11
by @mamuhgee
Aasiyah
Mamuhgee
11
Tsallaketa sukai batareda jin tausayinta ko imaniba ko kadan saima kan Baban da sukai wanda yake neman rasa ransa sbd azabar dayake ji take yafara kokarin magana amma sam babu arzikin yinta dan haka da gaggawa suka daukesa suna fitowa gidan dan yi asibiti jamilu ne ya samu daman tsayawa yana neman jamaa da gaggawa cikin tsananin tashin hankali da son duniya tasan meya faru yafara fadan cewa sun dawo sun tararda Baba Aisha ta zubawa babansu man gyada bayan masa duka daga karshe haqqi ya kamata a take man ya juye mata ta kone kurmus baban kuma anyi asibiti dashi.
Mutane na jin hakan hankali ya tashi aka fara shiga dubawa da tabbatarwa tareda fara isar da zancen koina da alhini tareda tsananin mamaki da tausayawa.
Acan asibiti kuwa ana karban Baba da gaggawa dan fara dubasa biyan komai khamis yayi da kudin Baba Aisha da suka debo barwa bulama komai ya koma gida sbd jamian tsaro da suka isa gidan.
Dan qaramin bincike akai da abubuwan da suka kamata aka dauki gawar aka tafi da ita tareda yiwa su khamis din tambayoyin da duka bakinsu yazo daya shine suna shigowa gidan abinda suka tarar kenan ta zubawa mijinta mai me tsananin zafi karshe ya xube mata ta kone.
Maqota aka tambaya wanda wasu daga ciki tabbas sunji fadan nasu kuma sunji ihun Baba Ashiru lokacinda ta zuba masa amma basu shigoba gaskia suka tabbatarda daga nan meya faru sbd ita basu ji ihunta ba.
Sun jima tareda jami'an tsaro hankalinsu a kwance babu abu daya dazai nuna ma suna gidan abin ya faru sbd kowannensu baya cikin kowace tsoro ko shakka bare nuna komai a natse suke har dare tukuna aka sallamesu suka koma asibiti.
Dukansu ukun a asibitin suka kwana tareda Babansu sai washe gari da safe sukaje akai janazah din Baba Aisha wadda sune sukai komai a matsayinsu na 'yayan mijinta dayake kwance kuma batada wasu yayan sai su.
Daga gurin janazah zaman gaisuwa aka dawo anayi da dukansu banda jamilu da aka baro asibiti gurin Baba,
Da yamma baban ya dan dawo hayyacinsa jamian tsaro suka taho asibitin suka tattauna dashi sukaji komai daga bakinsa wanda shima abinda yayansa suka fada shi ya fada cewan rufesa tayi da duka ta dauko mai ta zuba masa azaba ta sakasa tureta sai man ya zube mata gabaki daya tin daga kai sbd ta daga kenan zata zuba masa ya tureta din.
Yanda yayi bayanin shima cikin tsantsar azaba da yanayinda yake tabbatarda gaskia akan abinda ya fada ya saka jamian rubuta komai suka tafi aka barsa tareda rufe case din kawai akan hakan sbd batada wani gata ko galihun da zaace baa yadda da bayanansu ba bare aci gaba da bibiyar zancen dan haka kawai aka yadda aka bar komai daga nan.
Kwana daya sukai suna zaman gaisuwan na biyu suka watse suka koma jinyar mahaifinsu hankali kwance duk da tayi musu muguwar illar kona Baban dan kuwa kafafun sun sabule gabaki daya ba kyan gani sun soyu da kyau suma.
Kudaden Baba Aisha dake boye gidan kusan sun kwashe fiyeda rabi sauran kawai suka bawa yan uwanta tareda tarkacen wasu kayanta dan haka jinyar Baban sukeyi cikin dan sauki sbd akwai kudin hakama kusan duka tarewa sukai asibitin,
Shi kuwa Baban duniyarsa ta shiga wani irin matakin farko da duhu da baqin cikin dayafi na talauci dan kuwa kafafuwa dai da alama sai Allah dan kuwa namansu ya dahu yayi luguf ba alaman zai taba tsanewa ya koma daidai ga yayansa babu me sanaa ga kudin Baba Aisha din harsun qare a jinyar wadda yanzu ne aka fara dan kuwa haryanxu a danyace yake.
Buga bugar neman kudi gadan gadan suka fara dan jinyar Baban gabaki dayansu amma sam babu kowace hanyar samu komai ya sake toshewa ya tsaya cak talauci yayi musu mugun kamun kazar kuku gashi baban ne yake nemowa ya basu duk rintsi gashi kuka a kwance dan haka kansu ya sake daukan zafi akan yana rayuwa zata sauya musu suyi kudi kota halin yaya.
Ana cikin hakan Baba yayi kusan wata uku a kwance yana jinyar da babu sauki ko daya a cikinta kafafuwa dai sun rube bazasu taba warkewaba dan dahuwar naman kai sukai rugup babu mafita saita yankewa idan ansamu halin hakan me kenan.
Baqin ciki da baqin talauci qarasa zarar dashi sukai zuciyarsa ta kuma bushewa babu kalar mugun tinanin da baiyiba daga kwancen ta yanda zasu samu halin nema masa lafiya ya miqe,
Su kansu duk wani baqi da mugun tinani sunyi amma haram dinba da suke nema ido rufe tayi wuyar samu..
Lokacinda ya cika wata kusan biyar a lokacin ne ya tsayar da tinaninsa guri daya wato "HAJ MARYAM BINNAH" wato Uwar 'yayansa da lokacin komawansu rayuwarta yayi danma basu taba tinanin inda take ba bare wace rayuwar take da irin daular datake ciki sbd yayi mata kashewan gaske a zuciyarsu dako labarin komai basuda ko daya akanta.
Da daddare suna zaune a tsakar gida Baban yana kwance akan tabarma Bulama yana zaune gefensa da wata matacciyar tsohuwar waya a hannunsa wadda ko haskenta kawowa yake ya dauke yanata kokarin tura wani dogon sakon roqo dazai turawa wani amma taqi tsayawa sai mutuwa takeyi tana kawowa,
Khamis kuwa zaune yake akan kujeran katako ta tsuguno yayi shiru yayi nisa a wani irin tinanin yanda zai samu masu siyan sassan jiki ya shirya siyar da qodarsa dayaji ana iya siya matiqar zai fita daga wannan qangin da mugun daurin na talauci daya tsukesu tsam kaman zariya a qugun uztaz.
Jamilu dayake zaune yana cin wata busashiyar awarar da tin safe aka soyata har wata qasa qasa yakeji a ciki batafi guda biyar ba duka duka ya samu ya siyo yana ci yana durawa duk wanda yakeda hannu a aikin awarar tin daga wanda ya siyar da waken suyar da wadda tayi niqan da wanda ya siyar musu da itacen da aka dafa da wadda takai niqan da wadda ta dafa da wanda ma ya soya har wadda ya siyar da man da aka soya zaginsu yakeyi yana debe musu albarka sbd ta bushe qayau ba laushi ko cika a awarar sai uban qura.
Baba dayake jinsa bude baki yayi shima cikeda baqin ciki da takaici kaman zuciyarsa zata fado sbd abinda yakeji yace
"Da wannan tsine tsinen lokaci yayi da zaku nema maryam sbd itace BINNAHs gabaki daya yanxu,
Itace take juya duniyar BINNAH's,
Tayi arzikin da zata ita sauya duniyarku gabaki daga yanda kuke zuwa billionaires amma ta zabi rufeku da gogeku daga rayuwarta gabaki daya dan haka lokaci yayi da ko ita bata nemeku ba ku zaku nemeta ku koma rayuwarta dan arzikinta naku ne dan jininta ne yake yawo a jikinku"
Hadiye bushashiyar awarar bakinsa jamilu yayi yana kallan Baban yace
"Baba BINNAHs na qasar Cyprus kake magana ko wasu BINNAH's din aka samu?"
Wani 'dataccen baqin ciki mai yankar maqoshi baban ya hadiye yana bude baki a hasale yace
"Su dai da kuka sani na qasar wajen,
Shugaban familyn na yanzu shine mijinta,
Kunada haqqi mai girma akanta da lokaci yyi daya kamata kuje ku mallaka dan kuwa bazan iya mutuwa da baqin cikin nan ba na sanin tana cikin daular da zata iya sauya duniyarku da rayuwarku tareda tarihinku gabaki daya amma tayi shiru kafin ta haifi dan dasuke ganin yafi kowa duniya yanxu kune yayan data fara gani kune manyan yayanta daya kamata ace kune gaba a lamarintah."
Khamis zubawa Baban idanuwansa da sukai jajir atake yayi yana jin zancen kaman saukar aradu dan kuwa haka yakejin kowace kalma na ratsa kowace jijiyar jikinsa da kwakwalwansa tareda wasu lissafin rayuwar da baima taba tinanin zata bullo masa ta nan ba kirjinsa take ya tsaya cak daga kowace tinanin duniya bayan na Haj maryam binnah dayaketa maimaitawa.
Bulama ma take kansa ya cake cikin wani zazzafan tinani da mamaki mai nauyi ya kalli Jamilu wanda shima shi din ya kalla kafin suka juya suka kalli Khamis wanda idanuwansa sukai wani jajir jijiyoyin kansa na fitowa manya manya.
Shiru gurin yayi kowa ya shiga tinani da wani irin shock tareda kasa yadda da mahaifiyarsu da suka sani dai itace Haj maryam Binnah da suke ji a labaran media da radio.
Jamilu ne ya sake karfin halin iya bude baki yafara jerowa Baba tambayoyi akan BINNAHs da ita kanta Haj maryam din wadda sun kasa yadda da wannan labarin da zai sauya rayuwarsu sauyin da har abada sunyi hannun riga da talauci koda kuwa zasu maida kansu marayu ne dan komawa ga uwarsu.
#MAMUH
#THE ASHIRUs
#THE BINNAHS
CRAZIEST BETRAYAL
#BEST REVENGE
#BEST LOVE
#HOT ROMANCE
#SECRETS
#THRILLERS