BA DARAJA

9&10

by @nkds

❤️BA DARAJA!!!❤‍🔥
    (True Reality Series)

***

©® Nainarh KD⁂𝓝𝓴𝓭'𝓼❦♡

Page 9–10

– ** –

HALIMA...

Bata taɓa tunanin zuwan wannan lokaci mai cike da tarin abubuwa cunkushe ta ko'ina ba sauk'i ba cikin rayuwarta, duk da abubuwan da Mahaifiyar Abbas da shi kansa suke yi ma ta, tana d'auke kai bata tab'a hasashen b'acin rai zai yi sanadiyyar rasa igiyar aurenta d'aya ba.
A halin yanzu ba sakin ne ya fi damunta ba tun da an riga an yi lamarin ya riga ya faru, so she should move on, but how? What about her child's? Shin ya ya 'ya'yanta zasu kasance idan bata tare da su gashi mahaifinsu aure zai yi, Abbas ya hana ta d'aukan ko d'aya daga cikin 'ya'yanta duk dan ya bak'anta ma ta, ita kam ina zata saka kanta?
Da fari bata damu ba da hanata 'ya'yan da ya yi, duk da kuwa ta damun, sai dai bata nuna ba, har sai ranar da ta yi kwana guda a gidansu wani labari ya zo ma ta game da yarinyar da Abbas zai aura, hankalinta ya tashi kuma zuciyarta ta gaza samun sukuni ba nata makomar ba, na 'ya'yanta kawai take hangen yadda za su kasance, lokaci na farko ke nan tun bayan faruwar abin da taji zuciyarta tayi wani irin karaya sai take jin zata iya hak'ura ta koma gidan Abbas ko domin 'ya'yanta muddin ya nema hakan domin magana ake ta yara hud'u ba d'aya ko biyu ba.

“Allahumma innee a'oothu bika minal-hammi walhuzn, wal'ajzi walkasali walbukhli waljubn, wadal'id-dayni waghalabatir-rijal...”

Addu'ar da take karantawa ke nan cikin zuciyarta domin neman kariyar Allah daga tsoro, k'unci, rashin k'arfi da kasala ma da rinjayan namiji kuma sosai ta samu sassauci take jin kuma zata iya fuskantar Abbas da koma mene yake tafe da shi.

**

“Junaid, amma kam nayi mamakin ganinka anan.”

Halima ta fad'a lokacin da ta fito k'ofar gidan nasu bayan shigan k'aninta da ya sanar da ita Junaid d'in na nemanta da yake takan aiko sa gidansu wasu lokutan.

Junaid k'ani ne ga wani abokin Abbas dake k'auye karatu yake yi a cikin gari shi ne yake zaune a gidan Abbas d'in, kuma sosai akwai fahimtar juna tsakaninsa da Halima wanda kuma farar zuciya da kirkinta ne ya kaisu ga wannan b'igirin, domin kallon wata babbar yaya yake yi ma ta.

Junaid ya fesar da huci yana fad'in.

“Ba dole ki ganni ba Anti Halima, yanzu abin da ya faru ke nan, shi ya sa tun jiya da dare da na dawo Yaya Abbas yake ta min wani kwana-kwana da na bashi tsarabar k'auye ya kawo miki? A gaskiya banji dad'in abin da ya yi ba ai k'ara aure ba hauka ba ne.”

Ita dai Halima shiru ta yi tana dubansa ganin yadda yake maganar bilhakki shi ala dole an b'ata ma sa rai, sai ta yi murmushi kad'an.

“Wa ya fad'a maka saboda k'ara auren da zai yi ne ya sakeni?”

“Hmmm Anti ke nan ai ko ba'a fad'a ba nasan saboda hakan ne domin...”

Halima ta yi saurin katse shi da.

“Ka kwantar da hankalinka domin ba saboda aurensa ne ya sakeni ba, wani dalilin ne daban kuma duka laifina ne.”

“Ai Anti ba zan tab'a samun kwanciyar hankali ba har sai kin koma d'akin ki, Dan Allah kiyi hak'uri ki koma sannan ki dage da addu'a.”

Sai da ta d'an nisa kafin ta ce.

“Fad'a min meka sani dangane da yarinyar da Abbas zai aura, na san ba zaka rasa sanin wani abu ba domin yana aikenku shagon da take siyar da kaset-kaset da su TV da DVD.”

Halima bata damu da kallon mamakin da Junaid yake ma ta ba ta k'ara da fad'in.

“Wata magana ne aka kawo min dangane da ita duk da ko'a sauran auren da Abbas ya yi a baya bana biye masu kawo min tsegumi da 'yan gulma sai dai fa wannan karon duk yadda naso yakice maganar daga zuciyata abin ya gagara.”

Junaid ya sauke ajiyar kad'an ya na kuma fesar da huci ya jinjina kai kurum.

“Tabbas wannan mata da Yaya Abbas zai aura ta daban ce da sauran matan da ya aura a baya, na farko dai ita ba bahaushiya bace kamar sauran, ita Banupiya ce sunanta Ruk'ayya ana ce ma ta Rukky malamar makarantar secondary ce...”

Ya yi 'yar dariya irin ta shak'iyanci yana kad'a kai ya ce.

“Sai dai fa ba yarinya ba ce kamar yadda kike tunani domin ina ga idan bakuyi sa'anni ba to fa bai wuce ki bata shekaru uku ba, abu na biyu  kuma shi ne tabbas halinta ya banbanta da sauran saboda haka ki dage da addu'a kawai Anti Halima In Shaa Allahu komai zai zo da sauk'i.”

Duk da d'an fad'uwa da gabanta ya yi amma sai ta daure ta k'ak'aro murmushi tare da furta.

“Ya ka baro mutan k'auyen fatan duk suna lafiya.”

Junaid ya amsa ma ta.

“Suna nan qlau Alhamdulillah sun ce a gaisheku...”

Daga haka kuma sai shiru ya d'an ratsa kafin ya k'ara da fad'in.

“Suna kewarki...”

A raunace ta dubesa fuskarta na bayyana halin da zuciyarta ke ciki.

“I mean yaran ki suna kewarki sosai, na san ke mai hak'uri ce amma ki k'ara akan wanda na sanki dashi komai mai wucewa ne a rayuwa. In Shaa Allah, by time, everything will pass as if it didn't happen at all, so be strong.”

Ya k'arashe da d'an murmushi.

Ita ma sai ta d'an murmusa cikin son mayar da lamuranta ga Allah da mai da komai ba komai ba.

“Zaka fara wannan dogon turancin naka ba, bayan sanin kanka ne ƙwaƙwalwar bata san komai ba ta nan, ka gaida gida kaji Allah ya zab'a mana abin da yafi zama alkahiri.”

Junaid ya amsa yana bin ta da kallon tausayi domin yadda ya santa mace ce mai son karatu sosai sai dai Abbas yak'i duk yadda taso kuwa da ya barta ta ci gaba da karatun, domin bata gama secondary ba aka ma ta aure duk da anyi ne da sharad'in zata ci gaba da abin ta bayan auren kuma a lokacin Abbas ya nuna yardarsa sai dai bayan bikin da ta yi masa maganar sai ya nuna sam ba zai lamunta ba, Allah kad'ai ya san irin halin da ta shiga a lokacin domin ta saka rai ba kad'an ba a karatun.

**

A daren ranar Abbas ya zo biko, lokacin tana sallar issha'i taji sallamarsa da kuma karad'in yaran matar Yaya D'an Juma da yake da jimawa ya yi aurensa.

Koda ta idar sai ta yi zamanta a d'akin tana ji mahaifinsu yana cigiyarta amma ta yi kunnen uwar shegu tunani ta fad'a akan rashin ta idon Abbas, wato ya sakar ma mutumi 'ya kuma ba kunya yazo yana wani sunne kai lallai kam maza sai dai a barsu.

A takaice dai a wannan daren Abbas ya mayar da Halima bisa amincewarta bayan nasihu da ta sha a wurin mahaifinta kafin ya had'a daga ita har Abbas d'in ya yi musu nasiha mai ratsa jiki akan aure da kuma illar yanke hukunci cikin fushi da nadamar dake biyo baya, kamar dai yadda ta faru a kansu, duk da Abbas bai fito fili ya sanar dashi dalilin sakin ba haka ita ma Halima ta yi gumm da bakinta sai dai sun tattauna wani b'angare na maganar ita da 'yan uwanta.

Sai dai burin Abbas bai cika ba akan duk yadda yaso ta bisa a daren amma ta k'iya kuma mahaifinta bai ce dasu komai ba dan ya gama nashi.


Duk yadda yaso su kad'aice suyi magana nan ma tak'i basa dama a dole ya tafi bayan ya raba wa yaran matar Yaya D'an Juma mai suna Wahida kud'i.

A washegari ne kuma ranar da Halima zata koma 'yan uwanta mata su hud'u dukkanin su masu aure suka yi ma gidan tsinke kowa da abin da yake fad'a, daga masu bata hak'urin ta koma sai masu jin haushin Abbas na abin da ya yi ma 'yar uwarsu nan suka had'e da Wahida matar D'an Juma a gurguje dai zuwa bayan la'asar suka rakata gidan, basu tadda kowa ba makullin gidan ma Junaid ne ya kawo musu lokacin yarinyar Halima mai shekara biyar ta mak'alesa yazo tare da ita sannan ya musu sallama ya koma.

“To Halima adai yi ta hak'uri kinji rayuwar ma duka in an duba nawa take.”
Cewar Babbar yayarsu da suke kira Yaya Abu.

“Haba Yaya Abu ai ba a komai ne zata yi hak'uri a takata ba, kamar yadda ba'a komai ne sai ta yi k'orafi ba, bare ma wannan matar da zai auro an fa ce dogaggiyar 'yar boko ce...”

Wahida ta katse Hadiza wacce ta kasance ita ke bin Halima kuma take wannan zance.

“A'a Hadiza a dai bi komai a sannu kamar yadda Yaya Abu ta ce kuma ta yiwu ita wacce ta kawo mana wannan maganar fad'a kawai take dan ta zuga Halima.”

“E mana ai kyace haka mana tun da ita d'in k'anwar mijinki ce ba 'yar uwarki ba.”

Ita ma d'ayar mai bin Hadiza ta fad'a jin haka ya sa Wahida furta.

“To 'yan uwa Allah baku hak'uri.”

Ta fad'a tana mik'e wa da niyyar ficewa.

Sai a lokacin Zuwaira da ta kasance mai bima Yaya Abu da ke kuma duk ta fisu zafi ta yi magana.

“Azima karna sake jin muryarki anan ke kuma Wahida dawo ki zauna...”

“A'a dai matar Ibrahim da kin bari na fitan.”

Wahida ta fad'a da yake hakan take cema Zuwaira wasu lokutan.

Wani kallo da Zuwaira ta bita da shi mai nuni da tazo ta zauna kafin ta sake magana ya sa ta dawo ta zauna gefen Halima dake bakin gado.
“Wai da farko ba d'aki biyu ya baki ba ya akai naga yanzu kuma d'aya ne kayanki ke ciki?”

Zuwaira ta fad'a tana k'are ma d'akin kallo da yake ta jima bata zo gidan ba shi ya sa bata san ya koma haka ba.

“Hmmm.”

Kawai Halima ta iya fad'a yayin da Yaya Abu cikin sanyinta ta ce.

“Tun fa lokacin da zai k'ara wancan auren ne ya karb'e d'aki d'aya. Dan Allah mu aje duk wannan a gefe muyi abin da ya kawo mu.”

Ta fad'a ganin Azima ta bud'e baki zata yi k'arin bayani.

Sosai suka k'ara tausasar zuciyar Halima da kalamai na kwantar da hankali kuma koda suka lura da wasu akwatina biyu a d'akin sun fahimci abin da Abbas ke nufi da su ke nan ya k'aro d'aya ne akan akwati guda da ya yi da farko na kayan fad'ar kishiya sosai suka lallasheta kan ta yi hak'uri da duk wani abu da zata gani ta kuma kawar da kai.

Sai dare suka yi ma ta sallama suka tafi bayan sun bata shawarar ta d'aura girki ganin akwai komai na buk'ata dama wasu lokutan yakan d'an aje kayan masarufi kamar shinkafa, taliya da mai haka har ma da icce.

Daga ita sai d'iyarta Khairiyya a gidan kafin zuwa can Abbas ya shigo shi da sauran yaran.

Hauwa'u data kasance Babba kuma abokiyar haihuwar Habib mai rasuwa sai kuma Khadija mai bi ma ta dama tana tare da Khairiyya mai bi ma Khadija d'in sai kuma Ali da Abbas d'in ya d'aura saman kafad'a ga mamakin Halima har da sauran yaran nasa biyu yazo wato Saddiqa 'yar wurin Suwaiba da ta kasance kusan sa'anni suke da Khadija sai kuma Sulaiman na wurin matar da suka rabu recently.

Bata ce masa komai ba haka shima bai ma ta magana akan yaran ba kuma sannan bai bata hak'uri akan komai ba kana ko washe gari da taga Mama Tsahare bata kwana a gidan ba kuma ga d'akinta an kwashe kayan ciki nan ma bata ce k'ala ba, washegarin ranar da ta dawo d'in ne kuma take jin labarin a ranar aka kai kayan lefe gidan amarya a wurin k'anwar Abbas da suke uba d'aya da ta zo a lokacin kuma bikin saura kwanaki hud'u ne.

Shamsiya ta kuma gyara zama cikin zak'alk'alewa tana mai ci gaba da fad'in abin da ba'a tambaye ta ba.

“Hmmm lallai ma wato Anti Halima nake baki labari ashe haka mutanen nan 'yan uwan amaryar Yaya Abbas suke basu da mutunci, ashe ma basan auren suke ba wai saboda ya kasance bahaushe sai kace ba zaune suke cikinmu hausawan ba suna samun na rufin asiri, wai ashe ma ita ma amaryar da zai aura Rukky naji sun ce sunanta ko me wai ashe cewa ta yi bashi da aure shi ya sa ma da farko suka yarda da auren da kyar sai daga baya suke sanin ma yana da mata kuma har ya'ya bakwai garesa dan ma d'aya ya rasu kummm...”

“Shamsiya ya isa haka Dan Allah ni duk ban tambaye ki wannan ba.”

Halima ta fad'a ganin zak'alk'alewar yarinyar ya yi yawa har ta fama hawa ma ta kai da surutu sai kace ta tambaye ta.

**

An yi biki an gama lafiya amarya ta tare hankula sun kwanta sai dai ta b'angaren Halima tsananin k'arfin addu'a da kuma kawar da kai su ne suka sa damuwa bata kwantar da ita ba.
A zahiri ba zata ce bata kishin mijinta ba wannan ya zama dole domin kishi halitta ce bare kuma miji irin Abbas son kowa ga kuma ya'ya tsakani, sai dai wani abu da ya fi k'arfin a kirasa kishi shi ne ya yi ma ta tsaye a zuciya ga kuma yawan fad'uwar gaba shi ya sa ba dare ba rana a duk lokacin da zataji fad'uwar gaba ko wani abu makamancin haka sai take karantar.

“Rabbi inni lima anzalta ilayya min khairin faƙir³ Ra rabbi inni magalubun fantasir³  la haula wala quwwati illa billahil aliyal azeem³, Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un”

Da wannan ta samu d'an sassauci har ta saki jiki aka yi shagalin bikin lafiya aka gama.

Halima ta yi shiru tana jira taji Abbas ya had'a su domin gabatar ma juna da kuma 'yar nasiha kamar yadda aka saba sai taji shiru, hakan ya sa ta tattara kan 'ya'yanta tare da rufe d'akin ta ta yi kwanciyarta abin ta.

Sai dai me cikin dare tana bacci wani irin abu da batayi tsammani ba kuma bata tab'a cin karo da makamancin haka ba a duk k'arin auren da Abbas yake a baya ba shi ya kasance da ita.

Allah kad'ai ya san iya adadin lokacin da ta kwashe nan zaune bayan ta idar da sallah da ita kanta bata san adadin raka'o'in da ta yi ba duka a domin ta kautar da hankalinta daga tashin hankalin da take ji domin ta fahimci da gangan kuma da biyu amaryar ke abin da take yi duk dan ta nuna ma ta Abbas ya zauce a kanta.

Halima taja ajiyar zuciya jiki a sanyaye a zahiri idanunta akan yaranta dake bacci peacefully yayin da a bad'ini ta tafi duniyar tunanin yadda wannan sabon al'amarin zai wakana a gare ta domin ta lura wannan auren da Abbas ya yi tafe yake da wasu murd'ad'd'un lamurra, tana jin b'urutun Abbas da amaryarsa a tsakar gida cikin wannan tali'tailin daren amma ta kasa kwakkwaran motsi, a hakan wani nannauyar bacci ya yi gaba da ita.

**
A jerin kwanaki bakwai da suka biyo baya Halima ita ta san irin abin da ta gani daga amaryar da ko magana bata tab'a had'asu ba sai dai abubuwan da take yi domin janyo hankalin Halima har ta cusa ma ta haushi k'arfin addu'a ne kawai ya saka basu yi tasiri akan Halima ba.
Kuma tsawon wannan kwanaki gaisuwa kad'ai ke had'ata da Abbas shima kuma a tsakar gida sai dai alak'arsa da yaransa tana nan daram domin Abbas indai a b'angaren son yara ne wannan kam sai dai Halima ta bada labari domin kuwa yana basu full attention da lokacin sa da kuma duk wata kulawa da ta ce dace.

A safiyar ranar Lahadin da ya kasance sati guda ke nan da bikin, kuma har zuwa ranar Halima ita ke girki gaba d'aya har da amarya bawai dan Abbas ne ya buk'aci hakan ba sai a domin ita ta yi ra'ayi a ganinta hakan ne adalci tun da budurwa ya aura.

Tana zaune saman tabarma a k'ofar d'akinta yayin da take yanka wasu kaya, can gefe kuma Abbas ne ya saka yaran nasa a tsakiya yana koya musu karatu da rubutu kamar yadda ya saba.

Ruk'ayya dake daga d'aki ta kwala masa kira da fad'in.

“Darling! Darling! Dan zo mana please...”

Halima bata d'ago ba bare taga yanayinsa ta dai ji lokacin da ya cewa yaran su jirashi yana zuwa, kana ya shige d'akin amaryarsa.

Sai dai shiru-shiru bai fito ba tun yaran suna zaune suna jira har suka watse suka fara wasanni a nan tsakar gidan, da yake koda wasa muddin ba makaranta ba to fa kofa aike ne Abbas baya bari ayi musu ya gwammace yaje shi da kansa bare kuma zancen su fita waje wasa da yara ba wannan a tsarinsa.

“Mamma ki nuna min yadda zan rubuta wannan ban iya ba kuma Baba bai fito ba daga can?”

Halima tabi hannun yarinyarta Khadija da ta yi maganar tana aje ma ta book and pen d'in ta akan kayan da take yanka wa tare da yi ma ta nuni da hannunta ta saitin d'akin Ruk'ayya.

Sai dai ko kafin ta yi magana babbar 'yar ta Hauwa'u ta bawa yarinyar amsa da fad'in.

“D'akin sabuwar matar Baba, Baban ya shiga ba Mamma ta ce muna kiranta da Anti ba?”

“To ya isa haka nan, ke kuma ki jira Baban naku ya fito sai ya nuna miki kinga ni aiki nake ko?”

Jinjina ma mahaifiyar nata kai yarinyar ta yi tare da zama a gefe ta rafta tasa hannu tana tallafo fuskarta tana kuma jiran fitowar uban.

Can yarinyar ta gaza hak'ura sai ta  mik'e ba tare da Halima ta ankara ba ta yi wuff ta shige d'akin.

Ihun yarinyar da Halima taji ya sa k'irjinta bugawa da k'arfi yayin da lokaci guda ta tsinkayo muryar Abbas yana kwala kiranta kafin ya fito hannayensa damk'e dana yarinyar daga shi sai wando Three Quarter da vest.

“Halima wani irin shashanci ne ya sa zaki bar yarinyar nan ta shiga d'akin bayan kuma kin san ina ciki ko kuwa dai duk a cikin haukan kishin ne ya sa kike neman lalata min tarbiyyar ya'ya.”

Tun da ya fara maganar kanta yake a sunkuye bata ce da shi komai ba har sai da ta lura da ya gama sannan ta d'ago ta dubesa tare da mayar da dubanta ga matarsa da ta fito daga ita sai wata figigiyar rigar bacci mai shara-shara sai wani cika take tana batse wa, kafin Halima ta yi magana ta yi zuruf ta ce.

“Aw har ma sai ka tambaya ai da gani kishi ne ya sa ta turo a d'aukar ma ta rahoto, kuma wallahi rankwashin da nayi ma ta bai wadace ni ba, kodai ka zane ta ko kuma ni ka bani ita na koya ma ta tarbiyyar da bata samu ba...”

“Ya isa haka ba dake nake ba.”

Cewar Abbas yana d'aga ma ta hannu.
Sannan ya mayar da dubansa ga Halima.

“Dake nake fa!”

Ya fad'a a zafafe.

“To me kake so nace maka bayan kai da kanka ka yanke hukunci sai dai ka sani a da can ma da kake aura-aurenka ban nuna na damu ba bare kuma nayi kishi to akan me zan yi a yanzu sai kace wacce bata da aikin yi.”

Wani b'acin rai ne ya yi ma Abbas dirar mikiya da jin kalaman ta idan ya fahimta ke nan ma gaba d'aya bata kishi akan sa take son sanar da shi, ko kafin ya yi wata magana ya tsinkayo muryarta tana ci gaba da.

“Kana yi ma yara karatu ta kiraka, kaje kayi shiru ba dole yarinya ta bika ba tun da ka dasa mata son karatun arai sannan naga baka ce dani ya'yana karsu rab'i d'akin matarka ba dad'i da k'ari ban ma san ta shiga ba...”

Ta d'an nisa tare da fitar da huci kad'an.
“Sannan kai da matarka ku dena fitomin tsakar gida gaban yara da wannan shigar Dan Allah domin hakan bai dace ba.”

Tana fad'in haka ta ci gaba da abin da take yi bata sake ko kallonsu ba.

Shi kam kamar wanda jikinsa ya yi sanyi haka ya saki hannun yarinyar ya koma d'akin da ya fito. Ruk'ayya taja tsaki tare da bin bayansa domin ba haka taso ba.

Da Dare Halima tana zaune taji sallamarsa tare da shigowa d'akin Ruk'ayya na bin bayansa sai ta bisu duka da kallon mamaki.

Abbas ya d'an gyaran murya yana kauda kai kamar bai ga kallon mamakin da take bin sa da shi ba yayin da Ruk'ayya ta zauna kamar zata shige masa bayan ta gama k'arema d'akin kallo tana mele baki.

“Ahmm dama na taraku ne bisa al'ada domin sake had'a junanku da kuma jan hankalinku domin ku kasance abu d'aya ba tayar da hankali...”

Ya d'an yi shiru yana k'ok'arin janye Ruk'ayya daga jikinsa ganin tana neman rikitasa ya sake gyaran murya ita dai Halima bata ce da shi uffan ba, kuma tana hankalce da abin da Ruk'ayya ke yi sai dai bata nuna ta gani ba, ya ci gaba da jan hankalinsu da kuma 'yar nasiha yana fad'in da suyi k'ok'arin had'e kai ko dan suma 'ya'yansu a gaba su taso kansu a had'e ya k'ara da fad'in.
“Kamar yadda abin yake Ruk'ayya a matsayin ki na budurwa kin kammala kwanaki bakwai d'in ki kamar yadda addini ya tanadar saboda haka ku zab'a kwanaki nawa ne ya kamata a tsayar a tsakaninku daga yau.”

Zaraf Ruk'ayya ta yi tare da fad'in.

“Kwana d'ai-d'aya.”

Bai saurare ta ba sai ma duban Halima da ya yi.

“Kwana biyu shi ne ya fi dacewa.”

Halima ta fad'a a nutse. Sai Ruk'ayya ta yi saurin kallonsa domin taji abin da zai ce.

“Okay, hakan ma ya yi kwana biyu ake ma kowacce. Bisa tsari zan kwana a D'akin Halima daga hau har tsawon kwanaki biyun.”

Rai a b'ace ta mik'e ko kallon sa batayi ba a dole ta yi fushi domin bata kasance cikin mata masu b'oye abin da ke cin ransu ba.

“Okay, Good Night.”

Ta fad'a a d'an fusace tare da ficewa.

Ya yi 'yar dariya yana dawo da kallonsa kan Halima ya furta.

“Rakiya ke nan akwai daru sai kin yi hak'uri fa domin bata iya b'oye fushinta.”

Idan keken ɗinkin dake d'akin ta yi magana to Halima ta kulasa, ganin haka sai ya d'an muskusa idonsa a kanta.

“Madam wannan fushin fa? Ko dai tun abin da ya faru da safe ne?”

Wani kallo ta yi masa a ranta tana ayyana okay ya san bai yi daidai ba ke nan, sai ta basar tare da fad'in.

“Wannan ai ya wuce, bana jin dad'i ne kawai.”

“Ayya sorry, kin sha magani amma gaskiya ki aje yankan nan ki huta ke ke nan daga yanka sai ɗinki girkin ma a gurguje kike yi duk kin k'osa kiyi kud'i ne hala?”

Halima ta yi dariya jin abin da ya fad'a sai ta d'ago da murmushi tana dubansa ta ce.
“Kaji ka dai ba dole ba ai idan ma k'osawa nai kud'in nayi ba kaga laifi na ba ko ka manta 'yan mata biyu gareni Hauwa'u ga kuma Saddiqa dan naga tsawon k'afa take k'ara yi...”

“Ai kuwa kinga sai a had'a su duka a aurar lokaci guda nan da shekaru biyar haka”

Saurin zaro ido Halima ta d'an yi.

“Haba Yallab'ai shekaru biyar ai sun yi kusa ko ka manta Hauwa'u da kad'an tafi shekara goma ita kuwa Saddiqa Takwas take kawai saurin tsawon da ta yi ne yasa za'a yi tunanin sa'ar Hauwa'u ce...”

Abbas ya yi murmushi cike da jindad'in kasancewar su a haka cikin nishad'i da raha domin ya manta rabon dasu kasance a irin wannan yanayin.

“To ai shikenan na baki wuk'a da nama fad'a min nan da shekara nawa kike ganin ya dace a musu auren?”

“Humm ni dai ka bar zancen auren nan domin 'ya'yana sai sun yi karatu mai zurfi In Shaa Allahu.”

“Indai dan wannan ne karki damu domin kuwa Aure ba zai hana karatu ba...”

“Amma kuma miji yana hanawa ba?”

Ta yi saurin katse shi tana d'aura idonta cikin nasa.

Sai ya yi jim da alama maganar nata a bazata tazo mishi, sai kuma ya basar tare da fad'in.

“Wannan kuma ra'ayinsa.”

Ya fad'a a tak'aice tare da tallafo duka hannayensa ta bayan wuyansa, kamar mai tunanin wani abun daban.

Ruk'ayya dake lab'e tun fitarta ta d'an ja tsaki k'asa-k'asa cikin takaicin kasancewarsu cikin nishad'i, sam ba hakan taso ba, ganin ya mik'e tare da bawa Halima umarnin ta kai masa ruwan wanka zuwa d'akinsa ne ya sa ta yi wuff tare da shigewa d'akinta tana sauke haki.

**
Koda Ranar girki ya dawo kan Ruk'ayya, ranar da ta karb'i girkin na dare ne, sai ta yi tuwon shinkafa da miyan wake.

Kasancewar shi ne girkin ta na farko a gidan bai sa ta kira Halima domin ta nuna ma ta wasu abubuwan ba, domin kuwa tun zuwan ta gidan batasan wani abu wai shi tayen girki wa Halima ba, sai dai a dafa tazo ta d'auki nata a kwanakin farko, kafin daga bisani Abbas ya yi umarni da su dinga ci tare a kwano guda da Halima domin hakan na k'ara shak'uwa.

Lokacin da ta fara kiciniyar d'aura girkin Halima na daga bakin k'ofar d'akinta tana yanka sakamakon lokacin na zufa ne shi ya sa ta fito waje duk wani shige da fice da Ruk'ayya ke yi tana jin ta sai dai tun da bata nema taimakon ta ba ne, ya sa ita ma bata tsoma ma ta baki ba.

“Darling ya ce kayan abinci suna d'akin ki, amma me ya sa bayan kuma ga wancan d'akin da babu kowa ai shi ya sa ya kamata ya zama store.”

Halima ta tsinkayo muryarta a tsakiyar kanta.

Bata d'ago ba bare Ruk'ayya ta saka ran samun amsa, hakan kuma ya k'ara fusata ta. Ta d'aura hannu a k'ugu tana d'an jijjiga cikin halinta na masifa da bata iya danne wa bare kuma ya kasance an k'ular da ita.
“Hey, dake nake magana fa!”

Nan ma shiru ko kallon ta Halima batayi ba.

Fuu ta wuce d'aki tsawon mintina tana ciki kafin kuma ta fito.

“Ki bani shinkafar tuwo da sauran kayan had'in tuwon shinkafa Darling ya ce akwai komai da komai a wurinki.”

Ganin yanzu ta yi maganar da d'an sanyi ne, ba kamar d'azu ba, ya sa Halima sakin murmushi mara alak'a da nishad'i kafin ta kwalawa Hauwa'u kira sannan ta umarce ta da ta kawo dukkan abin da ya kamata.

Gwafa Ruk'ayya taja.

“Ba ma zai yiwu ba dole ma a canza wannan tsarin wallahi!”

Halima ta jita sai bata nuna alama ba, tana dai kula da yadda ta ci gaba da uzurinta tsakar gidan, kuma koda zata d'aura sanwa bata tambaya Halima adadin yadda ya kamata ta saka ba sai ta yi gaban kanta.

Zuwa dare ma da ta kammala sai ta d'iba da yawa a kula mai kyau da girma ta kai d'aki sannan ta zuba a wata robar Halima da take zuba tuwon safe a ciki, ta zuba tuwon shinkafar tare da kai wa k'ofar d'akin Halima ta aje bayan ta saka miya a kwano ta d'aura saman tuwon.

Shiru-shiru Halima bata ji an ce ga tuwo ba ga yaran sun fara isarta da k'ananun koke-koke, hakan ya sa tayo wajen.

Sai dai ganin yadda aka aje tuwon gaban d'akinta har tana kusan karo da shi, sai abin ya bata mamaki.

“Ruk'ayya! Mene ne wancan kika aje min?”

Ta fad'a lokacin da ta d'aga labulen d'akin Ruk'ayya'n ta shiga da sallama, domin ba zata d'auki sabon salon da ta kawo ba, kwara ayi ma tufkar hanci tun yanzu.

“Ba abinci kika gani ba, to naki ne keda yaranki...”
“To akan wani dalili ko haka kikaga ina yi?”

“Naga dai bakizo kin nuna min yadda zan yi ba.”

“Okay ke kuma baki da bakin da zaki tambaya ke nan? To a gaskiya ba zan lamunta ba wannan ya zama na farko kuma na k'arshe da zakiyimin haka domin yaran nan gidan ubansu ne saboda haka kowa yana da kwanon sa da idan an gama za'a zuba masa ciki.”

Daure zuciyarta kawai Halima ta yi bata sanar da Abbas abin da ya faru ba, duk da tuwon ma ba isarsu ya yi ba, yaran ta saka wa suka ci, yayin da ita kuma da yake takan d'an yi miya ta aje saboda lalura hakan ya sa ta aika aka siyo ma ta bread taci da miyar.

Da safe kuma sai Ruk'ayya ta k'ara fito da wani salon domin Halima tana jin lokacin da ta fito ta d'umama abincin sai dai bata ce a kawo abin da za'a sakama yaran ba, kuma kamar daren jiya ma bata saka musu kwano guda da Halima ba.

“Ah ah ya akai na ganku jigum haka, ba kunci abinci ba, ku taso mana na kaiku makarantar sannan na wuce, lokaci na tafiya.”

Fad'in Abbas ke nan lokacin da ya shiga d'akin Halima a shiryensa tsaf yana baza k'amshi.

“Matarka bata kawo abincin ba ai bare suci.”

“Ban gane ba, to me ya sa?”

“Wannan kuma ita za'ai ma tambayar?”

A d'an hasale ya dubeta sai kuma bai ce komai ba, ya shiga kwalawa Ruk'ayya kira kamar zai tashi gidan domin ba abin da ya fi b'ata masa rai kamar ganin yadda yaran su kayi jugum kana gani kasan yunwa ce.

“Ruk'ayya! Ruk'ayya! Wai kina mene haka kina ji ina kiranki?”

“Oh sorry Darling gani nima na shirya fito mu wuce.”

Ta fad'i hankali kwance tana daga k'ofa.

“Shigo ciki”

Jin muryarsa babu alamun wasa ya sa ba musu ta shiga tana wani d'auke kai.

“Me ya sa baki basu abinci ba?”

“Oh haka aka ce maka ban basu ba saboda a had'amu...”

“Shut up, kawai tambayarki nayi, ki bani amsa me ya sa baki basu abinci ba?”

“To to ai ita ce bata fad'a min adadin yadda ya kamata nayi girkin ba kuma ba ragowa ya k'are...”

“Amma me ya sa baki fad'a min ba?”

Shiru ta yi.

Sai ya jinjina kai yana ma ta wani mugun kallon da ya bata mamaki.
Wato akan yaransa yake ma ta tsawa da wannan mugun kallon ai kuwa ba zata sab'u ba, dole ma ta d'auki matakin da ba zai yi wa Halima da 'ya'yanta dad'i ba.

A lokacin dai hak'uri ta bashi maganar ta wuce, yayin da shi kuma ya fita da kansa ya siyo kwalin indomie da bread leda biyu sai kuma kayan shayi yakai d'akin Halima ba tare da ya tsaya sauraren Ruk'ayya ba.

Kuma ya zauna har yaran suka karya sannan ya tattara kan masu yawon da aka saka makaranta suka wuce.

“Darling, kai fa nake ta jira, gashi ka saka duk nayi latti, kayi sauri kazo mu wuce”

“Zuwa ina?”

Da mamaki ta dubesa sai kuma ta kawar da mamakin ta hanyar basa amsa da.

“Makaranta mana?”

“Kije ki sama abin hawa ki wuce yarana zan kai...”

“But naga ba makaranta guda kuke ba, su primary kai kuma a secondary kake koyarwa.”

“Ruk'ayya ki saurareni da kyau, dama tun farko ban miki alk'awari akan kaiki makaranta ba saboda haka karma ki fara idan kin matsu ki nema abin hawa ki tafi final.”

Ji ta yi kamar ta d'aura hannu aka ta fasa ihu, sai dai babu dama, da kallo tabi bayan machine d'in da ya tayar yay gaba abin sa ya barta nan tsaye.

“Lallai ma Abbas ni zaka wulak'anta, hmmm ba laifinka bane tabbas ya zama dole na jajirce domin zama bai gani ba.”

Wannan kalamai nata sune suka shiga kunnen Halima, da take bakin rijiya zata d'iba ruwa, da yake rijiyar nasu ta wurin k'ofa take sai aka yi ma ta katangar da ya raba su da k'ofar.

Ta sauke ajiyar zuciya tana neman tsarin Allah daga dukkan wani sharri da mugaye.

**
Zuwa yanzu da Ruk'ayya ta cika watanni biyar a gidan, Allah kad'ai ya san irin hak'urin da Halima ke yi da kuma kawar da kai domin ba'a kan komai Abbas yake iya katab'us ba.

Zuwa lokacin kuma ta gama karantar Ruk'ayya gaba d'ayanta irin mutanen nan ne da basu k'aunar zaman lafiya ko d'aya, kuma ta kasance akwai ta da fad'a akan k'aramin abu ma sai ta tada da jijjiyoyin wuya, sannan bata iya b'oye fushi ko abin da ke zuciyarta kuma bata da b'oye-b'oye ba munafunci a zuciyarta sai dai akwai kyashi wata k'ila har ma da hassada domin a yadda Halima ta fahimta shi ne; Ruk'ayya bata shigo gidan da niyyar zaman lafiya ba, sai dai tana mamakin yadda Abbas ya kasa gane hakan, sannan bata dena mamakin abin da ya gani ba a tare da ita da yake wasu abubuwan domin ita kam Halima idan aka tambaye ta game da ita Ruk'ayya kai tsaye ba zata kirata kyawawa ba duk da fara ce ba sosai ba sai dai abin da ya b'ata farin nata shi ne man k'arin hasken fata da take k'arawa sannan kai tsaye ba za'a kira ta doguwa ko mai jiki ba tana nan dai ita ba mai tsayi can ba kuma ba mara tsayi ba sannan bata da k'iba fuskarta da take circle kuma ta sha tsagu irin nasu na Nupawa dan ma hasken ta ya kan b'oye hakan.

Halima tana bakin k'ok'arin ta na ganin sun zauna lafiya sai dai ta b'angaren Ruk'ayya ba haka abin yake ba.

Wani abu da ya fara ciwa Halima tuwo a kwarya shi ne; yadda a gabanta ko yaranta sai Abbas yake aikowa da Ruk'ayya abubuwan ci ko sha daga shagon sa da ya kasance kayan provision ne mak'are ciki yana siyarwa, yayin da ita kuma zata zauna ta baje tabarma tana ci abin ka da yaro su kuma yaran sai su zagayeta suna kallo bata da rowa sam kuma abin hannunta bai rufe ma ta ido ba amma fa kafin ta basu sai sun gama shan zagi da bak'ak'en magana wannan kuma shi ne baya yima Halima dad'i sam.

Hakan ya sa watarana da ta gaza hak'ura ta tsare Abbas da maganar.

“Wai Baban Khairi me ya sa idan zaka kawo ma matarka kayan mak'ulashe baka had'owa da yaran nan ne? Idan ma ni d'in ba zaka bani ba, gaskiya bana jin dad'in abin da matarka ke yi sai ta gama zagarmin 'ya'ya sannan zata basu sai kace mara sa galihu.”

Ganin ya yi shiru yana kallon ta da alamar mamaki ya sa ta ci gaba.

“Gaskiya ya kamata tsarin ya canza muddin zaka aiko ma ta da shi to ni da yarana ma a had'o damu kawai...”

Ta k'arishe tana kauda da kai.

Sai ya yi dariyar da ya k'ara k'ular da ita kafin ya nisa tare da fad'in.

“To ai kema sai ki kawo kud'in ko?”

“Ban gane ba...”

“Ina nufin kema sai ki dinga siya domin ita ma kud'i take bayarwa ana kawo ma ta, muddin kika ga tana cin abin da ya fito daga shagona ba tare da ke ko 'ya'yanki an baku ba to da kud'inta ta siya.”

Ita dai Halima ta jishi ne kawai ba dan ta yarda ba.

Ta dai yi masa shiru ne da addu'ar idan ma cutar ita da 'ya'yanta ake to Allah na gani.

Gefe guda kuma tana sane ciki gareta tsawon watanni biyar sai dai bata nuna ma Abbas ta san da shi ba, duk da tana da tabbacin ba zai ce bai san da shi ba.

Kuma Ruk'ayya bata dena halinta ba na in an kawo ma ta aike daga shagon Abbas ta zauna tsakar gida tana ci da abin ya ishi Halima ne sai a duk lokacin da Ruk'ayya'n ta yi haka sai ta had'a kan 'ya'yanta a d'aki ta biyesu musu su shiririce da wani abin da zai mantar da su duka da wata Ruk'ayya, tun da ta soma haka sai ta sama sauk'i.

Kuma daga k'arshe shima Abbas da ya gane sai ya kasance kullum akwai tsaraban da yake bama yaran idan ya dawo da dare, da liyafa ta ci gaba ma so biyu ake basu, da rana da kuma dare.

**

“No way, ba zai tab'a yiwuwa ba Safiyya zuciyata zafi take ba zan tab'a bari matar nan ta haihu ba, bayan ni gani nan dab'as babu alamar ciki, Safiyya ki fad'a min abin da zan yi na sama salama Matar nan fa ciki gareta...”

Ta k'arishe maganar cikin tsananin huci tana safa da marwa cikin d'akin ta gaza zama ma tsabar abin da ta d'aurawa kanta.

“Ruk'ayya kina bani mamaki na rasa miye a tattare da Abbas d'in nan da kika lik'e masa, yanzu kuma an yi auren ma ba zaki kwantar da hankalinki ba, ina ruwanki na da cikin da matarsa ke da in banda d'aurawa kai aiki, kema ki dage da addu'a Allah ya kawo miki naki rabon...”

“Dakata Safiyya ba kiranki nayi kiyi min wannan zancen naki na banza ba, kuma ke idan baki ga wani abu tattare da Abbas ba ni na gani, kuma ba adadi na fad'a miki ni ba dan kud'i nakeson sa ba kawai son sa nake domin shi d'in nawa ne.”

Ta katse ta k'awar nata a zafafe.

“Okay, tun da haka ne ai babu amfanin ki kirani ko. Kuma wallahi Ruk'ayya idan baki kwantar da hankalinki kun zauna lafiya ba, tabbas zakiyi nadama a gaba, kina gani dai dama 'yan gidanku ba son auren suke ba. Kuma mutumi ki sameshi da matarsa da 'ya'yansa, ni na ma gaza fahimtar ina kika dosa sam, idan ta ciki ne kema fa baki sani ba wata k'ila yanzu haka ma kina d'auke da shi amma kinzo kina tada hankalinki Dan Allah k'awata ki aje duk wasu makaman yak'inki ku zauna da matar nan lafiya domin ni dai ban ga alamar da mugun nufi a zuciyarta ba.”

“Ba zai yiwu ba, magana dake ma b'ata lokaci ne, ban ma san dalilin da ya sa na kiraki ba, tsssww aikin wofi.”

Komawa ta yi gefen gado ta zauna tana nazari domin a gaskiya ba zata bari ba ace dai tanaji tana gani Halima ce zata ke haihuwa ita shiru.
Can kuma ta mik'e tayo waje.

“Ke! Zo nan...”

Ta fad'a a tsawa ce tana zare ido wa yaran.

Da yake yaran mugu-mugun tsoranta suke, yasa jiki na rawa yarinyar ta k'ari so gabanta.

“Ba zaki tsugunna ba, ina tsaye kina tsaye, saboda ba'a koya muku tarbiyya ba.”

Da sauri yarinyar ta yi k'asa tana shirin fashewa da kuka, domin yadda Ruk'ayya ke ma ta maganar duk ta firgice dama kuma da biyu ta yi domin Halima ta magantu sai dai ita Halima dake zaune bakin k'ofar kitchen tana gyara wake ta yi kamar bata gansu ba.

“Ungo nan jeki siyomin citta da kaninfari a gidan Larai...”

Sai lokacin Halima ta tanka ma ta.

“Indai dan wannan ne bama sai kin b'ata kud'inki ba, ina da shi bara na d'auko miki...”

“Ai nasan kina da shi d'in kuma na aiketa, idan kuma ban isa nayi iko da 'ya'yan mijina ba to sai a fito fili a fad'a min...”

“Sai dai kin san cewar Babansu ya hana su fita koda waje ne bare aike sannan kuma kina gani uniform ne  a jikinta islamiyya zasu tafi.”

Bata kula Halima ba ta dakawa yarinyar tsawa.
“Zaki tashi ki tafi aiken da nayi miki ko kuwa sai na b'ab'allaki a wurin nan? Nonsense!”

Idan Halima ta ce bata ji haushi ba to a gaskiya ta yi k'arya, amma sai ta zab'i da ta share dan ta kula neman rigima kawai take kuma bata fata ta biye ma ta su raba abin fad'a.

Hakan ya sa ta dubi sauran yaran ta ce.
“Hauwa'u ku tafi makarantar... Ke kuma Khadija ma za kije ki dawo...”

“Hmmm aina d'auka za'a nuna min bani da iko dasu ne, da kuwa an ga aiki da cikawa.”

Ta fad'a a gadarance tana juyawa ta koma d'aki sai dai bata yi mintina biyar ba cikakku, ta fara jiyo muryar Abbas a d'age yana surfa bala'i. Ta kwashe da dariya dama tana sane kuma da biyu ta aike 'yar. Da sauri tayo wajen jin yana kwala kiran sunanta.

“Darling, wani abun ne yake faruwa kake kwala min kira haka?”

“Me ya sa kika aike Khadija bayan kin san na hana?.”

Dafe k'irji ta yi tana fiddo da ido waje.

“Ya Allah! Na kwade, ban tumawo ba...”
Ta yi magana da Nupe ta k'ara da.
“Habba Darling akan me ina sane da dokar ka kuma zan karya bayan na san ka hana ana aiken yaran nan...”

Ganin ya yi shiru yana kallon ta ya sa ci gaba.

“Ni dai kawai abin da nasan ya faru shi ne; na kira ita Khadija d'in ta tayani wani aiki a d'aki saboda gaba d'aya kwana biyun nan bana jin dad'in jikina kwata-kwata, amma sai Halima ta hanata zuwa tare da bata kud'i wai ta siyo ma ta citta da kaninfari da nayi magana kuma ta hau ni da masifa har da gorin haihuwa take yi min wai gani nan na kusa shekara amma ko b'atan wata sai dai kawai naci nayi kashi, wai kuma sai dai naga tana haihuwa a gidan nann sass...”

“Ya isa haka!”

Abbas ya katse ta yana mai d'aga ma ta hannu. Tare da juyawa ga Halima da mamaki ya kusa kayar da ita nan zaune, jin wannan sharri da matar ta k'ulla cikin 'yan dak'ik'u. Bata k'ara shan mamaki ba sai da taji Abbas ya yanke hukunci ba tare da ji daga gare ta ba.

“Lallai Halima wato abin da kika yi ke nan kuma shi ne dan ki lalata min tarbiyyar yara kika saka Khadija ta yi min k'arya ko? Ba laifinki bane nasan hukuncin da ya kamata na d'auka...”

Fuu ya wuce d'akinsa.

Halima zata iya rantse wa taji lokacin da Ruk'ayya ta saka dariya kafin taga ta bishi d'akin sa can kuma ta fito ta koma nata d'akin kafin ta kuma fitowa sanye da hijabi a lokacin shima Abbas d'in ya fito a shirye ya canza kaya, suka fice bata ko ishe su kallo ba.

Ta sauke ajiyar zuciya tana girgiza kai da mamakin halin wasu mazan.

A lokacin da suka dawo bayan kamar ak'alla awanni biyu da rabi.

Tana d'aki taji shigowarsu.

Kuma tun daga ranar Halima ta lura da yadda ya k'ara ninka kulawarsa ga Ruk'ayya daga k'arshe ma yarinyar wurin Suwaiba da Halima take rik'o wato Saddiqa ya d'auka gaba d'aya ya bawa Ruk'ayya.

Sai a lokacin Halima take jin wai ashe ciki gareta, shi ya sa ya bata yarinyar take taimaka ma ta da wasu ayyukan.

Ai kuwa yarinyar tana gasuwa yadda ya kamata a hannun Ruk'ayya, domin koda masifarta kawai aka barka ka bani bare kuma komai yarinyar ita ke yi lokaci guda kuwa duk ta fige ta lalace.

Idan kaga tana walwala to fa Ruk'ayya bata gidan ne shi ne Saddiqa zata sama damar shiga cikin 'yan uwanta amma tana dawowa gidan shikenan zata d'aura ma ta daga inda ta tsaya.