BIYU A ƊAYA

Chapter 31

by @barista

BIYU A ƊAYA 
   ( Don't judge a book by its cover)


Page 31
Sayyada barrister 
***
YOTA 13 
The five ink legends 



Hannunsa har wannan lokacin yana kan fuskar ta bai sauke ba, yana sake kare mata kallo,  musamman yadda take rufe fuskarta baya iya ganin komanta sai idanunta, tabbas babu tantama ita ce, amma bai taɓa tunanin haka ba, ko ya fahimci wani abu ba, kuma duk yana mu'amala dasu amma bai yi arɓa da abin da zai nuna masa cewa mutum ɗaya ne b...

Bilqees jin sunan da ya kiranta da shi yasa ta sake waro fararen idanunta tana kallon shi, zuciyarta sai bugawa take yi jikinta ma haka yana rawa, a hankali ta yi baya amma sai taji ta haɗe da jikin garu, cikin nutsuwa ta ce

"Don Allah ka buɗe min na tafi, ana jira na"

Ya janye hannayensa ya maida su cikin aljihun wondonsa yana kallonta, kuma bai taɓa shaida muryar ba, sai dai kawai yanayin da banbanci ita Angel tana da nutsuwa Bilqees kuma me sanyi ce, ya sauke numfashi ya matso kusa da ita tare da cewa 

"Bilqees da Angel mutum ɗaya ne"

Ya yi maganar yana me tabbatar mata da hakan ne, take ta haɗa gumi, goshinta ya soma jikewa, da ƙyar ta haɗiye yawun da ya tsaya mata a maƙoshinta , tana kallon shi kamar yadda shima ya zuba mata idanu yana sake fahimtar wasu abubuwan, ya ɗan dafe bango da hannu ɗaya, ya kusanto ta sosai, har tana jin ƙamahin turarensa cikin brain nata, a hankali ta rufe idanu wasu abubuwan suke dawo mata...

"Wasa kike yi min da hankalina? A tunanin ki ba zan gane bane?"

Yana kallon kyakkyawar fuskarta, ganin ta haɗa gumi yasa ya sanya yatsansa yana goge mata shi sama² yana ji ta sauke ajiyar zuciya da ƙarfi....

"Kyakkyawar Aunty"

A hankali ya furta tare da ɗauke yasansa, ta buɗe idanunta tana bin shi da kallo, tana sake fahimtar wasu abubuwa, kenan shi yasa ya rufe ƙofar, a hankali ta ce

"Sunana Bilqees"

Murmushi ya yi, ya dube ta da kyau ya ce

"Tabbas sunanki Bilqees inkiyanki kuma Angel"

Bakinta na rawa ta ce

"Yallaɓai likita"

"Ki kirani da Ya Waahab ko Uncle"

A hankali ta sudda kanta ƙasa, shikenan ya fahimci komai, yau dubunta ya cika, amma ta rasa me za ta ce masa...

"I'm sorry"

Murmushi ya yi ya dawo da baya ya zauna bakin bed tare da cewa

"Assieds-toi"

Sit down ya faɗa mata ta zauna, don kada ta gaji, a hankali ta zauna kan carpet ta sauke numfashi har yanzu kanta na kallon ƙasa, ta yi magana 

"Ouvre la porte"

Open the door ta faɗa cike da tsoro, ka buɗe ƙofa, amma bai buɗe ba, ya ci gaba da karantar yanayinta sannan ya numfasa ya ce

"O'u Vas -tu?"

Where are you going? Ya tambaye ta ina za ta je? Idanu su ka yi raurau kamar ta yi kuka ta ce

"Eh ni ce Bilqees kuma ni ce Angel"

"To me yasa ki ka raba sunan? Ko in ce kika ɓoye min?"

"Je N'ai Pas"

I have no choice, bani da zaɓi ta faɗa. Ya sauke numfashi tare da cewa 

"Kamar yaya baki da zaɓi"

"Bilqees a gidan abinci kasanta Angel a wajen taimakon yara"

"To me yasa ba ki faɗa min cewa mutum ɗaya bane? Kuma kina gani nake zuwa Tumbin Giwa neman ki"

"Rannan na yi ƙoƙarin na sanar da kai amma ka ki ka saurareni"

"Quand?

When? Ya tambaye ta yaushe?

"Last zuwanka Tumbin Giwa, daman da farko zan ce ka janye ƙafafunka zuwa gidan mu da kuma sai na faɗa maka ni ce Bilqees wacce ke aiki a restaurant"

Shiru ya yi yana nazarin maganar ta, kenan shi ne bai fahimce ta ba, ya sauke numfashi tare da cewa 

"Me yasa ba ki son naga fuskarki? Ai na tambaya kuma kin ƙi buɗewa"

"Uhm tsoro nake ji kada ran..

Ta kasa ƙarashewa, a hankali ya taso daga bakin bed ya iso inda take zaune, ya rage tsawonsa tare da cewa 

"Angel"

Ta ɗago suka haɗa ido, duk ta haɗa gumi kamar wacce ta yi sata aka tuse ta, ya sauke numfashi yana kallon idanunta da suka sauya kala saboda tsoro da kuma ƙwall, ya fiddo da farin handky daga cikin aljihun wondonsa ya miƙa mata tare da cewa 

"Ki goge gumin dake fuskar ki"

Ta karɓa hannunta na rawa, ta goge ta ce

"Zan tafi"

"Ina?"

"Restaurant"

"Sai kin amsa min dukkanin tambayoyina"

"Ba zan iya ba"

"Ya zama dole"

Ta sauke numfashi kamar ta yi kuka, ya ce

"Na yarda wancen ranar kina son sanar dani ke ce Bilqees to amma me yasa ki ke rufe fuskar ki a iya wajen yaran da kike taimako?"

"Islamiyya nake tafiya, a cen ƙasa ake ƙaramin karatu, bana so a kalli fuskar ta"

"Saboda me?"

"Saboda neman ilimi"

"Ban yarda ba, kina soro wani ya ganki ne?"

"Eh"

"Waye?"

"Customers na ALAJA"

"ALAJA!'

Ya faɗa yana kallon ta, ta ce

"Eh a lokacin da bana rufe fuska ta, an faɗa mata ina zuwa ɗaukan karatu ta hanani ta ce aiki zan yi, to shine nake rufe fuska kada a ganni"

"Bata san kina saka niqabi ba?"

"Eh bata sani ba"

"Ƴan Tumbin Giwa fah?"

Jin ya ambaci Tumbin Giwa yasa ta kalle shi, zuciyarta na ci gaba da bugawa, ta ce

"Sun sani"

"Ok yaran da kike taimako fah"

"Saboda Allah nake yi shi yasa ban bari sun ga fuskata sosai ba"

"To ni fah?"

Suka tsaya ganin junansu, hannunsa ɗaure kan kirjinsa yana nuna mata kansa, a hankali ta sauke nata idanun, tana sauke numfashi shi ne mutum na farko a duniya da take masa kallon girmamawa da baiwa daraja na musamman, haka kurum take ji shi na dabanne...

"Kyakkyawar Aunty"

Ta sake ɗagowa ta sauke idanunta cikin nasa, ta fahimci Uncle mutum ne me son gaskiya, kai tsaye yake magana babu tsoro, irin mutanen nan ne ko a mutu ko a rayu suna kan gaskiyarsu a hankali ta yi magana 

"Yallaɓai likita, ba zayyu na buɗe maka fuskata a lokacin ba, da niqabi ka ganni, duk lokacin da kazo wajen yaran shi ne a fuska ta, ban san yadda zan yi na faɗa maka ni ce Bilqees ba"

"Amma saboda haka ki ka hanani zuwa gidanku"

"A'a saboda yanayin gidan mu bai dace da kai ba"

Ya sauke numfashi, tabbas yana jin takaici ace wancan ne gidan da Angel ke rayuwa, a hankali ya zauna sosai tare da naɗe ƙafafuwansa yayi zaman cin abinci suna face juna ya ce

"Saboda na ce wa Bilqees zan haɗu da mahaifiyarta shi ne Angel ta dakatar dani zuwa gidansu, kada naga gida ɗaya suke"

Ta sudda kai ƙasa tana wasa da siraran yatsun hannunta, jikinta ya yi sanyi, a hankali ta ce

"Ba da wata manufa nayi haka ba"

"To naji, ya aka yi, duk ranan da zan je Tumbin Giwa sai nazo cin abinci restaurant nake tafiya, kuma nake samun ki a gida?"

Kanta na ƙasa ta ce

"Jimawan da kake yi a waje ban fito ba, muna hanyar dawowa gida ne, da mun dawo kuma sai na samu na fito"

Yadda yake yi mata tambayoyi kamar ɗan sanda da ɓarawo, bata da zaɓi dole ta ba shi amsa...

"Kin ce in naga asalin fuskar ki ba zan sake zuwa wajen ki ba, haka ne?"

Kunya ta rufe ta, kamar ta nutse ƙasa Dr Waahab ya fahimci haka, ya yi murmushi ta ce

"Ba haka nake nufi ba"

"To menene?"

"Za ka yi fushi dani"

"Ba ki so na yi fushi ne?"

"Uncle"

"Angel"

Ta sake sudda kanta ƙasa, sai taji ta a takure, tana jin nawin Uncle sosai tana ganin girman sa...

"Kin iya acting da film kike yi, za ki zama babbar jaruma"

Har wannan lokacin mamaki yake yi, wai Bilqees ita ce Angel, tana da matukar wayo da dabara akwai ta da brain, duk tsawon wannan lokacin bata bari ya fahimci komai ba...

"Yallaɓai likita zan koma bakin aiki nah"

"Anan ma aiki kike yi"

Ta kalle shi ya ɗaga mata kai alamar eh, ta ce

"ALAJA za ta neme ni"

"ALAJA ita ce me Tumbin Giwa kuma ita ce mamallakiyar restaurant"

Wannan karon idanunta suka ciko da ƙwalla ta ɗaga masa kanta alamun eh duk nata ne, ya jinjina kai..

"Kina monitoring nawa a waje, kuma kina yi a nan cikin hotel"

"A'a Yallaɓai"

"Bilqees kuma Angel ya aka yi sunan ya fito biyu, a lokacin da naje gidanku da Angel suka sanki a restaurant kuma da Bilqees"

"Bilqees shi ne asalin sunana, da iyaye na suka sanya mini, Angel kuma ALAJA ce ta saka min tun ina karama"

"Ok kin san yadda aka yi na gano fuskar ki?"

Ta kalle shi ta girgiza masa kanta alamun a'a, ya numfasa ya ce

"Da farko ya jikinki?"

Da mamaki take duban, sai ta shiga ruɗani, ya aka yi yasan bata da lafiya?..

"Da sauƙi, amma...

"Jiya kin yi accident"

Ta waro fararen idanunta kamar yadda take yi masa su cikin niqabi, ya ci gaba da cewa 

"Nazo wajen yaran na tadda kun watse har zan juya sai na hango kina ƙoƙarin sallake titi, garin na ƙarso mu gaisa mota ta buge ki, anan naga fuskarki"

Mamaki ya rufe ta, Uncle yana wajen tayi hasari, a hankali ta ce

"Amma kuma baka hospital"

"Eh amma dani muka je hospital kamin ki tashi na bar wajen"

"Kai ne ka bani kuɗi?"

"A'a"

"To waye?"

Ta faɗa fuskarta ɗauke da damuwa ya ce 

"Uncle ne ya baki"

Karo na farko da tayi murmushi dimple nata ya lotsa sosai, murmushi ya yi mata kyau, ko don bata cika yi bane, ya shagala da kallon abin, don yana matukar burge shi, ta sudda kai ƙasa, a hankali ya ɗauke idanunsa daga kanta ya mik'e zuwa bakin kofa ya buɗe bayan ya sanya key ya kalle tare da cewa 

"Za ki iya tafiya"

Ta mik'e jiki a sanyaye ta iso zata wuce ya ɗan sanya hannu ya tare, ta dakata suna kallon juna, Uncle ya fita tsawo sosai ƴar ƙarama a kasan shi...

"Wanne suna zan kira ki da shi?"

"Duk wanda ka kira ni da shi dai-dai ne"

"Okay"

Ya faɗa ya bata hanya ta fice, da sauri ta bar wajen, tana fita ta samu dakali ta zauna tana sauke numfashi, shikenan Yallaɓai yasan asalin fuskar ta,  amma taso ya fara ji daga bakinta ba wai ya gani da idanunsa ba, haka ta iso restaurant tana tunani..

Kitchen ta shigo jiki ba kwari tana aiki a hankali, kenan jiya da daddare da Uncle yazo cin abinci yasan da ita ce Angel kuma bai nuna mata ba, tana ta zancen zuci tana aiki ALAJA ta shigo tare da cewa 

"Bilqees kin dawo?"

"Eh Maa na dawo"

"Ok yau kin jima"

Jiki a sanyaye ta ce

"Aikin ne da yawa"

"Haka ne, tun da sati guda ba gyara ko ina ce kwanaki"

"Haka ne Maa, me zan kawo miki?"

"Eh rice and stew nake so"

"To Maa yanzu zan kawo"

"Yawwa"

ALAJA ta fice, Bilqees ta haɗa mata abincin cikin kankanin lokaci ta kai mata, ta fito ta ci gaba da ayyukan ta..


********************

Zaune suke a dakali suna wasa kamar kullum, suna jiran kyakkyawar Aunty, yau ta ɗan jima bata zo ba, hankalin su ya tafi kan wasan da suke yi basu ma ji isowarsa ba, sai da ya yi musu magana sannan suka juyo da murna su ka yi masa oyoyo suka rungume shi, ya shafa jansu tare da cewa 

"Ku zauna abokai"

Suka zauna, tare da cewa 

"Barka da safiya Uncle"

Ya yi murmushi tare da cewa 

"Barka dai, waya koya muku gaisuwa?"

"Kyakkyawar Aunty ce"

"Oh kuna sonta sosai"

"Muna sonta, tana da kirki"

Ya yi murmushi sai yaji farin ciki da jin haka, ya ce

"Gaskiya ne tana da kirki"

Haneef ya ce

"To ka aure ta mana"

Da mamaki Dr Waahab ya kalle shi yana mamakin maganar da ya fito daga bakin ɗan yaron nan, ya sauke numfashi ya ce

"Ku yi layi na raba muku biscuits da BOBO"

Da murna su ka yi layi ya raba musu, suka zauna suna sha...

Ta iso wajen ta tadda Uncle yana zaune cikin yaran, suna hira Aicha zauna kan cinyarsa tana shan BOBO, a hankali ta ƙaraso don basu ganta ba hankalin su yana kan Uncle...

"Assalamu alaikum"

Su ka ji muryarta, da sauri suka ɗago suka kalleta, cike da murna su ka yi mata oyoyo, Dr Waahab ya amsa da 

"Wa'alaikissalam, sannu da zuwa kyakkyawar Aunty"

Ta kasa haɗa idanu dashi ta zauna tare da cewa 

"Barka da safiya"

Ya sauke numfashi tare da cewa 

"Barka Uncle"

Ya miƙa mata BOBO ganin bata ganinsa ya ce

"Auntyn yara ga na ki kema"

Ta miƙa hannu ba tare da ta bari sun haɗa idanu ba, ta karɓa tare da cewa 

"Na gode"

Shiru yaran suna shan BOBO Aicha ta gama shan nata ya buɗe mata biscuits ta karɓa tana ci, Dr Waahab ya fahimci ta kasa sakin jiki da shi, a hankali ya zaunar da Aicha ya fuskance ta sosai ya ce

"Angel"

"Na'am Uncle"

"Ki saki jikin ki, kada ki damu, ba zan faɗawa kowa cewa ke Bilqees ba ce"

A hankali ta ɗago suka haɗa ido ta sauke numfashi, ya ɗan numfasa ya ci gaba da cewa

"Sirri ne"

Ta ɗan saki jikinta, ya ce

"Ki gyara niqabinki"

Ta gyara, ya ce

"An san kin zo?"

Ta girgiza kanta alamun a'a, ya sauke numfashi ya ce

"To ki koma"

"To, zan raba musu abu"

"Ok"

Ta raba musu, ya ce su tafi gida, suka tafi bata motsa ba, Dr Waahab ya ce

"Zan koma cikin hotel, amma zan zo cin abincin dare"

"Allah ya kai mu"

"Amin"

"Keh!"

Suka ji murya kamar daga sama, ya iso yana cika yana batsewa, sanye da dogon wando bujeje da riga burgujejiya gaban rigar a buɗe sai farar vest dake ciki, da sarka dake wuyarsa gashin kansa cike yake kuma a tsassaye ya yi cibbiri² da shi, sai sheƙi yake yi, a tsorace Angel ta mik'e ganin yadda ya dire musu ga Uncle yana nan...

"Ki ɓace anan"

"Abraham"

"Ba ki ji me na ce bane? Ki bar nan wajen"

Dr Waahab kallo ɗaya ya yi masa ya ɗauke kansa, jin yana dakawa Angel tsawa yaji ransa ya soma ɓaci...

"Na rantse da Allah in ba ki bar nan ba sai na yi miki abin da ba za ki taɓa manta wa ba"

Ta fahimci Abraham baya cikin hayyacinsa, ta ce

"Abraham menene haka? Baka ganni da mutum bane?"

"Ni kike cewa ban ganki da mutum ba, ina mutumin yake, ai bai kai na yi masa magana ba"

"Abraham a girme ya girme ka, bai dace kayi masa haka ba"

"Allah yasa shi ya yanke wa ƙasa cibiya, don uban mutum"

Girgiza kai kawai Dr Waahab yayi, Angel ta ce

"Shikenan tun da abin ya zama haka, Uncle mu tafi"

"Ina za ku tafi, duk iskancin da kuke yi bai ishe ku ba sai kun...

"Ya isa Abraham kada ka kai ni bango, wannan ai cin mutunci ne, Uncle mutumin kirki ne"

"Dole ki cewa saurayin ki yana da kirki ai"

"Ba soyayya muke yi ba, aiki ne ya kawo shi...

"Soyayya muke yi"

Cewar Dr Waahab ya taso ya tsaya kusa da Angel yana kallon Abraham ya sake cewa 

"Na ce soyayya muke yi, what are you going to do?"....


__________________________

Sayyada ƙafa me na ci ban baka ba, a guje na ruga na koma Alaja restaurant don wannan faɗan na manya ne😂



Ayi hakuri da typing errors, littafi dai yanzu aka fara, sai dai labarin Shari'a saɓanin hankali ne. Ku dai ku ci gaba da bibiyar littafin BIYU A ƊAYA thanks fan's much love you 😘




Comment and share fisabilillah