ƊAURIN ZUCI

Chapter 19

by @maryamstar248

***

𝘿𝘼𝙐𝙍𝙄𝙉 𝙕𝙐𝘾𝙄🔐
         𝘽𝙔
𝙈𝘼𝙍𝙔𝘼𝙈 𝙐𝙈𝘼𝙍 

Chapter 19-------------
    Jinjina kai tayi tare da gasgata maganar Yahaya driver sannan ta ce.
     "Tabbas haka ne maganarka gaskiya ne kuma nagodr ƙwarai da shawararka zankuma cigaba da yi mashi addu'a hankalina ya tashi ne da yanayin da yake ciki bana so wani abu ya sami yarana su biyu jal Allah ya bani bazan juri ganinsu a damuwa."
     Kashe motar yayi bayan ya take burki sannan ya ce.
   "To hajiya agaisar mani da shi bansani ba ko ana bari a shiga dana shiga na duba shi nima Allah ya ƙara afuwa."
   Buɗe murfin motar ta yi sannan ta ce.
   "Ka shigo mana ku gaisa indai idon shi biyu ana shiga."
Da haka suka ɗunguma suja nufi cikin asibitin yayinda  Yahaya driver ya ɗaukar mata basket ɗin ya riƙe yana biye da ita yana ƙarewa asibitin kallo yana jinjina haɗuwa da tsarinta.
    
"Haba Alhaji ƙarami bansanka da haka ba da tawakkali haƙuri da juriya na sanka." Yahaya ya faɗa fuskar shi ɗauke da damuwar halin da yaga Mujaheed.
    "Yanzu ya ƙarfin jikin naka, da alamu kana jin jiki to Allah ya ƙara afuwa sannu kaji."
    Ya faɗa cike da kulawa.

"Jiki da sauƙi Baba sannunku da zuwa." cewar Mujaheed yana kallon robar ruwar da ke aje da alama yana son sha.
   Kura da hakan da Yahaya driver ya yi yasaka ya ɗauki robar ruwan tare da ɓalle murfin ya miƙawa Mujaheed.
   "Nagode Baba."
Ya faɗa lokacin da yakai hannu ya amshi robar.
    Shiru ɗakin yayi suna sauraron nasihar da Yahaya driver ke yiwa Mujaheed musamman daya tambaya akace mashi ciwon zuciya da damuwa ke damun shi.
    Bai jima ba yayi musu sallama ya tafi yana jin tausayin Mujaheed ɗin na mamaye shi.
.    "Yanzu mi kake so ka ci?" Momma ta tambaye shi tana ƙoƙarin hana hawayenta zubowa.
   Kamar da kai gefe Mujaheed ya yi tare da ƙoƙarin komawa ya kwanta, ganin haka da hanzari Momma ta riƙe hannun shi kwalla na kawowa a idonta amma taƙi basu damar fita ta ce.
     "Haba Mujaheed ka tausaya min mana dan Allah bazan iya jurewa wannan yanayin ba kaji tausayina please."
    Karo na farko daya ke jin anzo gaɓar da zai magantu akan Mommah dan haka sai ya juyo ya fuskance ta idanuwan shi na tara ruwan hawaye zuciyar shi cike da ƙunci ya ce.
   "Mi kike so ince, ya kike so inyi bayan du abin da ya faru bayan komi ya rigada ya faru mi kuma ya rage wanda kike buƙata daga wajena.
   Tun farko Mamma tun farko kafin insan kaina kafin insan mi nike ji kafin insan asalin abin da ke wakana a rayuwata ke kika fara  sani, ke kika fara fuskantar ina tsananin so da ƙaunart hasalima daga kalamanda kike yi min na soma fahimtar abin da nike ji dangane da Angel soyayya ce soyayyace ƙaƙƙarfa wacce ta kafun tun gabanin in san kaina, nayi biyayya tun a lokacin wajen ɓoye hakan dudan saboda in faranta miki amma mi yasa?."
   Ya jefa mata tambayar hawaye na ɓalle ma shi, zata yi magana ya dakatar da ita ta hanyar ɗaga mata hannu sannan ya ce.
   "Koda na minti laya tak baki taɓa bani dama na bayyana abinda ke azalzalar zuciya da ruhina ba, shin baki tausayina ne ko baki san hantara da korar da kike yi min ba akan ta yana min ciwo, nayi biyayya na kuma baki lokaci ina fata da yaƙinin  komi zai wuce zuwa gaba amma kuma sai kika kakkarye fatana kika guntule yaƙinina kika saka ƙafa kika yi fatali da cikar muradina."
    Sai yaja dogon numfashi sannan ya fesar haɗi da share hawayen shi.
    "Na so Zunaina kamar rayuwata na sota kamar raina na ƙaunaceta kamar bugun zuciyata na damu da uta kamar shaƙar numfashi na na riga na gama tsara yanda rayuwata zata cika a tare da ita, na bata space ne saboda ke na yi nesa da ita ne saboda ke na kasa bayyana mata irin tarin ƙauna da begenta da nike dudan saboda ke yanzu ki faɗa min minene asalin dalilinki na aikata hakan, ki bani gamsashiyar hujja da zata saka inji na yarda da ke inkuma yafe maki cutarwar da kika yi min ta hanyar rabani da abar sona ta ƙarfi da yaji bayan inada hanyoyi mafi sauƙi da zan iya mallakarta?."
    Du yanda taso ta hana hawayenta zubowa abu ya faskara bata san sa'ilin da suka soma kwararowa ba, wata iriyar kunya da takaicin kanta akan abin da ya faru suka dabaibayeta nan take.
Kama hannuwan shi ta yi a cikin nata tare da soma magana cike da fatan ya fahimceta.
    "Luck son bawai nayi abin da nayi bane dan tauyeka akan abin da nasan kana tsananin so, tabbas inada hujja da dalilina na yin abin da na yi, zan so ka kwantar da hankalinka ka samu lafiya ta hakane kawai zan samu nutsuwa fayyace maka hujja da dalilaina na amince ka ƙalubalance ni idan dalili da hujjata basu gamsheka ba na baka dama ka hukunta ni da kanka."
    Yawata idanuwan shi yake a kan fuskarta kamar me son karantar abin da ke cikin zucitarta.
     "A karo na ƙarshe Mommah daga wannan bazan sake sauraren ko bi tsarinki ba na gani haka nan na gaji da komi ciki harda rayuwata akan in rasa Zunaina gara inmutu inbar duniyar nan ke mahaifiyata ce kuma nasan kina tsananin so da ƙaunata don haka na baki dama ki tattaro gamsasun hujjoji da bayanai daga yau har ƙarshen wannan satin.
   Daga haka aka samu daidaito tsakanin uwa da ɗa, duda har ƙasan zuciyar Mujaheed yana jin zafin abin da Mommah tayi ma shi amma kuma ganin yanda ta shiga damuwa har ƴar rama yaga ta yi sai ya nuna komi ya wuce ya sake mata suka ɗanyi fira har yake tambayarta Afnan.
    "Afnan na school yau dai anyi sa'a ta je ita dakanta ta nuna zata je ta gaji da zaman gida wai yana mata babu daɗi saboda babu Anty Zunaina."
    Baice komi ba illa shiru daga nan firar tasu ta tsagaita....
  
******

MUHAMMAD
    Zaune suke kamar kullum shi Zunaina da kuma sabon abokinsu da ya shigo rayuwarsu suke jin daɗin zama da shi wato Kaizul mujulu wanda suka amshe shi da hannu bibiyu musamman da yake taimaka musu ta fannin wasu abubuwan.

   Ɗaga kai Muhammad yayi yana kallon hasken da ke baibaye da Kaizul yace da shi.
    "Yanzu ta wace hanya kake ganin zan iya fitar da ita daga cikin wannan gida ta koma gidan mahaifanta koda ni ban samu damar fita ba ita ina so ta tsira da rayuwarsa bana son wani abu ya sameta."
     Ya faɗi yana kallon fuskar Zunaina da itama kallon nashi ta ke tana jin yanda maganar shi ke sukarta.
   "Zaku fita ku dukanku ɗaya bazai fita yabar ɗaya ba domin ƙaddararku a dabaibaye da juna ta ke, kamar yanda kake tunanin tseratar da ita itama a naya ɓangaren hakan ta ke kawai ta rasa ƙwarin gwuiwar faɗin hakan ne saboda batada iko da sarrafa zuciyarta."
    Kaizul ya faɗi cikin muryarsa me fita da ƙara.
     "Yanzu ta wace hanya kake ganin zamu iya fita daga gidan nan?."
   Muhammad ya sake jefa ma shi tambayar.
    "Muhammad Abdallah Mafaka, da ace idan na faɗi zaka yarda ka kuma aminta to amma sanin halinka da na yi na tabbatar da ba lallai ne ka yarda da ni ba."
    Ɗaure fuska Muhammad yayi kamar bazai sake cewa komi ba sai kuma ya ce.
     "Miyasa?."
"Kasan abin da ya sa ai."
Cewar Kaizul yana tashi daga kishingiɗen da yake ya miƙe tsaye hasken shi na ƙaruwa sannan ya ce.
    "Lokacin dana ɗiba ya cika zan tafi ana jirana sai na sake zagayowa."
    Yana gama faɗin hakan ya ɓace ɓat kamar walƙiya ya barsu da sauran hasken shi da yakan ɗauki lokuta bayan ɓacewarshi kafin ya disashi.

Kallon farar fuskar Zunaina Muhammad ya yi aran shi yana tsoron kar ace Aljani Kaizul ya karanci abin da kw ran shi game da ita, saurin kawar da tunanin ya yi dan baya son ya yardarwa kan shi abin da yasan ba me faruwa bane kuma abin da yake tsoron faruwar shi tun sanda ƙaddara ta saƙalesu waje ɗaya.
    "Mouhan."
Ta faɗa da wata siririyar murya marar hayaniya kuma me sanyi, wacce sanyinta ya shiga har cikin ƙashin Muhammad.
    Kama hannunta ya yi wanda riƙe shi ya zama ɗabi'ar shi a ƴan kwanakin da suka kwashe tare, yana jin nutsuwa ta musamman na saukar ma shi adu sanda fatar hannunshi ta haɗu da tata.
    Sassanyan murmushi ya saki kafin yaɗan ware idan shi akanta cikin sigar wasa ya ce.  "A,a ba Mouhan ba Muhammad nike  amma dai tun da kin maƙalamin babu yanda na iya dole zan amsa."
   Wani tattausan murmushi ta sakar ma shi tare wanda ya saka shi sake kusantar inda ta ke ba tare da ya shiryawa hakan ba.
   Cikin kasalalliyar murya ya ce da ita.
    "Please sake faɗa inji." Zunaina wacce lokaci ɗaya ta ji wani ƙaƙƙarfan abu kuma me sanyi  ya dabaibaye saman zuciyarya bata san sanda ta ce. "Muhammad." ba sai da sautin ya fito da wani sanyi wanda ta ji shi har cikin ƙashinta.
    Wani irin harbawa zuciyar Muhammad ta yi da ƙarfi wanda hakan ya saka ya rirriƙe kafaɗun Zunaina babu shiri yana jin azaba na huda du wata kafa ta cikin shi, lokaci ɗaya ya haɗa gumi idanuwan shi suka soma ƙanƙancewa launinsu na sauyawa.
     Itama Zunaina rirriƙe hannayenta ta yi tana jin makamancin abin da yake ji amma kallon fuskar shi da take direct na rage mata raɗaɗi tana jin shi ne a iya gangar jikinta bam bata bawa zuciyarta damar da zata karɓa ba.

    Murya a wahale Muhammad ya ce.
    "Zunainah!!!." Lumshe idanuwanta ta yi akan shi sai kuma ta buɗe alamar tana sauraren shi.
    "Kin shirya?."
Ta ji maganar da yayi mata amma bata fahimci tambayar ba, duda a yanzun da taimakon Kaizul tana fahimtar wasu abubuwan saboda yana ƙoƙari wajen rage ƙarfin tsafin da aka ɗaure zuciyart shiyasaka take iya yin tunani da aiki a wasu lokutan, a yanzunma da yayi mata tambayar wani sashi na zuciyarta ya fahimta amma ɗayan sashen wanda yafi ƙarfi bai bata damar aika saƙon a kwanyarta domin tantancewa ba.
   Bata san yanda aka yi ba sai tsintar kanta ta yi da gyaɗa kai alamar ta amince, duda bata  gane mi tambayar ke nufi ba.
    "Kin tabbata za ki iya jurewa, zaki jure komi idan nace komi ina nufin komi da komi." ya faɗa yana jin tsoro a sashe ɗaya kuma yana fatan ta amsa koda ba har cikin zuciyarta bane bazai iya lamuntar tace a'a ba kamar yanda baya son ya yanke mata hukunci yafi so yayi mata adalci."......✍🏻
MARYAM SYAR