.
Yana jin maganganun su Uncle na damun kunnuwan shi hakan ya saka shi juyawa ya kalle su bayan ya buɗe ɗan mitsilin bakin shi wanda ke ɗauke da pink lips masu taushi sosai ya ce.
"Uncle and Fahad problem, kuna takura rayuwata wallahi surutun ku ya hanani fahimtar abin da ya dace."
Ya faɗa da cool voice ɗin shi.
Baki hangame Uncle da Fahad ke kallon shi, kafin cike da shaƙiyanci Uncle ya taso tare da zagayawa ta bayan shi ya soma dafe kafaɗun shi da ƙarfi.
Ganin haka sai shima Fahad ya taso ya ɗauki tea cup ɗin da ke kan ƙaramin study table ɗin, gana guntse dariya ya nufi saitin bakin shi da shi.
Taune lower lips ɗin shi yayi na ƙasa yana tunanin rainin hankalin da mutane biyun nan suke yi ma shi.
"Oya Sir buɗe bakin mana."
Fahad ya faɗa yana ƙoƙarin kai ma shi cup ɗin dagaske.
"Yo to ina dalili haka kawai kazo kana mana feleƙen wai mun takura maka, kawai de kace kayi missing waɗannan gardawan da ka tara cikin gida suna maka bauta, ina tausa ce nima na iya dan akwai ƙwanji kamar dai kai ɗinan idan ma baka saniba to wajena ka gado."
Uncle ya faɗa yana taƙarƙarewa wajen dannar kafaɗun Jay.
Lasar lips ɗin shi ya yi tare da shanye girman idanuwansa ya marƙasa hannayenta ta baya ya saƙalo na Uncle da duka ƙarfinsa har sai da kan shi ya kwanto ta kafaɗar shi.
Da wani irin sauri Fahad ya saki cup ɗin jikin shi na rawar mazari sai da ya tabbatar da ya saita hanya sannan ya ce.
"Kutumar to wallahi Uncle kayi takanka dan Big bro baya da maraba da wanda akewa allurar doki wajen ƙarfi, to wai kai waya aikeka danna kafaɗun shi kamar dai baka ga aiki yake yi me muhinmanci ba."
Uncle wanda tuni ya gama jiƙewa da gumin azaba ya kalli Fahad cikin wani yanayi gwanin ban tausayi ya ce.
"Dan ubanka Fahad ni abokin wasanka ne maza ka zo ka taumaka ka cece ni kar ya karyan hannu."
Zaro Ido Fahad ya yi tare da faɗin.
"Wa? ai idan ka ganni lahira kai ni aka yi, babu dalilin da zan kawo kaina wajen mutuwa kai da taka ta ƙarato ina maka fatan sauka lafiya ni nayi nan."
Yana gama faɗin haka ya kwasa a guje yana ƙyalƙyala dariyar zufar azabar da ya ga Uncle ɗin na yi, a fili ya furta.
"Ashe dai har yanzu ya Junaid na nan da muguntarsa aiko zanyi takaina dan wallahi yanzu nasan ciwon jikina ba zan biyewa Uncle ba ayita gana min azaba."...
Tattausan murmushi Jay ya saki sanda yaga Fahad ya tafi sai sannan ya sassauta riƙon da yayiwa Uncle da damatsansa, cike da raini wayo ya ɗaga kai yana kallon Uncle da ke miƙar dole, ga gumi nan na zirara daga cikin kan shi wanda ya tabbatar da na azabar riƙo ne.
"Ayya sorry my Uncle ban kula kaine a wajen ba."
Wata baƙar harara wacce ta saka Jay sakin guntuwar dariya Uncle ya wurga ma shi tare da faɗin.
"Mugu kawai azzalumi wallahu sai Allah ya saka min kuwa na rantse daga yanzu ka gama zaluntata wannan lalacewa har ina ace ɗa na dukan ƙanin ubansa."
Wannan maganar da Uncle ya yi ce ta haskowa Jay wani shuɗaɗen lokaci, lokacin da ya riga da ya shuɗe da wasu al'amurra wanda bai isa ya manta da su ba.
****
Yara ne su uku, biyu kan su ɗaya sai kuma ɗaya wanda ya kasance ƙaraminsu, zaune suke a garden gaban su cike da kayan marmari wanda suka tsinko, ɗaya daga cikin yaran wanda suke kai ɗaya ne ya ce.
"Yauwa Junaidu ka tsaya abi ta gaskiya banda son kai, nida kai girman mu ɗaya saboda haka namu kason shi zai fi yawa, shi kuma Fahad sai mu sammashi ɗan kaɗan ko?."
Ya yi maganar yana kallon Junaid ɗin, wanda ya ɗauki mintuna biyu bai ce komi ba sai kuma zuwa can bayan ya murtuke fuska ya ce.
"Lallaima Uncle ɗin nan, ka cika azzalumi shi Fahad ɗin ai shine ƙarami kuma naga idan ta gaskiya za'a bi ya fimu ci saboda haka babu wani son kai dole a raba daidai."
A harzuƙe yaron da aka kura da Uncle ɗin ya miƙr tare da dafe ƙugun shi irin na yarinta ya ce.
"To wallahi baka isa ba Junaidu dole ayi yanda na ce ai nine Uncle ɗinku ku duka biyu haka Ummy ta ce, yanzu umarnina zaku bi."
Daga nan musu ya kaure a tsakaninsu, inda har takai su ga dambacewa yaron da zaune wanda aka kira da Fahad ne ya tashi ya fice da gudu daga garden ɗin ya nufi cikin gida.
Ba'a ɗauki lokaci ba sai gashi ya dawo shi da wata balarabiyar mata, wacce ita ta raba faɗan kafin ta kama hannayensu suka zauna akan ciyayinda ke wajen tana murmushi tare da shafa kawunansu ta ce.
"Miya haɗa Uncle da son ɗin shi faɗa harda dambe kuma."
Nan yaron da ake kira da Uncle ya soma tada jijiyoyi tare da bata labarin abin da ya faru, Junaid jin bai ƙara kiya rage komi ba sai bai tanka ba yana jiran jin abin sa Ummy ɗin zata ce.
Ilai kuwa abin da yasani ne ta aikata kama kunnen shi ta yi bada ƙarfi sosai ba ta soma faɗi cikin harshen larabci.
"Bana hanaka yiwa Uncle rashin kunya ba, shi ne gaba da kai kuma tamkar Abiy ɗinka ya ke du abin da ya ce kuyi ku daina musawa kai da ka zaƙalƙale kace ba haka ba shi Fahad ɗin da kan shi yace min ya yafe baya so kusha ku biyu."
*****
Yana zuwa nan a tunaninsa ya yi sauri shanye ruwan da ke ƙoƙarin taruwa a idanuwansa tare da rufe loptop ɗin gaban shi ya tashi a zafafe ya soma ƙoƙarin barin wajen, yana jin muryar Uncle can sama sosai yana yi ma shi magana, sai de baya jin zai iya tsayawa bare kuma ya saurari abinda ya ke faɗin, bai dakata ba sai da ya dangana da ƙofar room ɗin shi a zafafe ya murɗa handle ɗin ya shiga ya kullo da ƙarfi.....
*****
Yauma kamar kullum kwance ta ke tana fitar da wani irin numfashi wanda ke cire da tsananin azabar da take jin na game ruhinta, farar fatarta na nan da haskenta sai sheƙi ta ke ƙarawa gami da wani sihirtaccen kyau me ɗaukar hankali, babban abin da yafi bata takaici a rayuwarta na yanzu bai wuce yanda jikinta ya ƙi bada haɗin kai wajen nuna ainahin azabar da take ciki ba, gangar jiki da ruhinta bai taɓa sararawa ba daga ƙunar azaba amma fatarta da jikinta kullum ƙara kyau suke.
Kamar yanda ta saba adoka yaushe idan Mafaka ya yi tarayya da ita, cike da tsananin dauriya ta silale ta sauka daga kan bed ɗin ta rarrafa kamar wata yarinya ta nufi ƙofar toilet ɗin da ke ɗakin, tana gab da isa wajen kamar daga sama ta tsinkayo muryarsa.
"Rimsha, mi kike ƙoƙarin yi?."
Mafaka wanda ke kwance yana barci ya faɗa still idon shi a kulle alamar barci ya ke.
Wani tarnaƙin ɓacin rai gami da raunine suka baibayeta nan take, yayinda zuciyarta ta cigaba da nanata mata tambayar da kullum ta ke jefa mata.
'Shin dawa kike tarayya ne Rimsha, kin tsaɓi sadaukar da rayuwarki wajen shanye azabar mutumin da baya da alaƙa da mutane, shin rayuwarki da cancanci ƙarewa a haka tare da jinsin Aljannu bayan gwagwarmayar da kika sha a baya, mi yasa ba za ki yi wani abu ba da zai kawo sauyi a rayuwarki."
Batasan yanda aka yi ba, sai kawai ganin shi ta yi a gabanta shi da tawagar Aljanunshi sunci burki a kusa da ita.
Fashewa ta yi da matsanancin kuka tana rufe fuskarta da duka tafukan hannayenta saboda bata son ganin shi, shida tawagar shi suna firgitata matuƙa suna son juyar da tunaninta da yayi rauni.
Kamar an riƙe ta da ƙarfe haka ta ji hannun Mafaka daya damƙi wuyanta ya ɗagata sama akan iska, cijin cakuɗaɗɗiyar muryar shi wacce ta soma sajewa data halittun da ke tarayya da shi ya soma faɗin.
"Ban hanaki yin wannan wankan ba adu sanda muka kaɗaice da ke, ban hana ki koda taɓa ruwa ba a du ranar da muka buƙace ki, mi yasa kike da taurin kai har haka?."
Ya yi maganar yana zare duka girman idanuwanshi akanta.
Bata iya ganin shi kamar yanda can sama sosai take iya jiyo gurnanin maganar shi, kafin kuma tayi wani yunƙuri tuni numfashinta ya katse daga ƙirjinta wani shiru ya gifta ta cikin rayuwarta....
Bata san lokacin data ɗiba yashe a wajen ba, amma daga yanda ta ji jikinta ya ƙara tsami fiye da yanda yake mata ya tabbatar mata da lallai ta jima, da ƙyar ta buɗe idanuwanta daga da bata iya gani sosai da su, da jan jiki ta tura ƙofar toilet ɗin dake kusa da ita ta shiga bayan ta karanto addu'a can ƙasan zuciyarta.
Ƙur ta ƙure abin da idanuwanta ke haska mata da kallo babu ko kyaftawa, bata san lokacin da ƙarfin halinta ya ƙare ba kawai ta sulale a ƙasa tana furta sauti daga can ƙasan maƙoshinta da muryarta ta disashe.
"Innalillahi wa'inna ilaihi raju'un."
Tana kallon jinin da ke gudu a ƙasa, ya lalata ruwan du dan kada ta tsarkake jikinta ya lalata ruwan du dan kar ta yi ibada, tashin hankali ne ya kuma riƙito mata har numfashinta na neman tsayawa a ƙirjinta.
Kamar wacce ta tuna sai ta zabura dan ta miƙe azabar data ziyarce ta ne ta saka ta saki wata kasalalliyar ƙara, a wahale ta ja jiki ta fita tana ƙyarmar azaba.
Kitchen ta nufa a dudduƙe babu komi a jikinta daga ita sai ɗan guntun towel ɗin data sufe jikinta a toilet, a hargitse ta ke duba ko ina ko zata samu ruwa amma hata da cikin fridge da tab ɗin sink duka abu ɗaya ne ya rigada ya lalata duka ruwan gidan ya mayar da su jini da tsafinsa, nan take zazzafan zazzaɓi ya rufar mata bayan wanka harda azababen ƙishi da ke neman kaita lahira ne ya rufar mata.
Jinkina ta gi da jinin Kitchen Islan tana fashewa da marayan kuka ita kaɗai, tana jin inama Allah ya ɗauki rayuwarta a wannan lokacin wataƙila ta huta da wannan baƙar azabar.
Sai de abin da bata saniba shi ne, yanzu ƙaddara ta sake buɗe mata wani shafin na rayuwa, ƙaddararta na bibiyarta kamar innuwa tana mata rumfa....✍🏻
ALLAH SARKI RIMSHA ABAR TAUSAYI, ALLAH DAI YA KAWO MAKI ƘARSHEN WANNAN BALA'I
Masu karatu kuci gaba da bina sau da ƙafa domin faɗakantuwa, ilimantuwa harma da nishaɗanyuwa a cikin wannan zazzafan labarin me take ƊAURIN ZUCI.
MARYAM STAR CE....✍🏻