3&4
by @nkds
🔥❤️BA DARAJA!!!❤🔥
(True Reality Series)
©® Nainarh KD – 𝓝𝓴𝓭'𝓼❦♡
Page 3_4
SA'ADA...
Tashi zaune ta yi da ƙyar, sakamakon jikinta da ya yi nauyi saboda ta dade a kwance. Gefe guda kuma tana amsa sallamar mai gidan nata da ya shigo ɗakin, hannunsa riƙe da wata baƙar leda babba.
Idanunta da suka ɗan firfito suka yi zuru-zuru ta zuba masa tare da ɗan murmushi a fuskarta, murmushin da idan ka kalla ka san na ƙarfin hali ne. Ta furta:
“Barka da dawowa, mai gida.”
Shi ma kallonta yake sannan ya amsa:
“Yawwa Sa'ada, kin ji shiru ko? Wallahi gari ya yi gari. Kin ganni tun safe da na fita, wannan kawai aka samu yanzu. To ya za a yi tuwo ko dambu?”
Ya ƙare maganar ta sigar tambaya tare da sauka daga kujerar da ya zauna, yana buɗe ledar da ke ɗauke da masara.
Jinjina kai ta yi, idanunta suna tara ƙwalla saboda ba ta ci komai ba tun safe da ya fita da sunan sai yadda garin ya kasance tun da acewarsa bai kwana da ko sisi ba. Shi ne bai dawo ba sai yanzu wuraren biyar da rabi na yamma.
Galaɓaituwa ta yi sosai da yunwa, ga cikin jikinta mai watanni biyar kacal. Tun da safe har yanzu ba ta ci komai ba, fa ce ruwa da ta ɗura wa cikinta. Sallah ce kaɗai ke tashinta daga kwance. Amma yanzu, tana jin kanta ya kai maƙura wurin yunwa, ba ta jin za ta iya tashi tsaye bare yin aikin tuwo ko dambu, kamar yadda ya tambaya.
Ya ɗan ƙifta idanunsa a kanta ganin ta zuba masa ido ba tare da ta ce komai ba. Sai ya maimaita maganar cikin ƙosawa:
“Gashi, banda wannan, ba ko sisi a jikina.”
Ya faɗa yana miƙa ma ta ɗari biyu da ya ciro daga aljihu.
Sa'ada ta share ƙwallar da ta taru a idonta cikin dabara. Allah ya sani tana cikin azabtarwa da wannan halin da suke ciki kullum: shi bashi da aiki, kullum sai ya ce babu ko kuma gari ya yi wuta. Ba wai tana ƙaryata hakan ba, amma abin ya yi ma ta yawa. Yanzu ga ƙaramin ciki. Idan ita ta haƙura ba ta ci komai ba, abin cikin nata fa? Shin shi ma hakurar zai zai yi?
“Toh shikenan, bara sai a yi tuwon kawai. Ina ganin akwai ragowar daddawa da manja. Sauran kayan cefane sai an siya. Amma gaskiya, ɗari biyun ba zai isa ba. Ga gidan Lami kuma, har yanzu ba a kai ma ta kuɗin biyan bashin da ta biyo ba...”
Ta yi maganar cikin sanyin murya, tana ƙoƙarin ta miƙe tsaye domin ta fara gyara masarar. Sai dai me?
Kafin ta kai ga yin wani yunƙuri, ta ji wani irin jiri ya rufeta. Duniyarta ta fara juyawa, ta ɗaga hannunta tana ambaton sunan Allah. Amma kafin ta iya cewa uffan, sai ta zube saman kujera a sume.
Da haka yayi daidai da shigowar wata matsakaiciyar mace gidan tana rafka sallama da jin shiru ya sa ta nufo ɗakin tana sake maimaita sallamar.
“Rabi'u! Lafiya?”
Ta faɗa a zafafe kuma lokaci guda tana kallon Rabi'u da ya taro Sa'ada wacce babu alamar numfashi a tare da ita.
A sukwane ta ƙari sa bankaɗa labulen tare da shiga ciki sannan cikin ruɗu ta ci gaba da faɗin.
“Wani zaluncin kayi ma ‘Yar uwata na ganta yashe a jikinka babu alamar numfashi?.”
Ta kai ƙarshen maganar tana mai shimfiɗar da Sa'ada da ta karɓa daga hannunsa a kan doguwar kujera kwallin kwal dake ɗakin.
“Miye kuwa zan ma ta ina a matsayin mijinta kuma?”
Shima ya faɗa yana ciccin magani ganin mugun kallon da take wurga masa.
“Wallahi ka dai ji tsoron Allah, domin ai kasan nasan irin baƙar azayar da kake gana ma ta a cikin gidan nan...”
Hanyar barin ɗakin ya nufa yana karkaɗe rigarsa bayan ya zura ɗari biyun da ta faɗi daga hannun Sa'ada a aljihu.
Cike da takaici ta dubesa sannan a kufule ta sake cewa.
“Au tafiya ma zaka yi ka barni da ita dan baka da mutunci?.”
Sanin halinta na rashin mutunci da ta dama shi ta shanye ya sa shi jan tunga yana wani ɗaɗɗaga kai irin kar ma ta kawo masa wargi ɗin nan.
Sai kuma ya ce.
“To Yaya Mari idan banje na kira mai duba ta ba so kike ta ci gaba kasance a sume sai abin da ake gudu ya afku?...”
“Bakin ka ya sari ɗanyen kashi Rabi'u muddun fatan mutuwa kake yi wa Sa'ada in Sha Allahu ba zata mutu a ƙarƙashin mugun miji irin ka ba...”
Yaya Mari ta ci gaba da sababi cikin ɓacin rai yayin shi kuwa ya yi gaba a zuciyarsa yake faɗin.
‘Ai sai kinga na dawo gidan ne zaki ci gaba da wannan sababin ai gaki nan ga ƴar uwar ta ki ku ƙara ta.’
Ya ƙare zancen zucin yana barin gidan.
Ita kuwa Yaya Mari cikin taimakon Allah ta samu Sa'ada ta farfaɗo bayan shafa ma ta ruwa da ta dinga a saman fuskarta.
Kwance take akan doguwar kujerar yayin da Yaya Mari take yi ma ta firfita kuma har yanzu bata dena sababi ba akan baƙin hali irin na Rabi'u domin bashi da tausayi sam kuma duk wani rashin imaninsa akan baiwa Allah Sa'ada yake saukewa matar da ta yi ma sa rana a Rayuwa.
“Amma Sa'ada wannan miji naki an yi mara mutunci yanzu dama abin da ya ci gaba da yi miki ke nan amma kika yi shiru da bakinki dan rashin hankali? Ace ka aje ɗan mutum bana dabba ba amma ba zaka sauke duk wani nauyi nasa da ya rataya akanka ba, an ya Rabi'u yana da tunani kuwa ace ka aje mace mai ciki tun safe baka barta da uwar komai ba kuma ka wani kwaso ƙafa da wata shegiyar masara wai ayi tuwo ko dambo a'a abin da ya fi tuwon za'ayi, oh ya ilahi ni kam Mariya ina ganin rashin imani kwando-kwando a wurin Rabi'u...”
Ta ƙare maganar har da zabga tagumi ta kakkafe Sa'ada dake kwance bayan ta samu taci burodi da lemun da Yaya Mari ta fita ta siyo ma ta, shima da ƙyar ta samu ya zauna domin da fari amai ta dinga kelayawa kamar zata fidda ƴan hanjinta.
Sa'ada ta sauke ajiyar zuciya ganin yadda Yayar ta ta ta ɗauki lamarin da zafi cikin sanyin muryarta na hallita ta ce.
“Kiyi haƙuri Yaya amma inaga baki fahimci abin da na faɗa miki bane shi fa cewa ya yi bashi da kuɗi kuma ba ƙarya ya yi ba domin idan yana da shi baya barina da yunwa domin rabon da na kwana da yunwa tun damina wancan da al'amuran suka rincaɓe....”
Ai maimakon kalaman Sa'ada su sassauto da Yaya Mari sai ma daɗa hawa da ta yi tana ta masifa cike da ɓacin rai ta inda ta shiga bata nan take fita ba domin kuwa wannan karon Rabi'u yana nema a ƙure malejin haƙurinta har faɗi take ita kam ta yi datasanin tsaya masa da ta yi har Sa'ada ta amince da aurensa dan bashi da mutunci.
Ta ci gaba da sababi suna cikin haka sai gashi ya dawo gidan wannan karon abinci ya siyo ma ta da lemu sai kuma shinkafa da ya auno mudu biyu dama ba wai bashi da kuɗin bane kawai rashin mutunci ne irin nasa. Da kuma jahilci na rashin sanin nauyin hakkin da ya rataya a kansa kai koda ma ya sani to tabbas take sanin yake yana shuka tsiyatakun da yaga dama.
Ai kuwa dawowarsa bai saka Yaya Mari ta yi shiru da sababi ba musanman ganin irin kayan tsiyar da ya siyo daga baya acewarta.
Daga ƙarshe dai da ya sauke nasa ji da kan ya bata hakuri da alƙawarin irin haka ba zata sake faruwa ba sai kuma ta sassauto ta shiga yi masa nasiha da tunatar wa akan Sa'ada amana ce a wurinsa kuma Allah ba zai barsa ba matuƙar ya ci gaba da zaluntar ta.
Daga ƙarshe ta yi musu sallama ta bar gidan bayan ta bawa Sa'ada wani abu taja jali domin zaman haka nan ba nata bane dan ta san halin Rabi'u ba wani canzawa zai yi ba.
Yaya Mari ke nan akwai ta da faɗa musamman idan aka ɓata ma ta rai amma sam bata da riƙo nan da nan zata sauko da ta sauke ɓacin ranta. Asalin su Fulanin Katsina ne ita da Sa'ada, yayin da aure ya kawo Yaya Marin nan Kaduna da hakan ya zama silar da Sa'ada ta dawo wurinta da zama duk da kasancewar su ɗin ƴaƴan wa da ƙani ne amma azabar da Sa'ada take karɓa wurin matar mahaifinta acan ruga ya sa Yaya Mari ta nema alfarman da a bata Sa'ada ta zauna wurinta kuma cikin sa'a babu musu aka bata da sanadin hakan ya yi silar haɗu war Sa'ada da Rabi'u har ta kai su ga Aure bayan Rabi'u ya yi lulluɓin biri na halayensa gare su domin a matsayin mutumin kirki yazo ma Sa'ada har ta auresa ashe shi ɗin lumbu-lumbu ne wutar ƙaiƙayi....
HALIMA...
Tana da watanni huɗu da haihuwar ta na biyu suka tare a sabon gidansu da Abbas yaja lokaci wurin gini domin gini ne na alfarma ya fafaro.
Tariyar da da ƙyar Mama Tsahare ta bari akayi ta domin tada bala’i ta yi bayan zuwa ganin haɗaɗɗen ginin da Abbas ya yi tayita faɗa wai shi ke nan akan mata zai ƙarar da ƴar dukiyar da ya fara samu ai kamata ya yi yay ginin daidai aljihunsa ba wai yadda zai takura kansa ba haka dai aka sha fama da ita kafin daga bisani kuma ta yarje musu tariyar domin da fari hanawa tayi acewarta wai gidan ya yi ma su Halima girma da yawa.
Da yake tun farkon ginin Abbas ya yi ne har ɗakin Mama Tsahare shi ya sa hankalinta ya kwanta kuma ita ma ta fara shirye-shiryen komawa can domin ta ce ƙafarta ƙafar Abbas da hakan ya yi ma sauran surukanta matan yayyi da ƙannin Abbas daɗi domin gaba ɗaya ta addabesu ta hana su rawar gaban hantsi.
Basu cike shekara ba da komawa sabon gidan kuma kwatsam saki ya gifta tsakanin Abbas da amaryarsa Suwaiba a lokacin ita ma ta haihu ko yaye yarinyar batayi ba, Halima ta girgiza da wannan al'amari domin lafiya lau suke zaune da Suwaiba amma ganin tsakanin su sun fi kusa dama shi ya gani ya ce yana so sai taja bakinta ta tsuke bayan ta yi jaje sai dai duk da haka bata tsira ba daga bakin mutane, domin wasu gani suke ita ce ta yi shige da ficen da ta fitar da Kishiyarta Suwaiba domin haka Mama Tsahare ta yi ta yayatawa sai kuwa gari ya ɗauka musamman ganin ba mutunci Abbas ya kwace ɗiyarsa dake shan mama ya danƙawa Halima ita kuma bata da zaɓi akan dole ta riƙe ƴar domin ba yadda batayi da shi ba akan ya bari ko yaye yarinyar ne Suwaiba ta yi kafin ya karɓe ta amma ya yi kunnen uwar shegu da ita to da yake yarinyar ma mai haƙuri ce kuma bata da rigima to sai Halima ta sama sauƙi.
Nainarh KD – Nkds
***.
Or
***.