ƊAURIN ZUCI

Chapter 16

by @maryamstar248

***

𝘿𝘼𝙐𝙍𝙄𝙉 𝙕𝙐𝘾𝙄🔐
         𝘽𝙔
𝙈𝘼𝙍𝙔𝘼𝙈 𝙐𝙈𝘼𝙍 

Chapter 16
     Ɗaure ya fito da babban towel daga ƙofar da nuni da bathroom ce, yalwataciyar sumar shi me tsayin gaske ta kwanta luf akan fatar shi kasancewar a jiƙe ta ke da lema.
   Gaban miro ya nufa cike da kuzari ya jona handryer ya soma busar da jiƙaƙen gashin kansa, cak ya tsaya da abin da yake yi yana shanye girman idanuwansa a jikin miro zuciyar shi na dokawa da tarin abubuwa mabanbanta, tsoro mamaki zullumi haɗi da ɗimauta sune abubuwanda suka dabaibaye shi nan take, ƙamewa yayi ƙyam yana sake kallon yanda zanen tanbarin ya soma girma yana mamaye duka miro ɗin cikin ƙanƙanin lokaci.
   Kamar ƙyastawar ido haka zanen ya ɓace lokaci ɗaya kamar bai taɓa wanzuwa a wajen ba, lamarin da sake dagula lissafin Junaid yai tsaye kamar wanda aka dasa al'ajabi kwance akan fuskar shi.
     A gaggauce ya shirya cikin shiga irinta larabawa ya fice bayan ya ɗauki wayar shi.
     Kai tsaye ya nufi sashen Abiy wanda ke down stairs zuciyar shi na luguden duka yayinda yake tarawa gami da kuncewa a cikin kan shi.
     Sai a lokacin ya saki numfashin da ya maƙale a ƙirjinsa tsayin mintuna lokacin da yayi tozali da ramamiyar fuskar Samunaka da ke kwance alamar yana barci daga ganin barcin kasan ba ƙaramar azaba yasha ba kafin ya ɗauke shi.
     Rintse ido ya yi tare da ƙarasawa gaban gadon ya soma karanto azkar ɗin marice yana tofa ma shi tare da shafe mashi ilahirin jikin shi, bayan ya gama ya zauna yana kallon fuskar shi a zahiri amma a baɗini tunani ne fal ran shi wanda ke neman zautar da shi.
   "Ya Allah."
Ya faɗa cikin sautin da ke nuna gajiyawa tare da bayyananniyar damuwa.
   "Mi nene asalin abin da ke damunka Junaid, gaskiya, iya gaskiya kawai nike son ka sanar da ni ban yarda da amsarka ba akan babu komi buɗe baki zaka yi ka sanar da ni gaskiyar da kake binnewa a ƙirjinka."
   Uncle yayi maganar yana maida yanayin shi serious wanda hakan ya tunawa Junaid yana tare da Uncle ba abokiba ba kuma wannan me saka shi rahar da nishaɗi ba, wannan mutumin ƙwalli ɗaya da zai nuna a matsayin ƙanin Abiy ɗinsa.
    Baisan yanda aka yi ba sai tsinkayar sautinsa ya y can ƙasa sosai yana faɗin.
   "Na sake gani wannan tambarin ya sake bayyana."
    Ya faɗa yana sake kallon hoton tambarin da ya zanu raɗau a cikin kan shi.
    "Shine wanda kake bincike akan shi ko, shine wanda ka tattara duka lokacinka wajen binciko abin da sanin shi ke baraza da rayuwarka, to miyasa?."
   Bai yi magana ba illa haɗiyar yahu da yayi yana jin ɗaci a maƙoragaronsa sannan ya ɗaga hannunsa.
    Bin yatsun hannunsa ukku da ya ɗaga Uncle yayi da kallo, fuskar shi na washewa da wani yanayi wanda ke nuni da yana cikin damuwa, ba kuma tare da ya tauna maganar da ke ƙoƙarin kubtowa daga zuciyar shi ba ya ce.
    "Ummy, akwai Ummy, sai Yaya to waye ɗayan kuma?."
    Kamar an fizgo maganar daga bakin shi da wani irin amo yace.
   "MUHAMMAD sai Habibynah Muhammad shi ne cikon na uku."
    Ya faɗa wata wutar ɓacin rai na bayyana a idanuwansa.
    Girgiza kai da sauri Uncle yayi fuskar shi na ɗinkewa da tsananin tsoro firgici gami da razana ya ce.
   "Muhammad dai Muhammad dai wannan yaron hatsabibi mugu azzalumi Aljani a suffar mutum shi kake nufi?."
   Ya yi tambayar yana zaro duka idanuwan shi waje.
      Haɗiyar yawu Junaid ya kuma yi akaro na babu adadi sannan ya ce.
   "Ih kuma a'ah shi kuma ba shi ba, ina nufin Muhammad wanda ka sani amma ba wanda ka ambata ba a yanzu Muhammad ɗina ba  haka yake ba."
    Da wani irin zafin nama Uncle ya isa gaban shi tare da cakumar kwalar rigar shi yana faɗin.
     "Junaid faɗa min gaskiya ka faɗa min gaskiya nace, Innalillahi wa'inna ilaihi raju'un garinya  tayaya haka zata faru mi yasa??."
    Ya jero maganganun idanuwan shi na rufewa da tsananin tashin hankali.
    Sama-sama numfashin shi ke fita yayinda jini ke fita ta hanci da bakin shi, bakin shi na rawa cikin ƙaramar murya wacce ciwo ya gama cinyewa yayi maganar data saka Junaid hankaɗe Uncle da tsananin ƙarfi yayi baya ba shiri tare da ƙoƙarin tsayuwa akan  ƙafafuwansa yana hana kanshi faɗuwa saboda ƙarfin bangazar da Junaid yayi ma shi.
    "Ruwa son bani ruwa in sha ina jin ƙishi."
Abeey ya faɗa yana shaƙuwa.
     A rikice ya rarumi robar zamzam ɗin daya shigo da ita ɗakin ya buɗe tare da kama shi cike da kulawa ya soma bashi ruwan yana hana tashin hankalin shi bayyana asarari.
      Hannun shi ya saka yana goge jinin da ke biyo gefen baki da hancin Abeey wani abu na dunƙulewa a ƙirjin shi....



*****
SHINKAFI

Yau kimanin sati ɗaya kenan da soma faruwar lamarin da ya dasa tsoro da zullumi a zuciyoyin mutanen musamman mazauna unguwar Shinkafi da lamarin  yafi shafarsu, a cikin sati ɗaya babu ranar da ba za'a tsinci gawa ba ko mutuminda aka cirewa wasu daga sassan jiki, yara kuwa sunkai talatin waɗanda aka kwakulewa ido, kowa ka gani a firgice yake har sun manta da wani abu wai shi murmushi ko dariya.
    Da suka lura anfi yin ta'asar da marice sai suka dinga killace kawunansu da yaransu, suka daina hada-hada da zurga-zurga suka rungumi kawunansu don tsira da lafiya da rayuwarsu.
     Sai de kuma duda hakan ba'a fasa ba domin yanzu takai har cikin gida ake bi ana kashe su ko a ciri wasu daga sassan jikinsu bayan an zuƙi jinin lamarin da ya sake hautsina hancin cikunnansu, gasu kamar waɗanda shafewar basira ta same su gaba ɗaya sun gaza samo mafita ko abin yi game da lamarin, sun yi meeting akai kai koke a gwamnati saide hakan bai yuwuba saboda labarin sauke Samunaka da suka samu tare da kuma rashin kafiya me tsanani daya kamu da ita, daga nan aka same musu ɗan gwarin gwuiwar da suke da shi raka sai da fatansu ya rushe suka zauna zamab jiran tsammani da kuma ɗauki daga Allah.

    A ƙofar wani gida, wata fara tas ɗin matashiyar budurwa ce wacce  tai shiva kamar wata tsohuwa, a gindin wata ƴar bishiya da ke dashe gaba kaɗan da gidan ta tsuguna tare da tsinkar ganyayyakin jikinta bata damu da ƙayar dake caccake hannayenta ba.
    Yanayin duhu da kuma shirun unguwar sam bai dameta ba, sannan hasken napep ɗin daya haske ta bai saka ta ɗago daga abin da take yi ba har sai da ta tsigi adadin da take buƙata sannan ta ɗago tana kare fuskarta daga kallon hasken wanda ke shigewa kai tsaye har can cikin idonta, matsowar da napep ɗin tayi zuwa gabanta bai saka ta gudu ba saima ƙara  lulluɓe jikinta da tayi da tsohon zanin atamfar data yafa tana ƙarewa mutumin da ya fito daga ƙurƙurar kallo tana son tantance kamaninsa.
   Ba tareda shamaki ba idonta ya sauka akan ƙarama kuma kakkaifar wuƙar dake cikin hannunsa wacce ta kasance ƴar ƙarama sosai dan kaɗan kan wuƙar ya fito da cikin yatsu sa duda yana ƙoƙarin ɓoye hakan.
    Cikin abin da bai wuce ƙyastawar ido ba ta gama gane launin abin da ke jikin wuƙar launin ja ne, kuma nan take ta tabbatarwa kanta da jini ne da alama kuma bai daɗe da taɓa wuƙar ba saboda har ɗiga taga yayi sau ɗaya, kuma zata iya rantsewa akan ta ji ƙarar saukar shi akan ƙasar wajen.

       Wata irin kakkarwar jikin Malam ya soma yi sanda ya kusanceta sosai har baisan sanda ya jefar da abin da ke hannun shi ba ƙafafuwansa na karkarwa da bayyananen tsoro.
     Wani makirin murmushi ta sake tare da duƙawa saitinsa ta ɗauki abin da ya yadda ta riƙe cikin ɗayan hannunta ba tare da tace komi ba ta wuce tana barin wajen ta shige cikin ƙaramin gidan wanda ko ƙyauran kirki baya da....

   Ƙaƙƙarfan numfashi Malam ya sake sanda ta shige gidan, a hanzarce ya juya tare da shigewa napep ɗin shi yaja a sukwane yabar wajen.
     A ƙofar gida ya tsaya a hargutse ya fito ya afka cikin gida babu ko sallamar basajar daya saba yi.
    Iske Huwaila yayi na dama fura da ruwa amma kallo ɗaya yayiwa Furar ya gane da jinin mutum ta damata bada ruwa ba, a harƙitse yajata ɗaki har yana fatali da kwanon furar....✍🏻

TOFA GA KUMA WATA CAKWAKIYAR, KO MI YA RAZANA MALAM OHO

ku kasance tare da ni domin jin ya da zata kaya, ina ganin like ɗinku kuna faranta raina ina godiya masoya Allah yabar tare ya kuma bani ikon faranta rayukanku ta hanyar kawo muku zaffafan labarai masu cike da darasi ilimantarwa harma da faɗakarwa nice taku har kullum ke ƙaunar nishaɗin ku.

MARYAM STAR CE