BAYA TA HAIHU

15

by @rabiattu0444

*BAYA TA HAIHU*
15

Ummu Maher (Mrs green)🍀

*AREWA WRITTER'S ASSOCIATION*


*🗣️Kar ki wuce ba tare da kin karanta ba Please👏🏻 domin na tabbatar da kuma watarana za ki zama kamar Ummufadeel da ga shirye sai ki fara siyarwa👏🏻🗣️💃🏼*

*_UMMUFADEEL!_*
_*UMMUFADEEL!!*_
 FOODMART🍊🍋🍎🍏🥦🥬🥑🥝🥥🍇🍓🍒🍌🥔
*UMMUFADEEL*
*Ƴar Jos💃🏼*
*UMMUFADEEL*
_Gidan sauƙi_
*Ummu fadeel me gidan gonar kayan marmari kowanne iri, da nau'ikan kayan tsirrai ko wanne iri, tana bayarwa akan sari*

*_SHIGA GROUP DOMIN GANIN KOMI DA IDONKA_*
***
*1_Citta ɗanya🫚 buhu ko bucket*
*2_Kaninfari kwano ko buhu*
*3_Cinnamon*
*4_Kimba*
*5_Masoro*
*6_Rosemerry*
*7_Tafarnuwa*
*8_Amla*
*9_Habbatussauda*
*10_Man kwakwa*
*11_Zaituun*
 Da dukkan nau'ikan kayan ƙamshi na gida da na waje, dukkaninsu za ku same su cikin sauƙi da kuma rahusa gami da aminci, trust and thrusted.
_______________
*_Kar ku ga Ummu Maher ta fiye faɗin sunan, ku tambaye ni menene? Tabbas Ummufadeel ta shahara a fannin kawo muku kayan tsirrai, da kayan lambu, nau'in su Fruits, vegetables, ko wani nau'in kayan fruit da na lambu tana kawowa, kamar su;_*
*Strawberry🍓*
*Roseberry🍒*
*Inibi🍇*
*Ayaba🍌*
*Fiya🥑*
*Kwasha kwasha🥝🥝*
*Apple 🍎🍏*
*Mango🥭*
*Plum*🍑
*Cocumber🥒*
*Latas🥬*
*Cornflower*
*Doya🥔*
*Dankalin turawa*
*Dukkaninsu tana siyarwa a raha da kuma rahusa, ku dai ku hanzarta ku neme ta akan lambarta kamar haka ****

*_Idan na ce zan jero muku za mu daɗe ba tare da na gama ba, sannan tana siyar da na'uikan tsirrai kusan rabi da kwatansu tana siyarwa cikin aminci da kuma rahusa, tana siyar da danƙwala-danƙwalan doya, dankalin turawa, dankalin Hausa, makani._*


Billy sai lallaɓa Hafsah take har suka isa wani ƙayataccen private hospital, ko kafin su je asibitin ma duk jikin Hafsah ya gama yin laushi it kaɗai tasan irin yadda take ji saboda tun da take ba ta taɓa jin irin wannan ciwon ba, sai take ji tamkar dai babu wani abu me suna jini a jikinta.
Kai tsaye likita ya auna ta jikinta babu zazzaɓi a lokacin saboda haka sai ya ba ta gwajin fitsari, Billy ta tashi tana rawar jiki domin a zuciyarta dariya kawai take yiwa Hafsah wato uwar ɗakinta, ji take in ma ace da disko ta yi rawa tasan dai a yanzu ko tana so ko ba ta so dole ne ta bar mata Habibu, ta tabbatar ciki ne da Hafsah domin kwana ta yi tana amai sannan tasan Hafsah in har tana al'ada tana fama da matsanancin ciwon mara, rabon da taji ta ce tana ciwon mara idan ba ta manta ba kusan wata biyu ne ko da ba a yi wata biyu ba an kai sati bakwai, amma da yake Hafsah sokuwa ce ba ta gane komi ba, rayuwarta kawai take ta saɓo sannan ga sauye-sauye na gani da ido da suka bayyana a jikin Hafsah ɗin.


Likitan ta fara musu baya ni bayan an kawo mata gwaje-gwaje.
Ta kalli su Billy sannan ta ce"wacece Hafsah a cikin ku?.
Billy ta yi saurin nuna Hafsah sannan ta ce"likita ai ni ko kama ban yi da masu suna Hafsah ba".
Likita ta murmusa sannan ta ce"ai sunan mutum ba a kama yake ba mafiyawanci a halayya ne".
Billy ta ce"yauwa halayya zan ce na ce kama, gaskiya halayyar ma ba ɗaya bace balle wata kama".
Sosai Hafsah ta kalli abokiyar cin mushen na ta wato Billy, ta ɗan yi mamakin kalaman ta amma da yake ita ba mutum ce me fahimta da wuri ba sai ta juya wajen likitar ta ce"ni ce Hafsah".
Likitar ta kalle ta sosai sannan ta ce"congrat Madam".
Billy ta yi karaf ta ce"ban gane congrat ba, na me fa?.
Likita ta ce"Madam tana ɗauke da ciki ƙarami".
Ai ba Hafsah da ba ta san komi ba, hatta Billy sai da hantarta ta kaɗa amma da yake ƴar bariki ce sai ce wa ta yi"likita mijinta fa baya nan kusan wata uku".
"To koma sai menene ni dai na faɗa muku tana da ciki sauran bayanin idan kun je gida kwa yi, idan kuma ba ku yarda da wannan gwajin ba sai kuje wani asibitin a kara tabbatar muku domin mu dai ba za mu yi muku ƙarya ba".


Tuni Hafsah ta zunduma wani uban ihu, sannan ta fara ce wa"na shiga ukuna ni Hafsah asirina zai tonu innalillahi wa inna alaihi raji'un". Gaba ki ɗaya ta fara fita daga hayyacinta sai gunjin kuka take, haka dai Billy ta ruƙo ta suka fito daga asibitin dai-dai za su fito ne wata nurse ƴan unguwar mahaifan Hafsah ta ganta, sai kuka Hafsah take a lokacin tana ce wa"na shiga uku Billy, tabbas na yi asarar rayuwata Billy da me zan kalli..."

Dai-dai lokacin ne wannan ƴar unguwar ta su ta ce"a a Hafsatu lafiya kuwa?.
Da sauri Hafsah ta gimtse kalamanta sannan ta yi saurin cigaba hawaye Masu matuƙar zafi suna saukar mata a kumatunta.
Suna shiga Mota, direba ya fara tafiya Billy ta dinga kallon Hafsah tana raya wasu abubuwa a zuciyarta tabbas ya zama dole ayi wani abu akan cikin Hafsah idan ba haka ba, aurenta ma sai lalace bare rayuwarta daga nan ta shiga mawuyacin hali.

Ba ta bari direban ya buɗe mata murfin motar Ba ta yi gaggawar fitowa ta shige gidan da gudu tana kuka tamkar dai an buɗe famfo. Ta faɗa kan lallausar kujerar dake falon, Billy ta shigo da mayafin Hafsah a hannu tana ce wa"ke wai meye haka ne, so kike ki tonawa  kan ki asiri? To sai wallahi ki mayar da hankalinki jikinki mu yi magana, idan ba haka ba BAYA ZA TA HAIHU, azo a yi ta tonon asiri wanda duk faɗin katafanin danginku ba za su iya ɗauka ba".
Hafsah ta tashi ciki da bala'i da danasanin kasancewarta da Billy, sai take ganin rabi da kwatan masifar da take ciki kamar akwai sa hannun Billy ɗin.

"Billy wannan ita ce rana ta farko ta karshe da za ki ba ni shawara in bi, ga shi nan kin jefa ni a cikin mummunar masifa, wacce nake ganin hanyar rushewar rayuwar jin daɗin dana fara ɗanɗanawa".

Da sauri ta ce"kar ki kuskura ki shafa min tsaba kaji su bini, dama da halin ki na same ki za ki wani ce ni na jefa ki, kuma kin san Allah ba ki isa ka ce za ki rabu dani ki zauna lafiya ba, ina da evedence ɗin da zan tona miki asiri kowa ya ji ya tsane ki, kuma wallahi duk inda mijinki yake sai na bishi na nuna masa komi saboda haka ki nutsu ki ji hanyar mafita idan kuma ba haka ba BAYA TA HAIHU".

Hafsah ta share hawayenta ta tashi ta isa har inda Billy take sannan ta ce"Billy kenan ni na yi kuskure ai tun a baya dana tsamo ki a cikin matsala na zo na ajje ki a cikin gidana, kici , kisha, har ma da sutura kin ga kuwa dole ki faɗi duk abin da kike so".

"To wai Hafsah gori kike min komi, wallahi ni nasan mijinki idan da yasan abin da kika aikata sai yafi jin daɗin kasancewata a gidan nan da kuma abincin da nake ci, saboda haka ni ce kaɗai a yanzu zan rufa miki asiri mu binne ba tare da kowa ya sani ba, amma idan kin ƙi za ki gane ba ki da wayo".

Hafsah ta rushe da kuka, ba tada wata dabara ko wayo ta saba da shawarar Billy saboda haka a yanzu ma dolenta ta ji shawarar da za ta ba ta.
Billy ta kalli Hafsah, ganin jikin Hafsah ya yi sanyi sannan ta ce"to abu na farko shi ne a kira Habibu, sannan kuma a zubar da shegen cikin kowa ma ya huta".


"Billy kina ganin hanya ce mai ɓillewa, kin san fa yadda muka rabu da Habibu kina ganin zai yarda bana bin wani bayan shi".

Billy ta gallawa Hafsah harara sannan ta ce"wallahi sam Hafsah ba ki da wayo, ke sai kace ba mace ba bakisan hanyar da za ki yaudaro sa yazo ba? sai komi na faɗa miki? Sannan shi ne fa ya fara sanin ki a ɗiya mace, kin ga kuwa yasan ba za ki bi kowa ba kiyi abin da nace kawai kiyi amfani da basirar ki da hikimar ki ta ƴa mace sannan sai ki faɗa masa kina da ciki bayan haka a zubar da cikin, in har kina son kuci gaba da hulɗa wata ƙila ma ya gane kina da cikin ne shi yasa ya gudu".


Hafsah ta yadda da maganar ƙawarta, Billy ce ta yi jinyarta har na sati ɗaya ta ɗan fara warware kaɗan.





***
_HAMMAH HAMZA_



Yana durƙushe gaban mahaifiyarsa, tana masa nasiha akan riƙon sakainar kashin da ya yi wa Hafsah Ammin na sa ta ƙara da ce wa"Hamza Allah zai tambaye ka akan yadda ka riƙe matarka, ace wai wata kusan tara da aurenku amma ace ko shimfiɗarka ba ta taɓa zuwa ba, yanzu ma ba don ta faɗawa Baby komi ba da sai dai ka yi ta zama kana zaluntar yarinya, to bari kaji babu ruwan Allah da ba ka santa, matuƙar ka zalunce ta sai Allah ya saka mata".

Sosai nasihar Amminsa ta shige ta, yaji tsoron Allah sosai kuma ya sanyawa zuciyarsa gyara ɓarakar da ya yi, sannan ya yi alƙawarin ba zai ƙara barin Hafsah anan ba zai dinga tafiya da ita.



To ni fa Ummu Maher na ce Ammi kin ɓallo ruwa, matsala za ta ɓarke za a yi yaƙin basasa na biyu, bari na fece kar a haɗa dani na ɓuya a bayan window na dinga leƙowa, ana yi muna jin daɗi.


Kai tsaye daga gidan Ammi gidansa ya taho, tun da daga Airport gidan Ammi ya yi daga nanne da Ammi ta yi masa nasiha ya yi gidansa da bai yi niyyar zuwa gidansa a yau ɗin ba gidan ɗaya gidan da ya gama gina wa kwanannan can zai tafi.


Hafsah tana kwance a falo lamo da ita, kamar kazar da aka tsamo a ruwa ba tada aiki sai barci amai dai yanzu babu shi tsaf amma kasala da barci kam ko kasa albarka, Billy kuma ta tafi gida taje ta dawo domin ba ta wani nisa da Hafsah domin ita burinta tasan komi na ta, tasan inda take ajiye duk wata dukiyarta watarana ta yashe ta ta gudu, domin Hafsah sani ne ba ta yi ba Billy muguwar karfa ce domin hatta ƴan uwanta sun rabu da ita saboda mugun hali, sata, bin maza, damfara, rashin kunya, rashin daraja na gaba, duk dai halinta ne sunan ma da ake faɗa mata a garin su Jalingo shi ne KARA DA KIYASHI (ɗaukar mara sani).


Sosai Hafsah ta kaɗu, ganin mijinta Hammah Hamzah jikinta ya ɗau tsuma saboda rabon da ta ganshi yau wata 7 kenan tun bayan aurensu da ya dawo sau ɗaya bai ƙara dawowa ba, sai dai yana yawan aiko mata da saƙo tun da tana da account ɗinta, da yake mutum ne me kyauta kafin ma su ƙare ya ƙaro mata wasu.

Shima saboda yanayin jikinsa a sanyaye yake da jin kunyarta akan abin da ya yi mata kawai sai ya wuce ba tare da ya amsa sannu da zuwan ta ba.



***


_AMMINSU HAFSAH_


Tana zaune tana gyara shinkafar tuwo wacce ƴar albarka Mero ta kawo mata, sunan da take kiran Mero kenan tana yi tana waƙar Mamman shata Allah yajiƙansa da gafara me taken _Lafiya jari Mamman baban galadima ɗan musa._

Tana bin waƙar tamkar dai ita ce ta rera waƙar, sallama ta ji ta amsa da ce  wa



 "Wa'alaikumussalam".


Lantana ce ta shigo wacce suke kiranta da anti nurse.
Ta shigo da fara'ar ta tana ce wa"sannu Ammi ana ta gyara shinkafa sannu da aiki".
Ammi ba ta gama mamaki ba ta amsa domin ita dai a iya saninta bata taɓa shigowa gidansu ba, idan ma wani ne ba shi da lafiya har gida ake kai shi ayi masa allura ba wai ita ta so ba, amma da yake yasan ba mutum ce ita me fitina ba shi yasa ma ba ta wani kawo batun tashin hankali ba, amma sai tun da har ba ta san menene ba dolenta ta yi mamaki.


Ta ce"Ammi nasan za ki yi mamakin ganina ko?".
Ammi ta ɗaga kai da sauri ta ce"sosai ma amma ban sani ba ko allurar aka fara yi gida-gida ba".
Anti nurse ta yi dariya kaɗan sannan ta ce"yaiwa Ammi wata magana ce na zo miki da ita, ɗazu dana je asibiti da safe na ga Hafsah ita da wata ƙawarta, sai dai a yanayin dana ga Hafsah sai na ji a jikina kamar akwai matsala, sannan ni wannan bai wani ɗaga min hankali ba, abin da na ji tana faɗawa ƙawarta ne ya ɗaga min hankali".


tsakanin uwa da ɗa sai Allah, duk da Hafsah ba ta taimaka mata sai da ta ji zuciyarta ta buga ta yi saurin ce wa"me ta ce Anti nurse?.

Ta faɗi hakan da matuƙar firgici da kuma tunanin me za ta faɗa mata.

"Uhum ji na yi tana ce wa"Billy na shiga uku na janyowa kaina masifa da bala'i yanzu da me zan kalli dangina".  Gaban Ammi ya yi mummunar bugawa ta fara salati gami da ce wa "bayan haka ba ta ƙara cewa komi ba?.
anti nurse ta ce "no gaskiya ba ta faɗi komi ba, dai-dai nan ta juyo ta ganni sai ta yi sauri ta shiga mota da tasan za ta ganni da ba ta faɗi maganar ba, domin daga ganinta ba ta da lafiya sosai sannan sai kuka take cike da tashin hankali".

Ammi ta tsure tamkar za ta saki zawo, sai ta ce "bari na tashi yanzu nake gidan na ji me yake faruwa Allah dai yasa ba wani mummunan abin bane?.
Ta faɗi hakan amma ba ta da wanda zai ba ta amsa, ba ta san mummunan abun kunya ya faru ba wanda da duniya za ta sani sai ta tsinewa Hafsah kuma sai an daɗe ba a goge tarihintaa ba na irin cin amanar da ta yi wa ƙanwarta uwa ɗaya uba ɗaya.


Tun kafin Anti nurse ta fita Ammi ta fara shirin zuwa gidan Hafsah, tana shirya wa tana jin bugun ƙirjinta yana ƙara gaba sosai tana cikin shirin ne Baffah ya shigo ɗauke da sallama, Anti nurse tana zaune ta gaishe shi ya amsa ga mi da cewa"likita ce a gidan na mu? Ko allura aka zo ayi mana ƴata?.

Da yake Baffah zai haife ta sai yake tsokanarta, mijinta ya rasu shekara huɗu ba ya tana da yara huɗu, a unguwar uwar marayu suke ce mata.
Anti nurse ta yi murmushi ba tare da ta ce komi ba, da yake dama tana jin kunyarsa ta ɗaukesa tamkar mahaifinta.

Baffah ya ga Ammi tana ta shiri har ta sanya hijabi za ta fito, sai kuwa Baffah ya ce"ina za ki je ne haka Fatsima?.
Hankali a tashe ta faɗa masa abin da yake faruwa, Baffah ya ce"au sa ban shigo ba tafiya za ki yi baki tambaye ni ba? Sannan ma na tambaye ki? Babu waya ne da ba za ki kira ki tambaye ta ba har sai kin je?.

Ammi ta yi rau-rau da ido kamar za ta yi kuka, don ba ta son Baffah ya tsayar da ita, ai kuwa kamar ya shiga zuciyarka yaji abin da ta ce ya ce"zauna bari na kira ta ko mijinta na ji abin s yake wanzuwa?.
Jikin Ammi ya yi sanyi ta zauna tana karanta wasikar jaki.



Duk lambobin su da ya kira babu wanda ya ɗaga saboda haka ya ce"ki bar maganar zuwa an jima za je har gida na ji komi".
Ammi ba haka ta so ba, ta  cire hijabin ta cigaba da tuwonta, tana ta tunanin abin da ya faru. Anti nurse kuwa bayan ta tafi Baffah ya same ta a waje, ya ce yan buƙatar lambarta za suyi magana.

Uhum ni kuma Ummu Maher dana ɓuya a bayan taga, na leƙo don gulma in ji me zai ce? Sai ya yi maganin gulmata ya wuce abin sa bayan ya karɓi lambar, na ce ai kuwa sai na yi ta bibiyarsu domin na ji me zai cewa anti nurse.




***

_MERO_


Ina kwance akan ƙirjin Hammah Habibu, yana ta buga game da ya gaji sai ya ba ni na cigaba da yin game ɗina ga cikina ɗan wata 6 ya fito gwanin sha'awa.

Ƙarar shigowar saƙo ne yasa na miƙa masa wayar ba tare dana ga wanda ya turo saƙon ba, kuma dama ƙa'idata ne ko kiransa aka yi bana kallon fuskar wayar balle nadan wanda ya kira, saboda bana son shigowar zargi ko kaɗan a cikin zamantakewar mu.

Ya amsa yana ce wa"ba zai wuce mtn ko aitel ba, su ne ba sa mantawa da mutum kullum suyi ta turo saƙ...

Bakinsa ne ya ƙame ƙam biyo bayan karanta saƙon Hafsah da ya yi, yaji wani irin mugun bugawar ƙirji wanda har sai da ya sanya hannunsa na daga ya riƙe ƙirjin.
Ganin haka yasa na yi saurin ta shi, har sai da ɗan cikina ya motsa ina tambayarsa me ya faru?.






Uhum to dama ance garin kwaɗayi ake kashe ƙuda, sannan rana dubu ta ɓarawo rana ɗaya tak ce ta mai kaya.


Ciki dai ya tonawa Hafsah da Habibu asiri.




Mrsgreen ce.