Chapter 23
***
𝘿𝘼𝙐𝙍𝙄𝙉 𝙕𝙐𝘾𝙄🔐
𝘽𝙔
𝙈𝘼𝙍𝙔𝘼𝙈 𝙎𝙏𝘼𝙍
Chapter 23
Ahankali kuma cike da fargaba Muhammad ya kusanta bakin shi dana Zunaina, lokaci ɗaya ya ji kan shi ya sara da wani irin ƙarfi, zuciyar shi yahau watsalniya a cikin ƙirjin shi, a cikin kan shi ya ke jin tabbas akwai abin da Kaizul ya shirya ma shi.
Ko da ya saka bakin shi ya zuƙo numfashinta, ya ji wani iri ɗumi da tururi da numfashin nata ya fito da shi, wannan ya sake baki ƙarfin gwuiwar cigaba da zuƙowa yana barinta ta fesar ta hanci, har sai da shi kan shi ya ji ya aminta da ta fitar da duka tsafin da ke jikinta amma kuma sai ya gagara sarrafa kansa, ya kasa danne abin da ya taso ma shi kamar yanda ya gagara samun nutsuwa.
Duda tsoron da yake ji, du fargabar da yake ciki akan abin da zai je ya zo haka ya daure ya cigaba da aikata son ran shi....
Da ƙyar da mugun ƙyar ya samu ya raba jikin shi da nata yanajin yanda yanayin shi ke sauyawa, so yake ya ɗaga hannun shi ya toshe kunnuwan shi daga hayaniyar da yake ji tana tashi a cikin kan shi, amma saboda rawar da jikin shi ke yi ya gagara koda motsa yatsar shi.
Daga inda ya ke yana iya jin fitar numfashin Zunaina cikin wani irin yanayi, yanayin da bai tsammata ba, da ace yasan hakan zata faru da ya taka burki ya tsaida kan shi kota ƙarfin tsiya ne daga aikata abin da ya aikata yanzun
Rintse idanuwan shi yayi da tsananin ƙarfi tare da yunƙurawa akarona babu adadi, a yanzun ya yi nasarar motsa jikin shi harma yaɗanja kaɗan zuwa wajen Zunaina, hatta da fatar jikin shi yana jin yanda take amsawa da tsananin ciwon da ya soma cin ƙarfin shi, hannu ɗaya ya saka ya dafe zuciyar shi da yake jin kamar ya fizgota waje ko zai huta da azabar da take yi ma shi, jini ne ya soma fita ta hanci da bakin shi harma da kunne, cikin ƙanƙanin lokaci kamanin shi suka sauya kamar ba shi ba fuskar shi ta kumbura tai suntum kamar an hura iska a leda.
Zunaina kam zata ce ta fi shi fita a hayyacinta domin kuwa bayan azabar zuci harda da gangar jikinta da ke amsawa da tsananin azaba, cikin abin da bai wuce mintuna goma ba, ta manta komi ta manta ko wacece ita ta manta da duka abubuwan da suka faru da ita, zuciyarta da ke azabatacen ciwo ta tsaya cak daga bugu a ƙirjinta, numfashinta ya ɗauke cak ya daina shiga da fita a ƙirjinta duniyarta ta ɗauki wani irin shiru, shirun da ya nesatanta da sukanin wani abu me motsi.
*****
Vice president Obinna Ike shine zaune akan ɗaya daga cikin kujerun da suka zagaye long table ɗin da ke cikin Conference Hall, bashi kaɗai ba harda Senator Bukar Musa tare kuma da Governor na jihar Kataina me ci a yanzu Isa Mani Suna tattauna akan abu me muhimmanci.
Ɗan zame glashin idon shi Obinna ya yi cikin lafiyayen turancin shi ya soma faɗin.
"Na zaɓe ku ne domin ina kyautata zato akan ku, kamar yanda na nemi da ayi wannan tattaunawar cikin sirri saboda mu haɗu mu shawo kan wannan matsalar wacce kw ɗaure kawunan mu da sauran al'umar ƙasar nan.
Kowa ya sani President Abubakar Saminaka tsayayen mutum ne guda har da ɓari wanda ya hidimtawa ƙasar shi cikin shekaru biyu da watanni uku da ya yi akan mulki, kuma inada yaƙini akan ko yanzu da yake a kwance yana jinya da ace za'a bashi dama tofa tabbas idan ya warke zai iya ɗorawa inda ya tsaya saboda kishin ƙasar shi a jinin shi ya ke."
Sauke ajiyar zuciya yayi yana ƙarewa fuskokin su kallo yana son fahimtar wani abu game da su, kafin yaci gaba da faɗin.
"Kafin ya cuta ta kama shi ya fara ƙaddamar da ƙudurin kawo wasu sababin aiyuka da zasu sake bunƙasa arziƙin ƙasa, kuma ya fara ƙaddanar da shiri tare da gabatar da hujjoji tare da tarin bayanai wa manyan ƙasa, kuma aikin na shi ya kafu domin kuwa har an soma farawa sai kuma ga wannan lamari na jinya ya same shi, ganin kuma an ɗauki watanni bai warke ba hasalima babu alamar sauƙi tunda cutar kullum gaba ta ke yi, daga nan shirin aiki ya rogaje komi ya taɓarɓare yanzun ina so inji ra'ayoyinku ne game da wannan aikin shi ya kuke gani, minene shawararku???."
Senator Bukar Musa ne ya soma yin gyaran murya, cike da farinciki ya soma faɗin.
"Godiya ta tabbata ga Allah amma tabbas wannan tunani ne me kyau, ni a ganina yin hakan zai kawo cigaba sosai a wannan ƙasa tare kuma aikin nan sosai zai taimakawa matasa musamman wajen rage masu zaman banza, a gaskiya naji daɗin farfaɗo da wannan aikin babu abin da zance sai jinjinar ban girma a gareka haƙiƙa ka soma yin koyi da adalin shugabanmu Abubakar Saminaka, muna fatan zaka zame mana tamkar shi a sigar adalci."
Nan shima Governor Isa Mani ya ɗora nashi bayanin, sosai suka tattauna a kai har sai da suka cimma matsaya sannan suka yi sallama tare da tabbatarwa junansu wannan tattaunawar zata zama sirri agare su babu wanda zai sani har sai komi ya kammala sannan saboda basa son matsala.
Haka suka watse rayukansu fas domin indai wannan babban aikin ya tabbata tabbas ƴan ƙasa na cikin alheru kuma ba za'a taɓa mantawa da Abubakar Saminaka ba saboda shi ya ƙirƙiro kuma shi ya tsara komi domin kuwa a cikin kayan aiki harda dukiyar shi ta shi ta ƙashin kanshi.
Wani zazzafan huci Ƙwaro ya fesar tare da kallon Makafa da ya kawo mashi ziyarar bazata.
"Ka riga daka gama ginuwa a yanzun sam bakada buƙatar taimakona ka je kawai Abdullahi kaci gaba da tafiyar da komi ina da tabbaci akan zaka iya saboda kana da jajircewa akan abin da ka saka gaba."
Ya faɗi yana shafa sira-'siran furfurar da suka cike kasnshi.
Sosai Makafa yayi ƙoƙari wajen danne kan shi tare da danne halittun da ke ƙoƙarin tunzura shi akan ya shaƙi wugan Ƙwaro da tsafi, sai de sanin da yayi matsayin shi bai kai ba ya saka ya saisaita kan shi da kyau cike da sarewa ya soma bawa Ƙwaro haƙuri tare da nuna nadamar shi a fili.
Wani makirin murmushi wanda ya ƙara fito da tattarewar da fatar Ƙwaro ta soma yi irin na tsofaffin ƴan gayu da hutu ya ratsa yake aikawa Makafa, tare da yin amfani da tsafin shi na sirri ya soma ƙoƙarin buɗe zuciyar Makafa domin ya karanto abin da ke cikinta.
Kallon Ƙwaro Makafa yayi da ƙwala-ƙwalan idanuwan shi da suka kaɗa suka yi jazur babu kyan gani, da hanzari ya karanta damatsalan tsafi ya ƙara ƙwararawa zuciyar shi tsaro ta yanda babu yanda za'ayi ƙwaro yayi kutse a ciki bare har ya gano asalin abin da yake ɓoyewa a cikinta, yasa tabbas idan har ya gane asalin abin da yake ɓoye ma shi tofa zai riski juma'ar shi a laraba saboda ya kwana ya tashi da sanin waye ƙwari tun a zamanin ƙuruciya ya kuma hima da haddace abun da zai iya yi da kuma wanda zai saka a aikata cikin ƙanƙanin lokaci...
"Ina so ka bani damar da zan gyara kuskuren dana aikata ta hanyar goge laifina domin tabbas nasan fushin da kake yi da ni shi ya zama silar soma rikicewar al'amurrana."
Cikin salon iskanci Ƙwaro ya lumshe idon shi yana hasaso hoton suffar Rimsha wacce ta tsaya raɗau a cikin idanuwan shi.
"Ka kawo min ita a gidan tsafina a farkon dare."
Ya faɗa a takaice yana ƙawata fuskar shi da murmushi, murmushin da ya daki ƙirjin Makafa a da tsananin ƙarfi yana jin kamar ran shi zai fice tsabar kishin abin da Ƙwaro ke shirin aikatawa, sai de kuma bashida damar musawa dole yana da buƙatar Ƙwaro a wannan tafiyar dan haka zai jure komi zai shanye ba zai bari ginin da ya ɗauki shekaru masu tsayi yana yi ba ya rushe saboda ƙanƙanin abu irin haka ba...
*****
MARYAM
Bayan ta kammala sallah ta yi tazbihi ba tare da ta damu da hasken ranar da ya hasketa ba.
Wajen biyun saura ta kammala ta tashi tare da naɗe abin sallar ta mayar ta aje sannan ta nufi wajen Kaka ta soma tada shi daga barci domin ta yi mashi alwala.
A kuma daidai lokacin ne aka kwala sallama daga waje, da sauri ta tashi tana ƙawata kyakkyawar fuskarta da murmushi sannan ta miƙe ta fice zuwa ƙofar ɗaki tana faɗin.
"Wa'alaika salam Kakana na kaina gaskiya yau ka taushe hannu sosai harna fara tunanin yin aikin naka dan na yi tunanin wani abu ne ya tsayar da kai.
Murmushi ya sakar mata tare da faɗin.
"To ai dayake aikin kine ya tsyar da ni, na tsaya nemo miki kuɗin da zaki yo siyayya shiyasa ban zo da wuri ba." Ya faɗa yana zaro tarkacen kuɗaɗe daga aljihun shi ya matsa kusa da ita ya kama tafin hannunta ya ɗora kuɗin sannan ya ɗauko ɗayan hannun bata ya ɗora ya dafe yana sakar mata murmushi da fuskar shi data manyanta.
Wasu ruwa ne suka soma taruwa a cikin idanuwanta, wani irin tausayin Kakanin nata da su kaɗai take da na mamaye ruhinta du yanda taso haɗiye kukanta kasawa ta yi sai da ta sake shi tare da faɗawa jikin shi ta soma jeranto ma shi addu'o'i tare sa godiya akan hidimar da yake yi da ita.
Sauya launi idanuwan Kaka Abu suka yi baƙin cikinsu ya ɓace ɓat sai iya farin, shima yayi wani iri haske daya zarce misali, idan akwai abin da Aljani Kaizul da ɗan uwan shi Hanzul Dhakar suka tsana bai wuce ganin hawaye a fuskar yarinyar da suke jinta har ƙasan ruhunansu ba.
Da sauri ya saita kan shi ya dawo da idanuwan shi Normal sannan ya cirora daga jikin shi yana faɗin.
"To gaskiya ki bani kuɗina tunda kuka za ki yi min kuma kinsan bana so."
Ya faɗa yana wani marairaice fuskar shi cikin tsokana.
Sassanyar dariya ta sake me nuni da farincikin da take ciki ta ce.
"Ai Kaka Abu wannan kuɗin tunda suka riga da suka zo hannuna tofa nawa kaɗai ne babu me su kama daina tunanin zan mayar maka da su harda wani marairaice min."
Jinjina mata kai yayi still da murmushi akan fuskar shi yace da ita.
"Tabbas naki ne ke kaɗai bama ni ba babu wanda ya isa ya taɓa abin da yake mallakinki."
Daga haka ya katse firar tasu tare da giftata ya shige cikin ɗakin.
Ɗakinta ta shige tare da shiryawa cikin dogon hijabi me hannu kamar blue me haske sosai ta saka takalma suma kalar sannan ta fito tana kakkaɓe hijabin da yabi jikinta ya zauna ɗas tayiwa su Kaka Abu sallama sannan ta fuce cike da nishaɗin zata je siyayya, siyayyar data zama hanyar ƙwalli ɗaya jal da ke sadata da mutane har tayi mu'amala da su.
Sai da ta ɓace daga layin sannan Hanzul Dhakar ya kalli Kaizul tare da faɗin.
"Haƙiƙa ɗan uwana ina cikin matsananciyar damuwa idan na tuna da zan ranar rabuwarmu da Noor ta gabato hankalina yana tashi matuƙa.
Ya faɗi hakan yana zura harshe shi ya lashe kunun data dama a cikin kofi sannan ya gya kishingiɗar da yayi akan iska yana kallon Kaizul.
Murmushin da hasken shi ya fito kamar hasken warƙiya Kaizul yayi tare da kusantar ɗan uwanshi ya zauna a saman shi yana faɗin.
Akwai abu da zai faru da ita a yau kuma a yanzu babu jimawa aje komi mu nishaɗantu da kallon wannan haɗin na Ubangijin Gaskiya."
Ya faɗa yana saka hasken shi ya tsaga du wata hanya da Maryam zata bi ta je inda take son zuwa.
Kanannaɗewa Hanzul yayi a jikin Kaizul tare da zuba idanuwan shi da a yanzun suka koma zallar haske yana kawar da du wasu ƙananun ababen cutarwa da zasu iya cutar da ita....
MARYAM STAR