Chapter 15
***
𝘿𝘼𝙐𝙍𝙄𝙉 𝙕𝙐𝘾𝙄🔐
𝘽𝙔
𝙈𝘼𝙍𝙔𝘼𝙈 𝙐𝙈𝘼𝙍
Chapter 15
Barcin wahala ne ya ɗauke ta a tsayen, barcin da sam bata shirya yin shi ba a wannan lokacin.
Ba ita ta farka ba sai lokacin da taji alamar motsi, motsin da ta ji shi har can ƙasan ranta, domin kuwa motsi ne dake alamta mata wanzuwar wanda a duniyar nan babu abin da take tsoro bayan mahaliccinta sai shi, da ace zata iya data cire wannan tsoron na shi da yakamata ace yanzu ta daina ji kodan irin baƙa ƙirin ɗin azabar da yake gana mata, amma sam ta gagara hasalima a kullum wannan tsoron yana ƙaruwa ne kuma bata jin anan kurkusa zai ragu.
Tura door ɗin yayi bayan ya murza handle daga bakin ƙofa yake ƙare mata kallo, yanda farar fatarta ke sheƙi da kuma yanayin tsayuwar da ta yi na sake saka ma shi yanayin buƙatuwa ta yanda yake jin halittun kan shi na sake azalzala shi.
Sanin da yayi ba zata taɓa jure ɗaukar shi sau biyu ba ya saka shi haɗiye kwaɗayin shi, yana ƙawata mummunar fuskar shi da wani baƙi ƙirin ɗin murmushi wanda ya sakata rintse idanuwanta da suka yi nauyi saboda zazzaɓin da ta ke yi.
"Halan neman ruwan ne ya kawo ki har nan, to kin samu ne?."
'Na samu?.'
Ta maimaita tambayar a can ƙasan ranta tana jin wani takaici na gume ta, a fili kuma sai ta zame ta zauna a wajen tana jin yanda jikinta ke rawa ƙafafuwanta na sake yin tsami suna dandaƙa irinta wanda zazzafan zazzaɓi yayiwa mugun kamu.
Washe gari.
Zuwa lokacin ta gama fita a hayyacinta hatta da numfashi da ƙyar ta ke yi.
Sarai ta ji sanda Makafa ya shigo shi da wani wanda take kyautata zaton Ƙwaro ne idan ba shi ba babu wanda ke zuwa inda ta ke, ilai kuwa zarginta ya tabbata lokacin da ta ji shigar wannan abin me tsananin azaba, wanda hakan ke alamta mata suna zuƙar jininta ne kamar yanda suka saba du ƙarshen wata musamman sanda period ɗinta ke kurkusa da zuwa, nan take wani tashin hankali ya kuma rikito mata yayinda azaba ta haɗu da wata azabar nan take ta fice fit daga hayyacinta.
Wata iriyar jijjiga ta soma yi idanuwanta na yin sama ƙirjinta na ɗagawa sama tana wani nishin azaba hannuwanta na rintsewa da tsananin ƙarfi.
Cak Ƙwaro ya tsaya da abin da yake yi nan take notikan kan shi suka soma warwarewa sanda yayi tozali da cikakkiyar halittar ƙirjinta da suka bayyana a sarari.
Jijjigar da Mafaka yayi ma shi da ƙarfi wacce yaji ta har can cikin ƙashin shi ce ta dawo da shi duniyar zahiri nan ya fahimcin katoɓarar da yayi, amma dayake ɗan duniya ne lamba ɗaya sai ya maze bai ko kalli sashen da Makafa wanda iskokan shi suka fara huci ba alamar ya shiga ɓacin rai, a cikin wata ƙwalba ya zuba jinin sannan ya kulle bakin da ƙarfi cike da kulawa ya riƙe ƙwalbar sannan ya fuskanci Makafa bayan ya sake satar kallon Rimsha data gama fita a hayyacinta.
"Zamu iya tafiya na gama."
Ya faɗa yana ɗage gira irin na riƙaƙun ƴan duniya.
Wani irin kallo Makafa ya bi Ƙwaro da shi, yana ƙare ma shi kallo sama da ƙasa.
Bari ne tas da shi dogo wanda saboda tsayin shi har ranƙwafawa yake yi, baida wani jiki sosai amma akwai alamun hutu sosai tattare da shi wanda ya ɓoye asalin tsufan shi.
Huci Makafa ya fesar daga bakin shi yana tabbatarwa kan shi duda Ƙwaro ya girme shi nesa ba kusa ba amma yafi shi kyawun halitta me ɗaukar hankali, iya kallon farar fatar shi da yake yana motsa ma shi kishi, kishin tashi halittar data kasance ba irinta Ƙwaro ba, halittar shi da tazama tsanin da ya hau har ya iso matakin da yake a yanzu.
"Ko akwai wani abu na musamman ne da kake buƙatar yi kai kaɗai?."
Ƙwaro ya katse ma shi tunani ta hanyar tambaya.
A tare shi da halittun kan shi suka saki huci, wanda ya saka ɗakin ya ɗauki zafi nan take, sai kuma yakai duban shi kan Rimsha da har lokacin bata dawo hayyacinta ta daina fizge-fizge ba.
"Kada ka kuskura ka sake raya wani abu makamancin hakan, kana da hutumi akomi amma banda wannan wajen, ka kiyaye hakan ya zama na ƙarshe."
Makafa ya faɗi yana jin haushin yanda ya kasa yin kutse cikin zuciyar Ƙwaro domin ya ga ainahin abinda ke cikinta.
Wani lalatacen murmushi Ƙwaro ya sakarwa Makafa sannan ya doshi ƙofar zai fita.
Daga inda yake ya saka aka ɓatar da ƙofar ta shafe kamar bata taɓa wanzu a wajen ba.
"Mi shirunka ke nufi?."
Makafa ya jefawa Ƙwaro tambayar ran shi na sake ɓaci.
"Baka sanniba har yanzu, baka gama tantance ainahin halayyata ba, karka manta nine sama da kai akomi ka kiyaye, kariga da kasan asalin abin da nike nufi daga sanda na bayyana maka and kota halin yayane dole zan samu."
Ya faɗi yana saka tsafi ya ɓula bangon nan take ya ɓace daga wajen.
Da wani irin tashin hankali wanda har ya saka halittun kan shi fasa wata tsaya data girgiza gidan gaba ɗaya Makafa ya tashi tsaye yana zare idanuwansa marasa kyawun gani, ba abin da Ƙwaro ya faɗi bane tashin hankalin shi yanda yaga yau bayan tsayin lokaci yayi amfani da tsafi, tsafin da yake tunanin ya raba shi da shi tun shekaru da dama, tsafin da yake tunanin dashi ne yake juya ƙwaron duda kasancewar shi ubangidan shi a da, to minene zai faru ayanzu da hakan ta faru......
Idanuwan Ƙwaro ne suka juye baƙin cike ya ɓace ɓat, farar ƙwayar kuma ta koma jazur.
Wasu kalamai marasa tushe ya soma karanto, yana kulle kan shi a cikin bishiyar da ya shige ta hanyar siddabaru, da sandar hannun shi yayi amfani kasancewarta ta tsafi ya buɗe ƙirjin shi zuciyar shi ta bayyana, bai jirayi komi ba ya ɓalle murfin kwalbar jinin Rimsha daya ɗiba ya zazzage kusan rabi a cikin zuciyar shi sannan ya ɗaga ya shanye sauran tas, ya mayar da ƙirjinshi ya kulle kamar bai taɓa buɗewa ba, sai da jinin ya gama shiga ya gauraya da cikin shi sannan ya aje ƙwalbar ya warware tsafin ya fito daga cikin bishiyar yayi siddabaru ya ɓace daga wajen ran shi fes sanin da yayi muddin buƙatar shi bata biya ba tofa lallai Makafa ba zai samu abin da yake so ba.....
*******
JUNAID
Gyaɗa kai yake yana sake tabbatarwa Abiy da gaskiyar abin da Uncle ke faɗa.
"Yaya please ka yarda da wannan tafiyar in sha Allah zaka samu lafiya, komi zai wuce wannan yanayin da kuma komi daya faru sun isa su tabbatar maka da butulcin al'umar da ka mulka agareka, sun manta da kai sun manta da halaccinka sun manta da tarin alkairan daka cike rayukansu da shi, yanzu lokaci yayi da zaka zubar da komi ka kunce zuciyarka ka fuskanci rayuwarka badan su ba, sai dan mu, dan ni da bani da kowa sai kai da zuri'arka dan Junai da ya rasa mahaifiya sai kai kaɗai, dan su Fahad da sauran yaranka dake tsananin buƙatarka, please Yayah ka amince da hakan."
Rintse idanuwa Samukana yayi yana jin ciwon abubuwan da suka faru kuma suke kan faruwa a rayuwar shi,kamar yanda ƙaninsa ya faɗa gaskiya ne, ya kamata ya mance da kowa da komi ya fuskanci rayuwar shi, bai dace ya ɗorawa kan shi damuwar akan al'umar da ya ƙwallafawa rai wajen ganin ya inganta rayukansu ba, bai dace ya jefa ahalinsa cikin tashin hankali ba, zai yi komi domin al'umarsa su yi farinciki haka kuma zai yi komi domin faranta ran iyalansa ahalinsa da suke buƙatar shi, kamar yanda yake ji a can ƙasan zuciyarsa al'umarsa ma na buƙatarsa.
Cikin disashiyar muryarsa da ciwo ya gama cinyewa ya ce.
"Na amince kunema min lafiya amma bazan fita ko wace ƙasa ba, a maimakon hakan zan so ku tarkata mu koma Katsina canne tushena can ne asalina inada yaƙinin zan yi farincikin rayuwa a can ina son ku ina son farincikinku, amma bazan iya barin ƙasarnan a wannan yanayin ba ku yarda da ni sanadiyyar ƙasata nike a wannan halin kuma a sanadiyyarta zan samu lafiya."
Fesar da zazzafan huci Junaid yayi daga bakinsa, yana jin yanda kan shi ya soma ciwo bisa taurin kan Abiy ɗin shi, ya so ace yabi shawarar shi ya bishi zuwa Dubai da tabbas yayi bankwana da 9jah koda da sunan ziyara ba zai yarda ya zo ba, bare kuma sake dawowa cikinta da sunan zama, amma ko yanzu gaba dai gaba dai dole wata rana koba da son ran shi ba ya ɗauke shi tun kafin ƙasar ta saƙe maimai irin rashin adalci da butulcin da tayi mashi a wancan karo, yanzu shirye ya ke tsaf wajen ganin ya cimma muradan sa.
"Its okay yand ka ce haka za'ayi abiy amma kuma a yau ba sai gobe ba nike so mubar garin nan zanyi mana bucking fly daga yanzu zuwa yamma bana so muyi dare."
Jay ya faɗi yana miƙewa tsaye hannunshi cikin aljihun fara ƙal ɗin jallabiar jikin shi wacce ta sake fito da kamar shi sak balaraben usul.
"Big bro miye na gaugawa kuma da yau da gobe ai duk ɗaya ne a wajen Allah, ni zanzo ace sai goben muka tafi tare da shi kodan Doctor da zai zo ya sake duba shi a yau ɗin."
"No a yau in sha Allahu ba sai gobe ba Abiy zai bar garin Abuja, du wanda ya zama ready a cikinku zai iya tahowa daga baya."
Yayi maganar cikin muryar da ke nuni da baya son jan zancen bare har yayi tsayi.....
Da misalin ƙarfe huɗu na yamma jirgin su Junaid ya ɗaga daga Abuja, bayan sun sha wahala don har ance sai de da safe saboda babu safinja amma haka ya nace akan zai siye duba ticket ɗin, ganin haka sai kawai kowa ya shirya tare da ɗaukar abubuwa masu muhimmanci domin tafiyar ta riske su ne a bazata, koda yake yakamata ace zuwa yanzu sun saba da abubuwan dake tunkararsu a bazata, musamman rashin lafiyar Daddy wacce ita ce ta soma sauya komi, daga ranar da ya kwanta ciwo baƙin al'amurra keta kusantarsu.
Zaune ya ke akan kujerar jirgin a zahiri idon shi akan Abeey wanda aka sakawa abin shaƙar numfashi amma a baɗini ya rigada ya afka duniyar tunani me zurfi tunanin da yashe duka sauran abubuwan da ke tsare a cikin kanshi.
Ɓaro-ɓaro yake hangen yanda zanen ke kasancewa a wajaje mabanbanta, babban abinda yafi ɗaure kan shi tamau bai wuce yanda zanen ke sake haskuwa a wajajenda bai taɓa zato ba, binciken da yayi kuma akan zanen na saka jinin jikin shi ƙafewa saboda tsabar tsoro razana da kuma tashin hankalin da ke baibaye shi idan fuskokin waɗanda ya taɓa yin tozali da zanen a wajensu suka haska a cikin kan shi....✍🏻
Kuyi haƙuri da abin da ya sawwaƙa sai mun haɗu a karo na gaba domin warware wannan tirka-tirkar.
MARYAM STAR CE