5&6
by @nkds
❤️BA DARAJA!!!❤🔥
(True Reality Series)
©® Nainarh KD⁂𝓝𝓴𝓭'𝓼❦♡
Page 5_6
A ɗan tazaran shekarun da suka biyo baya abubuwa suka ci gaba da gudana rayuwa tana tafiya cike da darussa daban-daban cikin rayuwar auren Halima domin kuwa bayan rabuwar Abbas da Suwaiba sau biyu yana ƙara aure amma duk ba inda suke zuwa domin ma ko shekara basa yi suke rabuwa ta biyun ma da suka rabu da ciki a jikinta daga ƙarshe ma data haihu sai kawowa Abbas Ɗansa suka yi ko yayesa ba'ayi ba kuma shi ne ya takura sai da ya karɓa yaron.
Ba kunya kuma ya kawowa Halima ita kuwa a lokacin sai ta ƙekashe ƙasa ta ce ba zata iya ba babu abin da zai saka yana aura-aure ita kuma ya dinga ɗaura ma ta hidimar ƴaƴa nata ma sun ishe ta saboda haka ya san yadda zai yi idan ma dawo da mahaifiyar yaron zai yi ita dai duk wannan bai dame ta ba, a lokacin sosai aka kai ruwa da Halima kuma taƙi karɓar Ɗan, domin ta fara gajiya da halin Abbas na aura-aure gashi a gari bata tsira ba daga zagi da zargin jama'a a kanta domin kallon wacce take hana mijinta zama da ma ta ake ma ta kuma surukarta Mama Tsahare ce ummul aba isin komai.
Abbas da ya fusata da ƙin riƙe masa ɗa da Halima ta yi sai ya karɓa har da ɗiyar wurin Suwaiba dake wurin Haliman ya damƙawa mahaifiyarsa Mama Tsahare da tuni ta dawo gidan da zama a cewar ta ba zata zauna daga gefe Halima tana hana ɗan ta jin daɗin rayuwa ba ta hanyar hana sa zama da mata shi ya sa ta dawo gidan domin koma mene ne zai faru ya faru a gabanta.
Sai dai duk abin da Mama Tsahare take faɗa da yayatawa akan Halima bata taɓa samun ta ta kowacce hanya da maganar ba bare kuma ace ta yi ma ta faɗa da nasiha akan abin da take zarginta duk da bata tabbatar ba, batayi wannan ba sai ma yayatata a gari da take yi kuma wannan abu shi ke cima Halima tuwo a kwarya a ganinta ai gwara in ma da gaske tana aikatawa ɗin to Mama Tsahare ta same ta ita da ita da maganar ba wai ta baza ta a gari ba, amma dai ta yi hakuri tana jurewa tun da ta san zuciyarta kuma Allah yana tare da mai gaskiya.
– ** –
Wasu ƴan mata ne su biyu zaune a saman wani dogon benci ƙarƙashin bishiyar dalbejiya cikin makarantar primary ta gwamnati kana ganinsu kasan malamai ne a makarantar.
“Kina bani mamaki da halayenki Rukky.”
Baƙar budurwar mai pink kala ɗin hijabi ta faɗa tana juyo fuskarta sai tin budurwar dake zaune kusa da ita fara ce amma fari natural ba fari ne irin na kanti.
Cikin halin ko in kula wacce aka kira da Rukky ta ce.
“Da aka yi me kuma?.”
“Hmmm abubuwa da yawa mana, na farko dai na kasa gane nufin ki, kina son mutum amma kin haɗa sa da wata ya aura yanzu kuma ya sake ta ban san kuma mene tsarin ki na gaba ba. wallahi ƙawata kiji tsoron Allah bawan Allah'n nan da gaske sonki yake tun da yake yin duk abin da kika buƙata gashi ke da kike wajen ke kike tsara komai amma zargin yana akan matarsa ta gida ne ana ma ta kallon mai bin bokaye wacce ta hana mijinta riƙe mata bayan ga master plan ɗin a gabana gaskiya Rukky kiji tsoron Allah fa kina cutar da matar can da yawa....”
Wani murmushi Rukky ta saki mai cike da ma'anoni tana girgiza kai Safiyyah ba zata gane ba koda tayi ma ta bayani shi ya sa ba zata wahalar da bakinta ba gwara ta yi shiru kawai..
“Koda nayi miki bayani kwakwalwarki ba zata taɓa gane nufina ko kuma ina na dosa ba Safiyya saboda haka ki zuba ido kawai kisha kallo.”
“Hmmm uhmmm ahhmm.”
Safiyya ta ja ajiyar zuciyar magana ne cike a bakinta amma ba zata furta komai ba domin ta rasa gane inda ƙawar tata ta dosa.
Rukky ta miƙe tsaye sannan ta kalla Safiyya bayan ta saɓa jakarta a kafaɗa.
“Tun da baki da wata maganar ni zan yi na gida sai gobe.”
Har ta yi gaba sai kuma ta juyo tana kallon Safiyya da ta bita da ido.
“Karki damu ba wani abu nake nufi da Abbas ba domin aurensa zan yi nan da wata guda in sha Allah domin Abbas nawa ne, ni kaɗai!”
Tana faɗa ta yi gaba yayin da ta bar Safiyya baki buɗe cikin mamaki.
Rukky tana fita daga gate na makarantar ta fara waigen ta inda zata hango sa.
“Da alama yau kam idanun nan naki basa gani yadda ya kamata domin gani ata nan amma kina ta faman kalla-kalle.”
Ta yi murmushi mai kyau tana mayar da hankalinta kan Abbas dake jingine da babur ɗin sa a ɗan gabanta kaɗan kafin kuma ya turo babur ɗin ya ƙari so zuwa gabanta.
“Ai nayi tunanin bakazo ɗaukata ba ne domin wata ƙila kana can matarka ta kanainaye min kai har fa na fara fusata.”
Ta faɗa lokacin da ta hau bayan babur ɗin shi kuma ya tayar sannan ya fara tafiya yana ɗan murmushi ba tare da ya ce komai ba kamar yadda ta zata dama tasan za'ayi haka domin indai zata ɗauko masa magana akan Matarsa ko domin ta bugi ruwan cikinsa taji wani aibu na Halima to fa baya taɓa bata dama ta nan ɓangaren kam Abbas yana sirri don komai rintsi bai yarda da sanar da sirrin gidansa ga kowa ba hatta Mahaifiyarsa bare kuma budurwa.
“Lokaci yana ta tafiya biki kuma yana ta ƙaratowa, faɗa min shirye-shiryen da kike.”
Ya faɗa lokacin da suka isa Kofar gidansu ta sakko daga babur ɗin tare da tsayawa tana fuskantar sa yayin da shi kuma yake zaune daga kan babur ɗin.
“Shirye-shirye kam ana ta yi domin har na nema hutu ma a school har sai bayan bikinmu ina fata dai zuwa yanzu ka sanar da matarka game da bikin namu?”
“No, tukunna dai ban riga na sanar ma ta ba...”
“To amma me ya sa? Sai kace zaka aura maƙiyiyarka, gaskiya ya kamata a ce zuwa yanzu ta sani domin bata hakkinta.”
Ta fara maganar a zafafe sai kuma ta ƙare cikin son nuna masa hakan ne ya kamata.
Abbas ya ɗan sauke ajiyar zuciya idanunsa akan ta yana ɗan murmushi ya furta.
“Okay, zan faɗa ma ta shike nan?”
Ta yi murmushi.
“Yawwa Angon Rukky.”
Dariya ya yi.
Sun ɗan taɓa fira kafin daga bisani yaja babur ɗin sa domin komawa wurin aikin da ya bari ya taho ɗaukarta a makaranta kamar yadda ya saba, yayin da ita kuma ta tura Kofar gidansu tare da shiga ciki da sallama.
“Kin dawo?”
Cewar matar dake duƙe tana gyara kayan miya, ta faɗa bayan ta amsa ma ta sallamar, Rukky bata dubeta ba ta amsa murya can ƙasa.
“E.”
Matar bata sake cewa komai ba ta ci gaba da abin da take yi yayin da ita kuma Rukky ta shige ɗakin da yake mallakinsu ita da ƙanwar ta Jummai. Tana cikin shirya wa ta jiyo muryar Mommy da alama har ta dawo daga makaranta domin ita ma koyarwa take yi sai dai ba makaranta ɗaya suke koyarwa ba.
“Oyoyo Mommy”
Rukky ta faɗa lokacin da ta fito sanye cikin wata doguwar rigar material baƙa mai adon stones, tana kallon Mommy dake zaune saman tabarma a kofar ɗakin ta tana hutawa.
Kamar Mommy ba zata kulata ba sai kuma ta kalleta tana kawar da kai ta amsa. Sannan ta ƙara da faɗin abin da har hau bai dena ci ma ta tuwo a kwarya ba.
“Yanzu ke Rukayya kin kyauta ma kanki ke nan gaba ɗaya kin dage sai wannan Bahaushen sai kace baki da masoya bakyaji baki gani ke sai shi... Nan kika zauna kina mana rantsuwa akan yaron nan bashi da mata ashe ƙarya kike kin faɗa ne kawai saboda a barki ki auresa, ashe bama mata ba mata biyu garesa bayan haka ma aura-aure yake yi kusan mata uku duk ya rabu dasu yanzu ke irin wannan mijin kike ma kanki sha'awa...”
Wani irin duba Rukky take yi na Mommy jin abin da take faɗa sai dai tayi shiru bata ce komai ba yayin da Mommy ta ci gaba da faɗin.
“To a gaskiya muddun kin ɗaukeni a matsayin uwa a gareki to fa ban yarda ki aura wannan yaron Abbas ba, ni ba zan hanaki auren bahaushe ba wai dan kina a matsayin Banufiya amma ban zamunce ki aura wannan ba gaskiya ki nemo wani.”
Mommy ta kai maganar cikin nuna gaskiyarta da kuma lallashi ga Rukky'n da ta lura ta yi nisa bata jin kira.
Tsakani da Allah yaron bai ma ta ba sam kuma duk da ba ita ko mai gidanta ne suka haifi Rukky ba, amma suna raye ba za su bari ta jajibo abin da zai cutar da ita ba su kyale, bare kuma shi dama mai gidan nata ba son Rukkyn ta aura bahaushe yake ba kwata-kwata, dan ma dai ta nace ne kuma ga Rukky da taurin kai ba laifi, shi ya sa suka kasa tankwarata amma da tuni wani zancen ake ba wannan ba.
“Hmmm, Mommy ina ga abin da ya kamata kiyi ma wannan lamarin kawai shi ne fatan alkahiri, ki kuma bi da addu'a domin ina son Abbas kuma matarsa bata wani ɗaɗani da ƙasa ba, bare wani aura-aure da yake nasan ina shiga gidansa zai daina domin shi ɗin nawa ne, kuma da kike faɗin bahaushe ne, shifa Abbas ba fa bahaushe bane Mahaifiyarsa da take asalin bafulatana ya biyo baki ganshi ba jajur ga baƙin gashi mai sulɓi, mahaifinsa ne bahaushe ba wai shi ba!.”
Cikin takaici Mommy dake duban Rukky ta ɗauki mafirffici da take firfita da shi ta wurga ma Rukky tana faɗin.
“matsamin daga gani ja'ira kawai ba dai kin nace sai Bahaushe ba, to ai gaki ga Abbas ɗin nan muna zaune dake wata rana zai gwada miki halin nasu na rashin riƙon aure!.”
Mommy ta yi maganar da biyu tana yi ma kishiyarta da ita ma ta kasance bahaushiya ce kallon ƙasan ido.
“To ke Anty Rukky ki haƙura mana da aurensa tun da duk su Mommy basaso, kawai ki aura aura mai sonki mana Yah Bello tun da shi Banupe ne yarenmu guda, daɗin daɗawa kin san shi da halayensa shima kuma haka sannan ɗa ne ga ƙanwar Mommy, nifa ina jiye miki dana sani ne zuwa gaba muddun kika aura Bahaushen nan.”
Ƙanwar ta Jummai dake daga cikin ɗakin Mommy tana yi ma ta marking a papers na yara ta faɗa cikin son bada nata shawarar.
Cike da masifa dama kuma a kufule take da yadda mutanen gidan nasu suka kasa fahimtar ta bare bata gudunmawa Rukky ta juya ga Jummai tana faɗin.
“Ki fita idona fa na rufe Jummai, babu ruwanki da rayuwata, idan shawara kike bani to bani buƙata idan kuma umarni ne ba zan bi ba sai naji bugu.”
Ta faɗa tare da tashi fuuu ta koma ɗaki. Daidai lokacin kuma Daddy ya shigo gidan da sallamarsa tare da Bello yana take masa, yayin da Bello yabi Rukky da kallo ita kuma Mommy ta girgiza kai cike da takaicin taurin kai da kafiya irin na Rukky shi kuwa Daddy tambayar abin da yake faruwa ya yi Jummai ta labarta masa komai.
SA'ADA...
Bayan kwana biyu da zuwan Yaya Mari abubuwan da Rabi'u ya siyo suka ƙare sai zaman nasu ya sake komawa kamar baya dan yanzu ta ɗan fara sana'arta da kuɗin da Yaya Marin ta bata don ba laifi ta bata da ɗan kauri, shi ya sa wani lokacin bata tsayawa jiran Rabi'u sai dai ta fita ta aika yaro ko ta shiga makwabtansu ta siya abin da take buƙata gudun kar ta zauna da yunwa ga kuma ciki.
A haka rayuwar nasu ta ci gaba da gangarawa Rabi'u na ci gaba da fito da sabbin halaye yayin da Sa'ada ke ci gaba da zaman haƙuri da shi har zuwa lokacin da ta haife cikinta.
Ta sha wahala sosai domin tun yamma ta fara naƙuda a tsaitsaye kuma da yake haihuwar fari ne batayi dabarar faɗa wa wani ba haka ma zuwa dare da Rabi'u ya dawo duk da tana jin ciwo, haka dai ta daure suka kwana a haka sai dai cikin dare da abin ya matsa sun kasa bacci daga ita har shi sai dai duk yadda take yi masa magiyar yakaita asibiti lokacin da gari ya waye ƙi ya yi duk da yaga yadda ta galaɓaita sai ma cewa da ya yi.
“Haba mana Sa'ada yanzu ke baki tausayina ne? kin san fa haihuwa zakiyi kuma hidimar haihuwa ba kaɗan ba, yanzu kina maganar na kaiki asibiti ga asibiti da shegen kashe kuɗi so kike na ƙarar da duka tanadin nawa ne a wurin kaiki asibiti? Gaskiya ki daure kawai ai da haka sauran mata duk suka saba kuma ai naga wuya ma bata kisa bare lamari na haihuwa ko mutuwa fa kika yi kai tsaye aljanna kika nufa ba wata gargada.”
Duk faman zuban da Rabi'u dake tsaye daga can bakin kofar ɗakin jingine da ƙofa hannuwansa kuma naɗe a ƙirji ita Halima ba ganewa take yi ba domin tsananin wahala da azaba ya sa take ƙoƙarin fita hayyacinta.
Jin ta yi shiru sai nishi da take yi sama-sama kuma da kyar ne ya saka ba shiri Rabi'u ya ƙari sa ciki yana kiran sunanta amma shiru gudun kar ta mutun masa ne ya sa ba shiri bai san lokacin da ya yi waje ba domin neman agaji.
Yana fita kuwa yaci karo da wata maƙociyarsu da ta fito zata wuce bai tsaya wata wata ba ya fara nuna ma ta cikin gidansa yana faɗin ta taimaka matarsa ce ke naƙuda.
Jin hakan ya sa cikin hanzari ta yi cikin gidan, da yake ma suna mutunci da Sa'ada kuma tasan cikinta haihuwa Yau ko gobe ne shi ya sa bata tsaya jan zancen ba ta afka ciki.
Sai dai koda ta shiga ta tarar da Sa'ada cikin wani hali domin ta gama yin lakwas da wuya ma ta iya haihuwa da kanta ganin hakan ya sa ta duba Rabi'u da duk ya bi ya haɗa gumi ta ce.
“Gaskiya da wuya Sa'ada ta iya haihuwa da kanta domin ba sauran ƙarfi a tare da ita shawara ita ce kawai ka samo abin hawa a miƙa ta zuwa asibiti.”
Rabi'u ya sharce gumi cikin damuwa ya ce.
“Ki dai taimaka mana Maman Habib ina ce kece Sa'ada take bani labarin cewar kin fara karatun likitanci amma baki ƙari sa ba nasan dole kin san wani abu da ya kamata dan Allah daure ki taimaka ta haihu da kanta ki bar batun zuwa asibitin nan.”
Sak Maman Habib ta yi tana duban Rabi'u da tsananin mamaki na jin kalaman dake fitowa daga bakinsa a wannan ƙadamin da ake ciki na rai ko rayuwa.
“Ba maganar nayi karatun likitanci ake ba Malam Rabi'u ', maganar rai da rayuwa ake yi a halin yanzu, dan girman Allah kaje ka nemo abin hawa akai baiwar Allah'n zuwa asibiti.”
Maman Habib ta faɗa cikin son danne ɓacin ranta da abin da ya yi sai kace wani jahilci yana ganin mace na naƙuda macen ma matarsa amma shi ne yake wani kawo ƙabli da ba'adi.
Jiki na rawa Malam Rabi'u ya juya ya fice daga gidan yayin da Maman Habib ta koma ta ci gaba da taimakawa Sa'ada da abin da zata iya tana kuma jiran dawowar Malam Rabi'u, sai dai shiru-shiru ba Malam Rabi'u babu labarinsa tsawon mintuna talatin kuma zuwa lokacin haihuwar tazo gadan-gadan wannan dalilin ya sa Maman Habib dage wa wurin taimakawa Sa'ada domin a samu ta haihu gefe guda tana mamakin abin da ya tsayar da Rabi'u daga fita samo abin hawa amma shiru kakeji kamar an aiki bawa garin su.
Cikin taimakon Allah Maman Habib ta samu Sa'ada ta haihu da kanta amma fa ta sha wahala sosai, ba kuma tare da ɓata lokaci ba, nan da nan Maman Habib ta fara yin abin da ya kamata kama daga yanke wa jaririyar cibi da sauran abin da ya kamata, bayan mintuna kaɗan da haihuwar sai ga Malam Rabi'u ya shigo gidan kamar wanda aka jefo tare da shi kuma babban aboki kuma amininsa ne wato Malam Lurwanu.
A lokacin da Malam Rabi'u ya fita domin nemo abin hawa cikin gaggawa sai kwatsam suka ci karo da Malam Lurwanu da farko ma shi kam Rabi'u ba gane abokin nasa da ya fara washe baki daga ganinsa ya yi ba har sai da Malam Lurwanun ya kamo rigar Rabi'u yana ƙara faɗin.
“Ah ah Malam Rabi'u wani abin ne ke faruwa ina ta magana baka kulani ba zaka wuce an ya kuwa ka ma ganni?”
Sai a lokacin Rabi'u ya ganshi kuma ya ganesa domin har ga Allah hankalinsa ya yi gaba sai yanzu tsoro ya shigesa kar Sa'ada ta mutu ta barsa.
A gaggauce ya faɗa wa Malam Lurwanu abin da yake faruwa, yana shirin yin gaba domin neman abin hawan da za'a kai Sa'ada asibiti sai ji ya yi Malam Lurwanu ya kuma riƙo rigarsa yana faɗin.
“Haba mana Malam Rabi'u karka faɗa min da gaske abin hawan zakaje nema, haba wai sai kace baka san halin mata ba, ai nake faɗa maka raki ne kawai irin na su na mata, amma ban da haka haihuwar fari ma da ake basu abin a kyauta an ce fa ba wani wahala...”
Shiru Rabi'u ya yi kamar mai nazari yana kuma sauraren bayanin abokin nasa, ganin hakan ya sa Malam Lurwanu yin ƴar dariya yana kauda fuska sai kuma ya ci gaba...
“Ai nake faɗa maka mu tsaya anan mu ɗan jira na wasu mintoci muna komawa zaka sha mamaki domin idan taji uwar bari da kanta zata haihu ba sai ta tsaya jiran a kaita asibiti ba, Allah na tuba idan taje asibitin ma fa ba cire ma ta ciwon zasu yi ba dole dai da kanta zata haihu.”
Cike da gamsuwa da kalaman abokin nasa Rabi'u ya zauna saman dakalin ƙofar gidan yana wani gyada kai ya furta.
“Kuma fa haka ne gaskiya abokina ya taimakeni da tuni fa sai dai a ci kuɗi na a banza.”
Ya yi maganar yana wani washe baki. Yayin da shi ma Lurwanu ya yi dariya kamar wanda ya yi abin kirki yana faɗin.
“Ai nake faɗa maka yanzu mu jira kafin mu shiga ciki zakasha mamaki kuma zaka ƙara yarda da ni.”
Daga haka sai suka ɗauko wani firar sai kamar bayan mintuna sha biyar sannan Rabi'u ya miƙe ya nufa gidan malam Lurwanu yana take masa baya.
“Ma sha Allah ta haihu ke nan?”
Suka haɗa baki wurin faɗa yayin da Rabi'u ya cusa kansa cikin ɗakin Sa'ada dake kwance saman gado tana hutawa bayan Maman Habib ta taimaka ma ta ta kimtsa shi kuwa Malam Lurwanu ya tsaya daga ƙofa yana wani zura kansa ciki baki washe ya ƙara da faɗin.
“Tabbas ta haihu kai Alhamdulillah abokina kaga abin da nake faɗa maka ko?”
Ya mayar da akalan maganar yana ɗauke kallonsa daga kan Babyn da ya hango gefen Sa'ada dake kwance yana mayar wa kan abokin nasa.
“Kwarai kuwa na kuwa ga zahiri.”
Rabi'u ya faɗa yana miƙa masa hannu suka yi misabaha..