FreeArewaPen original
FARAR TUMFAFIYA
- 1views
- 1chapters
- 0audios
- words
- 0likes
Share:
The story
Synopsis
No synopsis yet.
Sample · Page 1
...FARAR TUMFAFIYA©FATIMA SUNUSI RABIU UMMU AAFFAN_1/10/2026_Godiya ta tabbata ga sarki Allah, dubun tsira da aminci su ƙara tabbata ga fiyayyen halittu Annabi Muhammad sallallahu alaihi wassalam._*Shimfiɗa.*_Shin da gaske ne idan duniya ta tsane ka, ko barkono ka kasa sai a ce ba shi da yaji? Abu mafi wahala a rayuwa shi ne lokacin da maƙiyi ya ɓoye cikin rigar masoyi, mutum kan yarda da wani saboda kalamansa masu daɗi da nuna ƙauna, ba tare da sanin cewa a bayan waɗannan kalaman akwai shirye-shiryen da za su iya rusa abin da ya kwashe shekaru yana ginawa ba, sau da yawa ba ƙarfin da maƙiyi ya yi bane yake karya mutum ba, sai amincewar da ya yi wa wanda bai cancanci hakan ba. Haka kuma idan mutum ya bar damuwa ta mamaye zuciyarsa da tunaninsa, matsalolinsa sukan zamo tamkar sun fi ƙarfinsa, yakan ji kamar babu mafita, babu sauƙi, kuma babu ranar da zai sake samun kwanciyar hankali, amma a mafi yawan lokuta, ba girman matsalar ne yake hana mutum ci gaba ba, sai yadda yake kallonta da kuma yadda ya ɗora ta a zuciyarsa.Girman jarabawa ba a aunawa da abin da ya faru kawai, ana aunawa ne da yadda zuciya da tunanin mutum suka karɓe ta, zuciyar da ke cike da tawakkali haƙuri da kyakkyawan zato ga Allah, tana iya ɗaukar abin da wasu suke ganin ba zai yiwu a iya jurewa ba, amma zuciyar da ta rasa wannan yakinin ko ƙaramar matsala na iya zama wacce ba ta da mafita, saboda haka kada ka bar damuwa ta fi ƙarfin imaninka ka bai wa Allah girma a zuciyarka fiye da girman matsalolinka, don duk wata jarabawa tana da iyaka amma rahamar Allah ba ta da iyaka. Gamu cikin wata sabuwar tafiyar FARAR TUMFAFIYA da fatan zaku biyo alƙalamin Ummu Affan domin jin da me yake tafe a gare ku, da gaske ne nan gani nan bari farar Tumfafiya dashe ne na Lillahi._Bismillahir Rahmanir Rahim._Page *1**Nakasari behind school of nursing Sokoto.*Barirah.Ta ƙara ɗaga ƙafa ganin yadda hadarin ke ƙara haɗuwa, ga wata iska da ke fesar da ƙasa da yayyami tana sama da hijabin da ke jikinta tamkar zai yaye daga jikin nata. Yadda iskar ke tashi ne ga ƙasar da ke shiga ido ya sakata fara rufe idon tana buɗewa saboda kar ƙasar ta shigar mata, ba tare da ta lura ba taci karo da wani ƙaton dutse da ya sakata tuntsirawa babu shiri nan take kuwa ta faɗi ƙasa tum, ƙara ta saki sakamakon wani zazzafan zafi na ya ratsa ɗan yatsan ƙafarta saboda tuntuɓen da taci da dutsen, ba tare da ta ankara ba ta saki ledar da ke hannunta, lokaci guda kuma ta kama ɗan yatsan ƙafar tata tana ƙara mai ɗan sauti, don ji take tamkar ɗan yatsan nata ya karye ko kuma tayi gocewar ƙashi don har da jini sai da ya fita, sai taji kamar zai fita daga jikin ƙafar tata tsabar azaba."Wayyo Allah!"Ta furta tana ƙoƙarin miƙewa tunowa da tayi ta saki l...
Contents
Table of contents
Preview every chapter, see what is free, and continue reading when you join ArewaPen.