FARAR TUMFAFIYA

Page 1

by @ummuaffan

‎...FARAR TUMFAFIYA
‎©FATIMA SUNUSI RABIU
‎        UMMU AAFFAN



_1/10/2026_
‎
‎
‎Godiya ta tabbata ga sarki Allah, dubun tsira da aminci su ƙara tabbata ga fiyayyen halittu Annabi Muhammad sallallahu alaihi wassalam.
‎‎
‎
‎_*Shimfiɗa.*_
‎Shin da gaske ne idan duniya ta tsane ka, ko barkono ka kasa sai a ce ba shi da yaji? Abu mafi wahala a rayuwa shi ne lokacin da maƙiyi ya ɓoye  cikin rigar masoyi, mutum kan yarda da wani saboda kalamansa masu daɗi da nuna ƙauna, ba tare da sanin cewa a bayan waɗannan kalaman akwai shirye-shiryen da za su iya rusa abin da ya kwashe shekaru yana ginawa ba, sau da yawa ba ƙarfin da maƙiyi ya yi bane yake karya mutum ba, sai amincewar da ya yi wa wanda bai cancanci hakan ba.
‎   Haka kuma idan mutum ya bar damuwa ta mamaye zuciyarsa da tunaninsa, matsalolinsa sukan zamo tamkar sun fi ƙarfinsa, yakan ji kamar babu mafita, babu sauƙi, kuma babu ranar da zai sake samun kwanciyar hankali, amma a mafi yawan lokuta, ba girman matsalar ne yake hana mutum ci gaba ba, sai yadda yake kallonta da kuma yadda ya ɗora ta a zuciyarsa.
‎Girman jarabawa ba a aunawa da abin da ya faru kawai, ana aunawa ne da yadda zuciya da tunanin mutum suka karɓe ta, zuciyar da ke cike da tawakkali haƙuri da kyakkyawan zato ga Allah, tana iya ɗaukar abin da wasu suke ganin ba zai yiwu a iya jurewa ba, amma zuciyar da ta rasa wannan yakinin ko ƙaramar matsala na iya zama wacce ba ta da mafita, saboda haka kada ka bar damuwa ta fi ƙarfin imaninka ka bai wa Allah girma a zuciyarka fiye da girman matsalolinka, don duk wata jarabawa tana da iyaka amma rahamar Allah ba ta da iyaka.
‎   Gamu cikin wata sabuwar tafiyar FARAR TUMFAFIYA da fatan zaku biyo alƙalamin Ummu Affan domin jin da me yake tafe a gare ku, da gaske ne nan gani nan bari farar Tumfafiya dashe ne na Lillahi.
‎
‎
‎_Bismillahir Rahmanir Rahim._
‎
‎
‎Page *1*
‎
‎
‎*Nakasari behind school of nursing Sokoto.*
‎
‎
‎Barirah.
‎Ta ƙara ɗaga ƙafa ganin yadda hadarin ke ƙara haɗuwa, ga wata iska da ke fesar da ƙasa da yayyami tana sama da hijabin da ke jikinta tamkar zai yaye daga jikin nata. Yadda iskar ke tashi ne ga ƙasar da ke shiga ido ya sakata fara rufe idon tana buɗewa saboda kar ƙasar ta shigar mata, ba tare da ta lura ba taci karo da wani ƙaton dutse da ya sakata tuntsirawa babu shiri nan take kuwa ta faɗi ƙasa tum, ƙara ta saki sakamakon wani zazzafan zafi na ya ratsa ɗan yatsan ƙafarta saboda tuntuɓen da taci da dutsen, ba tare da ta ankara ba ta saki ledar da ke hannunta, lokaci guda kuma ta kama ɗan yatsan ƙafar tata tana ƙara mai ɗan sauti, don ji take tamkar ɗan yatsan nata ya karye ko kuma tayi gocewar ƙashi don har da jini sai da ya fita, sai taji kamar zai fita daga jikin ƙafar tata tsabar azaba.
‎
‎"Wayyo Allah!"
‎
‎Ta furta tana ƙoƙarin miƙewa tunowa da tayi ta saki ledar hannunta da Yayansu Usman ya aiketa sayen awara, ga shi gabaɗaya ta zube kuma ƙasar da ke tashi duk ta buɗe awarar, nan take taji ciwon da take ji a ɗan yatsan nata ya kau na wucin gadi, sai wani tashin hankalin da ya ziyarceta lokaci guda.
‎
‎"Na shiga uku!"
‎
‎Ta kuma furtawa a karo na biyu tana nufar inda ledar ke yashe, hawaye har ya fara bin kuncinta tunowa da gargaɗin da Yayanta Usman ya yi mata kafin da fita.
‎
‎"Kiyi sauri ki amso mini yunwa nake ji kafin Andi ta gama girkin can, sauran kuma kije ki zauna ko ki zubar tunda ba a aikenki ki dawo lafiya, kin ji na rantse muddin ki ka zubar mini sai kin ɗanɗana kuɗarki."
‎
‎Tuno hakan ya sa tana kwashe awarar da duk ta gama buɗewa da ƙasa tana hawayen tausayin kan ta, ga shi iskar da ake yi ta sassauta sai yayyafi da ya fara sauka a hankali.
‎   Da sassarfa kuwa ta shiga cikin gidan nasu tana jan ƙafa da alamu ba ƙaramin zafi take ji a ƙafar ba duba da yadda take ɗingishi yanayinta babu daɗi ko kaɗan.
‎
‎"Ke Barirah, kin ganni nan ɗakin Iyah zo ki ba ni awarata."
‎
‎Muryarsa taji daga ɗakin Iyah yana ba ta umarni kamar daga sama, ta ɗan ƙara ɗaga ƙafa kuwa tana janta ta shige sakamakon ruwan da ya sakko da ƙarfi kamar da bakin kwarya. Tana ƙarasawa gabansa yanaci gaba da faɗin.
‎
‎"Yadda na kwaso yunwar nan ji nake tamkar zan haɗiyi babu, ga shi yadda ruwan nan ya sakko nasan Andi ta kai isha'i ba ta gama abincin nan ba, gara naci kuɗina nasan kuɗina naci atoh."
‎
‎Hankalin Barirah ya kuma tashi jin furucin na Yaya Usman, ta sani duk cikinsu shi ne ma ke ɗan raga mata har ya iya aikenta duk kuwa da yasan irin asarar da aiken nata ke jawo masa,, amma yakan daure ya yi da saka yaƙinin babu abin da zai faru sai alkhairi, duk da idan an samu akasin ma na jaki yake nakaɗa mata, amma kuma gobe ba zai hana ya kuma aiken nata ba, acewarsa idan taji wuya zata bari iskanci ne ke sa ta aikata duk abin da tayi niyya.
‎   Jiki a sanyaye ta miƙa masa ledar da ke hannunta, idanuwanta da suka yi raurau da ruwan hawaye suna kallon fuskarsa.  Da so samu ne tana miƙa masa ta gudu daga wurin, duk da ta sani ko ina zata ɓuya zai iya nemota a cikin gidan, amma a wannan yanayin da take ciki ji take ina ma ta gudu daga ɗakin Iyah, ba tare da ya buɗe saƙon ba? Sai dai babu dama sakamakon ruwan da ke ƙara kwararara sosai tamkar an buɗe furfin fanfo. Tana miƙa masa ta rakuɓe gefe guda har lokacin idanuwanta a kanshi tana jin tsoron irin hukuncin da zai ɗauka a kanta. Iyah kuwa duk tana jin su domin tana zaune a ɗaya daga cikin kujerun da ke parlourn amma ko kanzir ba ta tanka ba, sai bin su da namujiya da take yi tana murmushi ƙasa-ƙasa.
‎Shi kuwa yana amsa ya ajiye a ƙasa tare da sakkowa daga saman kujera ya zauna saman carpet ya jawo robar zoɓon da ya ɗauko ɗakin Andi na sayarwa da take ya fara kiciniyar buɗe ledar. Iyah dai tun da taga yanayin da Barirah take ciki ta girgiza kai a ranta tana aiyana 'Ai fa an kuma.' Amma ba ta furta komi ba gudun kar Usman da ya ƙosa yaci awarar ta katse masa hanzari.
   ‎Sai da ya kurɓi zoɓon sannan ya buɗe ledar, sai dai tunda ya ɗauka yaji ƙasa duk jikin awarar tana taɓa ma hannunsa, ya sake ta da ƙarfi kuwa yana kallon Barirah wacce ta ƙanƙame jikinta wuri guda tana hawaye.
‎
‎"Wallahi faɗuwa nayi, ɗan yatsa na ma ya karye."
‎
‎Tayi saurin maganantuwa ganin irin kallon da yake aiko mata da shi, yadda ya taso kanta kuwa kamar wani mayunwacin zaki ya jawota da ƙarfi ya wullata gefe, ai kuwa kanta ya bugu da garo, ta saka 'yar ƙara tana girgiza kai.
‎
‎"Don Allah kayi haƙuri yaya Usman, wallahi ban yi da gan-gan ba!"
‎
‎Ta kuma faɗa muryarta da alamun kuka, shi kuwa cikin ɓacin rai ya fara magana.
‎
‎"Haka dai ki ka so Barirah, yanzu babu wandaa ya isa ya aike ki a wanye lafiya? Kin san irin yunwar da nake ji kuwa? To ko ki biyani kuɗina ko na bugi kuɗina, kina ganin ruwa ma ake yi babu damar kuma fita yanzu, zo ki biyani kuɗina kafin na haɗa miki jini da majina!"
   
‎Da ƙarfi yake maganar saboda ruwan da ke sauka kar ya faɗa ma ba taji abin da ya ce ba. Iyah kuwa girgiza kai ta kuma a karo na barkatai kafin ta ce,
‎
‎"Ai daman amfanin zunubi romo, tunda dai kai ka sani duk abin da ya shiga hannun Barirah sai ya lalace ko wani mummunan ƙaddarar ta hau kan sa, na sha faɗa maka yadda kowa ya haƙura da aikenta kai ma ka zare hannunka akan lamarinta amma kaƙi, ai ga irinta nan kar ka kuma dukan yarinyar nan ka ji na faɗa maka."
‎
‎Robar zoɓonsa ya ɗauka yana jan tsaki da yi mata wani kallon zamu haɗu da ke ne, ya fice daga ɗakin, ta gefe-gefen barandar da ke gidan yabi don kar ruwan da ake yi ya taɓa shi ya nufi ɗakin Andi.
   ‎Bayan fitarsa Iyah ta dawo da dubanta ga Barirah wacce ke kuka a hankali, ba abin da Yaya Usman ya mata ba ne ya sakata kuka, a'a don idan da sabo ta riga ta saba nashi kaɗanne ma akan na kowa saboda shi a hakan yafi jin tausayinta akan sauran 'yan'uwan nasu kar maace yaya Aliyu. Yadda ɗan yatsanta ke raɗaɗi yafi komi ɗaga hankalinta, don yanzu wani zugi yake mata yana ratsa duka sassan jikinta. Duba na tsanake Iyah ke bin ta da shi kafin ta furta.
‎
‎"Ke lafiyarki ƙalau kuwa?"
‎
‎Sai ta ɓare baki tana nuna ɗan yatsanta.
‎
‎"Iyah yatsana ke mini zafi ban sani ba ko karyewa nayi ko ya goce ne, amma yanaa mini ciwo sosai."
‎
‎"Zo nan na gani!"
‎
‎Ta ya fito ta da hannu, ta taso da ƙyar tana jan ƙafa, ta zauna gaban Iyah wacce ta kamo ƙafar ta ɗaura akan jikinta, ta haska tocilan wayanta a ƙafar, nan kuwa taga ɗan yatsan har ya fara kumbura, kasancewar ta iya jan ƙafa ya sa ta gane yatsan ya goce ne, ajiye ƙafar tayi ta shiga ɗaki ta ɗauko man zafi sannan ta dawo ta kuma ɗaura ƙafar jikinta ta fara ja mata, nan Barirah ta fara kuka sosai saboda azabar da ke ratsa ta, da haka har ta gyara mata ta shafa mata man zafin tana faɗin, bari ruwan nan ya yi sauƙi a samo ruwan zafi a gasa wurin.
‎Gyaɗa mata kai kawai take kamar kadangaruwa tana jan numfashin wahala, kamar yadda ta faɗa bayan ruwan ya ɗauke taje kitchen inda Andi ke sanwa ta samo ruwan zafi tazo ta gasa mata yatsan Barirah kam tana ta wash-wash.
‎   ‎Misalin ƙarfe takwas da rabi na dare suna madaidaicin parlourn gidan domin cin abincin dare, Kawu Balarabe ya fara faɗa akan yadda Barirah na ɗaukar nata abincin, farantin ya faɗi ƙasa, nan take abincin da ke ciki ya tarwatse.
‎
‎"Anya kan ki ɗaya Barirah? Abincin ne ki ka saki haka saboda baki san zafin nemansa ba?"
‎
‎"Hmmm! Ai gara ta nuna maka mummunan halin nata ka kwana biyu ai ba ka gani ba, shi ya sa bana saka mata abinci a farantin tankaran ko wanda zai iya fashewa, don mugun abin ta duk zai iya shafarsu, ka ga dai na roba ne, shi ma bai sati ba ta ga bayansa ba!"
‎
‎Cewar Andi cikin tsananin tsanar Barirah da ganin irin wulaƙancin da take aikatawa don acewarta kamar Barirah mai shekaru goma sha shidda a duniya ai ya kamata tayi hankali ta kuma natsu, amma komi aka ba ta sai ta lalata shi ko ta salwantar, ita ba ta amfana ba kuma ba za ta bar wani ya mora ba.
‎
‎"To kuwa kin bar ƙara cin wani abinci tun da ki ka zubar da naki, Rakiya kar ki sake ki zuba mata wani ta kwashi na ƙasan taci."
‎
‎Kawu Balarabe ya faɗa yana kallon Andi, wacce ta gyaɗa kai cike da jin daɗin furucin Kawun. Yaya Usman da Iyah ne suke dubanta ganin yadda jiki a sanyaye ta duƙa ƙasa tana kwasar na ƙasan inda bai ɓaci ba tana zubawa a farantin, a wurin ta zauna ba tare da ta tashi ba taci wanda ta samu kafin ta miƙe ta nufi wajen ruwa, Yaya Aliyu ya bita da harara yayin da Saudatu da Faruk suka bita da dariya Faruk har da gwalo.
‎
‎
‎*Ƙofar Kaɗe Sokoto.*
‎
‎Sadauki.
‎Ya fesa turaren da ke hannunsa ta ko ina a jikinsa yana ƙara ɗaga hannu sama kafin ya ajiye ya kalli ɗan madaidaicin madubin da ya buga a jikin bangon ɗakinsa yana sakin murmushi.
‎
‎"Kai ma sha Allah, idan kyau ne fa Allah ya ba mu na cilawa a gari, dube ni fa sai ka ɗauka wani shege ne ko ɗan wani ƙusan a faɗin Sokoto."
‎
‎Ya faɗa cikin hausarsu ta Sokoto yana shafa kewayayyen sajen da ya ƙara ƙawata kyakkyawar fuskarsa.
‎
‎"Sadauki! Saudauki!!"
‎
‎Muryar Inna yaji daga bakin ƙofar tana ƙwala masa kira tamkar wani ɗan ƙaramin yaro.
‎
‎"Sadauki, shin ko ka fita ne nake da buɗe bakina?"
‎
‎Ta kuma faɗa tana wangale ɗan matsakaicin labulen ƙofar daidai ƙarasowarsa wurin.
‎
‎"Ina ciki Inna, yanzu dai nake shirin fitar."
‎
‎"Oh ko ince, ɗumamen tuwo ne na kawo maka don kar ka fita da yunwa naga jiya da dare ma da ka shugo ba ka ɗaukin kwanonka kaci ba."
‎
   ‎Ya ɗan yamutsa fuska yana kawar da kai gefe.
‎
‎"A'a Inna, bar tuwon nan ki ƙarawa su Maryam, shi ya sa nake ta so na samu na bar ƙasar nan ko ma huta daga ni har ku, 5m ce fa za ta kai ni China biza da komi na zamana a can, Allah idan naje China mun huta ina mu ina cin wani tuwo Inna?"
‎
‎"Ka dai bi a sannu Sadaukina, na sanka da zafin nama da kuma mayar da hankali a dukkan abin da ka saka a gaba, don Allah ka bar tafiya China ɗinnan ka zauna a garin nan ka gina kanka ka kama sana'a zai fi maka, yanzu da kaje China da miliyan biyar da ka ke magana ba gara ka samu ka kama kasuwanci anan da su ba? Ina ma zaka same su dai a wannan yanayin idan ba ɗaurawa kai ba, don Allah Sadauki ka daina hangen samanka ka dubi ƙasanka ko zaka dawo daidai."
‎
‎Inna ta faɗa tana miƙa masa kwanon tuwon, ya kuwa ƙara ja baya da sauri kamar wanda ake biƙawa wani mugun abu.
‎
‎"Don Allah Inna na ce fa ni na ƙoshi, ba zaki gane rayuwar da nake hango mana ba sai idan naje kin fara jin saukar kuɗaɗe a asusun da zan buɗewa Maryam kafin na tafi, nifa ba na buƙatar komi da ta wuce addu'arki, yanzu ma gidansu abokina zan tafi wanda zai mini hanyar fita China ɗin."

‎Ta bishi da kallo lokacin da yake sakawa ƙofar ɗakin nasa ɗan makulli, yana rufewa kuwa ya doshi ciki inda mashin ɗinsa yake yaje ya hau, har ya fito tana tsaye a zauren ƙofar ɗakinsa.
‎
‎"Sai na dawo Inna!"
‎
‎Ya faɗa tare da ficewa daga gidan, tabi shi da ido har ya fice, kafin ta sauke numfashi ta koma ciki.
‎Yana fita a hankali yake tafiya cikin unguwar saboda yawan kwatoci chaɓali da ya damarmare unguwar musamman yadda aka sha ruwan sama jiya, duk sai layin ya ɓaci ga sawun ƙafafun mutane da bubura nan don mota kam ba ta iya bi ta wajen, da ƙyar ma ya samu ya wuce yadda yara suka cika ko ina wasu na wasan kwallo wasu na tafiya makaranta wasu aikensu aka yi, manya ma maza da mata kowa na sha'anin gabansa, masu shaguna masu sayar da abubuwa gefen hanya su gyaɗa mangoro duk sun ja layi suna harkokinsu.
   ‎Umar da iyayensa ke kira Sadauki a makaranta kuma aka fi saninsa da DK wai Sadauki kenan sai aka cire S ɗin farko aka bar DK ɗin kuma sosai yake son sunan. Shi ne babban ɗa a wurin iyayensu malam Sani da suke kira Baba da mahaifiyarsu Inna Zainu, Zainabu ne asalin sunanta amma da Zainu dangi da 'yan'uwa ke kiranta yayin da yaranta ke kiranta da Inna, dukansu 'yan nan asalin garin na Sokkwato ne gaba da bayansu, malam Sani Allah ya mashi rasuwa shekaru goma baya, tun Sadauki na da shekaru ashirin a duniya. Ƙannansa biyu duka mata Maryam mai shekaru goma sha takwas sai Ummul Salama mai shekaru goma sha huɗu, shi kuma yanzu yana da talatin, mahaifinsu tun yana raye bai da kuɗi sai kasuwanci da yake a ciki ne yake ciyar da su, bayan rasuwarsa kuwa Sadauki karatu yaci gaba dayi cike da yakinin wata rana zai zama wani babban mutum ma'aikaci da zai taimaki mahaifiyarsu da ƙannansa mata.
‎Gidan da suke ciki nasu ne, sai dai duk ya zagwanye ya lalace kuɗin da za a gyara shi ma babu, hakan ya sa kullum cikin tunani suke musamman ɗakin su Maryam da ya zube sai a ɗakin Inna yanzu suke kwana, cike da addu'ar Allah ya sa su ga wucewar damuna lafiya ba tare da wani abu ya kuma samun wani ɗakin ba, don akwai na mahaifinsu, shima tun shekaru uku baya katangar ta zube a haka ɗakin yake har yanzu.
   ‎Da ƙyar kuwa da jiɓin  goshi Sadauki ya kammala karatunsa tare da taimakon amininsa wato abokinsa Mansoor da ke taimakonsa a lukuta da yawa. Umar na da wani abu tun yana ƙarami idan ya ce zai yi abu to fa duk hanyar da ta dace wala daidai ko akasinta zai fi domin ya tabbatar da wannan abin, shi ya sa ma tun yana yaro Baba ya fara kiransa da Sadauki kamar wasa kuwa sunan yabi shi da yawa ma wasu ba su san asalin sunansa  Umar Sani ba ne sai dai Sadauki.
‎Burin Sadauki ya fita ƙasar China a yanzu, musamman yadda yaji social media ta ɗauka cewa da 5m za ka iya zuwa, kuma ya tabbatar da cewa ba ƙaramin kuɗi ake yi ba a ƙasar musamman shi da yake ganin yana da takardun digiri ɗinsa a hannu, to fa acewar wasu daga cikin abokanansa da anje can ake samun aiki, hakan ya sa ya ɗaura ɗamarar zuwa China ko ta wanne hali domin burinsa a dare ɗaya na ganin ya zama wani hamshaƙin da zai ginawa mahaifiyarsa wani ƙaton gida ya koma rayuwa mai kyau kamar yadda kullum yake hasashe.
   ‎A kullum rayuwar mutanen da ke samansa yake kallo yana da son kuɗi da son ya yi arziƙi na ke ce raini, kullum a can ƙololuwa yake hangen kansa, wannan dalilin ne ya sa ko sana'a ya kasa farawa, gani yake tunda yana da ilmi aiki na nan zuwa, musamman ma yanzu da ya sakawa ransa zuwa ƙasar waje, hatta mashin ɗin da yake hawa abokinsa Mansoor ne ya saya masa, kasancewar shi iyayensa masu kuɗi ne sosai, kuma shi ɗaya tilo Allah ya ba su shi ya sa suna ƙaunarsa sosai tare da yi masa duk wani abu da yake so, yana ɗaya daga dalilin da yasa Sadauki ya ƙara shigewa Mansoor, don a ganinsa shi ne daidai da shi ba yaran unguwarsu ba.
‎Idan ya ɗauki wanka kuwa da gayu yana ƙamshi mai ratsa zuciya sai ka rantse ɗan gwamna ne, ko wani babban mutum ɗin, kuma Allah ya ma shi kyawun fuska da ta jiki daidai gwargwado, fari ne tas kuma yana da tsayi daidai misali haka duk abin da zai samu daga amininsa Mansoor a sayen ƙananun kaya da turaruka kuɗin ke ƙarewa, sai kuma taliya ko makroni da yake sayawa su Inna katan ɗaiɗai idan kuɗin suna da yawa har katan biyu ma yana saya musu, da yake suma suna sana'a a gida, da farko Maryam ke ɗaukar talla Sadauki ya yi ruwa da tsaki ya ɓata ransa akan baya son ƙannansa na zuwa talla karatu zasu yi, ga shi dai ya kasa saka su bokon tun bayan Primary ba su ƙara zuwa makarantar boko ba sai islamiyya, amma tallah kam ya ce ba zasu yi ba, sai Inna take sana'ar cikin gida saboda dole fa sai an samu abin cefane, duk da 'yan'uwa ba su manta da su ba, sukan taimako da su masara da dawa wani lokacin har da shinkafa musamman idan kaka ce tayi, to fa a haka suke lallaɓa rayuwar.
   ‎Inna tana matuƙar ƙaunar Sadauki sosai, ko dawowa gida idan bai yi ba ta dunga saka Maryam tana ma shi flashin don taji abin da ya tsayar daa shi, haka kome ta dafa kwanansa yana nan sai dai ba kullum yake cin abincin gidan ba musamman idan tayi tuwo dambu su ɗan wake duk ba cimarsa ba ce acewarsa....
‎
‎*To Mutanena, mutanen Iyar Affan kunji wannan karon kuma da labarin da nazo muku, ina fatan zaku biyoni sannu a hankali har mu kai inda nake son muje a labarin nan, ina muku fatan alkhairi.*
‎
‎#FararTumfafiya
‎#UmmuAffan
‎#Barirah
‎#Murjanatu
#Sadiya
‎#UmarDK
‎#NazifiHunƙuyi
‎#2026Novel
‎***
‎

Ina masu buƙatar kyawawan atamfofi da  lace, mayafai, shoes and bag. Tare da kyawawan kayan kitchen na 'yan gayu masu kwaliti, zaku iya tuntuɓar ASHNURR COLLECTION wacce ke Kano kwari market domin ƙarin bayani ku tuntuɓeta a lambar waya kamar haka *** Tana aika kayanta ko ina a cikin aminci.



Shin kuna da labarin AK ASHKAD COLLECTION to ku matso kusa ku ji, ita ce wacce take kawo muku kyawawan  abayas na gani a faɗa na shiga ko wanne guri kai tsaye, haka tana kawo muku  kitchenwares masu kyau da aminci cikin farashi mai rahusa zaku iya tuntuɓarta a 070444564938 ko *** shafinta na Instagram ashkad_collection adireshinta Daura, Katsina State tana aika kayanta ko ina cikin aminci.

Kuna da labarin UmmuAffan GHT Supplement, tana sayar da Supplement na kamfanin ght masu kyau da inganci tana garin Kaduna tana aika kayanta duk inda kuke a faɗin ƙasar nan dama wajen ƙasar nan, kai tsaye kuyi mata magana ta lambar waya kamar haka *** sayen na gari mai da kuɗi gida, sai kunzo.