RU'UYAA (The dreams we never lived)
23. ... Kitten...🖊️
by @autum17
Washegari Lahadi,da sassafe Mama Asabe ta kawo min wani haɗin da ban san ko a ina ta samu ba, Karɓa nayi na shanye koba komai meye ciki?
Yau gaba ɗaya ma'aikata kamar jiya muka haɗu muna aiki kamar ba gobe. wani sashe mai ɗakuna uku da ya tsaru ya gaji da tsaruwa aka buɗe,kusan mu dayawa aka tura wurin gyara shi,bayan ko mutum ɗaya ya isa ya gyara ɗakin ya goge...
A kitchen ma'aikatan sai gudu suke nan da can kamar kaji..su Seraphina da yan uwanta aka kwasa aka tafi wurin gyaran jiki hakan ya cecemu daga matsalolin su...wurin ƙarfe sha biyu wata mata mai jiki ta iso da wasu yan mata uku masu shegen jiji da kai,kowace fuska ta babbake tsabar bleaching...sai girman kai da ɗagawa...ashe ƙanwarsu Alhaji ce Hajiya safara'u da ake kira Hajiya Momma...
Parlor ta zauna tarin ma'aikata suka yi kanta wasu na mata tausa,wasu suna cika gabanta da abun ci da abun sha amma sai ashar take ɗura masu...yan matan nan suma suka fara bada oda nan da can... nikam ɓoyewa nayi daga ganin su dan bana son raini...
Gidan ya ƙara duhu bawai duhu na duhu da haske ba...duhun yanayi dan ni wa'yannan mutanen kallon matsala nake musu...sai data gama ci ta ƙoshi sannan ita da ya'yan ta suka haura sama...oh ashe kowacce cikin su tana da ɗaki a gidan...
Kitchen na wuce ɗaya daga cikin ma'aikatan ya kirani,plate ya nuna min dake ɗauke da kayan ciye ciye na gida Nigeria da ƙasar waje yace in kai 3rd floor wanda shine ɓangaren Alhazozan da matayensu....wannan shine karo na farko da zan tafi wurin...
Ɗaukar plate ɗin nayi nabi stairs fuska ba walwala..kusan stairs talatin da shida na taka kafin in iso makeken parlorn daya haɗu ya gama haɗuwa...komai na wurin golden ne harda kujerun,da labulayen...sai carpet ɗin daya kasance ja...daga tsakiya akwai ƙaramin table..sai TV... dispenser daga can gefe,da flowers da aka jera saman wani shafaffen faranti cike da ƙasa...wurin ya game da ƙamshin turarukan su da kuma air freshener...
samun matan gidan nayi zaune suna hira kowa cikin shigar alfarma harda hajiya Momma dabata daɗe da zuwa ba... gaishe su nayi na ajiye abinda ke hannu na sun amsa gaisuwar ko akasin hakan? Ban sani ba...
Nake jin idonsu na yawo a kaina ba dalili..ɗagowa nayi idona ya shige cikin na Hajiya Momma ta dafe ƙirji harda zabura ta zaro ƙananan idonta
'' Innalillahi wa inna ilaihi raji'una...harda Mayu kuka koma ɗauka a matsayin masu aiki Ruqayyah? Duba min idon yarinyar nan...'' ƙara kafe ni sukayi da kaifafan idonsu nikam na rasa abunyi ko in tsuguna ko in tashi...
'' Ba mayya bace Ni,haka idona suke...''
'' ƙarya kike..idan ke ba mayya bace contact lenses kike sawa kenan?" Kowa ya kafe ni da ido and I felt so helpless...daga cikin matan akwai wani kallo na musamman mai cike da tsana da nake ji har cikin ƙasusuwana da yasa gashin jikina miƙewa...na rasa sanin ko daga ina wannan kallon ke zuwa
Ƙatuwar matar ta tashi ta damƙo hannuna ''buɗe min idon in duba da kyau in gani''...inji Hajiya Momma tana ƙoƙarin tale min ido ta tsoma hannu ciki...na shiga uku ni Abeedah..kuma babu ɗaya daga cikin mutanen wurin dake ƙoƙarin hanata...su wa'yannan mutanen ata yin abun mugunta gaban su babu mai hanawa dan basu ake yimawa ba...
'' wallah...''
'' yimin shiru...'' ture ni ƙasa tayi ta zaune min ƙafafu ta riƙe hannayena..jajayen idonta abun tsoro..naji wasu daga cikin matan sun kwashe da dariya...abinda nayi ma Seraphina na sake maimaitawa
Wannan harda cizonta nayi...da alamu sauran matan sun tsorata dan tashi sukayi daga inda suke zaune suka maƙe wuri guda jikinsu na rawa...
Na dinga sakin ihu ina shille shille,na jefar da hijabina ina ɗage riga kamar zan cire itama na samu na canja muryata zuwa ta abun tsoro convincingly baiwar da ban san ina da ita ba...sai wannan lokacin
Hajiya Momma tasha yagalgala daga gare ni...matar sai ihu take...Farzan ne ya shigo wurin ganina zaune saman ƙatuwar matar
Hajiya Momma tace'' Farzanu ka taimake ni...'' taban dariya sosai...zuwa yayi ya ɗage ni ya fitardani daga parlorn muka shiga elevator tare...naso in cigaba da acting ɗina, fahimtar ya gano ni yasa na dawo daidai,ina rungume hannayena a ƙirji kafin ya tambaya na shiga mashi bayani da fuskar tausayi
'' wai cewa tayi ni mayyace kuma so take ta tsiyayar min da ido...'' na gwalalo ido ina nuna mashi ƙwayar ciki da take dark gray... ɗauke idonshi yayi
'' and you decided to turn into a maniac huh? You are more dangerous than you seem" gumi naji ya ɗan tsatstsafo min..na fahimci abinda ya faɗa amma ban san me yake nufi da..Uhmm..
🍁: Maniac
Ban san meyake nufi da maniac ba...amma sai na waske kada ya fahimci ban sani ba...
'' Next time xan barki kisha duka ne,who knows nan gaba your gray eyes will have silver in them and that's it! You're a witch!"zaro ido nayi jin abinda ya faɗa wai zan koma mayya
'' gashinki ma zai koma gray,at least a cikin littafai haka kamannin witches suke...'' da sauri na shafa kaina da hular ta faɗi,naji kunya ta kamani,na ɗago ido na slow naga ni yake kallo fuska a ɗinke
gyaɗa kaina nayi kamar ƙadangare elevator ta buɗe a second floor..yai tafiyarshi nima na juya ina tafiya jiki a sanyaye..na kawo wurin wani ɗaki zan sha kwana naji an hankaɗa ni ciki an rufe ƙofar daga waje...duk yanda nake bubbuga ƙofar anƙi a buɗe
'' shegiya nan ciki zaki mutu!" Muryar Fauziyya ce ba kuskure... cigaba da buga ƙofar nayi tsoro na kama ni...ɗakin babu ko ɗigon haske kuma babu taga bare iska ya shigo..kenan babu oxygen..idan babu oxygen mutuwa zanyi...
Cigaba da buga ƙofar nayi numfashi ya fara min wahalar ja...ga uban zafi ga tarin ƙura..faɗuwa ƙasa nayi ina cigaba da buga ƙofar...na ɗauka mutuwa zanyi...idona sun fara rufewa naga an buɗe ƙofar wata yarinya da ban taɓa gani a gidan ba duk da buji buji nake ganin ta...ta shigo tana kiran sunana
04:00
Buɗe idona nayi na ganni a sashen mu Mama Asabe tayo kaina tana shafa goshina '' kin tashi?" Gyaɗa kaina nayi na tashi zaune...'' sannu kawo ki akayi wai kin suma...''
'' Fauziyya ta rufe ni a wani ɗaki mai duhu,ba wai na ganta bane amma naji muryarta tana faɗin in mutu...''
Mama Asabe ta kalleni da damuwa...'' dole mu faɗawa Madam..'' na jinjina kai ina tunani ai Fauziyya bata tsoron Madam Aatika sai da nayi sallah ina zaune aka kira Ni wai Madam na ƙasa tana jira...tashi nayi na tafi ƙasa ɗin na samu duk sauran ma'aikatan suma suna nan harda Fauziyya However ba Madam Aatika bace, Madam Amina..
Bayan na gaisheta ta tambaye ni meya faru? Ido na haɗa da Fauziyya take min alamun idan har na kira sunan ta zata kashe ni...ɗauke idona nayi daga kallonta
Badan ina jin tsoronta ba na faɗi abinda ya faru amma ban kira sunan ta ba tunda bani da tabbaci... Madam Amina ta haye mu da faɗa tana ƙara gargaɗin mu akan irin wannan halayen...daga ƙarshe tace gobe kafin in tafi makaranta in haɗu da ita ..na jinjina kaina sannan ta tafi
Zan koma sama Fauziyya ta biyoni '' kin yima kan ki adalci da baki kira sunana ba..''
Kallon ta nayi nace ''.idan kina tunanin tsoron ki ake...well,ke ce mafi yaudarar kai a gidan nan!''
Ɗage kafaɗa tayi baki kyaɓe tace '' kuma ina shawartar kida ki rabu da sir Farzan! Duk inda kika ganshi ki kauce daga wurin kin jini ko?" ta damƙi cinyar hannu na riƙo bana wasa ba..toni ina ruwana dashi?
Cike da haushi na gatsa mata cizo kamar vampire ban sake cewa komai ba na barta da yarfin hannu...
A ƙasan raina nake tunanin ko wace mai mutunci ce a gidan ta taimake ni? oho...
Da daddare bayan na gama duk ayukkan daya dace nayi na sake hawa har 5th floor cikin lambu na shiga na tsaya daga gaban wurin ina kallon sama..duk da kuwa ance kada mu dinga yawo yau ba taurari saboda hadari daya taru...
naji ina nishaɗi dana tuna gobe zan fita daga gidan nan a karo na farko tunda nazo...zama a gidan nan is quite suffocating babu wanda zai san da hakan sai wanda yake a ciki...
Da ƙarfe goma lokacin aikin mu ya ƙare na sauko zan tafi sashen mu...na haɗu da Waleeda tayi min murmushi isa wurinta nayi ta riƙo hannuna muna tafiya tare muna hira
'' da ace mutum zai iya rubuta ƙaddarar shi,da ban kasance a nan ba...'' ta faɗa min
'' wata rana zamu girmi duk wannan ba zamu bautama wasu ba,sai dai a bauta mana!'' farin ciki nagani a fuskar ta sosai bayan nayi wannan maganar tace
'' tunda kin faɗa...zan fara addu'a akan hakan...ada na ɗauka hakan kawai zai faru dani a mafalki duba da yanda rayuwata take lilo...you gave me hope...na gode..''
Jinjina kaina nayi ta rungume ni kafin mukayiwa juna sai da safe muka wuce ɗakunan mu
Dana shiga ɗakin mu har Mama Asabe tayi bacci banda Hansa'u dake danna waya... gado na haye na rufa badaɗewa ba aka tsuge da ruwa
'' ashe ni ake jira in ɗaura kaina a matashi...'' nayi murmushi da wannan tunanin...
Da safe kamar jiya haka Mama Asabe ta sake bani irin wancan abun,naso inƙi sha tace ai yana ciko mace ya gyara ta...naji kamar inyi dariya amma bana so in ɓata mata ƙoƙari yasa na shanye abun...na miƙe na shirya cikin uniforms ɗina da suke a goge amma fa sun tsufa..ban damu ba dai ..
Hula nasa ruwan toka,na shafa kwalli da turare mai daɗin ƙamshi...jakar leda ta na ɗauko ina duba komai da komai akwai a ciki...
Duk da Nasan ba kowa bane zai dawo ranar da aka dawo duk da haka na kasa haƙura da tafiya wannan ranar...kawai ina so in bar gidan nan ne...waya tana ɗauko na kira gida bayan mun gaisa na faɗa ma su Asma'u suzo makaranta...
Tare muka fito da Mama Asabe muka karya da sauran masu aiki a dining da babu abinda suke magana akai sai dawowar biyun nan a yau, cikin hirar tasu naji ana cewa ɗaya daga cikin biyun ɗan Italy ne..ko kaɗan banji ina so in ga suwaye ba...
Kafin a gama breakfast ɗin nasha harara da baƙaƙen maganganu a kaikace amma ɗokin zuwa makaranta ya hanani jin baƙin ciki...sai ma nake mayar musu da maganganu masu kyau maimakon biye masu taɓaci...
'' ke Abeedahtu ashe bakya sign-in..hakan zai iya zama matsala fa...'' Mama Asabe ta nuna min littafin ko sau ɗaya ban taɓa sign in ba ko sign out na manta duka
'' zan kiyaye...'' na faɗa sannan nayi sign in na yau kafin na fito saye da hijabi daban dana makaranta....
Kitchen na tafi dani da wasu ma'aikatan muka shirya abinci a dining...koda yan gidan suka hallaro har mun gama...duk wanda yazo sai mun risina mun gaishe shi..saɓanin koda yaushe da nake jin haushin hakan yau harda murmushi..babu abinda ya dameni kawai ayi a gama in tafi makaranta...
Harda hajiya Momma tazo...muna haɗa ido ta Harare ni da jajayen idonta murmushi nayi na sadda kai...yau hirar su ta ta'allaƙa akan mutane biyun da zasu dawo,yan matan kowa ka kalla zakaga fuskokinsu ɗauke da annuri nake mamakin waye wa'yannan? Kuma wane muƙami suke dashi a gidan da kowa ke maganar su..duk da samarin basa ɗoki kamar sauran....
Yau munci sa'a mu yan aiki cin mutuncin da aka saba yimana ya ragu sosai...
Farzan ne na ƙarshen zama ya gaishe da manyan fuskar shi ba annuri dama kuma ba wani fara'a ne dashi ba..ban taɓa ganin yayi murmushi ko dariya ba....
Nayi nisa cikin tunani naji ance '' ke!" A firgice na kalli Khaleesat dake harara ta '' baki ji ana magana bane ko kin kurmance?"
'' ai tunda tasa wa'yannan koɗaɗɗin kayan take jin kanta ya ƙara girma...aikin banza!" Jameelah ce tayi maganar tana harara ta
'' dalla miƙo min ketch up!" Ɗaukar ketchup ɗin nayi na miƙa mata '' oh ni zan zuba kenan?"
Danne takaicina nayi na buɗe abun na fara zubawa..sai ihu take min..bana son ɓata ranar farkon komawa makaranta yasa naja dogon numfashi bance komai ba
'' Hajiya Momma meya faru da hannun ki haka?" Ayaan ya tambaya yana bin hannun ta da kallo
'' wannan shegiyar yarinyar ce ta kusa illata Ni..'' ta nuna ni da mamaki kowa yake kallona
Gabana ya faɗi idan fa aka Kore Ni?
'' the girl is dangerous...ya kamata a kula da irin masu aikin da ake ɗaukowa!" Alhaji Sulaiman ne ya faɗi hakan...
Itama Seraphina ta faɗi abinda nayi mata..kowa yayi min caaa!
'' ayi haƙuri Madam bada gangan bane hakan bazai sake ba...''
'' matsiyaciya ai haka zaki faɗa...'' ji nayi idona sun fara ƙaiƙayi..na taune leɓena amma na kasa haƙura
'' ka kuwa san abinda ake nufi da hakan?" Na kalli Arman da yayi maganar ido cikin ido...kusan pausing sukayi da abincin dake gaban su
'' tsiya ba shine kasancewar mutum talaka ba,tsiya shine rashin wadatar zuci...rashin sanin darajar ɗan Adam! Dan kawai Allah ya baku kuɗi mu kuma ya ajiye mu a ƙarƙashin ku,ba finmu kuka yiba! Ba kuma dabarar kubace ta sa ya baku!''
'' wannan yarinyar ta cika shegen ji da kai da girman kai! Wai meyasa baza'a kore taba?" Hajiya Momma ta faɗa
Mufeedah tace'' yarinyar da alamu mayyace ta cinye mu ta lashe shine yasa!"
Ranar dai nasha faɗa da ɓacin rai nabar gidan bayan na haɗu da Madam Amina ta tura ni makaranta da wani daga cikin ma'aikatan gidan don a biya kuɗin makarantar mu...da alamu na samu advance payment ...
Bayan mun isa makaranta mutumin ya biya kuɗin aka bani receipt guda uku,nawa, Asma'u da Anaam...nayi farin ciki sosai
Nayi mashi godiya da muka fito filin makarantar kuɗi ya ciro daga aljihun yace idan an tashi in hawo abin hawa in dawo gida sannan ya tafi....
Makarantar na kalla hakukuwa da ciyayi sun girma sunyi tsawo... ganyayyakin bishiyoyi sun bushe sun faɗo...
Murmushi nayi na isa wurin ƙaraurawa na buga ina dariya... mutane tsirara ne a makarantar ajin mu na wuce ba kowa...
Zama nayi bakin taga bada daɗewa ba mutane suka taru....muka zauna muna hirar yaushe gamo kafin assembly prefect ta buga ƙaraurawa muka taru a assembly ground...inata kallon inda zan gasu Asma'u...kuma yan SS 3 ne kawai hutun su ya ƙare...
Muhimman abubuwan daya kamata mu sani suka faɗa mana kafin suka samu kwasar desk daga office ɗin principal zuwa ajujuwan da zamu zana jarabawa ciki...
Wurin ƙarfe goma duk yanayi na ya canja na fidda rai daga zuwan su Asma'u naji an rufe min ido daga baya...kafin in juyo ƙamshinta ya sanar dani wacece...Jay D
Juyowa nayi tareda sakin ihu na rungumeta...itama ta ƙanƙame ni....'' wayyo Allah na Jay D...''
'' Bee...'' ta kira da farin ciki..naji baƙin cikina ya ragu sosai...muka rabu muna kallon juna...naga ta ƙara min kyau...
'' Abeedah kin ga yanda kika ƙara kyau kikayi fresh kuwa?" Dariya nayi sosai '' ji wadda ke magana...''
'' da gaske nake...da muka dawo na tafi gidan baki nan...''
'' ina tsaraba ta?" Na miƙa hannu kamar na bata ajiya
'' banyi tsammanin zaki zoba sai gobe!"
'' Abeedatuwoooo!!!!!'' Anaam tayi tsalle ta haye ni...muka faɗi ƙasa Asma'u ta faɗo kan mu...Jay d ta tsaya daga gefe tana dariya...
'' wash zaki karye ni!" Anaam na dariya tace '' duk cikin murna ne...'' tashi mukayi
Muna kallon juna kafin muka sake rungumewa..naga duk sun canja suma sai faɗi suke na canja...
Ƙarƙashin bishiya muka zauna muna hira nake basu labarin wurin aiki na duk da ban faɗa masu wahalar dake ciki ba...na ɗauki receipt na miƙa masu....
Farin cikin dana gani a fuskar su yasa na ajiye a raina zan jure komai a gidan nan har sai mun kai tsayawa da kan mu...
Wasu daga cikin yan ajin mu suka ƙaraso ana hirar dasu cikin farin ciki da nishaɗi...
'' ina Diyaam?" Na tambaya amma babu wanda yasan wani abu game da ita
Lokacin tashi su Asma'u suka ce in biyo su mu tafi gida amma baxan iya ba saboda Madam Amina ta gargaɗe ni...
Badan mun soba muka rabu bayan Jay d tabani lambar ta...yau gani ina bin hanyar da mutane da yawa ke bi amma bana farin ciki saboda babu su Jay d...
Yau babu rana kun dai san yanda yanayi yake kasancewa idan rana bata fito ba kuma mutum na cikin baƙin ciki...nake ji kamar an ɗaura nauyin duniya a kafaɗa ta...da sauri nayi ƙoƙarin saita yanayi na...ranar ta kasance mai daɗi kuma zamu sake haɗuwa gobe...kada in bari rabuwar mu tasani a baƙin ciki ko?
Da wannan tunanin farin ciki ya dawo min nake tafiya a hankali ina lura da abubuwan da tafiyar mu ta farko ban lura dasu ba
Na ɗauka tafiya ƙasa mai sauƙi ne kuma zan isa gidan da wuri...da sauri na fahimci kuskure ne dan Saida na shafe awa biyu ina tafiya kafin na kawo ...
Na ɗau lokaci ina kallon unguwar abinda ban samu damar yiba a karon farko...wurin nada kyau sosai... murmushi nayi sai kuma na fara tafiya da sauri na isa bakin gate...buɗe wa sukayi na shigo na gaishe da gayen dake wurin...sannan na wuce sashen mu
Ma'aikatan na samu suna magana akan yanda ɗaya daga cikin biyun ya ƙara kyau da komai...a gajiye nake yasa bayan na gaishe su na wuce ɗakin mu...Mama Asabe bata nan..Baye na shiga nayi wanka na sauya kaya zuwa uniforms Brown da suka dace da kalar fatata na fesa turare kaɗan nayi sallah..har xan kwanta na canja shawara...sabon hijabi na ɗauka ash na fita daga ɗakin... kitchen ɗin mu na shiga na zubo abinci waleeda da Aina'u suka zauna gefe na muna hira suke faɗa min sunga ɗaya daga cikin biyu ɗin,amma na biyun yanzu da yamma zai dawo...
Ina sauraren su har na gama muka wuce babban gidan tare...wurin Madam Amina na fara zuwa na gaisheta nayi mata godiya ta samin albarka
Kowa daga cikin mu ya kama aiki...plate aka cika da kayan ciye ciye aka bamu mukai ma yan gidan a Movie room dukan su suna can...
Ɗauka mukayi... muna ƙunƙuni akan hawan stairs... Aina'u take bamu labarin garin su yanda suke hawa bishiya da kuma wasannin da suke da tafiya rafi ɗibar ruwa wata rana wani Mutum ya biyo su suka saki tulukansu suka kwasa da gudu...
Muna dariya nida waleeda har muka iso movie room ɗin,mun ɗauka harda yan mata..mazan kawai muka iske suna kallon fim ɗin iskanci....a tare jikin mu ya ɗau rawa...mukayi tsaye daga bakin ƙofa babu wanda keda niyar matsawa cikin mu
'' anan zaku cigaba da tsayuwa ne?" Abdul Jalal yayi maganar da alamun jin haushi saurin suka bimu da kallon rashin ɗa'a...ƙarasawa mukayi a tsorace muka ajiye abubuwan dake hannun mu...da sauri muka fita daga wurin zuciyoyin mu na dukan tara tara musamman ni da nake jin idon Mukhtar akai na....
Bari na sukayi suka nufi 3rd floor Dan suna da aikin da suke a can suda sauran ma'aikata... kitchen na sake komawa...
Leonardo ya nuna min sabon faranti da aka cika da wani abu da turanci yace '' ana kiran shi da 🦐🦐 shrimps..master yana son su shine yasa na dafa...ki ɗauka ki kai Room no 207...'' yayi min bayani ganin kallon da nake bin abun dashi
''.ka tabbatar bazasu cije ni ba?" Na zaro ido dan gani nake kamar suna da rai...sauran masu girkin suka sa dariya Naeem yace '' baki ga an soya suba? Koke idan aka soya ki zaki iya motsi...''
Harara na jefa mashi nace'' ko zaka gwada ne?" Matso ni ya shiga yi yana wasa wuƙa...da sauri na figi farantin na tsere daga kitchen ina jiyo dariyar su...Nima murmushi nayi... wannan shine karo na farko da mukayi magana mai tsawo...
Stairs na fara hawa ƙafafuna suna tsananin ciwo saboda tafiyar da nayi a ƙasa...ƙwanƙwasa ƙofar nayi ina sauke ajiyar zuciya daga ƙarshe dai na kawo...
'' Come in..'' murya mai zurfi ta amsa daga ciki..tura ƙofar nayi da sallama na wuce parlorn zuwa ɗakin bacci... ɗakin da muka gyara ne ɗazu duk da ba haske saboda labulayen masu nauyi da aka saki ƙamshin turare da air freshener ne ke tashi...ganin wanda keda muryar nayi kwance saman gado ya rufe daga ƙugunshi zuwa ƙasa da bargo faffaɗan bayan shi a buɗe...gabana ya faɗi sai kuma naji haushin sa ya cika ni...
'' yallaɓai ga abincin ka!!"nayi maganar da takaici kamar in kife masa shrimps ɗin a jiki! da kasala ya nuna min table a gaban gadon yace
'' ajiye nan...'' ƙarasawa nayi na ajiye ya sake faɗin
''kwashe labulen''...na matsa zan kwashe labulen ya yunƙura ya tashi zaune,sai nayi pausing
Nabi bayanshi da kallo ƙatone sosai saye yake da baƙin jeans amma ba abinda ya dameni ba kenan..gani nayi ya nufi ƙofa...yawu na haɗiye garƙame ni zaiyi ne?
Zuciyata ta fara abinda ta saba...tsoro yasa na dena motsi...ban san me yayi ma ƙofar ba na dai ga ya taɓa handle sound ɗin rufewa da mukulli ya shiga kunne na... Innalillahi... ya juyo
Rufe idona nayi na kurma ihu kamar zan cire mashi dodon kunne...ganin yana tunkaro ni yasa na fashe da kuka ina roƙon shi akan ya rabu dani tsayawa yayi gabana yace '' what nonsense!" Ji nayi kamar muryar na taɓa jinta amma firgici ya hanani tantancewa... saukar tattausan hannun shi a nawa yasa a rikice na zare hannuna daga fuskata hawaye na sintiri kamar an buɗe pamfo zan fara roƙo...
Zaro ido nayi ganin Khalil tsaye gabana fuskarshi a ɗaure... eventually mamaki ya bayyana a fuskar shi shima....
'' kitten?.."