CHAPTER 20
***
𝘿𝘼𝙐𝙍𝙄𝙉 𝙕𝙐𝘾𝙄🔐
𝘽𝙔
𝙈𝘼𝙍𝙔𝘼𝙈 𝙎𝙏𝘼𝙍
Chapter 20
Kallon shi ta yi na ƴan sakanni kamar ba zata tanka ba sai kuma zuwa can ta buɗe bakinta kamar an fizgo maganar ta ce. "ehy."
Wani riƙaƙƙen numfashi ya saki da yana jin nutsuwa na ratsa gangar jiki da ruhinsa, cike da kulawa ya ce.
"To ki shirya shirina sosai mun kusa fita daga gidan nan zan maida ke gidanku kici gaba da rayuwarki kamar yanda kike a baya."
Ga mamakinsa sai yaga Zunaina ta soma jujjuya ma shi kai da wani yanayi akan fuskar ta kafin kuma da murya a rarrabe ta soma faɗin.
"A'ah ni bana so zan zauna anan tare da kai."
Sai kuma ta ɗora da faɗin.
"Amma bana son wannan halittun suna bani tsoro ka cire su please."
Ta faɗa tana kallon hayaƙin Aljanun da ya soma tasowa yanzu alamun sun kunce daga ɗaurin da Kaizul yayi musu.
Kallon su yayi shima tare da fesar da huci sannan ya ce.
"Karki damu indai har kin shirya fita kuna za ki iya jurewa wannan ba matsala bane da zarar mun fita daga nan wajen ba za ki sake ganinsu ba."
Ya yi maganar cike da tabbatarwa, sai de me? kafin ta sanu zarrar yin wata maganar suka jiyo sauti daga can sama ana cewa.
"Nima zan so ku tafi da ni idan kun tashi fitar."
Da wani irin ƙarfi Zunaina ta faɗa ƙirjin Muhammad tare da ƙanƙame shi tana fizgar numfashi da ƙarfi.
Da wani irin takaici akan fuskar Muhammad ya ke kallon Makafa da ke tsaye saman iska ya zubo musu mayun idanuwansa marasa kyawun gani.
A hankali ya soma saukowa ƙasa yana ƙarewa ɗakin kallo yana ji a jikin shi kamar akwai abin da ba daidai ba kamar an samu sauyi, sai de kuma du ƙarfin sihirinsa ya kasa gane hasken Kaizul ne daya ke ziyartar wajen, su kansu halittun da ke tare da shi sun kasa gane abin da ke faruwa a wajen amma suna jin sauyu sosai a wajen.
"Mi ya kawoka nan wajen, mi kuma ka zo nema ko kazo ka kashe mu ne?."
Muhammad ya jefa ma shi tambayar yana wurga ma shi kallon tsana da takaici.
Da sandar tsafinsa ya soma buɗe bubbuɗe wasu wajajen yana bincikawa sannan ya ce.
"Muhammad kenan idan na ce kashe ku nazo yi fa mi zaka yi?."
Wata iriyar harbawa zuciyar Muhammad ta yi a ƙirjinsa nan take azaba ta dabaibaye shi sakamakon harbawar da tayi da ƙarfi, ya fuskanci yawan motsinta ke haifar ma shi da ciwo, a ɗan razane yace.
"Kenan kashe mun ka zo yi?."
Ya yi maganar yana ƙara damƙe Zunaina a jikin shi yana jin yanda gumin tashin hankali ke tsatstsafo ma shi.
Wani baƙin murmushi wanda ya ƙara futo da munin shi yayi sannan ya ce.
"Muhammad taurin kanka na tuna min da kai ɗin tabbas jinina ne, ko jinjirin jaki nan ya ganni ya barni wajen azabar taurin kai, badan ƙudurina ba daya shallake komi a wajena da tabbas zan barka da rayuwarka kodan ka dinga yin irin abubuwan da nayi sanda ina kamanka ina jin daɗin kallo, amma kash buri da muradina ya shata layi a tsakani, duda bana wani jinka a raina amma zan ji ba daɗi idan na kashe ka."
Ya yi maganar yana saka sandar tsafin shi ya fincike Zunaina daga cikin shi ya watsar da ita a gefe har kanta na gwaruwa.
A mugun razane Muhammad ya yunƙura yana sakin ƙara amma sai Makafa ya saka tsafi ya ɗaure shi tamau.
Muhammad na fizga muryar shi a cunkushe ya soma yin maganar da ya kasa gane mi yake baɗa, har Makafa ya matsa kusa da shi ya ɓarge rigar jikin shi ya dasa wani abu me wuta a saitin ƙirjin shi ya yi amfani da tsafin shi wajen ɓatar da abin ɓat sannan ya sake shi ya faɗi ƙasa kamar marar rai.
Wajen Zunaina ya ƙarasa itama yanda yayiwa Muhammad haka ya yi mata yana ƙoƙarin dannar kan shi daga aikata abin da halittun shi ke so, domin tashin farko suka kwaɗaitu da Zunaina shi kuma yanzu baya ra'ayin hakan shi yasa yayi hanzarin barin wajen bayan ya gama abin da ya kawo shi.
******
Ƙwaro ne zaune a ɗakin shi na tsafi yana cin wasu daga sassan jikin mutane da aka sarrafa ma shi gefen shi kuma fa cup cike tab da jini, ta jikin hangon ya hango Makafa tafe shi da tawagar bayan shi, hakan ya saka ya haɗe gabas da yamma tare da cigaba da cin naman shi.
Da isowar Makafa bai jirayi komi ba ya umarci ɗaya daga cikin halittun kan shi akan ya janyo manshi kwanon gaban Ƙwaro, sai de yana kusantar wajen aka hankaɗa shi har sai da yayi tafiya me nisa sannan ya faɗa cikin ruwan wani kogi.
Kallon aika-aikar da Ƙwaro ya aikata Makafa yayi yana jinjina ƙarfin tsafin Ƙwaron.
"Lokaci ya yi da zamu aje komi a gefe mu fuskanci abin da muka saka a gaba, muradina na dab da cika gashi kuma muna da sauran buƙatu a gaban mu."
Mafaka ya faɗi yana zama tare da ɗaukar kofin jinin yasha kusan rabi sannan ya ajiye yana kallon fara tas ɗin fuskar Ƙwaro yana raya wani abu a ran shi.
Cikin abin da bai fi ƙyastawar ido ba Ƙwaro ya shata layi a tsakaninsa da Makafa inda ya saka katangar tsafi a tsakaninsu ta yanda Makafa baya iya ganinsa shi kuma yana ganin du wani motsin shi.
A gigice Makafa ya tashi tare da soma aika tsafinsa du dan ya ruguje katangar amma abu ya faskara, ya kuma bawa Aljanu dama suma suka kasa domin kuwa kusantar inda katangar take ma ya gagare su bare kuma ruguzata, hakanan Mafaka ya tafi badan yaso ba domin dai haiƙan yana buƙatar Ƙwaro a kusa da shi musamman a wannan lokacin daya fahimci bazai iya yin komi shi kaɗai ba dole sai da Ƙwaro domin kuwa nesa ba kusa ba ya fi shi ƙarfin tsafi....
******
Rimsha.
Zaune ta ke akan wani farin kyalle da alama kallabi ne ko veil saboda ƙarantarsa, gama rama sallolinta kenan na kwana da kwanuka da Makafa ya haramta mata yi saboda gurmata ruwan gidan da yayi, sai yau ya maido da shi normal.
Tana jin yanda acan cikin jikinta ta rame saboda azabar ciwon da tasha amma a fuska ba zakataɓa ganewa ba saima wani sihirtacen kyawu data ƙara gami da haske me jan hankali.
Bata firgita ba kamar yanda ta saba yi du lokacin da Makafa ya bayyana a gareta ba saima ci gana da maimaita kalmar: "Laahaula walaƙuwwata illah billah." Da ta yi asaman laɓɓanta bayan ta runtse idanuwanta gam tana jin yanda tsigar jikinta ke mimmiƙewa.
Wani dummm Makafa ya ji sanda ya tunkareta gadan-gadan domin aiwatar da muradin shi, tsayawa ya yi kamar sakarai yana binta da kallo tun daga kan abin da ta shimfiɗa ta yi sallah har zuwa kanta da lulluɓin da ta yi, yanda yaga tana dangwala gaɓoɓin yatsutsan hannagenta ya tabbatar ma shi da tasbihi ta ke yi, nan take ranshi ya dugunzuma ya sake yunƙurawa da niyyar tunkararta amma sai ya kasa nan take halittun kan shi suka shiga yi ma shi surutai a kai har suna niyyar zautar da shi daƙyar ya mallaki kan shi ta hanyar amfani da tsafin shi ya dakatar da su sannan ya fice daga ɗakin yana sharce gumi.
Nannauyar ajiyar zuciya Rimsha ta sauke sanda ta tabbatar da ya fice shi da tawagar shi sannan ta buɗe ido hawaye na gangaro mata.
Karo na farko bayan shuɗewar lokaci me tsayi daya iya tuna wani abu, wani abu me muhimmanci a tattare da ita wanda sam bai dace ace ta banta da shi ba, ɗaga fari sol ɗin hannunta ta yi tare da ƙurama wani ɗan ƙaramin tabo da ya kusa disashewa saboda hasken da fatarta ke da shi ido tana kallo, tunanin lokacin da ta ji ciwon na dawowa a tsakiyar kanta...
****
Da gudu suka shigo parlorn hannun Junaid riƙe da ƙaramar wuta wacce ake daddatsa fruit, yayinda Uncle ke biye da shi yana faɗin.
"Junaid idan na riƙe ka ba zan maka ta sauƙi ba zaka bani wuƙar ko sai na cimmaka na ƙwata ta ƙarfi bar gamin ka fini ƙira tsaf zan danne..."
Bai ƙarasa faɗin abin da yake son faɗa ba ya saki kwandon fresh fruit ɗin hannun shi lokacin da Junaid ɗin ya yi karo da centar table ƙafar shi ta gurɗe ya tafi kamar zai faɗi.
A kuma lokacinne ta ƙarasa wajen ta sauri ta saka hannu zata taro shi, amma dayake da ƙarfi faɗuwar ta zo ma shi sai ya faɗi ƙasa bayan wuƙar da ke hannun shi ta cake ta a wuyan hannu.
Sam bai samu da gurɗewar da ƙafar shi ta yi ba saima ƙoƙari tashi da yayi cikin hanzari yana taɓe ƙaramin bakin shi bayyananen tashin hankale kwance akan kyakkyawar fuskar shi.
****
Har cikin kanta ta ji sautin da yayi amfani da shi a lokacin wajen kiran ta da sunan da a yanzu ta mance rabon da ta ji an danganta ta da shi. "Ummyyyyy."
Sautin yayi amsa kuwa a cikin kanta kamar a lokacin ne ya kirata, kasa riƙe kukanta ta yi ta sake shi da iyakar sautinta tana jin zuciyarta na ƙuna akan zaluncin da aka aikata mata aka rabata da ɗanta farincikinta, tana kuka tana kiran sunan "Junaid." a ƙasan ranta tana fatan ya amsa ya ji kiran da take yi ma shi koda a cikin mafarki ne.
*****
JUNAID
A gigice ya farka daga barcin da ya ɗauke shi babu shiri yana furta: "Ummyyyy." da duka ƙarfin sautinsa tare da miƙewa tsaye ya soma tafiya yana lalube kamar ƙaramin yaron daya farka daga barci cikin duhu gana neman mamansa.
Karon da yayi sa bango ne ya saka shi buɗe idon shi da suka yi ma shi nauyi, nan take kan shi ya sara da ƙarfi saboda abu biyu, na farko mafarkin kiran sunan shi da Ummyn shi ta yi na biyu kuma dokuwar da kan shi ya yi wacce ya ji tsafin ya shige shi nan take.....✍🏻
ALLAH SARKI RIMSHA TANA GANIN JARABAWAR RAYUWA ZAMA DA MATSAFI ABIN AKWAI CUTARWA SOSAI, ALLAH YA BATA MAFITA CIKIN SAUƘI.
MARYAM STAR CE